Showing 75001 words to 78000 words out of 123375 words
Chapter 26 - RUBUTACCIYA BOOK 1-2-3-4 Complete Document by Fatima Dan Barno.txt
nasan irin farin cikin da nake tsintar kaina da zarar na shaki Kamshin nan.�
Yumnah ta yi dariya, haka ma Dr Astlaf, kuma gaba daya suka zuba mata idanu domin da gaske suke yi, suna jin dadin Kamshin nan. Yumnah ta dauki wayarta ta ce, sanya lambar nan tukun, 08068906212. Babu musu ya kwafe lambar yana sake dubanta domin neman Karin bayani. Ai kuwa ta dan gyara zama,
“Sunansa Jafar, yana kasuwan sabon gari a birnin Zaria, haka duk inda kake a fadin duniyar nan yana aiko da kaya. Shago ne da ya amsa
sunansa, kaf Zaria suna alfahari da shi. Kana zuwa Sabon Gari wajen kasuwar mata, ma kawai ka ce shagon Jafar kake nema, za a kai ka har can. Duk kalolin sabulai humura dilka da komai da komai da ya Kunshi Kamshi yana saidawa, haka yana siyar da kaya Original baya kawo kaya marasa kyau. Idan kana neman ko misk ne, indai mai kyau ne, to ka garzaya shagonsa.�
Ta dan muskuta ta gyara zamanta sosai, don ta ji dadin yi masa bayani. Ta ce “Kuma babu abinda zai baka mamaki sai idan na gaya maka da dubu dayanka ma idan kaje shagon Jafar za ka sami abubuwa masu inganci.Yadda kasan domin talakawa aka bude shi, Idan a wani shago ana siyar da abu dari uku a wurinsa za ka samu a dari biyu da hamsin. Ban taba ganin wanda ya siya abu a gunsa ya dawo yana danasani ba. Kayan gyaran gashi kuwa, abin ba’a magana, ka dai ga yadda kan Nasreen ya yi kyau da cika da tsawo, wannan duk aikin shagon nan ne dai da nake gaya maka na Jafar. Za ka gane abinda nake gaya maka ne, idan ka je shagon ka gan shi cike da matan Shuwa, sai abin ya baka tsoro. Hausawan mu ma ba a bar su a baya ba, duk sun gane sirrin. Doktona ka matsa min kana son sanin sirrin Kamshina, yau dai ga Yayana ya sanya na fada ban shirya ba, kuma abinda ya sa na gaya masa, don dai Nasreen din mu bata gani ne, haka bata san gari ba.�
. Ta Karasa tana zura idanunta a cikin na mijinta, a lokaci guda ta kashe masa idanu tana jifansa da shu’umin murmushi.
Shi kuwa Sultan ji yake idan ma miliyan ne zai kashe a shagon Jafar. Zai je da kansa ba aike ba, ya sake siyawa Nasreen, duk da ta gaya masa Kamshin ya zauna sosai a jikinta, hakan ba zai hana sake siya mata ba. Babu namijin da a ~ duniya zai ce baya son Kamshi sai dai idan bai samu ba. ,
Aslaf ya dubi matarsa cikin kulawa ya ce, “Na gode maki da wannan bayanin, nima yanzu zan tura wa amaryar da zan Karo lambar Jafar din,ta je ta nemi Kamshin nan, domin kuwa abinda ya hanani Kara aure kenan, tunanin yadda zan iya hada shimfida da wata, bayan bata kasance mai irin Kamshinki ba, ko bata iya girki ba. Babu matsala zan ci da hakuri, amma rashin Kamshin nan matsala ce, saboda tana cire soyayya a Zuciyar miji.�
Yumnah ta kafe shi da idanu har ya dire maganar sannan ta yi murmushi, “Oho sai-ta Zo. Akwai inda har abada bata isa ta kamo ni ba, in dai ni ce babu duka babu zagi, babu habaici, da Kafafunta za ta fice ta bar min gidana, domin sunanta wacce ta zo kallon baKin ciki.�
Sultan ya shafi kansa yana murmushi, “Mata! Kun shiga uku da kishi. Kun ce ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne, anya da gaske ne? Idan gaskiya ce, ai murna za ki yi da zuwanta, sannan ki gaya mata dukkan sirrikan rije miji.�
Yumnah ta dalalo idanu ta dafe Kirji, “Wa? Ni? Allah ya tsareni Yaya Sultan. Ai lokacin da zan gaya mata sirrina na shiga uku na lalace, a lokacin ni kuma za ta yi ta Kokarin ganin ta watso ni waje, da ni da ‘ya’yana. Mutanen yanzu ne sam babu Allah a zuciyarsu, za ka ga kai ka rike mutum da zuciyarsa guda, shi kuma yana can yana haKa maka Katon rami. Wallahi idan na ga mutum a rana ba zan sake ingiza shi ba, amma kuma zan ratsa in wuce shi. Kai dai Allah shi kyauta, Allah kuma ya tsare Nasreen da wannan Zakiyyar don naga babu Allah a ranta.�
Kamar ta fama wa Sultan inda yake masa KaiKayi ya yi murmushi wanda iyakarsa fuska ya shafi sajensa yana sake duban yadda Aslaf ya
~ kafe Yumnah da idanu kamar mai son fahimtar wani abu. “Ni zan koma gida, tunda na sami abinda nake so. Haka kuma Umma tana gida takan so in zo mu zauna muna ‘yar hira.�
Aslaf ya mike yana cewa, “Yumnah babu abinda zai sa in Karo maki kishiya, saboda matan yanzu ba a Kwankwasa su bare ka gane ta gari. Kada in zo in auro wacce za ta raba ni da ke, ta raba ni da ‘ya’yana. Kin ga kuwa mutuwa zan yi, tunda ku ne rayuwata.� .
Sultan ya jinjina kai ya ce, “Kai dai kawai ayi addu’a. Da Umma za ta bar ni sai na dauke Nasreen daga gidana, in sauya mata wani gidan. Idan basu ganin juna komai zai zo da sauKi.� Aslaf ya dubi Sultan ya ce, “Ahaf! Ni tausayinka nake ji duk ranar da Umma tasan cewar ka zuga anyi mata kishiya. A wannan ranar sai ka gwammace baka fito duniyar ba.�
Sultan ya yi murmushi, “Kasan Kara auren kamawa take yi, yanzu hankalin mahaifina da na danginsa duk sun kwanta. Abbana ya yi Kiba ya ci gaba da harkokinsa kamar kowa. Duk da har kullum yana yawan yi min maganar Umma, Abba yana son Umma Aslaf, amma Umma ta
kasa gane hakan. Ni insha Allahu ma ranar da za ta san da wannan labarin tuni bana Kasar, ina can _ ina neman lafiyar idanun matata.�
Cikin raha suka rako shi suna ‘yar hira atsakani. Aslaf ya tabbatar masa da zai zo ya gaida Umma.
Da isarsa gida ya sami Nasreen ce kadai a falo tana goge-goge. Saura Kiris wata kwalba ta fado mata, ya Karasa cikin sauri ya rike kwalbar tare da sauya mata wuri. Ransa ya kai matuKa abaci don haka ya ce, “Ke! Waye ya sa ki wannan aikin? Iyye Nace wa ya sanya ki aikin nan?� Nasreen ta yi shiru saboda wani irin tsoronsa da take ji, ga shi dama dazu ta gama kukan rashin Nawfal dinta a kusa da ita, da yana nan duk irin ayyukan nan zai iya amsa yayi Ga masu aiki nan birjik a gida, amma Umma ta tsani ta ganta a zaune yanzu za ta hau Kirkirar aiki tana sanyata. Ita ba gani take yi ba..Ta Kone a hannunta, don haka bata son ya guni ta dunKule jikinta, duk da . irin azaban da hannun yake yi mata. Da Karfi ya � daka mata tsawan da yasa ta daya hannunta har ya ci nasarar ganin Konewar da ta yi. Shiru ya yi yana duban hannun, hakan yasa hawayen � fuskarta Samiun daman ci gaba da sauka. Yana da
6/10/22, 10:23 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 3🦚*
CHAPTER 7
*BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO*
MUN TSAYA
Da isarsa gida ya sami Nasreen ce kadai a falo tana goge-goge. Saura Kiris wata kwalba ta fado mata, ya Karasa cikin sauri ya rike kwalbar tare da sauya mata wuri. Ransa ya kai matuKa abaci don haka ya ce, “Ke! Waye ya sa ki wannan aikin? Iyye Nace wa ya sanya ki aikin nan?� Nasreen ta yi shiru saboda wani irin tsoronsa da take ji, ga shi dama dazu ta gama kukan rashin Nawfal dinta a kusa da ita, da yana nan duk irin ayyukan nan zai iya amsa yayi Ga masu aiki nan birjik a gida, amma Umma ta tsani ta ganta a zaune yanzu za ta hau Kirkirar aiki tana sanyata. Ita ba gani take yi ba..Ta Kone a hannunta, don haka bata son ya guni ta dunKule jikinta, duk da . irin azaban da hannun yake yi mata. Da Karfi ya � daka mata tsawan da yasa ta daya hannunta har ya ci nasarar ganin Konewar da ta yi. Shiru ya yi yana duban hannun, hakan yasa hawayen � fuskarta Samiun daman ci gaba da sauka. Yana da
ZAMU TASHI
tabbacin Watarana sai sun kashe masa ita sannan hankalin su zai kWanta. Sakin hannun yayi yana sake dubanta cikin tausayawa ko wanene yayi masa hakan bai kyauta masa ba.
Umma ce ta fito tana fadin, “ihun da kake yi na menene? Babu yadda ba ayi da yarinyar nan ba, ta bari ga masu aiki nan amma ta ki amincewa: Shi ne ta Kone� amma bata haKura ba. Duk nan babu wanda zai tsaya wai sai ya lallaba Nasreen, domin ta fi kowa sanin abinda ya kamata da wanda bai kamata ba.� Ran Sultan ya sake baci, kawai ya rufe ta da fada, “Na gaji da lamarinki Nasreen, na kusan daukarki in mayar da ke gurin Abba. Me zai sa ke ba gani kike yi ba ki ce wai dole sai kin yi ayyukan nan, ina kika taba ganin hakan? Kinsan Allah nan gaba kika sake yin rashin hankalin nan. dukan tsiya zan yi maki.�
Farin ciki ya kama Umma yana kallonta da gefen idanu yadda take murmushin mugunta. Nasrecn kuwa kuka sosai take yi. Ga zafin Kuna � ga zafin sharrin da Umma ta yi muta, ga kuma zatin kalaman Sultan akanta. Kuka tayi sosai har da shessheka. Umma ta ce, “Oh ji gulma. Ke shi kenan babu wanda ya isa ya yi maki dada sai ki kama kuka? Duk kai ka lalata yarinyar nan Wallahi.�
Sultan dai bai ce komai ba, sai kamo hannun Nasreen da ya yi yana cewa, ‘Mu je insa maki magani a ciwon. Idan kin gadama ki yi kukan jini ma bai dameni ba, jikinki ne ke kike jin zafin ba ni ba.� Sultan ya kama hannun Nasreen suka shiga cikin dakinsa, a lokacin su Hafsat suka fito suna KyalKyatar dariya, har da tafawa. Sultan yana shiga dakinsa ya mayar da Kofa ya rufe, ya maidota jikin Kofar ya rungumeta tsam yana mayar da ajiyar zuciya. Sai a wannan lokacin ta tsagaita da kukan, itama ajiyar zuciyar ce ta Kwace mata da Karfi. Cikin natsuwarsa yake magana, “Sorry Wife. Ciwon nan da kika ji ya gigitani matuKa. Bana son dai-dai da sauro ya cizar min fatan nan naki. Ban yarda ke kika kai kanki wajen wuta ba. So gaya min me ya faru?� Nasreen ta sake sanya . marainiyar kuka, ita ta san ta tabbata marainiya. Bubbuga bayanta yake yi, daga bisani ya rabata da jikinsa ya dubeta yadda take kukan, yasa hannu ya dauke hawayen fuskarta sannan ya Sake mayar da ita kafadarsa, “Bana son kukan nan Nasreen, idan kina irin wannan kukan zuciyata tana Kuna ina jin kamar ina cutar da ke, idan hakanne kina sane da sai Allah ya kama ni? Ki yi hakuri ki natsu.� Ta daina kukan amma hawayen nan kamar ruwan famfo. Hannunta ya kama ya dawo da ita kan gado ya zaunar yana sake dubanta. “‘Nasreen naso a ce kina iya ganina da kin ga irin tashin hankalin da nake ciki, duk da haka za ki iya fahimtar yanayin da nake a ciki idan kika taba zuciyata da ke Jullue a cikin Kirjina.� Hannunta ya tura a daidai saitin zuciyarsa, tana iya jin yadda yake bugawa da Karfi. Jikinta ya yi sanyi ta yada kanta a fadarsa, ya ci gaba da cewa, “Idan nayi maki fada a gaban Umma, ba wai nayi da gaske bane, a’a nayi ne domin su yi zaton bana sonki, yin hakanne kadai zai rage maki wahalar da Umma take shirin baki a cikin gidan nan. Ina jin daci idan na zo na sami fuskarki ba yadda na barki ba, ina jin ciwo idan naga kina aikin da bai kamata a ce kina yin sa ba. Gara in yi maki fada a gaban jama’a in shigo daki in lallashe ki. Soyayyar da nake yi maki ta yi yawan da bana iya boyeta a gaban kowa, shiyasa na nemawa kaina Control.�
Nasreen har yanzu bata yi magana ba, amma kuma tausayin Kanta da na mijinta yana sake kama ta. Bata san a nan gaba me kuma zai faru ba. A hankali ta yi magana, “Ka yarda da ni Dee? Ka amince ba zan taba ha’intarka ba? Ka yarda da tarbiyya irin naka
Sultan ya sake dauke hawayen fuskarta yana dubanta, “Idan har za ki iya aika ta
idan kika ji zafi za ki kiyaye sake Kona min fatan jikin ki.�
Nasrecn tana murmushi tana daga kanta alamun ta amince. A gadon ya mayar da ita ta kwanta, ya hada kansu wuri guda ya dan bata fake, ta shafi kumatunta tana murmushi, “Idan irin wannan horon shi ne horo, lallai kullum zan dinga aikata laifuka masu tarin yawa don in sami horo mai sanyi daga gun Dee.� Shi ma murmushin yake yi, yana son ganinta cikin nishadi.Mikewa ya yi da nufin dauko abu, kawai ya ji anbanko Kofar dakin , babu Sallama. Ya mance shaf bai sa key a Kofar ba. Zuba wa Hafsat idanu yayi yana jin ransa yana Kuna. Ta yaya za a koyawa budurwa shiga dakin matar aure babu Sallama? Idan ta taso a hakan watarana za ta yi hakan a in da bai kamata ba. Ita kuwa Nasreen tsoron Karar Kofar da ta ji yasa ta maKale jikinta. Sultan ya kafe ta da
-idanunsa da suka rine saboda bacin rai,
“Ina jin ki wani uzurin gareki kika shigo min daki babu Sallama?� Kame-kame ta kama yi, ta rasa me Za ta ce, sai kawai ta juya da nufin fice wa daga dakin. Sultan ya fincikota ta dawo, ya hada kanta da bango wanda yasa ta saki razanannan Kara. Tuni ya rufe Kofarsa ya murza dan makulli. Ya je ya dauko Belt dinsa ya dinga shimfida mata a jiki. Ihun Hafsat kawai ake ji, a ya yin da Umma da Zakiyya suke ta buga Kofar, Umma tana masifa tana cewa idan bai bude Kofar ba, sai ta tsine masa, amma ina Sultan baya ma jin abinda take cewa. Nasfeen kuwa kuka take yi da iya Karfinta tana roKonsa, sai dai itama baya _ sauraren muryarta. Dole ta tashi tana lalube, Hafsat tana . ganin hakan ta fahimci so take ta taimaketa, don haka ta koma bayan Nasreen tana kuka tana roKonsa, idanunsa sun rufe baya gane komai, domin yana ji a ransa da ta zo ta same su a wani yanayi bai san irin kunyar da zai ji ba. Haka yana da tabbacin sai ta gayawa mahaifiyarsa.
Nasreen tana KoKarin kareta, Sultan yasa hannu ya fizgo Nasreen ya watsar da ita gefe, hakan yasa ta fadi akan hannunta har hannun ya yi wani irin Kara. Nasreen ta fasa ihu, ta zube a wurin. Hakan ya jawo hankalin Sultan akan abinda zuciyarsa ta jawo masa ya aikata. Cikin tashin hankali ya Karasa wurinta, yana jijjigata. Abinda bai sani ba, tuni hannun ya gurde, idan ba karaya ba, gocewan Kashi.
Hafsat kuwa sauri ta yi ta bude Kofar ta fada jikin Umma da suka gaji da bugun Kofar, � suka tsaya jigun-jigun. Kuka take yi sosai saboda duk ta gigice. Ga jini ta gefen bakinta, haka jikinta duk ya farfashe saboda duka. Umma ta zura kanta cikin dakin nasa, sai dai a yadda suka ga Nasreen yasa kowa ya tsaya kallon ikon Allah. Sultan gaba daya ya fita hayyacinsa girgiza ta kawai yake yi, yana shafar kanta, amma babu ko alamun motsi.
Cak ya dauketa da nufin kaita asibiti, Umma ta Harare shi ta ce, “Gidan uban wa za ka kaita? Maza ajiyeta babu ida za ka je da ita. Al shi mai zuciya Karshensa danasani ne. Mayar da ita. Ke Zakiyya samo ruwa a watsa mata. Yadda Hafsat ta sha wahala ita ma sai ta dandani wahalar nan. In banda ka raina ni, saboda ina zaune a gidanka shi ne za ka tasa Kanwarka da irin wannan duka kamar ka sami jaka? � Kawai Umma ta sa kuka. Hankalin Sultan ya sake tashi ganin mahaifiyarsa tana zubar masa da hawaye. Dole ya mayar da ita ya shimfide ya karbi ruwan da Zakiyya ta kawo yana shafa mata a hankali. Dago kansa ya yi yana son rokon mahaifiyarsa ta yi hakuri ta bari a kaita asibiti,
sai dai dukka sun watse babu kowa akansa. Mayar da idanunsa ya sake yi kan Nasreen, ya rasa me ke masa dadi. Ganin tana motsi ya sa ya saki ajiyar zuciya da Karfi, “Nasreen ki yi hakuri ki tashi, ban san lokacin da na aikata maki hakan ba. Bai kamata ina daki da matata, Kanwata ta fado dakin babu Sallama ba, idan ‘na barta haka za ta ci gaba, har ta zo watarana ta aikata hakan a in da za ta yi danasani. Ki yi haKwri Nasreen.� KoKarin tashi take yi ta ji hannunta ya riKe wani azaba ya ziyarci Kwakwalwarta, ta fasa Kara. Da sauri ya mayar da ita ya kwantar yana shafar gashin kanta, “Nasreen kin fadi akan hannunki akwai matsala a ‘hannun, ki bari zan kira mai dori yanzu ya zo ya duba ki. Ina tunanin karyewa kika yi, yadda hannun ya saki.�
Nasreen ta mayar da kanta ta kwanta, sannan ta yi magana a hankali, “Allah ya rubuto sai hakan ya faru. Ka daina tayar da hankalinka Dee, babu wanda ya isa ya kauce wa faruwan hakan.� Tana magana tana cije wa saboda tsananin azaba. Bai iya furta komai ba, ya mike ya bar ta a nan yana tafe yana sake waiwayo ta. A falo ya sami Umma tana ba Hafsat taimako. Bai dube su ba, ya yi waje abinsa, hakan ya sake Kona wa Umma rai. Yana fito wa ya tashi dan sanda daya ya tura shi ya zo da mai dori a duba Nasreen. Yana dawowa ya sake wuce su Umma ya nufi gun Nasreen, domin har yanzu ji yake kamar