Showing 123001 words to 123375 words out of 123375 words
Chapter 42 - RUBUTACCIYA BOOK 1-2-3-4 Complete Document by Fatima Dan Barno.txt
kuka, ta ce, “Ayya Abbana ba gaskiya bane, lafiyata kalau.� A nan duk suka fahimci abinda Sultan yake nufi, aka yi ta mata dariya. Cikin ‘yan kwanaki Ashmaan, Aslaf, Alameen, Barr Tajjud da su Khamis da Mahbub suka shirya da matansu za su fita Kasar, kowannen su cike da farin: ciki, domin ansan sabuwar soyayya za a bude a can. Sai mu ce Allah ya dawo da su lafiya.
BAYAN SHEKARU HUDU
Nasreen ce zaune tana baiwa Danta Lukman wanda ake kira da Asaad, ya ci sunan Abban Sultan abinci, yaron dan shekaru uku da rabi
yi wayo abinsa. Kanwarsa Saudat wacce ake kira da Yesmeen watanta biyar a duniya tana ta sharar barcinta. Sultan ya shigo hannunsa dauke da ledoji.
Cikin sauri ta tare shi, ta amshi kayan ta ajiye a Kasa ta rungume shi sosai a jikinta, “Barka da dawowa yallabaina. Tun kana hanya naji Kamshinka ashe da gaske kana tafe.� Kallon Asaad suka yi gaba daya a ya yin da ya shige sakiyarsu yana fadin “Deedina Oyoyo.� Nasreen ta zaro idanu, “Ka ji min yaro da Kwace. Deedinka, ko Deedina. Maza kaje ka . nemo Dee dinka a gidan Babanka Naufal, ko Baba Haidar.� ° Yaron ya noke kafada yana miKawa Sultan hannu. Sultan ya dauke shi yana juya shi, sai KyalKyatan dariya yake yi abinsa. Sannan ya sauke shi yana cewa, “Ina Mamana farin cikina? Don Allah dauko min ita.� Nasreen ta ce, “Ayya Dee barci take yi.� Ya Karaso har in da take kwance ya ce, “Kema kinsan duk barcin da take yi idan na dawo sai na tashe ta. Bana tunanin zan iya zama na minti biyar a gidan nan babu uwata a kusa da ni. Ita fa ta Haifa min matar da nake so fiye da kowacce.� Nasreen ta jawo Asaad ta rungume tsam, ta ce, “Ni kuma ina ji da wannan gwarzon wanda ya Haifa min miji na gari, ya kuma tsaya tsayin daka ya taya mijina renon matarsa. Bana jin ina da abinda zan iya biyanka da shi Abbana.� Gaba daya suka dubi juna suka yi murmushi.
ALHAMDULILAH MASHA ALLAH ANAN MUKA KAWO KARSHEN WANNAN KAYATACCEN LITTAFIN MAI SUNA RUBUTACCIYA WANDA MUKA FARA TUN DAGA LITTAFI NA DAYA HAR IZUWA NA HUDU ALLAH YA BAMU IKON AMFANA DA DARUSSAN DAKE CIKINSA