Showing 102001 words to 105000 words out of 123375 words
Chapter 35 - RUBUTACCIYA BOOK 1-2-3-4 Complete Document by Fatima Dan Barno.txt
zan ga Naufal?�
Kuka take sha babu KakKautawa, ita Karan harbin da ta ji shi yake gaya mata ankashe Sultan. A can bangaran kuwa tuni sun ci nasarar guduwa sai suka bar wanda aka harba. Sultan ya fito yana duban mutumin idanunsa a rufe. Sai a lokacin ya tuna da wayarsa, haka kudin ciki bai Kare ba, ya daga ya mayar kunne yana fadin Hello! Sai dai baya jin komai sai sautin kukanta da irin kalaman da take yi tana fadin. “Ka san zaka mutu ne shiyasa ka turo ni nan? Wayyo rayuwata ta zama abar tausayi, waye zai sake zama gatana a gidan duniya?�
Kashe wayar ya yi tare da kiran Office din su, cikin gaggawa motar ‘yan sanda suka bayyana a gidansa. Yana nan tsaye aka tafi da shi, wasu suka tsaya a gidan, haka ya hana a taba ‘yan sandan ya ce a bar su har su tashi da kansu. Shi kuma ya koma ciki ya zauna a falon yana mayar da ajiyar zuciya. Sai da ya dan natsu sannan ya je ya bude Kofar su Umma da suka dami ko ina da ihu.
Yana budewa gaba daya suka fada jikinsa, ya ce, “Umma lafiyata Kalau don Allah ku daina kukan nan.� Umma ta ce, “Idan suka kashe min kai ba zan taba yafe jinin dana ba, Sultan duk tsaron da ke gidanka me yasa ‘yan fashi suka iya shiga cikin gidanka? Ina ‘yan sandan?�
Furzar da huci ya yi mai zafi sannan ya dawo falo ya zauna haka suka biyo bayansa kamar wanda zai sake bace masu. Wayarsa ya zaro ya kira Nasreen, tana jin kukan waya ta dauka hannunta na rawa, “Hello.� Yadda ya ji muryarta tana rawa yasa shi yin murmushi, ““Waye ya gaya maki an kashe ni? Kukan nan da kike yi kamar za a zare ranki na menene? Wa ya gaya maki har kin tabbata marainiya? Kina nan da gatanki insha Allahu, share hawayenki ki kwanta zamu yi magana gobe.�
Ta kasa magana sai hawayen farin ciki da ke sauka a kumatunta. Ya katse wayar yana duban su Umma har yanzu hankalinsu baya cikin jikin su. “Umma turo su akayi akan wani Case da ake son dole sai na ci hanci. Ni kuwa ko rayuwata za su dauke ba zan bi su ba. Umma Case din fyade ne ‘ya’yanmu da Kannanmu ake Gatawa rayuwa. An yi wa babbar budurwa fyade
ta mutu bare Kananan yara wadanda basu wuce shekaru hudu ba? Umma a Kaduna a kowacce rana sai mun sami case din fyade idan yau mun sami na yara ‘yan shekaru hudu gobe zamu samu na ‘yan shekaru biyar, jibi za mu samu na ‘yan shekaru shida. Umma a haka za a yi ta bata rayuwarsu? Sannan ba za mu Kwato masu ‘yancin su ba, sai a nuna wa hukuma kudi ko kuma a dauki rayuwarsu? Bana jin ko mahaifina na kama da wannan abin zan iya barinsa, duk girman son da nake masa kuwa.�
Umma da tunda ya fara maganar idanunta suke bude saboda tsoro, ta gyada kai, “Na tsani mazinaci, mazinacin ma mai bata rayukan yara Kanana. Ina tare da kai Sultan ka Kwatowa � ‘ya’yanmu hakkin su. Ka tona asirin su duniya ta gansu. Mutanen nan-su suke bata mana Kasa. Na amince maka ka tafi ka Kwatowa bayin Allah hakkin su.� ;
Sultan ya sake samun Kwarin guiwa yanzu ya kula da babu Zakiyya, haka Hafsat tana Kudundune tana aikin kuka. Ya yi murmushi ya ce, “Hafsat zo nan kusa da ni. Ashe haka kike son Yayanki? Lallai yau na ji dadi tunda naga kulawar Hafsat akaina.�
Ba su san lokacin da suka yi murmushi ba, Anan falon suka yi barci shi kuma ya tashi yana Kwankwasa Kofar dakinsa da Zakiyya tasa key, Da Kyar ta bude sai da ya tabbatar mata da shine. Ko a yanzu ya gane su waye dolensa? Su waye suka shirya sadaukar da rayukansu akan tasa rayuwar. Bai yi barci ba, bai kuma yi mata magana ba. Kawai yana zama ta zauna ta hau taba shi. Tana cewa, “Wai kai ko irin wasa na ma auratan nan baka iya yi bane? Kullum fuskarka babu wani annuri.�
Sultan ya fizge jikinsa yana aikata mata wani irin kallo. “Ke wacce irin macece mara tunani? Ba ki iya bambance lokacin da mijinki ya ke cikin farin ciki da akasinsa? Ban iya wasan ba, idan za ki iya zama da ni a haka ki zauna idan ba za ki iya ba ga hanya Please! Kin ga ta inda Nasreen ta fi ki kenan, ita tana da natsuwar da take bambance lokacin wasa da_ lokacin lallashi. Duk da tana yarinya Karama amma ta fi ki hankali da sanin ciwon kai. Wasa kuma sai mace ta gyara kanta take samun yadda take so a wurin miji. Kada ki sake matsoni a lokacin da nake Kunshe da damuwa.� Yaja filo ya kwanta kawai. Karfin turarenta da ta yi amfani da shi
suka hade da warin jikinta suna bayar da wani irin tsami. Ji ya yi gaba daya ya tsani kansa, yana matukar kokari wajen yi mata kawaici. Dole ya yi alwala domin yin Sallah ya mika godiyarsa ga Allah, ya fice zuwa falo. Har asuba idanunsa biyu, yana karatun AlKur’ani domin ya sani yaKin da yake shirin tunkara ba abu bane mai sauki. Shiri yake na tonawa dukkan wanda yake da alhakin shigar masa gida asiri, ko waye shi. Ana kiran Sallar asuba ya fito zai je Masallaci ya sami ‘yan sandansa sun farka har
sauran sun yi masu bayanin komai. A nan suke cewa su ba su ji motsi ba, sai farin fauda da suka
gani ya bade ko’ina. Wasu ‘yan sandan suka yi masa jagora zuwa Masallaci, yana dawowa ya yi wanka a gurguje ya yi shirin zuwa office.
Da isarsa ya kira Ashmaan a waya ya kira Mahbub da Khamis duk suka hadu a Office dinsa. Ya gaya masu dukkan abubuwan da suke faru ya Kara da cewa, “Akan case din nan ba zan bari rayuwata ta zama a cikin hatsari ba, bai � kamata in ci gaba da boye su bayan su rayuwata suke nema data iyayena ba. Don haka Ashmaan za ka iya zuwa ‘yan sanda su matse mutumin da na harba a Kafa, sai ya gaya mana wadanda suka turo su, ku buga a cikin Jaridarku daga ta hausar har ta turancin. Ba zan sake yin gangancin da nayi, har aka shigo gidana ana neman rayuwata ba. Na dauki hakKkin Umma da Hafsat, hatta Nasreen da ke can London sai da ta sha kuka har ta gode Allah, kalamanta sun bani tausayi, gani take yi na tura ta can ne saboda zan mutu. Don haka sai sun biya tashin hankalin da suka sa iyalina ta hanyar fanshe abinda suka shuka.�Khamis ya yi shiru can ya ce, “Sultan ka ba ni case din nan mana ya dawo hannun sojoji, ta yadda za mu kakkarya kayayyakin banza mu sake hade su.� . Ashmaan yace, “Ba za a yi haka ba, a dai tona masu asiri kawai.�
Mahbub ya saki ajiyar zuciya, “Wai kai ma kenan da kake sama da ni. Na tsani aikin dan sanda sosai, wasun mu‘su suke jawo mana zagi a duniya, ake hada mu ana cewa ba mu da mutunci. A yi yadda ya kamata din.� Cikin hukuncin Allah Ashmaan ya sami yin hira da mai laifin ya kuma samu abinda yake so, sunayen wasu manya ya kirawo daga ciki har da Alhaji Sulaiman da aka yi zaman meeting da shi, da kuma sunan Ogansa. Don haka kafin fitowar jarida Sultan ya kira Meeting da dukkan manyansu meeting din gaggawa. Ogansa yana ganin Sultan gabansa ya dinga faduwa.
Sultan ya tsaya a tsaye bayan ba su girma da ya yi ya fara magana cikin bacin rai, “Ku yi hakuri na kira wannan tattaunawan ne saboda in gaya maku abinda ke faruwa a tsakanina da Oga.�
Sultan ya kwashe komai ya gaya masu, ya Kara da cewa, “Kai ba ka isa ka hada baki da wasu a nemi rayuwata ba, baka isa ka sani inci hanci dole ba, idan kai za ka iya amsar kudi a kan rayukan ‘ya’yanmu da suke cikin matsala, ni . ba zan iya ba. Na kuma gaya maka a baya ba siyan kwalina na yi ba, a’a da Karfina.na shiga � aikin.� Ya juya wajen babbansu ya sara masa ya ce, “Sir! Barin wadannan a cikin Kasa tare da kakin mu a jikin su tamkar Kara ruguza Kasar ce. Bayan Sultan ya gama jawabinsa ya zauna, a nan take aka yi ta tattaunawa cikin natsuwa babu wani kace nace aka ce a rufe shi, a cire masa kakin jikinsa, har sai an kammala bincike.� Sultan ya dawo gida cike da farin ciki, domin a ranar aka tura akamo su Alhaji
6/29/22, 18:05 - Ummi Tandama😇: RUBUTACCIYA BOOK 4
CHAPTER 5
BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
MUN TSAYA
Sultan ya tsaya a tsaye bayan ba su girma da ya yi ya fara magana cikin bacin rai, “Ku yi hakuri na kira wannan tattaunawan ne saboda in gaya maku abinda ke faruwa a tsakanina da Oga.�
Sultan ya kwashe komai ya gaya masu, ya Kara da cewa, “Kai ba ka isa ka hada baki da wasu a nemi rayuwata ba, baka isa ka sani inci hanci dole ba, idan kai za ka iya amsar kudi a kan rayukan ‘ya’yanmu da suke cikin matsala, ni . ba zan iya ba. Na kuma gaya maka a baya ba siyan kwalina na yi ba, a’a da Karfina.na shiga � aikin.� Ya juya wajen babbansu ya sara masa ya ce, “Sir! Barin wadannan a cikin Kasa tare da kakin mu a jikin su tamkar Kara ruguza Kasar ce. Bayan Sultan ya gama jawabinsa ya zauna, a nan take aka yi ta tattaunawa cikin natsuwa babu wani kace nace aka ce a rufe shi, a cire masa kakin jikinsa, har sai an kammala bincike.� Sultan ya dawo gida cike da farin ciki, domin a ranar aka tura akamo su Alhaji
ZAMU TASHI
Sulaiman. Talakawan da Sultan ya taimaka masu suna ta neman ‘Sultan domin su yi masa godiya, amma ganinsa ya zame masu wahala. Yana can kwanaki biyu ya zama sai a hankali baya zama, ita kuma Nasreen har an fara duba idanun, haka sun sanya ranar aikin. A lokacin ta yi Kokarin ganin ta yi waya da Sultan ya kirata yake lallashinta akan yana wani bincike ne.
Al-amcen ya karbi wayar suka tattauna, ya Kara yi masa godiya akan irin dawainiyar da yake yi da Nasreen da Naufal ya ce babu komai. A zaman Nasreen da Jidda Nasreen ta Karu da ilimi kala-kala ta ji dadin wannan zaman, haka hankalinta ya kara kwanciya tunda ta fahimei Jidda macece mai ban dariya da saukin kai, a lokaci guda ta shiga cikin jerin mutanen da take son ganin fuskarsu. Hankalin Sultan bai dawo jikinsa ba, sai da aka yanke masu hukunci, duk da Alhaji Sulaiman bai fada masu asalin wanda yake aikata wannan aikin ba. Yanzu yana jin kansa
kamar an sauke masa wani nauyi. Yau Umma ta dage tana son zuwa gida, tana yawan yin mugayen mafarkai. Dole ya shirya ‘yan sanda ya ce su kaita gida ya kuma, ce zai zo gobe. Su Umma suka
tafi, gidan ya sake yi masa fadi gabansa yana fadiwa akan abinda zai faru a garin Kaduna, gani yake kamar ya shirya ya bi su, sai dai idan ya bi su abin zai fi kwabcewa. Yana zaune Zakiyya ta fito ta zauna kusa da shi tace, “Ka yi hakuri idan nayi maka laifi.�
Sultan yana son mace mai bada hakuri a lokacin da ta san ta yi kuskure, sai dai bai taba zaton Zakiyya za ta kasance daga cikin ‘irin matan nan ba. Babu musu ya ce babu komai, a ranar dole ya biye mata, yana mai jin Kunci a zuciyarsa. Yanzu tunanin zuwa London kawai yake yi, domin Al-amcen ya tabbatar masa da anyi aikin idanun suna sa ran za a bude idonun ko wani irin lokaci. Don haka ya fara shiri kawai ba tare da ya gayawa Zakiyya ba. Da gaske yake jin gidansa ya yi masa girma ya saba da hayaniyar gidan. A gefe guda gabansa yana faduwa akan mahaifiyarsa. Umma tana isa Kaduna ta ce wa Driver ya wuce da ita gidan Hajiya Ladidi, babu musu ya wuce da ita. A gida ta sameta tana shirin fita
Umma ta zabga mata harara, “Kin bani mamaki butulu. Ba ni Salma za a yi wa haka ba. Kin kai sunan Sultan gidan malamai saboda baki da kirki, kika zugo ‘yarki ta yi min rashin kunya ko? Zan nuna maki baki isaba in dai da gaske ni na haifi Sultan zan nuna maki Karfin ikon a hannuna yake. Zakiyya kamar ta bar gidan dana ta gama. Ke Hafsat juya mu tafi.�
Hajiya Ladidi ta kamo hannunta ta marairaice, “Haba Hajiya idan aka gaya maki zan sa Zakiyya ta yi rashin kunya za ki yarda? Kuma ni ban kai sunan Sultan wurin boka ba, gani nayi yadda yake wulakantata yana maki ciwo shiyasa nace bari intaimaka maki inrage maki wahala kin san dan yau ka haife shi ne baka haifi hali ba. Ai ba zan mance karamcinki ba.�Umma ta yi Kwafa ta ce, ‘Me yasa ba ki daukar wayata?�Ta sake marairaicewa, “Wallahi saboda zancen mijinki da na fada maki ne na san ki da kishi shiyasa.�Umma ta saki ajiyar zuciya, “Shi kenan babu damuwa, yanzu zan je gida idan na huta zan leKo� Hajiya Ladidi tace, “Naso kuwa muyi maganar yadda ya kamata ayi da Nasreen dinnan naji ance har waje ya turata aikin idanu. Yarinyar nan tana neman ta zame mana masifa.� Umma ta dawo da baya, “Wannan maganar sai mun zauna, da bakin cikin hakan na dawo Duk da ita ma Zakiyya ta Bata min rai sosai.� Hajiya Ladidi ta ce, “Ai ba ta gaya min ba, ta san halina sai in yi tattaki inci mata mutunci.� Umma ta ji dadin kalaman Hajiya Ladidi don haka ta tafi tana murmushi. Tana wucewa Hajiya Ladidi ta harare ta tace, “An gaya maki bari zan yi ki rabo ‘yata da gidan mijinta? Sai dai ke in raba ki da danki rabuwa ta har abada, muje zuwa.� A mota Hafsat take cewa, “Umma ni ban yarda da matar nan ba, Karya take yi tace bata san abinda Zakiyya take aikatawa ba.�
Umma ta yi shiru, bata san dalilin da yasa gabanta ke faduwa ba. Suna isowa gidan aka shiga kwasan kaya ana kaiwa ciki. Ta sa kai ta shiga falon. Mairo ta samu tana matsawa Abba Kafafu shi kuma yana duba Jarida. Umma ta shigo tana zare idanu, ita kuwa Mairo tana ganin Hajiya ta mike jikinta yana Bari. A natse ya ajiye jaridar yana Karewa Hajiya Salma kallo babu wata damuwa a fuskarsa, shi kansa bai san zai iya irin wannan jarumtar ba. “Salma saukan yaushe?� Sa’a daya ya ci yana matsayin mijinta, da babu abinda zai hana ta liliyo ashar ta dura masa. Hawaye suka fara gudu a fuskarta, Hafsat ma ta fasa kuka tana cewa, “Mairo kin cuce mu kinci amanar mu. Yanzu Abbanmu kike irin wannan zaman da shi?� Umma ta saki jakar hannunta tana duban Abba, domin ya fi ba ta mamaki. Ta yi magana cikin sanyin jiki, “Yanzu wannan ne yardar da kake nema a wurina? Ka cuce ni ka cuce ni da har na hada zuri’a da kai. Mazinaci wanda baya tsoron Allah.� Jikinsa na rawa ya mike yana nunata da hannu, “Kada ki sake kirana da mazinaci. Matsayinku daya da Maryama don haka nake sake neman tsari da aikata zina. Ai nasan kin tafi kin bar ni ne saboda in aikata abinda kike fada, sai dai Allah ya nesanta zuciyata ma da wannan tunanin, domin mutuncin ‘ya’yana nake ji ba mutuncinki ba.� Hafsat ta yi cikin daki da gudu tana rusan kuka. Umma ta yi kukan kura ta yi kan Mairo tana cewa, “Yau sai kin bar duniyar nan, sai kin daina cin amana daga kaina. Ni Mairo? In maidoki mutum ki ci amanata? Mijina za ki aura kina Kazamarki da ke? har kin isa in hada miji da ke?�Abba ya samu ya raba ta da jikin Mairo da Kyar. Jikinta yana kyarma ta shako wuyan rigar Abba, “Kai kuma shugaban munafukai! Idan baka sake ni ba yau gidan nan babu mai yin barci. Ka sake ni ko kuma dukkanku indauki mafi munin mataki akanku. Ni za ka yi wa kishiya? Kishiyar ma mai aikina? Duk matan duniyar nan baka ga-mace bane sai Mairo? Ka sake ni nace bakin munafuki.� Tana maganar tana huci kamar zakanya.
Abba dai bai ce mata komai ba, ya dubi Mairo ya ce, “Ke Mairo wuce dakinki.�
Mairo ta raba gefenta za ta wuce ta saki wuyan rigar Abba ta koma ta fizgo Mairo ta hau duka babu ji babu gani, tana cewa “Babu inda za ki je makira, sai kin gaya min wanda ya baki shawarar aure min miji daga zuwa Unguwa indawo. Fada min dan ubanki, dama kuna neman juna ne? Ba za ki gaya min ba sai na kashe kayan banza?� Abba ya dago ta ya dora mata mahaukacin mari wanda ya yi sanadiyyar fashewan gefen bakinta, amma bakinta bai mutu ba, gaba daya ta zama mahaukaciya. Marin da ya yi mata ya tsaya masa a rai, danasani ya shige shi a lokaci guda. Sannan ya dubi Mairo da ke kuka kamar ranta zai fita ya ce, “Maryama zo ki wuce. Idan kin cika mahaukaciya ki sake taba min mata, za ki ga irin wulaKancin da zan yi maki. Na yi auren ‘nan ne don inbata maki kamar yadda kika bijirewa umarnina, kuma burina ya cika. Idan takardarki kike buKata ki je dakinki zan kawo maki yanzu, domin ni daman na gaji da halayyarki.� Umma ta fasa wani kuka mai ban tausayi a lokaci guda tasa hannu tana goge hawayenta, “Ban yi mamaki ba, sunanka namiji ne babu abinda ba zaka yi ba. Kaddarar namiji waccece bamu sani ba? Cin amana agun maza wannene bakon mu? Don haka ina son a yanzu ka furta da bakinka ka sake ni ba zan zauna a gidanka ba, na