Showing 30001 words to 33000 words out of 123375 words

Chapter 11 - RUBUTACCIYA BOOK 1-2-3-4 Complete Document by Fatima Dan Barno.txt

shigo yana sunkuyar da kai. Mamakinsa ya karu. Me yasa yaran basa son hada idanu da shi ne? Bayan sun � gaida shi ya dubi Haidar ya ce, “Haidar ka kammala karatunka me kuma kake jira?�
Ya dan sosa kai, “Har yanzu aikin bai fito bane.
Jinjina kansa ya yi, “Ka ba ni takardunka soja zan turaka. Zan ba Khamis shi zai yi maka komai.� Haidar baya son aikin soja, hankalinsa ya fi kwanciya a irin aikin Yayansa, amma kuma ba shi da yadda zai yi dole ya yi shiru kuwai. “Umma ki ba ni Hafsat intafi da ita Abuja.� Hafsat ta zaro idanu, yadda ta tsani takura idan ta koma gidansa ai ta shiga uku. “Ni dai Yaya nafi son nan.� Bai ce komai ba ya mayar da hankalinsa kan mahaifiyarsa da gaba daya ta sauya kamar ba ita ba. Umman ta daure fuska sosai, “Lafiya kake kallo na haka? Ni ka sanni Sarai na tsani irin kallon nan mai kama da na raini.� Murmushi yayi sannan ya dubi agogo, “Ya kamata in zo inkoma kada inyi yamma.� Abba ya girgiza kansa, “Babu inda za ka je, muna da bukatarka yau a gidan nan. Ka bari sai gobe sai ka koma.� Sultan bai zo da niyyar kwana ba, don haka ya fara zare agogonsa zuwa cire takalminsa. “Abinda kace ayi shi za a yi Abba. Idan ma kace in ajiye masu kakinsu indawo gida hakan zan aikata.� Abba ya ji dadin kalaman Sultan ba kamar su Haidar ba, da kullum suke yi masa rashin kunya. Zuwan Sultan ne yasa suke yi masa komai cikin girmamawa. Ya Kosa Hajiya Ladidi ta tafi, amma sai ta zauna a tsakiyarsu ta hana su motsawa. Hakan yasa ya dubi Abban ya ce, “‘Abbana zan je gidan Hajiya Gwaggo.� Abban ya mike yana satar kallon Hajiya Salma, “Muje nima na rabu da zuwa wurinta.� Sultan ya dan dakata yana kallon Abbansa. Bai iya yin magana ba, suka fito aka bude masu mota suka shiga. Sun fara tafiya ya dan waiwayo ya dubi Abba, “Yanzu Abba kana nufin Hajiya Gwaggon baka zuwa duba ta?� Abba ya hadiye yawu da Kyar ya ce, “Wato Sultan Hajiya Salma ta wuce duk yadda kake tunani. Ta kama komai ta yi kane-kane a kai. Yaran nan kada ka so kaga rashin kunyar da suke yi min. Ni na gaji watarana zaku iya nemana ku rasa.� Sultan ya yi shiru bai yi magana ba, gudun kada ‘yan sandansa su ji sirrin cikin gidan su. Hajiya Gwaggo tana jin murya ta tsaya kawai tana kallon su, kafin tai wuf ta shige cikin daki tana share
hawayenta. Abba ya durKusa a gabanta yana roKo. amma ko kallon sa ba ta yi_ ba. Sultan ya harde yana dubansu, har sai da ya tabbatar da ba za ta yi maganar da gaske ba, sannan ya shigo ya zauna kusa da ita. “Hajiya fushi kike da Abbana? Hajiya kin taba zama kinyi tunanin dalilin da zai sa danki ya gujeki bayan yafi kowa zumunci duk_ cikin ‘ya’yanki? Ashe danki ba zai iya shiga hatsari ki jawo shi jiki ki ji matsalarsa ba? Hajiya kin taba zama da danki kin ji matsalarsa? Mahaifina yana cikin wani halin da yake da buKatar addu’arki.� Sultan ya Karashe maganar idanunsa jazir, yana jin da zai iya zubar da hawaye babu shakka mahaifinsa zai fara yiwa kuka.� Hajiya ta dan sassauto ta dubi Sultan ta ce, “Sultan har gidansu naje a gabansa Hafsat da Haidar da uwarsu suka wulaKanta ni, amma ya kasa magana. Ban yi fushi ba, na sake dawowa haka suka sake cin mutuncina. Kai ba zan. taba mance wannan abun ba.� Sultan ya dan yi shiru kafin ya girgiza kansa, “Hajiya ki yi hakuri. Abba ya sauya daga Abban da muka sani shekaru talatin baya. Umma tana neman tasa Abba a wani hali. Hajiya kiyi wa Abba addu’a ta haka ne zai sami sassaucin abinda ke damunsa. Abinda yasa na tsani zuwa gida Hajiya kin sani, saboda su Nasreen. Da zarar na shigo sai zuciyata ta dinga gaya min zan gansu a kwance a daki. Hafsat kuma da Haidar ki zuba ido ki ga irin matakin da zan dauka akansu. Kin wuce mu tsaya muna kallon wasu su wulakanta mana ke, bare kuma mu da kanmu.� Haka ya yi ta ba ta baki har ta sauko ta kuma sawa Abba albarka, wanda yake jin kamar ansauke masa wani tarin kaya ne a kansa. Hajiya Gwaggo ta kawo masu_ tuwon shinkafa, suka ci kwano daya da mahaifinsa, sannan ‘suka bar gidan. A hanya suka wuce gidan Alhaji Mu’azzam, wanda ya fada harkar siyasa babu ji babu gani, kullum yana gidajen radio yana kumfar baki. Shi kansa ya ji dadin ganin Sultan har ya nemi taimakonsa akan abubuwan da yasa a yaba, Sultan ya nuna masa babu damuwa. Abin mamaki har suka dawo Hayjiya Ladidi tana nan a gidan, hakan yasa ya wuce dakinsa yana kallon yadda aka tsaftace dakin.
Shiru ya yi yana tuna ranar da ya kasance tare da Nasreen, wannan daren ya kasa Bace masa, haka sai da aka gaya masa matarsa ce ya tuna da irin murmushin da Abban ke jifarsu da shi a ranar da ya kamata ya yi masu fada. Rintse idanunsa ya yi, Ashmaan yana can yana bincike a kan mutuwar mahaifiyar su Nasrcen, ya Ki bari wai sai sun bayyana tukunna, kamar yadda suke tunani. Yana nan kwance ba barci yake yi ba, jira yake Hajiya Ladidi ta bar gidan ya ci mutuncin° Kannansa, domin abinda suka yi wa Hajiya Gwaggo ya tsaya masa a rai. Daga dakin yake jiyo surutai hakan yasa ya fito yana duban yadda Hafsat da Haidar suka hayayyakowa mahaifinsu, suna cewa yaje ya kwashe komai ya gayawa Sultan. Sultan ya kirawo ‘yan sandansa ya ce yana son su sauyawa Haidar kamanninsa. Ita kuma Hafsat ya zare belt ya dinga auna mata. Umma fa ta gigice, sai ta yi wurin da ake dukan Haidar da gudun gaske tana kuka, sai kuma ta koma tana zagin Sultan tana cewa idan bai daina dukan Hafsat ba za ta tsine masa. Ko kallon ta bai yi ba, hukunci kawai yake yi. Sai da Abbansa ya yi magana sannan ya dakata da dukan Hafsat ya kuma dakatar da dukan Haidar, wanda tuni ya zube a nan yana numfarfashi. Sultan ya dinga masifar da ya basu tsoro, ya botsare masu ya sauya kamar ba Sultan din da suka sani ba. Yana ji a ransa ba zai iya barin mahaifinsa a cikin gidan nan ba, kada watarana su kashe masa mahaifi su barshi da maraici. A take ya kira Khamis ya zayyane masa komai, Khamis ya ce, kawai ya turo shi Abujan shi zai yi maganinsa, kuma dole ya tafi aikin sojan nan. Don haka Hafsat kadai zai barwa Umma a gidan. Umma ta Karaso tana masifa ya dube ta duba sosai ya ce, “Umma zan dauke mahaifina daga gidan na rasa me ke masa dadi? Tunani ne fal a cikinsa. Ji ya yi ankwanta a bayansa, bai hanata ba, haka bai hantareta ba, kamar yadda zuciyarsa ke gaya masa, Haka ta shammace shi suka sake komawa wata duniyar. Shi dai ko dan bai saba bane? Idan ba haka ba, ya kasa jin wani abu mai kama da dadin kasancewarsa da ita. Amma kuma tana da Kima a idanunsa musamman da ta kama kanta. Barci take shaKa harda minshari, wannan abu ya sake daure
“masa kai. Minsharinta ya dame shi Kwarai domin ya tsani namiji ma mai minshari bare kuma mace,
Bubbuga ta yayi ta farka tana sake luma idanunta a
cikin nasa; Zakiyya wata irin jarababbiyar yarinya ce, wanda a farko ta yi masa kawaici amma a yanzu ba za ta iya ba, ya zama dole su sake komawa duniyar da suka fito. A idanunta ya fahimci abinda take nufi, ya ce, “TirKashi! Ni mace ma ba ta gabana bare har in iya yin abinda kike nufi.� � Mikewa ya yi ya shige bandaki ya sa key Zakiyya ta mike ta shige dakinta tana cizon yatsa Ya riga ya dandana mata zuma mai wahala mancewa. Shigewa dakinta ta yi ta kira mahaifiyarta, “Momi mutumin nan fa ya iya komai Naji dadi da kika hada ni da shi. Wallahi yanda nake jin sa babu abinda zai raba ni da shi, gashi baya ~ son hayaniya.� A nan ta yi ta ba mahaifiyarta labarin yanayin Sultan, wanda karaf sai a kunnensa.


MU HADU A LITTAFI NA BIYU
6/5/22, 10:38 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 2🦚*




CHAPTER 1






*BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO*






A JIYA MUN TSAYA


Minsharinta ya dame shi Kwarai domin ya tsani namiji ma mai minshari bare kuma mace,
Bubbuga ta yayi ta farka tana sake luma idanunta a
cikin nasa; Zakiyya wata irin jarababbiyar yarinya ce, wanda a farko ta yi masa kawaici amma a yanzu ba za ta iya ba, ya zama dole su sake komawa duniyar da suka fito. A idanunta ya fahimci abinda take nufi, ya ce, “TirKashi! Ni mace ma ba ta gabana bare har in iya yin abinda kike nufi.� � Mikewa ya yi ya shige bandaki ya sa key Zakiyya ta mike ta shige dakinta tana cizon yatsa Ya riga ya dandana mata zuma mai wahala mancewa. Shigewa dakinta ta yi ta kira mahaifiyarta, “Momi mutumin nan fa ya iya komai Naji dadi da kika hada ni da shi. Wallahi yanda nake jin sa babu abinda zai raba ni da shi, gashi baya ~ son hayaniya.� A nan ta yi ta ba mahaifiyarta labarin yanayin Sultan, wanda karaf sai a kunnensa.


ZAMU TASHI


RUBUTACCIYA 2


Sultan ya gama sauraren dukkan maganganun da take yi a waya, ya zuro kansa cikin dakin cike da takaicin jin matarsa tana bude masa sirrinsa.


Yana sanye da jallabiyarsa fara sol sai Kamshi ke fita daga jikinsa. Shigowa ya yi ya zauna yana duban ta. “Ke kuma haka Allah ya halicce ki fadin sirrin mijinki ko? A haka dai kamar mai wayo ashe sakarya ce. To daga yau na bar sake zama kusa da ke, tunda baki da sirri.�


Zakiyya ta gigice ta ce, “Wallahi ba wata bare nake gayawa ba, Momi ce ta kira nake bata labari kayi hakuri ba zan sake ba.�


Sultan ya zaro idanu sosai. Kamar zai yi magana sai kuma kawai ya fice abinsa. Mamaki ya ci gaba da dawainiya da shi, ta yadda yarinya za ta iya kallon idanun mahaifiyarta ta gaya mata sirrin da ke


tsakaninta da mijinta, abin ya yi masa tsauri sosai.


Duk yadda Mansur yaso ya ga ya sami kan Nasreen abin ya faskara, hakan yasa ya daina basu abincin, ya koma ba su wahala yana gana masu azaba kala-kala.


Da Nawfal ya gaji ne ya ce, ‘Nasreen ki amsa masa ko za mu samu a rangwanta mana. Ba ki jin tausayina ne Nasreen? Ina shan wahala.�


Nasreen ta goge hawayenta, tana laluban Nawfal da kwana biyu ya Ki yarda ta taba shi, sakamakon jikinsa da ya yi zafikamar wuta, “Nawfal don Allah ka zo kusa da ni, ka daina guduna kaji Nawfal?�




Nawfal ya Karaso ta rungume shi, a lokacin ta ji jikinsa zafi rau! Ta goce da kuka sosai, “Nawfal baka da lafiya ne? Me ya sameka? Nawfal so kake ka kashe min kanka? So kake ka sani maraici?� Dukansa take yi da dukkan hannayenta tana kuka. Shi ma kukan y.ake yi azaban ya ishe shi haka.


“Nawfal� bari Mansur ya zo sai ya nemo maka magani.�


Girgiza kansa ya yi, “Mansur ba ya nan, ya tafi ya barmu a Karkashin kulawan Kattan nan.�


Ajiyar zuciya take yi da Karfi. “Nawfal lallaba ka je waje ka samo ruwan_ sanyi ingoga maka a jikinka ko zai rage zafin.�


Babu musu ya aiwatar da abinda ta ce, ta sa gefen hijabinta a ruwa tana jiKawa tana goga masa a jiki. Sun dauki tsawon lokaci a hakan har jikinsa ya fara sanyi sannan ta sa kansa a Kafafunta tana tofa masa addu’a. Wani ya shigo yana dubansu ya ce, “Yanzu sai ki fara takaba barayi sun kashe Sultan.� �


Wani abu ta ji ya ratsa mata tsakiyar kanta, tunda ta fasa wata Kara ta kifa kanta a jikin Nawfal bata sake sanin inda kanta yake ba.


Nawfal ya tashi yana rintse idanunsa, da Kyar ya iya duban mutumin ya ce, “Ka ji tsoron Allah. Yaushe Deedi ya rasu? Na san


kun yi� hakan ne domin ku cimma wata manufarku ,akanmu.� Mutumin ya girgiza kai jikinsa,a sanyaye, “Da gaske Sultan ya rasu. Ni kaina naji rasuwarsa, kasancewar kisan wulakanci akayi masa. Haka kuma anrasa gane su waye ke da alhakin wannan _,aikin. Ka. taimaka ‘wa ‘yar uwarka ta farfado.� ~*~ ~ . Nawfal yasa kuka mai sauti yana jin zuciyarsa tana yi masa ciwo. Cikin kuka ya � dubi mutumin ya ce, “Don girman Allah ka sadamu da� gidansu Deedi muyi masa addu’a. Mutuwar Deedi tamkar tonan asirin mu ne.. Mun shiga uku don Allah ku taimake:mu ku kaimu gida mu zauna cikin ‘yan uwanmu domin yi wa Deedi addu’a.� Mutumin da ya fara jin tausayin su har cikin zuciyarsa ya girgiza kai, “Yin hakan zai iya jawo nima inrasa rayuwata agurin Oga Mansur, Zan baku shawara ku bi shi a hankali za ku rabu lafiya. Ka duba lafiyar ‘yar uwarka bari in kawo maku abinci ku ci.� Nawfal ya fara watsa wa Nasreen ruwa,


ta ja dogon numfashi, taso Kwarai yau da idanunta suna gani ta kalli mutumin da ya kawo mata wannan mummunar sakon. A yau ta sake kukan rashin idanunta. Tun Nawfal yana iya rarrashinta har ya koma ya zuba mata ido kawai. Ta kasa ci ta kasa sha, sunan Deedi kawai take fitarwa daga bakinta. Ta tabbata lokacin mutuwarta ce ta yl. Fuskarta suka kumbura suka yi suntum saboda tsabar kuka.


Washegari Mansur ya shigo gidan yana duban Nasreen, “Yanzu za ki iya aurena? Ki fara zaman takaba, ki samu ki gama so nake muyi auren gaske. Shi ya sa ban taba yunkurin cutar da ke ba. Ki zauna kiyi zaman takaba idan kika gama zan kawo malamai gidan nan a daura mana aure da ke. Allah ya jiKan Sultan yasa ya huta.�


Nasreen ta sake sa kuka mai ban


tausayi tana girgiza kai, “Deedi bai mutu ba, ban yarda ba, idan da gaske Deedi ya mutu ka dauke mu ka kaimu gida.�


Harararta ya yi ya ce, “Dama ance makahon mutum shegen kafiya gare shi. Da ni aka yi jana’izar mutuwar Sultan. Don haka ba yardarki nake nema ba. Zan fara Kirga daga yau.�� Nawfal yana jin su bai ce komai ba, shi kadai yasan abinda yake saKawa a cikin zuciyarsa. Haka bai taba jin zai iya daukar mataki wajen ficewa daga wannan wurin ba, � sai yau dinnan da aka sanar da shi mutuwar Sultan. Kai tsaye ya fara dora laifin akansa, ~* tunda babu yadda Nasreen ba ta roKe shi ba, a kan su koma gida, amma ya Ki amincewa.
Mansur yana fita ya dubi� Nasreen ya ce, “Nasreen. Gobe ki cewa Mansur kin amince da shi a matsayin miji.�� Nasreen ta rarumi sandarta za ta kwada masa, ya sa hannu ya amshe sandar.


Cikin zafi take magana, “Wallahi ba zan taba yin wani auren ba, tunda Deedi ya rasu me kuma zan nema a duniyar nan? Na rasa shi na rasa farin cikina. Nawfal kana ta juya min rayuwata kamar kai ka kawo ni duniya? Na gaji da irin abubuwan da kake yi ka fita ka bani wuri tun kafin fushina ya Kare akanka. Kana da yadda za ka yi mu koma gida, amma ka bar mu cikin wahala, har abin ya kwabe mana. Yanzu kana ganin waye zai iya fitar da mu a cikin gidan nan? Nawfal mutuwa zan yi, zan mutu Nawfal komai ya tsaya min, zuciyata tana yi min


ciwo na kasa amincewa na rasa tsayayyen mutum kamar Sultan. Don Allah ya zan yi? * Ya zan yi?


“Nawfal Dee shi ya dauki dukkan dawainiyar mu, shi ne gatan mu a gidan duniya. Ya juri abubuwa masu yawa saboda kawai ya faranta mana rai. Yau ga mu muna da yadda zamu yi mu isa gare shi, amma muka gwammace mu nesanta kanmu daga gare shi, muka gwammace mu katange kanmu a wurin da bai kamata ba. Idan Umma ta yi mana laifi ba za ta ci albarkacin danta mu yafe mata ba? Na tabbata Dee ba zai taba yafe mana ba.


Nawfal ka fice min daga dakin nan tun kafin indaga sandar nan in kwada maka.�


Yadda ya ga tana cikin fushi ya sa ya fice kamar yadda ta ba shi umarni. Hada kansa ya yi da guiwa yana shessheKan kuka. Tana jin irin kukan da yake yi wanda bata taba jinsa yana irinsa ba. A take danasani ya shigeta, yau da babu Nawfal a rayuwarta da tafi haka wulakanta. Ya zama dole ta yi masa uzuri. ; “Nawfal!� Ta Kwala masa kira, babu


shiri ya taso ya Karaso wurinta suka rungume juna suna kuka mai ban tausayi. “Nawfal ka yi hakuri bacin rai ne yasa na gaya maka magana.. Amma kasan bamu yi wa Dee adalci ba, ba mu kyauta masa ba. Ga shi Dee ya yi kwanan Kabari babu mu a cikin masu yi masa addu’a. Nawfal gaya min kana da mafita? Ko wurin Abba ne mu samu muje na tabbata kafin mutuwarsa ya bar mana abinda za mu dinga tunawa da shi.�


Nawfal ya goge hawayensa, haka ya sa hannu ya goge mata nata hawayen da suke ta zuba. “Nasreen ya zama dole ki nunawa Mansur kin hakura kin amince da shi, ta hakane zai saki jiki damu har mu samu hanyar da za mu gudu. Ina da lambar Dee, ina da ta Abba, ban yarda Dee ya rasu ba gaskiya. Ki natsu ki bi Mansur har in . sami mafita.� Gyada kanta kawai take yi hawaye na . kwarara, bakinta ya mutu, ta ji dadin kalaman Nawfal a kan Sultan yana nan a raye bai mutu ba. Idan kuwa ya tabbata yana da rai, sai ta yi azumi uku domin nuna godiya ga Allah da ya bar mata Sultan a raye na wani lokaci.


“Yanzu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login