Showing 12001 words to 15000 words out of 123375 words
Chapter 5 - RUBUTACCIYA BOOK 1-2-3-4 Complete Document by Fatima Dan Barno.txt
Nawfal ta ce su je falon. Nawfal ya kafe Umma da idanu da ta rike Abba tana kuka tana fadin sai ya saketa ta bar masa gidansa, ba za ta iya ba. Ya sa danta ya rainata, yanzu kuma saboda a nuna mata iyakanta aka yi masa aure. Ta nemi a gaya mata wacece matar idan da hali a nuna mata hotonta amma yaki kallonta, don haka ita za ta bar masa gidansa. Haidar ne ya shigo yana duban mahaifiyarsu shi da Hafsat suka Banbare hannunta da Kyar Abba ya samu yana KoKarin ficewa daga gidan yana fadi a ransa zai yi maganinta. Kawai suka ci karo da Alhaji Mu’azzam! Kallon kallo suka aikawa juna sannan Abba ya dawo da baya suka gaisa babu yabo babu fallasa. Alhaji Mu’azzam. ya gyara zaman babbar rigarsa ya ce, “Anya Alhaji Lukman babu abinda ke damunka? Me yasa kake son mayar da kanka Karamin yaro ne? wanda bashi da ra’ayin kansa? Ta ya ya za ka yi wa Sultan aure wanda mu nan da muke dangin mahaifiyarsa bamu sani ba? Ko kana nufin bamu da hakki akansa ne? Akan ‘ya’yan zina kake son Sauya tsarin gidanka? To idan aure babu albarkar uwa auren nan bai dauru ba.� Abba ya yi saurin bashi amsa, “A fatawarka ba! Amma ni ne uban yaro kuma na aurar da shi ga diyar da ta dace. Zina kuma babu mai tabbacin wane yana aikata zina, sai idan yana da shaidu, kawo shaidun kuma akwai wahala. Ina yiwa kowa kyakkyawan zato. Kowa a duniyar nan yana da tarin matsala akansa, idan baka zina, kana shan giya, idan baka shan giya kana caca, idan baka aikata dukkan laifukan nan kana aikata mummunar laifi wanda yafi muni, wato shirka, hada Allah da wani. Ban ga dalilin da za ka dinga bin diddigin wani dole sai ka gano laifinsa ba. Kowa ya ji da tarin matsalarsa. Hajiya Salma kuma ta bi bayanka zan zo da abinda take buKkata, matar Sultan kuma bata isa ta santa ba, har sai ta tare, bare ta zagaya ta kashe masa auren. Ruwanku ne Hafsat da Haidar subi bayanta, sai dai ku sani irin naku rashin hankalin yafi kama da na uwar da ta haifeku, don haka binta zai fi burgeni fiye da zamanku a nan.� Ya sa kai ya fice a fusace. Nasreen tasa kuka, wanda ya jawo hankalin Alhaji Mu’azzam kansu. Wani irin faduwar gaba ya tsinci kansa da shi wanda bai taba jin irinsa ba. Bai taba ganin yaran ba, saboda irin tsanar da ya yi masu, sai yau da ya hada idanu da su. Bakinsa ya mutu murus, dole ya nemi wuri ya zauna, yana kallon yadda Hajiya Salma take kuka, Duk wanda ya san meke faruwa zai gane kukan korarta da Alhaji ya yi take yi. “Salma ki yi haKuri ki share hawayenki, ki zauna da ‘ya’yanki, Kada ki yarda akan ‘yar Karamar matsala ki baro dakin mijinki. Ni zan san matakin dauka haka zan lalubo inji wacce yarinya ce ya aura ma danki, Ki kwanter da hankalinki.�
6/5/22, 10:27 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 1🦚*
CHAPTER 5
*BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO*
A JIYA MUN TSAYA
Ruwanku ne Hafsat da Haidar subi bayanta, sai dai ku sani irin naku rashin hankalin yafi kama da na uwar da ta haifeku, don haka binta zai fi burgeni fiye da zamanku a nan.� Ya sa kai ya fice a fusace. Nasreen tasa kuka, wanda ya jawo hankalin Alhaji Mu’azzam kansu. Wani irin faduwar gaba ya tsinci kansa da shi wanda bai taba jin irinsa ba. Bai taba ganin yaran ba, saboda irin tsanar da ya yi masu, sai yau da ya hada idanu da su. Bakinsa ya mutu murus, dole ya nemi wuri ya zauna, yana kallon yadda Hajiya Salma take kuka, Duk wanda ya san meke faruwa zai gane kukan korarta da Alhaji ya yi take yi. “Salma ki yi haKuri ki share hawayenki, ki zauna da ‘ya’yanki, Kada ki yarda akan ‘yar Karamar matsala ki baro dakin mijinki. Ni zan san matakin dauka haka zan lalubo inji wacce yarinya ce ya aura ma danki, Ki kwanter da hankalinki.�
ZAMU TASHI
Daman ko bai ce ba, Hajiya Salma ba za ta iya tafiya ko nan da can ba. Don haka suka yi Sallama ya fice. Nasreen ta sa sandarta a Kasa tana KoKarin ficewa tun kafin fushinta ya sauka akansu. Nawfal ya rike mata sandar suka fice. Yau Sultan ya dawo garin, yana shaKar iskar garin Kaduna ya ji wata natsuwa tana shigarsa. Yana farin ciki yau zai ga twins dinsa. Mota tana yin parking a lokacin mahaifinsa ya fito zai fice. Farin ciki ya kama mahaifinsa, duk da sai da gabansa ya fadi. Rungume juna suka yi cike da farin ciki, haka yana nan a tsaye yana amsa gaisuwar ma’aikatan gidan. Daga nesa ya hangota fuskar nan dauke da farin ciki, tana rike da
sandarta tana laluben hanya. Nawfal ya Karaso wurinta ya rike mata sandar yana cewa, “Idan na gadama insakar maki sandar inrigaki zuwa inyi masa oyoyo. Nasreen ta yi dariya, ta ce, “Ai nasan ba za ka yi min haka ba.� Sultan yana magana da mahaifinsa ya kasa Karasa abinda yake fada ya kafeta da ido babu ko kiftawa. Ya rasa wannan wani irin wasan kwaikwayo ne haka? Abbansa yabi inda yake kallo.da kallo, ba tare da ya furta komai ba. Nasreen tana Karasowa ta saki sandar ta ce, “Didina ka kama hannuna intabbatar da kai ne.� Sultan ya kasa yin motsi sai kallonta kawai yake yi. A zatonsa wasa take yi, amma yanzu ya tabbatar da babu wasa a lamarin nan. Nawfal ya kama hannun Sultan yana cewa, “Didi sannu da zuwa. Na riga wata yarinya rike hannun Didi.� � Nasreen ta saki dariya ta ce, “Babu damuwa zan rama watarana.� A lokacin ta sami daman rike hannunsa kawai ta rungume shi. Hawaye suna sauka daga idanunta zuwa bayansa. Yana jin digar hawayen hakan yasa ya dan rintse idanu ya ware su da Karfin gaske. A lokacin ne Hafsat da Haidar suka fito. “Sannu da zuwa Yaya.� Su kansu bai amsa masu “ba, hakan yasa suka tsaya suna duban yadda ya yi kamar wanda ya mutu a tsaye. Da gaske ya rasa me zai ce, wacce tambaya ya kamata ya fara yi, kuma idan zai yi din wa zai wa? “Abba Nasreen ta daina gani ne?� Wannan ‘tambayar ce ta Kwace masa da karfin gaske ta : fizzo kanta ta samu ta fito. Abba ya girgiza kai, “Nasreen bata ganin komai. Kaddara ce ta Ssameta, muna fatan mu samu mu cinye. Ku zo mu shiga ciki.� Hannunsa daya yasa ya dan shafi bayanta kafin ya dagota daga kwancen da take, yasa hannu ya dauke mata hawayen idanunta, sannan ya riKe hannunta suka shiga ciki Har yanzu jikinsa a sanyaye yake haka ya kasa gazgata abinda ya gani. Dakinsa ya shiga ya kintsa sannan ya fito falon ya iso har gaban mahaifiyarsa ya duka ya gaidata. Ita kanta Hajiya Salma ta sani, kaf cikin ‘ya’yanta babu mai biyayyar Sultan, sai dai wani ra’ayi nata da yasa take jin haushin abinda yake aikatawa. A hargitse ya yi maganar da yasa kowa yake kallonsa, “Abba ashe ba zan iya barin amana a rike min ba? Waye zai aikatawa Nasreen irin wannan mugun abun? Nasreen ta makance amma ba a taba gaya min ba? Ko waye ya aikata mata wannan abun ba zan taba daga masa Kafafu ba.� Ya ajiye maganar ba yadda ya kamata ba. Nasreen ta Karaso tana lalube har ta iso gabansa, “Dee, wanda ya aikata min hakan ya fi kowa sanin dalilin da yasa ya yi min. Kuma ni na yafe ma wanda ya yi hakan, Kada bakin ciki yasa ka furta wasu kalaman da suka cika yin nauyi. Kayi haKuri kamar yadda Abba ya ce min inkarbi Kaddarata haka kaima ya kamata kayi. Ni bana jin damuwa, ina gode wa Allah a yadda ya � bar ni. Idan kuma kace za ka dauki mataki bansan wurin wa za ka je daukar matakin ba, domin nima bansan wanda ya aikata min hakan ba.� Sultan ya dubeta yana jin zuciyarsa tana yi masa wani zafi. Yana kallon manyan idanun nan masu tsari yau sunée a rufe bata gani da su. “Nasreen zan yi bincike zan kuma dauki mataki kamar yadda na fada. Bincike biyu ke gabana kuma Insha Allahu duk sai na aikata su. Duk wanda ya aikata maki hakan babu ko shakka zai iya yin kisan kai.� Hajiya Salma ta yi maza ta tari numfashinta, domin Sultan gaf yake da zageta, “A’a ya isheni haka. Idan ka tashi yin binciken sai ka hado da ubanka domin shima a gidan ya kwana, ko kuma duk ka kama mu ka rufe har sai ka gama binciken. Idan za ka wuce kaje ka ci abincinka ka wuce, idan kuma tsayawa za ka yi ka samu a gaba kana yi mana tambayoyin rainin hankali Bismillah.� Sultan ya duKar da kansa-ba tare da ya iya furta komai ba. Abbansa ya dafa shi, “Sultan, ka yi haKuri, kullum da Nasreen nake kwana da ita nake tashi a zuciyata. Na rasa gano wanda ya yi wannan aikin. Ka je kayi bincikenka, nima idan na kama wanda ya aikata min wannan aikin insha Allahu zan tsaya sai naga anhukunta shi, ko wanene kuwa. Haka kaima ka dauki mataki, tunda a lokacin da za ka fara aiki, sai da kayi alkawarin tsayawa akan gaskiyarka, ko da kuwa ni mahaifinka ni ka kama da irin wannan laifin, don Allah ka dauki mataki kada ka ragawa mutum. Idan kayi hakan zan san dana ya tabbata a cikin dan sandan mai amana da gaskiya. Allah ya yi maka albarka. Zan � bayyana maka matarka da zarar ta kammala Makarantarta, wanda bana jin za ta dauki lokaci, domin tana shekararta ta Karshe ne. Tashi kaje ka ci abincin.� Sultan ya dan sami natsuwa da kalaman mahaifinsa, kafin ya tashi Nasreen ta fara tashi, tana lalube saura Kiris ta fadi ya Kwala mata kira, “Nasreen! Tsaya.�� Babu musu ta tsaya ya Karaso ya kama mata sandar suka fice. Hankalin Hajiya Salma idan ya yi dubu to ya tashi, Sai taga kamar da Nasreen ta makancen sai abin yafi sake yin muni, Hankalinta ya Kara tashi ne da Hajiya Ladidi ta tabbatar mata, tunda anyiwa danta aure, to Alhajin ne da kansa zai auri Nasreen din, domin kuwa shi namiji bashi da kunya. Zai reni abu ya kuma aureta. Hauka ne kawai Hajiya Salma ba ta yi ba, domin ita ta kasance mace mai zafin kishi, akan Alhaji Lukman za. ta iya kashe rai. Sultan ya tashi hankalinta Kwarai akan maganar binciken da ya ce, zai yi domin kuwa kallonsa take yi a matsayin mayen ‘yan sanda. A _ dalilin Kwarewarsa yasa ake ta Kara masa girma. Dole ta yi yunkurin daukar mataki akan abubuwan nan tun kafin tana ji tana gani danta ya garkameta a Police Station ‘yan jaridu su sami daman watsata a duniya. Haidar ta aika ya kirawo mata Sultan yana shigowa ta dube shi sosai. “Kana jina? Idan na sake jin ka sami ‘yan aiki kana yi masu bincike ko Kannanka ban yafe maka ba. Nasreen wani Kato ya shigo ya rufe mata baki ba mu ji ba, ya yi mata wannan abin. Kai baka yarda da Kaddara ne? Kai ka sani ko mugayen da suka kashe mahaifiyarta ne suka gane akwai yaran a gidan nan? Ni shi ya sa tun farko ban so rikon su ya zamana a nan ba. Bana son kaje garin tone-tonenka ka jawo mana masifa har cikin gida.� Sultan ya zubawa mahaifiyarsa idanu kamar mai son gano wani abu. Hankalinta ya Kara tashi ta ce, “Laaahh! Ni kake kallo haka kamar ka sami barauniya? To tashi ka wuce na gama magana. Bai ce komai ba, bai kuma tashin ba. Can ya nisa ya ce, “Umma wai har cikin dakinta aka shiga aka aikata hakan duk baku sani ba? A lokacin kina…� A zafafe ta ce, “Ina dakin ubanka ne a lokacin. Ingama ce maka ka bar maganar nan amma kuma saboda tsaurin idanu za ka koma yi min tambayoyi? Sultan wai yaushe ka sauya ne? . Zuwan yaran nan rayuwarka sun sauya mun dana. Yauwa Sultan wai wacece matarka? Na yi bincike sosai antabbatar min ba ‘yar gidan Alhaji Mamman ba ce. Anya ya kamata ka amshi auren nan kuwa? Bana son yazo baka yi sa’ar mata ba, dan nuna min ita ko a hoto ne.� A lokaci guda bayan ta gama masifar ta yi Kasa da muryarta kamar mai rada. Sultan da ya gaji da tsugunnon da yake, ya jawo wata ‘yar kujera ya zauna yana fuskantar mahaifiyarsa, bayan ya dauki dabino | daya ya Sa a bakinsa. “Umma ban santa ba, ban taba ganinta ba, ban san sunanta ba, haka ban san ko ‘yar gidan waye ba. Kasan da ta tafi karatun ma ban san shi ba. Kawai abinda nake buKata addu’a Umma. Idan kika yi min hakan kin gama yi min komai. Kuma insha Ailehu zanyi maku biyayya wajen karbar zabinku.� Umma ta Harare shi, “Wajen karbar zabin mahaifinka ko kuma zabina? Ni zabin da na ‘baka ka karba ne? Ina son ka bude kunnunwanka da kyau ka ji ni. Ka je ka sami mahaifinka kace sai ya hadaka da matarka ko gaisawa ce ku dinga _ yi. Ya zama dole musan wacece da me za ta shigo gidan. Idan ba ta yi ba, sai ka botsare masa ka saketa kawai ta kama gabanta.� Muryar Abba suka ji yana magana, “Allah kadai zai iya shiryaki Salma. A duk ranar da shawararki ta yi tasiri a zuciyar danki ina tabbatar maki sai kin yi mugun danasani. Ba zan bayar da hoton ba, bazan kuma hada su ba, har sai lokacin da na gadamar yin hakan. Kai Sultan zo ka wuce.� Babu musu ya mike ya fice abinsa yana al’ajabin mahaifiyarsa. Ita kuwa hajiya Salma dubansa ta yi ta ce, “Ka dai san babu kyau labe ko? Babu daman inzanta da dana sai ka hau masifa?� Dubanta ya yi ya ce, “Labe? Waye dan naki? Yaron da kika ware shi a_cikin ‘yan’uwansa kika jawo masu rashin shaKuwa da juna? Ai da wannan kadai idan na bar ki Salma sai Allah ya hukuntaki.� Bai tsaya saurarenta ba ya sa kai ya fice abinsa. Sultan yana nan ‘tsaye, bayan ya tabbatarwa mai tsaronsa ya wuce kawai ga shi nan zuwa. Yana nan a tsaye yana kallon tsakar gidan. Hafsat ta fito da wani dutse ta ajiye a hanya ta koma ciki. Ba ta kula da shi ba, haka shima bai kula da abinda hakan ke nufi ba, domin kuwa tunaninsa ya yi nisa. Nasreen ta fito tana lalube sai kawai ta ci tuntube da Katon dutsen nan ta fadi a wurin.Sultan ya zaro idanu a lokaci guda kuma Hafsat ta fito daga maboyarta tana kwasar dariya. Zata wuce kenan ta ji anfinciko ta. A razane ta dago tana hada idanu da yayanta ta tsure, “Yaya me nayi?� Dau! Ya dauke ta da mari, daman kuma hannunsa babu kyau, a take fuskar ta kumbure ~ ta yi jazir, abinka da farar mace. Ya sake daga hannu ya yi ta kwada mata. Sannan ya watsar da ita. A gujen gaske ta yi cikin gida, domin wannan shi ne karo na biyu da ya taba dukanta a duniya, kuma duk akan mutum daya. Karasowa ya yi inda Nasreen din ke zaune ta yi shiru kawal. Yasa hannu ya kamota suka koma inuwa suka zauna. Yana jin dadin Kare mata kallo, baya gajiya da hakan. Ciwon da ta dan ji yake dubawa, bayan ya kama hannunta. A hankah yake shafar ciwon wanda yake sanya mata wata kasala, tana sake lullumshe idanunta, labbanta kamar za ta yi © magana, amman hakan ya gagara. Yanayin da ta shiga yasa mamaki ya kama shi, tambayar kansa yake ko dai ba Nasreen ba ce? Irin yanayin nan masoya kadai ke iya kasancewa a cikinta. Dayan hannunta tasa ta rike hannunsa tana girgiza kai, “Dee.. Na daina jin zafin yanzu.� Murmushi kawai yaji, kafin kuma muryar Umma ta wargaza masu yanayin da suke ciki. “Sultan! Yanzu akan yarinyar nan za ka yi wa Hafsat irin dukan nan? Ba ka da hankali ne ko mene ne haka?� Sultan ya yi magana kamar baya son yl, “Umma idan kannena suka yi laifi babu daman in hukunta su kenan?. Haba Umma meyasa zaki wareni daban a cikin ‘yan uwana? Laifi ta yi na hukuntata. � Ta yi Kwafa kamar za ta kai masa duka, “Ita ta kusa da kai ba ta laifi ne ko me? Kada ka sake dukar min yara na gaya maka.� Bai bata amsa ba haka bata daina masifar ba, har sai da ta gaji ta juya abinta. Shi kuma ya kamo hannun Nasreen suka shiga mota. Wani wuri ya kaita © mai dauke da sanyi irin na korama. Tana zama ta shaki irin Kamshin da wurin yake yi, ta ce, “Deedina ina jin wani irin yanayi mai dadi a jikina. Dee da ba ka nan na yi ta kewar ka, amma kuma ina yi maka addu’a.� Sai da ya zauna bayan ya gama kallonta sannan ya ce, “Nima nayi kewarku ke da Nawfal kamar insa a kawo min ku, sai nayi tunanin karatun ku. Nasreen zaki iya tuna wanda ya watsa maki abu a idanu?� Hawaye suka gangaro fuskarta kamar daman tana jira ne, “Deena bansan waye ba. Ka bar maganar nan abinda Allah ya aiko kenan.� Jawota ya yi ta kwantar luf a Kirjinsa tana sakin Wani irin ajiyar zuciya. Hakan ya haifar da abubuwa masu girma da wahalar fassarawa a tsakanin su. Sultan kenan! Kowa kallonsa yake miskili mara son hayaniya, haka alamu sun nuna idan ya kama mai laifi baya sarara masu. Idan ka ganshi tare da Nasreen za ka iya rantsuwa ba Sultan dan sanda bane. A kunnenta