Showing 96001 words to 99000 words out of 123375 words
Chapter 33 - RUBUTACCIYA BOOK 1-2-3-4 Complete Document by Fatima Dan Barno.txt
wuri ba, sai a buge da watsa na doki a tsakiyar ka?� Gaba daya sun fahimce ta, tana nufin Attachment din da ke kanta. Musulima ta yi saurin karbe zancen, “Akwai abin tausayi, musamman yadda Uwale ke manna kashin kaza mai kwanci a dai-dai Kasan na shanu.� Sun fahimceta, kashin kaza mai kwanci wari ne da shi, tana nufin Kasan mamanta ba a wanke wa, musamman yadda suka zube kamar wacce ta shayar, ta tabbata akwai wari a ciki, Dukkansu suka yi murmushi. Za su ci gaba da magana, Nasreen ta shigo tana cewa, “Don Allah duk wacce ta gama ta zuba min, Dee yana ta tambayar ba a gama bane? Nima kuma ina da buKata.�
Zakiyya ta shaKo wuyan rigarta, tana huci, “Ke kika gaya wa ‘yan gidan nan sirrin cikin gidan nan ko? Yau sai na kakkarya ki idan ya so daga can sai a duba lafiyar Kafar.�
Jidda ta juyo a fusace tana dauraye hannunta, Yumnah ta riqe rigarta. Hakan yasa ta! waiwayo tana duban Yumnah. Dole ta sakar mata hannu.
Tasleem da sauran gaba daya suka isa har gabanta suna dubanta. “Idan kika taba ta, babu shakka sai naki Kafafun sun karye.�
Nasreen ta yi murmushi ta ce, “Sakar min kwalar riga, bansan me yasa idan baki yi haushi ba, bakya jin dadi. Na fada maki Zakiyya ke karya ce, wacce kullum take haushi a titi ana
korarta da dutse. Kin Kware a dambe da wulakanta dan adam, kin ce miji na bar maki abinki, shi ne yanzu duk bai yi maki ba sai kin tozartani a gaban jama’a? Kin ji kunya Wallahi, kin yi girman banza! Kina nan kina dariya duniya tana can tana zaginki. Yabawar duniya tana taimakawa har zuwa makwancinki. Kin fitar da halinki kin jawowa kanki. Duk yadda miji ke sonki idan kin kasance daga fitinannu kin zama koma baya a wurinsa, wannan ba sai na gaya maki ba, nasan kin san hakan.�
Sau tari idan Zakiyya tana rigima da Nasreen, kaifin kalamanta kawai take tsoro, domin duk ranar da ta gaya mata magana kwana take babu barci. Jidda ta samu ta Karaso ta fizgo Zakiyya daga irin riKon da ta yi wa Nasreen ta waska mata mari mai tsananin zafi. Ta hankada ta baya. “Ki je ki gayawa duk wanda ya daure maki gindi ni Jidda Junaid na mareki.�
Zakiyya ta fita da ihu tana fadin ankasheta. Su kuma suka ci gaba da aikin su. Kowa zuciyarsa babu dadi. Ita kuwa Zakiyya kai tsaye falon ta shiga ta sami Sultan da su. Al-ameen
suna tattaunawa. Zakiyya ta shigo tana kuka ta zayyana masa komai.
Sultan bai ji dadi ba, amma saboda kawaici ya ce, “Ke kika jawo. Kuma babu yadda za ayi Jidda ta mareki haka kawai dole da abinda kika yi
Al-ameen da ransa ya yi matuKar baci ya dubi Zakiyya, “Kiyi hakuri Zakiyya zan dauki mataki akanta.�
Zakiyya ta juya tana kuka, Al-ameen ya mike yana huci. Sultan yace’menene haka? Don Allah zauna kada ka bata mata rai, ta ce ta fasa raka mu. Ka san dai halin Jidda.�
Al-ameen ya koma ya zauna bai ce komai ba. Suna nan har su Jidda suka fito da abincin da ( suka girka suna shirya falon. Jidda da kanta ta ~ kaiwa Umma komai sai albarka take sa masu. Tana shigo wa, Zakiyya ta leKo tana son ganin irin hukuncin da zai yanke a kan Jidda. Za ta fice yasa hannu ya fizgota ta fada jikinsa, ta zaro idanu sosai, “Me na yi maka don Allah?�
Ta fada tana me zura idanunta a cikin nasa, sai da ta tabbatar da ta ci nasara sannan ta zame kanta tana dubansa. Da Kyar ya ce, “Wai me Zakiyya ta yi maki kika mare ta? Ba ki jin magana ko?�
Kanta ta dora a kafadarsa tana magana cikin natsuwa. “Ba haka bane shigowa ta yi na ganta duk datti, sai na gaya mata idan Kazanta ce bata kaini ba, nayi mata maganganu, shi ne da shigowar Nasreen ta shake ta, wai sai ta yi mata dukan da idan muka fita waje sai dai ayi aiki biyu. Ni kuma da naga taki sakinta na dora mata tafi.� Ta Karasa maganar da dago kanta ta dan shafi fuskarsa ta ce, “Ka ji abinda ya faru.�
Dukka dakin suka yi ajiyar zuciya. Sultan kuwa jikinsa ne ya yi sanyi ya ce, “Matar da ke dauke da juna biyu menene nata na cewa za ta yi dambe?�
Yumnah ta juyo tana dubansa, “Waye ke da cikin? Ba dai Zakiyya ba?�
Ya gyada kai yana dubanta, “Zakiyya dai.� Ba ta sake magana ba, suka shirya masu komai._—_Jirgin yamma za su bi don. haka kowa ya gama shiryawa, sai a lokacin idanun Nasreen ya fara kawo Kwalla. Naufal ya Karaso kusa da ita yana magana Kasa-Kasa, “Nasreen kada kiyi kuka idanunki za ki taimakawa.
Ta gyada kanta. Motocin masu dauke da sunan dukkan littafan da suka fito a ciki, sune a jere a hanya za su nufi Airport. Da Kyar Umma ta yi masu addu’a ita kuwa Zakiyya dakinta ta shige abinta. Hafsat ce ma ta raka su har wurin mota. Haka su Al-ameen suka wuce da Sultan wanda bai gayawa kowa zai yi rakiya zuwa Lagos ba. Da isowarsu ke da wuya suka nufi masauki domin sai gobe za su wuce London din. Nasreen bata shiga huldan Sultan ba, sai ma ware kanta da ta yi ita da Naufal ta bar Jidda da ke maKale da mijinta. Sultan ya fahimci akwai + wani abu a zuciyar Nasreen tunda ya ga tana gudunsa.
Gajiya ya yi ya Karaso wurin su hannunsa rike da power Horse da shansa ya zame masa jiki. “Hutawa kuke yi, kuka ware Dee dinku?�
Nasreen ta dan yi yaKe, Naufal ya dube shi yana dariya, “Dee mun barka ne kaima ka huta.� Idanun Sultan suna manne akan Nasreen. Dubanta ya sake yi ya ce. “Nasreen babu abinda ke damun ki?�
Bata yi magana ba, sai daga kanta da ta yi. A tsakiyar su ya zauna suna dan taba hira da Naufal. Kiran Abba ya shigo wayarsa ya dauka
yana fadin gata Abba. Ya sawa Nasreen wayar a kunne.
Tana dauka ta gaida Abba cikin natsuwa. Abba ya ce, “‘Nasreen na sanki da Addu’a ki sake dagewa, mu ma nan muna nan muna yi insha Allahu za ayi aikin cikin nasara. Allah ya kaiku lafiya.� Muryarta tana rawa hawaye suna zuba take godiya. Sultan ya karbi wayar ya fice yana magana. Naufal ya dubi Nasreen cikin takaici ya ce, “Na ga Deedinmu yana maki magana kina sharewa ne? Me yake damunki?�
Nasreen ta ce, “Naufal ina ta son insami dama in gaya maka. Dee yana KarKashin ikon Zakiyya ne a yanzu, ba ya kula ni baya zuwa in da nake. Umma ta yi min, Zakiyya ta yi min, shima kuma baya tausayina., Ka fada min me zan yi? Na gaji da wannan abin.� Naufal ya dube ta ya ce, ““Haba Nasreen, ke da ya kamata kiyi masa addu’a? Ki daina fushin nan tunda tafiya za ki yi mai nisa, ko me Deedi zai yi ya fi Karfin wulakanci daga garemu, mu zama masu tuna alkhairi ba sharri ba. Ki dauka ya isa ya aikata komai na cin mutunci akanki, ba tare da kin ji kin gundura ba. Idan yana ganinki a
cikin damuwa shi ma zai damu, don dai baki gani ne da kin ga yadda yanzu fuskarsa ta sauya a lokacin da yake kallonki.�
Bata ce komai ba, ta yi shiru kamar marainiya. Zuwa can suka je suka ci abinci kowa ya gabatar da Sallah, sannan suka yanke shawarar zuwa wani park mai kyau domin baiwa idanunsu abinci.
Al-ameen yana kula da yanayin da Sultan da Nasreen suke ciki, don haka ya jawo Naufal da Jidda suka nausa wani wurin. Nasreen ta ji ankamo hannunta, ta gane hannun Sultan ne don haka ta saki ajiyar zuciya ya kamota suka zauna a wani wuri. Kwantar da kanta ta yi a kafadarta ta yi shiru. Bai dubeta ba ya fara magana, “‘Babyna fushi kike yi da ni? Ki yi hakuri babu wanda ya taba yin hakuri a Karshe ya tabe. Mai haKuri shike da nasara.�
Nasreen ta sake narkewa a jikinsa, tana jin nasihar Naufal tana ratsa ta. “Babu abinda kayi min mijina, idan da akwai shi ma na yafe maka duniya da lahira. Ba ka ba ni kudi ba, amma ka gina min rayuwata wanda a yanzu kudi bai isa ya siya ba. Ka bani kulawa. Da gaske nake yi na yafe maka dukkan abinda kay min da ma wanda za ka yi min anan gaba.
Sumba ya yi mata a tsakiyar kanta sannan ya shafa kan. “Na gode Nasreen. Ki dAina kuma cewa nayi maki abubuwa, idan kina fadan hakan sai in yi tunanin kamar ba dolena bane yi maki wadannan abubuwan. Ki dauka ya zama dole in yi maki kin ji?�
Shiru suka dan yi sannan ya ce, “Gobe za ku tafi ku bar ni. Zan yi kewarki sosai.� Murmushi ne manne a fuskarta, “Babu wata damuwa tunda muna kwana mu tashi baka ganni ba, baka j1 muryata ba, don haka wannan tafiyar ba za ta daga maka hankali ba, insha Allahu zamu je lafiya mu dawo lafiya.�
Ya gane abinda take nufi, da yake bai da abin kare kansa sai ya yi shiru. Can ya ce, ; “Nasreen akwai abinda kike� son ki yi min * magana akai, idan kika bude baki sai ki fasa. Gaya min mene ne?�
“Babu komai, Dama so nake inrokeka ranar da za a bude idanuna idan aikin ya yi kyau ina son ka zama mutum na farko da zan dora idanuna akansa. Kai kadai nake so ka zama
mutum na farko, Naufal zai zama na biyunka insha Allahu. Ka yi min wannan alKawarin.�
Shiru ya yi yana tuna ayyuka ne a gabansa ba na wasa ba, amma yana jin ba zai iya ce mata a’a ba a irin halin da take ciki, don haka ya ce, “Babu damuwa, zanyi iya bakin kokarina inyi hakan ya faru. Na gode da kika zabeni a cikin mutane na farko da zan hada idanu da ke. Wannan karramawar ba zan taba mance ta ba. Ina sonki Nasrcen, soyayyarki tana ilata ni a duk lokacin da ban ganki ba. Nasreen baki gani ne da sai kin tabbatar da raman da na yi. Zakiyya ta zame mani masifa, idan ban yi abinda tace ba, ji nake kamar an zuba min karara.��
Nasreen ta ce, “Kullum sai na yi maka maganar ibada, amma sai kayi fatali da maganata, ka nesanta kanka da Allah shiyasa wannan abubuwan suke ta faruwa da kai. Kadage da addu’a ka yaki duk mai nufinka da ; sharri.� Ya ce, “Babu komai zan sake dagewa, idan zan je Masallacin sai in ji kamar ansa igtyoyi andaure ni.� Suka sake yin shiru, can yace “Barci nake ji ko za ki raka ni?� Bata karga mayana ba, wayarsa ta dauki kara. Ganin lambar Umma yasa ya dauka, “Gidan uban wa kaje? Ashe da kai za a tafi lagos din shi ne bani da mutuncin da zaka gaya min?� Sultan ya shafi kansa kamar tana ganinsa ya ce, “Umma ki yi hakuri don Allah, gobe insha Allahu zan dawo.� Umma ta ce, “Ya yi maka kyau Sallamammai. Saura ka takura mata tunda kana sane aiki za ayi mata.� Umma ta fada haka cike da damuwa da addu’ar kada Sultan ya aikata wani kuskure da zai hada jininta da shegu. Sultan ya dubi Nasreen yana sauke wayar, yasan ta ji dukkan abubuwan da Umma take gaya masa, sai ya share kawai
Da daddare kowannen su suna dakin su, Nasreen tana kwance a Kafafun Sultan yana aika sako ta Email dinsa. Bayan ya gama ne ya daga ta ya shiga bandaki ya watsa ruwa ya fito, itamia ta shiga tayi wanka da ruwan da ya tara mata ta nufi ‘yar Jakarta ta shafa man Kamshin da ya karbo mata daga shagon Jafar, ta shafe jikinta. Kamshin yasa ya dago yana dubanta da Katon Hijabi a jikinta. Murmushi ya Kwace masa, gaba daya ya fara mance sakon me yake aikawa
6/29/22, 12:36 - Ummi Tandama😇: RUBUTACCIYA BOOK 4
CHAPTER 3
BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
MUN TSAYA
Nasreen ta ce, “Kullum sai na yi maka maganar ibada, amma sai kayi fatali da maganata, ka nesanta kanka da Allah shiyasa wannan abubuwan suke ta faruwa da kai. Kadage da addu’a ka yaki duk mai nufinka da ; sharri.� Ya ce, “Babu komai zan sake dagewa, idan zan je Masallacin sai in ji kamar ansa igtyoyi andaure ni.� Suka sake yin shiru, can yace “Barci nake ji ko za ki raka ni?� Bata karga mayana ba, wayarsa ta dauki kara. Ganin lambar Umma yasa ya dauka, “Gidan uban wa kaje? Ashe da kai za a tafi lagos din shi ne bani da mutuncin da zaka gaya min?� Sultan ya shafi kansa kamar tana ganinsa ya ce, “Umma ki yi hakuri don Allah, gobe insha Allahu zan dawo.� Umma ta ce, “Ya yi maka kyau Sallamammai. Saura ka takura mata tunda kana sane aiki za ayi mata.� Umma ta fada haka cike da damuwa da addu’ar kada Sultan ya aikata wani kuskure da zai hada jininta da shegu. Sultan ya dubi Nasreen yana sauke wayar, yasan ta ji dukkan abubuwan da Umma take gaya masa, sai ya share kawai
Da daddare kowannen su suna dakin su, Nasreen tana kwance a Kafafun Sultan yana aika sako ta Email dinsa. Bayan ya gama ne ya daga ta ya shiga bandaki ya watsa ruwa ya fito, itamia ta shiga tayi wanka da ruwan da ya tara mata ta nufi ‘yar Jakarta ta shafa man Kamshin da ya karbo mata daga shagon Jafar, ta shafe jikinta. Kamshin yasa ya dago yana dubanta da Katon Hijabi a jikinta. Murmushi ya Kwace masa, gaba daya ya fara mance sakon me yake aikawa
ZAMU TASHI
cikin wayarsa? Da kansa ya tako ya jawo ta � gabadaya jikinsa tayi luf’a Kirjinsa. “Babyna ina son Kamshin nan, idan naji rikitani yake yi.� Yana magana ne yuna aika mata sakonni. Ita kanta Wasu maganganu take yi wanda bata san kansu ba. Kai tsaye suka yi wa kansu makwanci a faffadan gadon suna jin wata natsuwa tana shigarsu. Da gaske sun yi kewar juna, Sultan ji yake kamar ya yi shekara rabonsa da ita. A hankali ya yi mata magana a kunne, “Baby kinyi kewata?� Ba ta yi magana ba, sai daga kanta da tayi yace, “Ok nuna min irin kewata da kika yi sai in yarda Kunya ta sa ta cusa kanta a Kirjinsa tana ‘yar dariya, a lokaci guda tana zakuda kafada alamun ba za ta iya ba. Washegari
bayan sun karya ne suka hau shiri babu ji babu gani. Ita dai Nusreen gani take yi kamar ma ba za ta sake dawowa ba, kamar ta tafi kenan. Da suka isa filin jirgi ne idanunta suka kawo hawaye, yasa hannu ya dauke su, ya kamo kafadanta, “Me yasaki kuka? Ko baki gaji
jiya bane insake mayar da ke gado in yi maki abinda yafi hakan? Kwanciya ta yi a jikinsa tana murmushi mai hade da hawaye, tana girgiza kai, sannan ta sa dan yatsanta ta ce, “A’a kai ne bana son intafi in barka. Ka kula min da amanar kanka, ka ci gaba da yi wa Umma biyayya. Daga Karshe ka kiyayi shiga hakkin Allah. Allah ya dafa maka a dukkan lamuranka na alkhairi, ya nesantaka da dukkan wani sharni. Addu‘ar iyaye tana tare da kai, bana tunanin ze ka tabe“Ina son ka Dee, na san kasan hakan kuma zaka ci gaba da riKe hakan a zuciyarka, ko bayan raina. Sai watarana.� Ta Karashe muryarta tana rawa. . Hannunta ya kama dukka biyun yana duban su masu kyau da haske. Ya manna masu kiss � wanda har sassanyar yatsunsa suka sauka abisa hannun. Ta ji sanyi har cikin zuciyarta, hakan ya haifar mata da sakin ajiyar zuciya a bayyane. “I love you too, Baby Girl.� Bata iya sake yin magana ba, ta juya abinta, tana jin wasu hawaye sabbi suna sauka daga idanunta. Naufal ya Karaso ya rungume Sultan, ya ce “Ka cika dukkan sharuddan kasancewarka Uba. Allah ya biyaka da gidan Aljannah, ya sakawa dukkan mutanen da suka yi sanadin tafiyar ‘yar uwata.
Ba zan manta wannan abun ba. Mum gode Father.�
Ya sake rungume shi hawayensa suna ci gaba da sauka a jikin Sultan. Gaba daya jikin Sultan ya muta ya rasa meke masa dadi? Ya yi Karfin halin dago shi yana duba shi, tare da share masa hawayensa, “to maza azo a wuce saura kaje kana yi masu Kauyanci don nasa a daukar min dukkan abinda ke faruwa acan. Kai ga mai “yar uwa ko? Maza wuce kada a tafi a barka kukanka ya fara, dan wannan kukan ta gulma ce.� Naufal ya yi dariya shima. Alameen ya Karaso a jokacin da Jidda take rike da Nasreen. Suka mikawa juna hanno suka gaitsa tare da rungume yuna. Sultan� ya fara magana cikin damuwa, “Prince ba ni da abinda zan ce sai Allah ya biyaka. Kayi min dukkan abinda wani dan uwanka ma ba zai iya yi maka ba. Kun nuna min Kauna tunda kuka nunawa Nasreen. Kasan komai ba sai na sake tunatar da kai ba, ka kula min da Nasreen. Na gode da wannan sadaukarwar.� Al-ameen ya yi murmushi, “Ba wannan ne a gabanmu ba, samun lafiyar idanunta sune babban matsalolin mu. Idan kana gode mana sai muga kamar bamu cika sharuddan zama ‘yan uwa ba. Ka dinga cin abinci sosai Abdullah, domin ka rame da yawa, ya kamata Nasreen ta bude idanunta ta ganka kafi da cika da kwanciyar ‘Rankali. Ka bar damuwa da Zakiyya idan ba haka ba, za ta iya kasheka ba tare da ta yi asara
ba.� Sakin juna suka yi yana tabbatar masa zai yi abinda ya ce masa. Ba ya son yin Sallama_ da Jidda don haka ya ce wa Al-amecn, “Ka fayawa ‘yar Kauyen matarka, saura ta je can ta ga turawa ta manne masu tana cewa, ‘yan uwan mamanta ne, ko kuma ta ga mutum ta yi zaton gunki ne tana shafa fuskarta.� Al-ameen ya yi murmushi yana ccwa, “Wallahi ka ci bashi za kuma ka biya shi.� Haka suka tafi jirginsu ya daga, Sultan