Showing 18001 words to 21000 words out of 123375 words

Chapter 7 - RUBUTACCIYA BOOK 1-2-3-4 Complete Document by Fatima Dan Barno.txt

haka yake yana da yawan leKa Kannansa domin tabbatar da lafiya lau suke kwance. Yana lekawa ya sameta zaune tana waya. Tana ganinsa ta katse wayar tana zare idanu, “Da wa kike waya? Ba zaki bani amsa ba!� Jikinta na rawa tace “Abokin karatuna ne,� Sultan ya zaro ido, “Abokin karatunki a wannan daren? Haba Hafsat! A wannan lokacin da ya kamata ace kina ganawa da Mahaliccinki? Ance ki fito da miji ayi maki aure, kin ce baki‘da samari. Amma yanzu gashi kina waya da garjejen Kato ko? Ki kiyaye, ki kama mutuncin kanki, watarana ke uwa ce.� Juyawa ya yi abinsa ya fice. so Sultan yana Office ya sami kira daga abokansa, sun hadu za su fara meeting. Da sauri ya Karasa dukkan abubuwan da ke gabansa sannan ya kama hanya. Gaba dayan su sun sami isowa shine na Karshe. Tajuddeen Abdulsalam jarumin littafin (Kowa ya kwana laftya), Haisam � Hayat, Jarumin littafin (Zuciya), Aslaf Mai nasara Jarumin littafin (Sir) Mahbub Muhd Daura, Jarumin littafin (Mafarin lamarin), Ashmaan Ashraf Jarumin littafin (Akaran kaina) Sai kuma Soja, Khamis § Idris Jarumin littafin (Akaran kaina), ga kuma Al-ameen Rabi’u, jinin Sarauta jikan sarki, Jarumin (Akwai_ lokaci). Dukkansu suna zaune kowa da abinda yake yi. Sultan ya basu hannu yana murmushi, “Ga -ni kuma, jarumin Rubutacciyya! Na gaida Karfin Zumuci irin na ‘yar mutan Borno, hakika tayi Www.bankinhausanovels.com.ng namijin KoKari da bata barmu mun watse ba, da ba haka ba, Ashmaan shi ne mutum na farko da zai fara datse mana zumuncin nan.� Dukkansu suka yi murmushi_ sannan Mahbub ya bashi amsa, “Idan Ashmaan bai kashe zumunci ba, ai kai sarkin watsar da zumunci, za ka watsar da komai. Kai dai kawai Allah ya sakawa ‘yar mutan Borno, ita ta riKe mu ta dage lya lyawarta da ba haka ba, da tuni kanmu ya rabu.� Dukkansu suna ji da kansu, kowa ya ci ya ture. Haka ga -dukkan alamu suna_ cikin kwanctyar hankali suna samun kulawa daga matan su. “Tuzuru bude mana taro da addu’a Kila sanadiyyar hakan ka samu ka shiga daga ciki.� Aslaf yake tsokanar Sultan. Murmushin ya _ yi sannan ya yi addu’a mai tsawo. Suka shafa. Wannan taron gaba dayansa akan Sultan akayi shi, saboda shi ya gayyato su. Don haka ya fara magana, “Da farko dai andaura min aure. Sai dai bana son doguwar magana, ko Korafi, Abba ne ya daura auren, ban santa ba, ban taba ganinta ba, yanzu haka wai yana jiran ne ta gama karatu ayi bikin tarewa. Ban wani damu ba, domin bani da budurwa, hakan ke nuni da ina da bakin jini Irin na wannan yaran�� Ya nuna Mahbub da hannu, duk suka yi murmushi. a hakan sai da suka yi korafin meyasa tun a lokacin bai gaya masu ba? Share su ya yi kawai ya ci gaba, “Ina da babban Case a hannuna na kisan kai, Case din akwai buKatar natsuwa da kuma sanya hankali a cikinsa: Mahaifiyar Nasrecn nake son sanin waye ya kasheta tsawon shekaru goma sha shida? Me yasa aka kasheta? Ta bani wani littafi da wasu hotuna, suna cikin wannan files din. Ban taba budewa ba, daman burina inkammala da kulawa da su, sannan insan,abin yi. Duk wanda ya kashe ta babu shakka ya yi kisan nan ne saboda gudun kada ta tona masa asiri, nayi alkawarin idan mahaifina ne mai kisan nan, saina daukar mata fansa, Sai kuma Nasreen da aka watsa wa guba aka makantar min da ita.� Tajuddeen ya fara magana, ““Wannan case din case ne mai girma, musamman na kisan nan. Haka duk wanda ya yi kisan bai san Nasreen da Nawfal suna nan a raye ba, da sai sun nemi kashe su. Wadannan abubuwan da ke hannunka za su tabbatar mana da komai. Don haka zamu yi lya yin mu muga abinda Allah zai yi. File din kuma za ka iya bani, ko kuma ka ba Mahbub, ko Ashmaan. Sai mu fara bincike. Abinda binciken mu ya bamu sai mu sake dawowa ayi meeting ko ya kuka gani? Dukkansu suka yi na’am da wannan shawarar. Al-ameen ya dube su, “Maganar idanun Nasreen, zan dauki nauyin fita da ita waje, ina da wani aboki da ya Kware da aiki akan irin wannan. Kafin nan zan fara bata kulawa a Asibitina. Dukkansu suka ce basu amince ba, sai kowa ya bada gudumawarsa a kan samun lafiyar Nasreen. Sultan ya rasa bakin magana sai duban su kawai yake yi. Da ace haka abokai suke da hadin kai tabbas da duniyar ma gaba daya ta zama abar sha’awa. Haka aka tashi taron Sultan kuma ya damka komai a hannun Barrister Tajuddeen, ba tare da ya bude ko shafi daya ba. Mahbub ‘yan sandansa suka bude masa mota, haka ma Sultan sauran kuma duk suka ja abinsu suka bace bat! Sultan yana isowa gida, ya watsa ruwa kafin ya iso falo inda mahaifinsa ke zaune. Bayan ya gaishe shi ne, yake gaya masa yadda suka yi da abokansa, daga Karshe ya rufe maganar da fadin za a yi wa Nasreen aiki a idanu, abokan suka dauki nauyi. Wannan magana da Hajiya Salma da ke shirin shigowa falon ta ji, shi ya tashi hankalinta taja da baya ta koma. Ko tambayar mijinta ba tayi_ ba ta dauki gyale. A gidan Hajiya Ladidi taja burki. Tana shiga ta sami Mansur a dakin, da alamu sun gama sheKe ayarsu da Hajiya Ladidi ne ya fito yana gyara .kwalar riga. Yana ganin . Hajiya Salma ya daure fuska, “Yauwa Hajiya ki gaya mata sai na dauki mataki akan dan nan nata sannan zan koma indauke Nasreen. Narantse da Allah sai na dauketa. Amma kafin nan sai na gama gyarawa danki zama.� Hankalin Hajiya Salma ya tashi ta ce, nan fa daya. Kada ka kuskura ka taba min lafiyar da. Za ka iya yin komai amma banda taba Sultan. Kuma Wallahi idan ka ce za ka taba shi sai kayi danasani, domin kana ganinsa nan ba Karamin tsayayye bane.� Mansur ya yi Kwafa, “Na fi ki sanin hakan ni da ya shake ni na nemi sheKawa lahira. Amma duk da hakan sai na koya masa hankali. Yanzu sauri nake yi zan sake dawowa.� Ya sa kai ya fice. Gabadaya suka zauna Hajiya Salma tana yi mata kallo cike da Kyama, “Hajiya da ‘ya’yanki da_ girmanki kike irin wannan Kazantar? Gaskiya bana son zina ko alama, ina tsananin Kyamatarta.� Hajiya Ladidi ta tabe baki ta ce, “Ba gara zinan ba, da irin ta’asar da kike yi a gidan mijinki? Malama ki fada abinda ya kawo ki kawai.� . Hajiya Salma tayi ajiyar zuciya ta natsu � sosai, “Kin ga wannan shashashan yana son ya kawo mana matsala. Ina ganin abinda ya kamata kawai ki samo wasu daga cikin ‘yan iskanki su dauke yaran nan su kai su can wani gari mai nisa, su jefar da su. Wai Sultan ne yake son fita da Nasreen waje su gyara mata idanun da bana fatan ta sake kallon wasu zuri’ana da su. Don haka nake son ta bar cikin iyalina kowa ya huta. Na mayar da yarinya makauniya, sai take son ta mayar min da miji da da ‘yan jagoranta.�
6/5/22, 10:27 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 1🦚*






CHAPTER 7






*BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO*






A JIYA MUN TSAYA


duk da hakan sai na koya masa hankali. Yanzu sauri nake yi zan sake dawowa.� Ya sa kai ya fice. Gabadaya suka zauna Hajiya Salma tana yi mata kallo cike da Kyama, “Hajiya da ‘ya’yanki da_ girmanki kike irin wannan Kazantar? Gaskiya bana son zina ko alama, ina tsananin Kyamatarta.� Hajiya Ladidi ta tabe baki ta ce, “Ba gara zinan ba, da irin ta’asar da kike yi a gidan mijinki? Malama ki fada abinda ya kawo ki kawai.� . Hajiya Salma tayi ajiyar zuciya ta natsu � sosai, “Kin ga wannan shashashan yana son ya kawo mana matsala. Ina ganin abinda ya kamata kawai ki samo wasu daga cikin ‘yan iskanki su dauke yaran nan su kai su can wani gari mai nisa, su jefar da su. Wai Sultan ne yake son fita da Nasreen waje su gyara mata idanun da bana fatan ta sake kallon wasu zuri’ana da su. Don haka nake son ta bar cikin iyalina kowa ya huta. Na mayar da yarinya makauniya, sai take son ta mayar min da miji da da ‘yan jagoranta.�


ZAMU TASHI


Hajiya Ladidi ta saki dariya sosai sannan ta ce, “Ashe ‘yan iskan nawa suna da rana? Shi yasa nace maki a hada aurensu da ‘yata amma wannan kafaffen mijin naki ya hana. Wannan aiki ne mai sauki, Rainbow dinnan dai shi za mu sake sawa ya yi aikin nan.� A nan suka gama kintsawa akan idan Nasreen za ta je Makaranta a nan za a saceta ita da Nawfal. Tana isowa gida ta sami Sultan yana gyara mata gashinta, da take ta mitan yana damunta ya taimaketa ya aske mata. Bai ce mata komai ba, ya tattare mata gashin ya Kulle a cikin Katon ribom. Hajiya Salma kamar za ta yi magana, sai kuma ta hadiye da ta tuna da komai ya kusan zuwa Karshe. Mikewa ta yi tana fadin, “Dee kama ni ka kai ni daki ina son shirin zuwa Makaranta, bansan inda Nawfal ya tafi ba. Babu musu ya kamata ta shiga dakin, ya fitar mata da kayan Makarantarta kafin ya fice daga dakin ya tafi neman Nawfal. A tsakar gida ya same shi yana Kwallo, ya Karasa ya tallabi Keyarsa tare da riko


kunnensa daya. “Kai baka jin magana ko? Karfe nawa yanzu?� Nawfal ya rike hannun Sultan yana rintse ido, “Wayyo Deedi ka yi hakuri don Allah na tuba ba zan sake ba.� Hannunsa riKe da kunnan Nawfal ya tasa shi gaba har cikin daki. Da suka tashi tafiya Makarantar shi ya dauke su da kansa ya kai su har Makaranta. Daren ya tsala wuri ya yi shiru, baka jin motsin komai, sai na tsuntsaye. Nasreen ta fito tana lalube a yanzu ta haddace inda komai na gidan yake, don haka ta nufi dakin Sultan. Yau bai kwana a office ba, yana gida don haka ta iso har kan gadonsa. Yana kwance yana kallonta, haka ya zuba mata ido ne kawai ya ga iya gudun ruwanta. Lalubansa take yi har ta tabbatar ga inda yake, sannan ta kwanta shiru a Kirjinsa, “Deena me yasa bana iya barci sai da tunaninka? Me ke shirin faruwa da rayuwata ni Nasreen? Ina jin damuwa a kwana biyun nan, ina jin kamar zan rasa ka. Deee ka tashi ka gaya min mene ne ke shirin faruwa da ni? Dee.,.� Ta ja sunansa tare da dora hannayensa a bisa fuskarta da ke kwararar hawaye. Shi dai bai ce komai ba, sai kallonta da yake yi. Ya zama dole ya ajiye wasan kwaikwayon nan shi da Nasreen ya tabbatar mata da yana sonta. Irin abinda Nasreen take ji, shi ya fi ta jin fiye da hakan. Hawayenta ya kafe da ido yana dubanta. Da gaske tana bashi tausayi musamman rashin idanun da yafi so fiye da komai. Idan ta ware idanunta tana dubansa, sai ya ji kamar ta kwashe dukkan kuzarin jikinsa ne. Ta ya ya zai iya fitowa ya ce Nasreen yake so? Me yasa? Idan ya yi hakan zai sa rayuwar Nasreen a cikin matsala! Haka kuma ba zai taba samun natsuwar da yake nema ba, saboda mahaifiyarsa duk za ta hana hakan, Sannan ba Zai iya ce mata yana sonta ba, har sai ya gano su waye iyayenta? Me ya jefa mahaifiyarta a cikin irin wannan halin bakar rayuwar? Yatsunta ya kafe da ido gabansa yana tsananta fadiwa. Babu inda ya tsunta ya bambanta da na Haidar Kaninsa. Kafafunta kuwa iri daya da nasu. Wannan abu yana sake daure masa kai Sai yanzu yake takaicin Kin bude hotunan nan ya fi tunanin a nan ne zai gano komai. Sai dai yasan ko wasu irin hotuna ne ba zai wuce hotunan . mahaifiyarta ba, shi kuma idan har zai dubi hotunan nan sai mutuwar Saudat ta dawo mata sabuwa fil! ‘““Nasreen.. Ya kira sunanta, wanda yasa ta yi firgigit! Ba ta yi magana ba, don haka ya dora, “‘Nasreen kina jin son Deedinki a cikin zuciyarki? Nasreen babu aure a tsakanina da ke. Ki dauke ni a yadda kike daukana a da kin ji? Nasreen Abbana shi ne mahaifinki anboye ne saboda wasu dalilai idan lokaci ya yi zaki san komai kinji? Nima da farko da bansan hakan ba, irin abinda kike ji shi nake ji, daga baya na sawa raina hakuri. Sannan idan auren za a yi, ban yi maki girma ba Nasreen? Yaro Karami zan baiwa aurenki, wanda bai wuce sa’an Haidar ba. Kin ga ni na wuce talatin ko? Maza _ ki share hawayenki.� Kukanta ya Karu da yawa, bata jin za ta iya cire abinda ke cikin zuciyarta, ba ta jin za ta iya rage son Sultan wanda bata ko tantama da soyayyarsa aka haifeta. Tana son tasan wacce irin alaKa ce ke tsakaninta da Deedinta. Duk da ta kadu da kalamansa, amma hakan baisa ko digo daya daga cikin soyayyarsa ta ragu ba. Tana sonsa da gaske. Ta shirya wa tunkarar kowacce matsala a kansa. Sake damKe hannunsa� ta yi tana jin duk wata kunya ta kau a idanunta, tana jin za ta iya gaya masa komai. “Dedena, ina son ka, zan iya mutuwa Ko babu aure a tsakaninmu zan zauna da kai. Ba zan taba iya yarda da wani namiji ba, yin hakan zai gurgunta rayuwata. Ka rike ni a gidanka zan zauna da matarka. Don Allah ka roKe ta kada ta raba ni da kai. Ban san kowa ba sai kai da Abba. Kai ka koya min wannan rayuwar, Sai dai na yi nisan da ba za ka iya cire min abinda ke cikin zuciyata ba.� | Kalaman da Nasreen take ambatowa sun yi matuKar bashi mamaki, ta yaya Nasrecn ta iya irin wannan kalaman? Ya aka yi Nasreen tasan soyayya haka? Yaushe ta cire kawaicinta ta iya furta masa wadannan kalaman? Tausayinta ya kwaranyo masa, baya jin zai iya hada Nasreen da kishiya bare har ta cutar masa da ita, Yana yi mata irin son da duk wanda ya kama da cutar da ita zai dauki matakin da sai duniya ta girgiza da irin matakinsa. Ya danganta rashin kawaicinta a yau da rashin idanunta, ya tabbata da za ta hada idanu da shi, ba za ta taba samun Karfin halin da za ta fada masa wadannan kalaman ba. Share mata hawayen ya yi ya rungumeta tsam a Kirjinsa. A lokaci guda yake jin kamar shaidan ke son cin galaba akansa, idan ya yi la’akari da yadda komai ya sauya daga cikinsa. Bisa labbansa yake magana, “Ina jin irin abinda kike ji Nasreen.� Shiru ya biyo bayan hakan, sakamakon saKon da ya bata mai matuKar tasiri. A lokaci guda ya zame kansa, yana jin meyasa zai zama mutum na farko da zai gurbata amanar da Saudat ta bashi? Sai da ya natsu sannan ya ce, “Nasreen ki tashi ki koma dakinki.�Shiru ta yi sakamakon yadda Kafafunta suke rawa. Haka ta tsinci kanta cikin wani baKon al’amari. Yawun baki wani irin abu ne mai kama da guba, idan suka hadu wuri guda suna sanya zazzafar soyayya da kuma shaKuwar dake da wahalar rabuwa. Hakan ce ta kasance da Nasreen @ wannan daren. Hannunta ya kama suna mikewa tsaye ta yi baya za ta fadi, ya yi saurin dawo da ita ta fadi a jikinsa, “Nasreen! No kada ki yi min haka. Ki Karfafa jikinki don Allah. Ki tuba ga Allah wannan abun haramun ne kin ji? Kada ki sa shi a ranki kin ji?� Ba tayi magana ba, amma ta dan Karfafa jikinta. Da kansa ya rakata dakinta ya kwantar da ita, tare da addu’a sannan ya jawo mata bargo ya rufeta. “Sleep!� Ya furta tare da hure mata fuska. Luf idanun suka sake rufewa. Ta shaki Kamshin bakinsa tana sake rurrufe idanun da daman a rufen suke. Ya tashi ya kashe mata wuta ya fice abinsa. Wannan lamari akan idon Umma ya faru, hankalinta idan. ya yi dubu to ya tashi. Abinda ya sake ba ta mamaki Abbansa ashe yana tsaye shi ma yana kallon su. Duban fuskar Abban ta yi da mamaki yadda yake ta murmushi. Ta sake leKa fuskar Abban ta tabbatar da murmushin yake yi. Kafin ta yi magana Sultan ya Karaso falon ya bude frij zai dauki ruawa. Domin ji yayi makoshinsa ya bushe saboda halin da ya tsinci kansa a ciki. Ji ya yi kawai an shaKo shi, kafin yayi wani abu, ya ji saukar mari ko ta ina @ fuskarsa, Sai huci take yi, “Kai kai! Baka isa ka kasheni ba, Zina kake aikatawa da Nasreen? ‘Ya’yan mazinatan ne suka shigo rayuwarka su Bata maka tarbiyya? Wallahi idan ka kasance mazinaci ba zan taba yafe maka ba a cikin gidan nan, sai na tsine maka kabi duniya! Kaf zuri’ata babu mazinaci, kai kuwa baka isa ka jawo min wannan abin kunyar ba. Dama sonta kake yi dan ubanka! Za ka yi min magana ko sai na kasheka a gidan nan?� Ta daga hannu da nufin sake marinsa, Ta ji anriKe hannunta. Abba ya tunkudeta gefe saura kadan ta kifa. Yana dubanta yana huci, “Insha Allahu ban haifi mazinaci ba, bana fata idan Allah ya jarabceni da da mazinaci ba zan tambaye shi dalili ba, haka ni nasan ban zagi ‘ya’yan wasu ba, sai dai idan alhakin zagin da kika yiwa ‘ya’yan wasu ne ya sauka akanki. Haka ba dai dana Sultan ba, sai dai idan ‘ya’yanki da kika lalata da irin halayyarki. Wannan yaron da kike gani, shi ne dan da nake fatan ya gado ni kuma na gode Allah. Kada ki sake danganta min da da zina, yin hakan zai jawo maki mummunan bacin rai Wallahi!� Umma ta dube shi da mamaki, “A gabanka fa ya fito manne da ‘yar iskar can!�

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login