Showing 114001 words to 117000 words out of 123375 words
Chapter 39 - RUBUTACCIYA BOOK 1-2-3-4 Complete Document by Fatima Dan Barno.txt
kallon Kwayar idanuna har kika gaya min Kalmar bana sonki. Nasreen na fara sonki ne tun kina cikin mahaifiyarki, a lokacin da baki zo duniya ba, bare kisan wahalar
zaman duniyar. A_ sanadiyyar in tsamo mahaifiyarki daga halin da take, har yau dinnan ban sake zama inuwa daya da mahaifiyata ba, a lokacin ne kyakkyawan ginin da mahaifina ya dade yana yi domin inganta rayuwar iyalansa ya wargaje. Ginin da har yau ba a sake tada gininsa ba, domin kuwa gyaransa sai Allah.
“Muna rayuwa cikin son juna, wanda har ta kai dangi suna alfahari da mu, suna yaba mana, suna kwatance da hadin kan mutanen gidanmu, rana guda, ranar da na hadu da mahaifiyarki wannan kwatance ya rushe. Tun daga ranar na zama bare a cikin gidanmu, tun daga ranar ‘yan uwana Hafsat da Haidar suka ware ni kamar ba dan uwansu ba.
“Haka na taso cikin maraicin ‘yan uwa. Mahaifina kadai ke bani goyon baya. Duk kina nufin hakan ba so ba ne? Tun zuwanku gidanmu ke da dan uwanki, mahaifina da matarsa Umman mu, suka raba hanya, ya kasance mahaifiyata tana yawan saba masa. Duk ni ne sanadi saboda na kawo ku cikin rayuwar gidanmu. Ra’ayina ba aikin dan sanda bane, amma saboda in sami daman aiwatar da bincike akan wanda ya yi sanadin zuwanku duniya, na sauya ra’ayina zuwa
aikin dan sanda. Duk kina nufin ba sonki nake ba? Ban taba yi wa iyayena gardama ba, haka sun jima basu ga hawaye a idanun dan su ba, sai a dalilin mahaifiyarki. Har gobe ina kallon Anti Saudat a idanuna, har gobe ban daina kai goshina Kasa ina yi mata addu’a ba, haka na kasa kallon tarin hotunanta da suka jima a hannuna, sai dai na ba abokaina domin su nemo abubuwa akanta. Mahaifiyarki musulunta ta yi, kuma har ta bar gidan duniya tana riKe da addinin gaskiya. Yanzu za ki ji dukkan abinda kike son ji akan rayuwarki.� Ya Karashe maganar cikin raunin murya, wanda za ta iya rantsewa bata taba jinsa da irin muryar ba. .
Nasreen ta dago cikin wasu hawaye masu tsananin zafi, tana girgiza kai. Idan da a ce bakinta zai iya furta magana a yanzu, da ta roki Sultan ya yi shiru da labarin da yake son bata, domin wannan ma kadai ya gigitata, ya tafi da dukkan sauran Karfin halin da ya rage mata. Tausayin kanta, tausayin Naufal, tausayin Sultan, su suka fara buga tsere a cikin zuciyarta, suna Kara sa mata damuwa.
A yau ta Kara yarda, duk duniya babu mai son su da gaskiya irin Sultan. Kunyarsa ta
lullubBeta, saidai kuma me mahaifinta ya yi da har Sultan zai yi aikin dan sanda saboda shi? Tana da buKatar amsoshi masu tarin yawa daga bakinsa. Wannan karon hawaye da majina suke sauka daya idanunta zuwa hancinta, ga wanii irin gumi da ke tsattsafo mata, ta jiKe ta yi sharkaf. Sultan ya mike tsaye ya kwashe yadda aka yi har ya taimaka wa Saudat zuwa haihuwarsu da ta yi, har ya gangaro kan renon su da ya sha cikin wahala. Duk ya yarda ya sadaukar da farin cikinsa saboda nasu farin cikin.
.Tun Nasreen tana iya fahimtarsa har ta daina fahimtar komai, numfashinta yana kaiwa yana komowa. Ta tabbata sun gama tozarta a duniya, tunda har ya kasance aka yi wa mahaifiyarsu fyade aka samar da su a duniya. Haka babu wanda ya san waye mahaifin su. Tabbas sun tabbata ‘ya’yan shegu kamar yadda Zakiyya take ta nanata mata a kullum, wanda hakan yasa ta haddace sunan shegu, saboda yawan ambata mata da ake yi. Da Karfi ta riKe kanta, hakan bai taimaka mata da komai ba, domin kuwa a take ta zube a sume.
Sultan ya tsaya kawai yana kallonta, ya rasa ma me zai fara yi mata domin bata taimakon
gaggawa. Sosai yasa natsuwa a zuciyarsa hakan yasa ya tuna da ruwa, ya je ya dibo yana shafa mata a fuska. Da Karfi ta saki ajiyar zuciya, ta ware idanunta tana dubansa_ dishi-dishi. Hannunsa ta kama ta mayar bisa kanta da ke sara mata.
Cak ya dauke ta ya kai cikin dakinta ya kwantar bisa gado.
Zakiyya da ta gama leKen su ta saki dariyar jin dadi ta shige abinta.
Nasreen tana riKe da hannunsa, ta Ki saki, gani take idan ta saki zai tafi ya barta ne. A hankali take magana, “Dee, na yi mugun
� mafarki, wal� Wai� Wai� Mu shegu ne, an yi wa Mamana fyade, ta yi rayuwa a Karkashin mota, ta yi bara a titi, sannan wai, wai kakannina ba musulmai bane.. Mafarkin babu dadi Dee, babu abin sha’awa a cikin rayuwar mu, bana son mafarkin, kayi min addu’a kada in sake yin irinsa.� Wasu surutai take yi tana kuka.
Sultan ya yi danasanin gaya mata wadannan maganganun, bai taba tunanin Nasreen za ta tashi hankalinta kamar yadda ta tasa a yanzu ba, bai taba tunanin Nasreen za ta: fita hayyacinta haka ba. Yana nan zaune bai iya cewa komai ba. Kafin yasan abin yi zazzabi mai zafi ya shiga jikinta sai rawar sanyi take yi.
Hankalin Sultan ya sake tashi, ya kira Aslaf a waya ya gaya masa duk abinda ya faru, Aslaf ya ce, “Amma da ka sani da ka dinga gaya mata a hankali ne, domin yarinya ce Kwakwalwarta ta yi Karama da daukar irin wannan tashin hankalin. Bari Yumnah ta zo yanzu ta dubata.�
Sultan ya sauke wayar yana sake kai dubansa gareta, har yanzu ta Ki sakin hannun, duk da irin karkarwar da jikinta ke yi. Shafo kanta ya yi da dayan hannunsa yana tofa mata addu’a, “Baby za ki ji sauki kin ji? Ki yi hakuri ki rage damuwar nan kin ga kin tada min hankali. Wannan Kaddarar ba a kanki aka fara ta ba, haka agun Allah kin fi wasu wadanda suke cikin musuluncin, amma basu yin aiki da abinda addinin ya fada. Ke baki da laifi, mahaifiyarki ma bata da laifi, mahaifinki shi ne mai laifin. A wurina kinfi wadanda aka Haifa ta hanyar halas. Babu wanda ya isa ya tambayi Allah dalilin aiko da Kaddara. Sai dai ma mu gode masa a dukkan yanayin da muka tsinci kanmu.� Haka ya dinga yi mata kalaman lallashi, kuma yana cin nasarar wargaza dukkan damuwar da suka taru suka hanata zaman lafiya. Yumnah da kanta ta tuko mota ta zo har gidan, ta dubata tare da bata allurai.
A falo suka fito suna tattaunawa da Sultan, ta sake tabbatar masa kada ya yi nisa da Nasreen, saboda su samu jininta ya sauka. A zahiri ta yi hakan ne domin ta nesanta Zakiyya da Sultan.
Kwanan Nasreen biyu ta wartsake, a lokacin kuma sunan da Sultan ya gani a cikin wayar Khamis ya tsaya masa a rai. Tunani yake yi waye Na kan titi? Domin tabbas ya taba jin sunan amma ya rasa a in da ya ji. Wannan zaman da suka yi shi suka kira da zama na Karshe, sun tabbatar za su yi Kundunbala su gaya masa komai, haka dole ya ba su hadin kai wajen zartar da hukuncin da ya dace. Sai dai fa duk taron su a cikin dakin taron, babu wanda ya iya furta komai. Yadda suka yi shiru haka Sultan ya yi shiru, ya yi alKawarin ba zai ce masu komai ba, don wulakancin ya ishe shi hakannan. Wayarsa yake latsawa, sai ga kiran wayar Alhaji Mu’azzam yayan Umma. Cikin girmamawa ya dauka ba tare da ya nemi izinin kowa daga cikin dakin ba, kamar yadda ya saba. Daga cikin wayar yake magana, “Sultan ina son nemanka,
ana son a lalata min suna, kuma antabbatar min masu KoKarin aikata hakan, suna da kusanci da kai, Ashmaaan, wani mara kunyar yaron nan dan jarida, da wasu dai haka. Ina son ganinka gobe insha Allahu.�
� Daga kai ya yi yana kallon su Ashmaan, zufa na karyo masa, a lokaci guda mamakin fuskarsa ta Karu da Ashmaan ya amshe wayar ya bude muryar gaba daya sannan ya fara magana, “Ashmaan ba mara kunya ba ne, domin yana girmama na sama da shi, idan suka kasance masu girmama kansu. Ba za ka sami ganin Sultan kamar yadda ka buKata ba, haka kai baka da laifi + ko alama a cikin maganar nan, masu laifin dai suna nan zagaye da kai, wanda kai baka san suna » aikata barna da sunanka bane. Muna fatan zaka yi hakuri ka barmu muyi aiki a kan Alhaji Kabir ba akanka ba. Mun gode.� Sultan ya rasa abin cewa sai kallon-kallo ake yi. Al-ameen ya yi alKawarin zai cire dukkan wata kunya da shakkar yadda maganar za ta iso cikin kunnen Sultan, ya yi maganarsa, ya gaji da yadda ake sa Meeting ana dagawa duk saboda tsoron Sultan yasan komai. Duban Sultan ya yi a lokacin da ya zare farin gilashinsa, wanda ke sake Kawata fuskarsa, “Sultan zauna mu yi magana.�
Babu musu ya zauna, tare da kafe idanunsa akan na Al-ameen, da alamun shi kadai yake saurare, yana son sanin dalilin hadin sunan Baba Mu’azzam, da irin maganar nan. Da alama dai basu san wanene suke alaKanta shi da wannan barnar ba.
Al-ameen ya sake duban Sultan ya ce, “Sultan Baba Mu’azzam Yayan Umma, wanda yake zaune a garin Kaduna, kuma mai Karya da addini, ina nufin ya shiga rigar addini yana abinda ya gadama, shi ne mutumin da muke ta nema akan matsalar Nasreen, ina nufin shi ne mahaifin Nasreen da Sultan. Shi ne mutumin da ya boye kansa yake ta bamu wahala wajen nemansa.�
Sultan ya mike yana duban Al-ameen. Tabbas da a kusa suke da juna da babu abinda zai hana shi shake shi, a kan Kazafin da yake son yi wa Baba Mu’azzam. Sultan ya sake dubansu ya tabbatar da dukkansu sun san da wannan maganar kuma sunyi na’am. Cikjn tashin hankali sultan
6/29/22, 21:01 - Ummi Tandama😇: RUBUTACCIYA BOOK 4
CHAPTER 10
BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
MUN TSAYA
ya gaji da yadda ake sa Meeting ana dagawa duk saboda tsoron Sultan yasan komai. Duban Sultan ya yi a lokacin da ya zare farin gilashinsa, wanda ke sake Kawata fuskarsa, “Sultan zauna mu yi magana.�
Babu musu ya zauna, tare da kafe idanunsa akan na Al-ameen, da alamun shi kadai yake saurare, yana son sanin dalilin hadin sunan Baba Mu’azzam, da irin maganar nan. Da alama dai basu san wanene suke alaKanta shi da wannan barnar ba.
Al-ameen ya sake duban Sultan ya ce, “Sultan Baba Mu’azzam Yayan Umma, wanda yake zaune a garin Kaduna, kuma mai Karya da addini, ina nufin ya shiga rigar addini yana abinda ya gadama, shi ne mutumin da muke ta nema akan matsalar Nasreen, ina nufin shi ne mahaifin Nasreen da Sultan. Shi ne mutumin da ya boye kansa yake ta bamu wahala wajen nemansa.�
Sultan ya mike yana duban Al-ameen. Tabbas da a kusa suke da juna da babu abinda zai hana shi shake shi, a kan Kazafin da yake son yi wa Baba Mu’azzam. Sultan ya sake dubansu ya tabbatar da dukkansu sun san da wannan maganar kuma sunyi na’am. Cikjn tashin hankali sultan
ZAMU TASHI
Sultan ya girgiza kansa ya ce, “Ku fada min sunan wani amma ba Baba Mu’azzam ba. Babu yadda za ayi Baba Mu’azzam ya aikata abinda ake zargi. Me yasa zaku zarge shi? Mene ne hujjarku? Kumaaa..�
Cak ya dakata a lokacin da ya tuna kamannin Naufal da Haidar, haka suna kama da ‘yan gidan su Umma. Can kuma ya tuna ai Baba Sani Kanin Umma yana can Kasar waje da iyalansa. Baba Sani biyu ne, akwai a dangin Abba, akwai kuma a dangin Umma. Na kan titi a gabansa wani abokin Alhaji Mu’azzam ya kira shi da sunan. Amma ta yaya Malami kamar Alhaji Mu’azzam zai iya aikata wannan rashin imanin? Kai bai yarda ba, ba zai taba yarda ba, babu hujja mai Karfi a cikin wadannan hasashen. Kansa a daure ya ce, “Amma mene ne hujjarku na cewa Baba Mu’azzam shi ne mahaifin Nasreen?�
Barrister Tajjud ya watso masa hotuna, sai a lokacin ya dubi hotunan da suke watse a gabansa. Ga mamakinsa, hoton Baba Sani ne, sai hoton Alhaji Mu’azzam wanda tare da Baba Sani aka dauka, abin mamaki har da shi a cikin hoton yana Karami. Ba zai taba mance lokacin da aka dauki hoton ba, a wata ziyara da Baba Sani ya dauke shi suka kaiwa Baba Mu’azzam, kasancewar Baba Sani shi ne dan gaban goshin Baba Mu’azzam. Hotunan Saudat ya kafe da idanu yana jin zafin rabuwa da ita. Kafin ya samu ya dawo hayyacinsa, Alameen ya mika masa littafin da Saudat ta yi ta rubuce-rubuce da turanci. Shafukan ya dinga budewa duk labaran soyayyarta ce da Baba Sani, sai kuma shafin da ya dauke masa hankali, shi ne shafin da ta rubuta sunan Alhaji Mu’azzam da manyan haruffa. Ya kasa dagowa saboda tashin hankalin da ya tsinci kansa.
Wannan karon Ashmaan ne ya ci gaba da magana, “Mun ki bude littafin nan da ka bamu ne, saboda muna son mu yi amfani da Karfin KwdKwalwarmu, domin wannan wani abu ne mai rikitarwa. Dukkan mu =mun_ yarda_ da Kwarewarmu shi yasa muka hada kai babu dare babu rana sai mun gano wanene mahaifin Nasreen. Alhaji Kabir ya bamu wahala, mun kasa gane komai akansa, har sai da muka hada masa tarko kuma ya fada. A lokacin da ya kiran domin ya ci gaba da yi min barazana sai na gaya masa, muna da masaniyar tare da Alhaji Sulaiman suke aiki, don haka zamu zayyano sunan su, sai hakan ya daga masa hankali, wanda a zahiri bamu san suna da alaKa ba, kawai Case din su Alhaji Sulaiman ya yi kama da irin Case din su Nasreen. Da haka muka samu suka yi ta bin mu, Suna son mu gana, sai na yarda da ganawar, ta hanyar hada tafiya a tsakaninmu mu dukka, kuma kowa ya tafi da shirinsa. Cikin ikon -Allah bayan mun hadu mun tattauna, ashe sun bi bayan Mahbub, wanda babu wanda ya ankare sai saukar bindiga a dantsen hannunsa.�Sulta ya dubi Mahbub kansa a daure yadda babu wanda ya taba gaya masa, haka kuma bai taba sani ba. Tajjudeen ya ci gaba da cewa, “Abubuwa sun faru mas� yawa, a dalilin neman shaidar wanda , ya yiwa Anti Saudat fyade. Abin burgewa a ranar Khamis ya bi bayan Alhaji Kabir ya kuma ga ina ne mazaunin su a duk lokacin da suka kwaso yara, domin zuwa yi masu fyade.� Sultan ya riKe kansa da Karfi daga bisani ya dubi Tajjud cike da tashin hankali ya ce, “Kana nufin fyaden Kananan yara? Har da Baba ake yi wa yara Kanana fyade?�
Ashmaan ya amshe maganar, “Kwarai kuwa. Baba Mu’azzam shi ne babban wanda ke
turawa a samo yara ‘yan shekaru biyar ko sama da hakan. Haka a kowacce rana yana aikata fyade ga Kananan yara sau biyar ko sama da hakan. A ranar da muka gane Baba Mu’azzam ne, mun shiga rudu da tashin hankalin, ta hanyar da zamu iya sanar maka. Haka mun bude littafin mun samu dukkan bayanan da muke nema. Yaran aikinka da ka watsa su anan Kawo, sun samo amsa dai-dai da irin namu, mu muka hana su gaya maka komai. Haka na sami Nora na nuna mata hoton Alhaji Mu’azzam ta tabbatar min da shi ne. Don haka kamannin da kake gani a tare da Haidar da Naufal, da gaske ne, jini daya ne, haduwar jininku shi yasa ka dage sai ka taimaka wa Anti Saudat. Mun yi ta kauce maka ne dan bamu son ka san abinda ke faruwa da wuri. Da fatan a yanzu zaka sami Umma domin ta amshi ‘ya’yan dan uwanta hannu bibbiyu?� Sultan ya koma ya zauna shiru.. Bai samu ya iya magana ba, sai da ya dauki wasu ‘yan mintuna, sannan ya ce, “Mahbub ka tafi Kaduna � gobe, ka shirya min motar ‘yan sanda, zan Karaso gidan mu insha Allahu, akwai abinda zan yi.� Gaba daya suka dube shi, ba su taba tunanin zai amince da hukunta Baba Mu’azzam da wuri haka ba. Sultan ya dube su yace, “Za ku iya biyo ni mu je mu Karasa aikin nan tare. Zan kama Baba Mu’azzam zan kuma tabbatar da kotu ta hukunta shi, ko da kuwa hakan yana nufin rabuwar shi da gidan duniya ce.�
Sultan ya dubi abokansa da yake jin su tamkar jininsa. Yana son ya yi masu godiya, sai dai ya san babu wanda zai so hakan. Don haka suka yi Sallama kowa ya shiga motarsa suka kama hanyar gida, a bisa sharadin goben a Kaduna kawai za su hadu. Sultan ya dai-daita muryarsa sannan ya daga waya ya kira Baba Mu’azzam a waya, ya tabbatar masa ya kashe maganar, amma kuma yana son gobe ya je gidansu ya roki mahaifiyarsa ta Kyale shi da matarsa Nasreen kada ta raba su. Babu musu Baba Mu’azzam ya amince da abinda Sultan ya roKa domin yana ganin ya gama rufa masa asiri tunda ya kashe Karar da ake son danganta shi da ita.
A ranar Sultan ya kasa barci, ya kasa zaune ya kasa tsaye, a bakin windo ya tsaya yana dogon tunani. Umma ta tsine masu yafi a Kirga, ta ce zuri’arta tsaftatattu ne, na wasu ne banza. Ta ce ta tsani mara addini, bayan mara addinin
tafi dan uwanta kamun kai. ‘tace ta tsani mazinaci, sai ga nata mazinacin da yara Kanana yake aikata irin nasa zinan. Umma ta tsananta tsanarta ga zina, ta yi tirr ta yi Allah wadai da mazinaci. Ta Kyamaci Saudat da abinda ta Haifa. Ji yayi an tabashi shi, bai waiwayo ba, ba shi da alamun kuma waiwayowan.
Nasreen ta goge hawayenta ta saita muryarta ta ce, “Dee me ya hanaka barci? Ko nice na bata maka?�
Juyowa ya yi gaba daya yana jin kunyar hada idanu da ita, kasancewar zuri’arsa ce ta ci mutuncin mahaifiyarta, dukkan halin wahalar da mahaifiyarsu ta shiga, a dalilin dangin Sultan ne, yana duba girman laifin fyade, da kuma kisa. A lokaci guda kuma idan ya tuna Karshen Kiyayyar Nasreen da Umma ya zo Karshe, duk lokacin da za ta ci mutuncinta, za ta tuna da alaka mai