Showing 66001 words to 69000 words out of 123375 words

Chapter 23 - RUBUTACCIYA BOOK 1-2-3-4 Complete Document by Fatima Dan Barno.txt

da akayi, a take kishin babu gaira babu dalili ya kamata, haka ta kasa tashi ta basu wuri. Gani take da zarar ta je ko nan da kitchen ne za a yi wani abun. Shi kuwa idanunsa Kyar a kan tv, wanda a zahiri ba tvn yake kallo ba, Nasreen yake kallo ba tare da Zakiyya ta ankare ba. Ya dube ta cike da Kosawa ya ce, “Tashi ki je ki hada min ruwan wanka.� Zakiyya ta dube shi sosai, ta fahimci yana


son raina mata hankali ne, domin bai taba sanyata tara masa ruwan wanka ba. Zamanta ta gyara tana hamma, “To zan tara maka zuwa anjima yanzu na gaji da yawa ne.�


Nasreen ta mike, “Deedi ina ne hanyar dakina?� Shima ya mike yace “Zakiyya, dama kin san sashenki. Ita kuma bari in kaita nata falon da kuma dakinta, wannan babban zai zama nan ne mahadinmu tunda falona ne.�


Zakiyya ta saki baki tana kallonsa. Kafin ya kama Nasreen har Zakiyya ta kamo ta tana fadin, “Mu je sashen naki daga nan in gani.�


Babu musu ta bi bayanta Sultan ya yi shiru yana nazarin matakin da ya kamata ya dauka don ba zai yarda da wannan iskancin ba. Haka ya taka Kafafunsa bai bi su ba ya shige bandaki ya watsa ruwa. Ya fito yana tsane jikinsa, Zakiyya ta shigo tana dubansa. “Na kai ta dakinta bangarenta gaskiya ya fi yi min kyau sosai.�


Ko dubanta bai yi ba ya ce, “Bayan mun je wurin Abba da ya ganta ya tambaye ni kayan dakinta na ce masa na siya maku iri daya ya ce ai alhakin siya mata kaya yana wuyansa ne, shi ya bada izinin aka kwashe irin nakin na zuba su a dakin baki, shi kuma ya sa aka shimfida mata wanda ya bada kudi aka siyo. Don haka idan basu yi maki ba, sai ki gayawa Hajiyarki ta siya maki wasu.�


Baki a sake take kallonsa, yadda ya soka mata magana ya kuma daure fuska. “Kana nufin gori kake yi min kenan? Na gode Allah ina da uba, kowa yasan ubana ba haihuwar titi ba ce.� Sultan ya juyo cikin tashin hankali, ya daga hannu ya wanke fuskarta da mari, yana dubanta, “Na san za ki iya yin karambanin nan, amma ba zan dauka ba. Wallahi duk ranar da kika kuskure kika yiwa Nasreen irin wannan gorin har ta ji, sai kin sha mamakin irin matakin da zan dauka a kanki. Ban auro Nasreen domin inkawota ki ce za ki taka ta, da haukan da ke kanki ba. Ubana shi ne uban Nasreen, zan bugi Kirji infadawa duniya hakan. Babu wanda zai sheganta min ~ mata in zuba idanu ina kallonsa, babu. Yadda kike taKamar namiji ya yi cikinki aka kawo ki gidan duniya, haka Nasreen ma za ta bugi Kirji ta ce namiji ne sanadiyyar kawo ta duniya ba mace ita kadai ba. Fice min a daki.�


Jikinta na kyarma, hannunta a fuskarta ta fice. Tsoro da firgici suka shige ta, ba ta taba ganinsa a cikin bacin rai irin na yau ba. Ta fahimci yana iya yin Kasa-Kasa da ita. Tana shiga daki ta rufe Kofa ta shaki kukanta. Can ta wanke


fuska ta fito domin tana tunanin Kila yana can wurin Nasreen.


A falonsa ta same shi, bai je gun Nasreen din ba, sakamakon Kuncin da kalaman Zakiyya suka sanya shi. Yana nan kwance ya ji Sallama


_ don haka ya daga kai ya ga ko waye. Mamaki shimfide a fuskarsa yake duban mahaifiyarsa. “Umma? Me ya faru kuma? Lafiya? Ina Abba?�


Gaba daya ya rude yana tunanin ko wata matsalar ce ta sami Abbansa shi ne har ta taso ta ZO.


Umman ta harare shi sannan ta shigo tana ~ bayar da umarnin inda za a ajiye mata Katon akwatinta. “Lafiyar ta kawo haka. Zuwa na yi ni ma in huta in yi kwana biyu, mahaifinka ya karbe office dinsa, don haka zan zauna a nan in sami hutu sosai. Hafsat ta dan durKusa tana gaida Sultan


Shi kuwa mamaki da bakin ciki sun taru sun hana shi sakat. Duban Hafsat ya yi ya ce, “Yanzu fa muka taho muka bar ku a Kaduna. Ke Hafsat makarantar kuma fa?� Hafsat ta ce, “Ai sun yi hutu.�


Kan Sultan ya sake daurewa bai fahimci dalilin da zai sa mahaifiyarsa ta yi wannan abin


ba, bayan ta san mahaifinsa bai da wata mata idan ba ita ba. “Amma Umma shi Abban da wa kuka bar shi a gidan?�


Umma ta ja tsaki ta nemi wuri ta zauna tana fadin, “Wash!� Tta gaji.


Sultan ya sake maimaita mata tambayar ransa a bace. Umma ta zazzaro idanu, “To zo ka dake ni ubana! Ko kuma kawai ka ce min in bar gidanka sai in san na haifi dan da ya gagare ni. Kana kallon yadda kake yi min magana kamar ubana? Ban sani ba! Ka je ka gaya masa ya Kara aure mana tunda na ga kaine ubanmu daga ni har shi! Ban bar shi da kowa ba, sai ka nemo masa mace ka sa masa a cikin gidan. Shashashan yaro kawai mara kishin kansa. Ke dauki kayan nan ki kai min dakin Nasreen a nan zan sauka.�


Zakiyya da farin ciki ya gama kashce ta, ta kwashi kayan ita da Hafsat suka nufi dakin Nasreen. Tana zaune bisa dadduma tana lazimi, sai kawai ta ji shigowar mutane babu sallama, mamaki yasa take tambayar ko su waye.


Zakiyya da Hafsat ba su yi magana ba har sai da suka dire kayan sannan suka dawo gabanta, “‘Umma ce da Hafsat suka zo, za su yi


kwana biyu, shi ne muka ajiye kayan a dakinki don a nan za su sauka.�


Nasreen ta Kara cika da mamaki, don haka tace ‘“Wacce Umma kuma? Haba ba dai Umma ba, yaushe muka tafi muka barta a gida? Ko ba Umman Kaduna kike nufi ba?� Zakiyya da Hafsat suka yi ta mata dakuwa da hannu suna yi mata gwalo, sannan ta bata amsa, “Mence ne na yi min irin wannan tambayar? Ko dai in koma in ce mata kin ce a kwashe kayanta ne? In ba haka kike nufi ba meye na dogon magana?��


Nasreen ta yi murmushi ta ce, “Babu wanda ya isa ya hana Umma zama a duk inda ta gadama. Kuma ni farin ciki nayi da har ta � tsallake dakin kowa ta zabi dakina. Ina yi mata barka da zuwa. Ga ni nan fitowa.� Duk suka bita da kallo, sannan suka fito suna cewa Umma Nasrcen sai tambayoyi take yi masu.


Ran Umma ya sake baci ta zabura za ta shiga dakin Sultan ya mike ya sha gabanta. “Don girman Allah Umma kiyi hakuri.�


Umma ta dawo ta zauna tana dubansa duba na takaici. Sultan ya mike ransa a Bace ya fice ya kira mahaifinsa, “Abba meke faruwa ne na ga Umma? Ko wani abu ya hada ku ne?�


Abba da yake zaune a tsakar gida ya yi tagumi, idanunsa jazir saboda bacin rai, ya ce *Wallahi ban sani ba. Bayan kun tafi kawai naga tana shiri ban ce mata komai ba, har sai da suka gama kintsa kayansu sannan ta gaya min wai gidanka za taje Duk yadda nayi domin ta ajiye tafiyar amma taki. Na_ gaji da lamarin mahaifiyarka sakinta zanyi.� Sultan ya ji babu dadi, haka ya ji tausayin mahaifinsa, amma fadin sakin nan yasa gaba daya Karfin guiwarsa ya suki. Baya Kaunar dalilin da za ace mahaifiyarsa bata tare da auren mahaifinsa. Don haka ya ce, “A’a Abba ka yi hakuri kada ka yi min haka. Abba mu ‘ya’yanka ba za mu taba son a ce wai babu mahaifiyarmu a gidan mahaifinmu_ ba. Shawara daya zan ba ka Abba, ka duba a cikin mata masu hankali da natsuwa ka aura.�


Abba ya dan yi shiru cikin dogon tunani. Daga bisani ya ce, “Sultan ni wa na sani da zan aura? Ka barni kawai inzauna ni dayan babu komai watarana sai labari.�


Girgiza kai Sultan ya yi cike da tausayin mahaifinsa, “Abba ka auri Mairo mai aikinmu, naga tana da hankali da natsuwa. Yin hakan Kila


ya sanya Umma ta dawo hayyacinta.


A zuciyar Abba ba ya son wata “ya mace . da ta wuce matarsa, Haka ba shi da ra’ayin Kara aure, amma halin masifa irin na Salma ya saya amince da abinda yaron ya gaya masa, don haka suka sa ranar da Sultan zaije a yi magana. Yana datse Wayar ya rintse idanu yana jin tausayin mahaifinsa da gaske.


Nasreen da ta jima tsaye tayi magana cikin muryar kuka, “Deedi da bakinka kake cewa ayi wa Umma kishiya? Me yasa ba za a lallaba ta ta koma ba? Ina jin tsoron abinda zai je ya dawo.�


Sultan ya mayar da idanunsa kan. makauniyarsa ya ce, “Nasreen na gaji da halin Umma. Idan aka yi mata kishiyar Kila za ta _ sauya. Amma kishiya kam dole sai Abba ya yi mata.


Nusreen taci gaba da cewa, “Kishiya ba ita bace mafita kayi tunani da kyau.�


Sultan ya karaso gabanta yana_ son Nasreen fiye da tunanin mutum, “Nasreen ki bar wannan maganar na rufe ta. Ya aka yi kika zo nan?�


Ajiyar zuciya ya Kwace masa. Mai aiki ta saita ni har inda kaKake. Su Umma suna


ciki suna cin abincin da dan sanda ya kawo. Yanzu kana ganin haka zamu zauna ana siya mana abinci? Ni ba idanu gareni ba bare in shiga kitchen.�


Sultan ya ce, “Wallahi ni kaina abinda ke damuna kenan. Yanzu ya zaa yi?�


_ Sai da ta jingina da bango kafin ta ce, “Ina ganin a shawara, ka sanya a nemo mana mai aiki wacce ta Kwarai a iya ayyukan abinci sai mu mayar da ita mai girkinmu. Amma ya ka gani?�


Sai da ya lakaci hancinta sannan ya ce, *‘Abinda kika ce shi za a yi. Wannan ma shawara ce mai kyau. Yanzu kin gane dalilin da yasa Umma ta sauka a dakinki?� Girgiza kai ta yi cike da rashin fahimta, : “Wallahi ban gane komai ba.� : Nan da nan fuskarsa ta nuna bacin rai, “Umma ta zo garin nan ne saboda ba ta son mu _ kadaice ni da ke. Na rasa irin wannan abinda Umma take yi.� Nasreen ta yi murmushi, “In dai haka ne ai ni ta taimaka. Allah ya Karawa Umma lafiya.� Mamaki yasa ya murde hannunta ya ce, “Maimaita abinda kika ce. Ni kuma tunda kika
6/10/22, 09:45 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 3🦚*






CHAPTER 4




*BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO*





MUN TSAYA


Nusreen taci gaba da cewa, “Kishiya ba ita bace mafita kayi tunani da kyau.�


Sultan ya karaso gabanta yana_ son Nasreen fiye da tunanin mutum, “Nasreen ki bar wannan maganar na rufe ta. Ya aka yi kika zo nan?�


Ajiyar zuciya ya Kwace masa. Mai aiki ta saita ni har inda kaKake. Su Umma suna


ciki suna cin abincin da dan sanda ya kawo. Yanzu kana ganin haka zamu zauna ana siya mana abinci? Ni ba idanu gareni ba bare in shiga kitchen.�


Sultan ya ce, “Wallahi ni kaina abinda ke damuna kenan. Yanzu ya zaa yi?�


_ Sai da ta jingina da bango kafin ta ce, “Ina ganin a shawara, ka sanya a nemo mana mai aiki wacce ta Kwarai a iya ayyukan abinci sai mu mayar da ita mai girkinmu. Amma ya ka gani?�


Sai da ya lakaci hancinta sannan ya ce, *‘Abinda kika ce shi za a yi. Wannan ma shawara ce mai kyau. Yanzu kin gane dalilin da yasa Umma ta sauka a dakinki?� Girgiza kai ta yi cike da rashin fahimta, : “Wallahi ban gane komai ba.� : Nan da nan fuskarsa ta nuna bacin rai, “Umma ta zo garin nan ne saboda ba ta son mu _ kadaice ni da ke. Na rasa irin wannan abinda Umma take yi.� Nasreen ta yi murmushi, “In dai haka ne ai ni ta taimaka. Allah ya Karawa Umma lafiya.� Mamaki yasa ya murde hannunta ya ce, “Maimaita abinda kika ce. Ni kuma tunda kika


ZAMU TASHI


fada hakan a gabanta zan dinga daukarki in wuce dakina da ke.�


Tana Kyalkyatar dariya ta ce, “Wallahi na yarda.�


Shi ma murmushin kawai ya yi suka ci gaba da ‘yar hirarsu. Da suka gaji ne ya kama hannunta ya saita ta a kan hanya sannan ya tsaya yana kallon ta har ta shige, shi kuma ya fice Zuwa gidan Ashmaan. Ba shi ya dawo ba sai dare, abin mamaki har yanzu suna nan zaunea a falon wai suna kallo. Sai da ya dan saci kallon Nasreen baiwar Allah barci take yi a zaune.




Ya dubi Umma ya ce, “Umma ku tashi ku ~ je ku kwanta dare ya yi.�� Umma ta tashi tana hamma ta bubbugi Nasreen ta tashi tana magagi, ta kamo hannunta ta juyo tana duban Sultan. “To sai da safe, ina ganin kamar Zakiyya ta yi barci ka tasheta.� Dama tuni Hafsat ta shige abinta. Takaici da bakin ciki suka hana shi sakat ya bi su da kallo kawai har suka shige. Gyara zamansa ya yi a falon, daman shi bai ce zai yi wa Nasreen komai ba, yana jiran har sai ta sami lafiyar idanu, ta yadda yana kallon kyawawan idanunta, tana kallonsa. Amma yana da buKatar kwana kusa da matarsa. Zakiyya ta tashi kamar tana magagi wanda a zahiri idanunta biyu, “Muje mu kwanta.� Ya dubeta cike da bakin ciki, “Kwananki ne? Ina zaton sai Nasreen ta yi kwanaki bakwai dinta kafin ma a raba girki? Ki je dakin ki taho min da ita.�


Zakiyya ta dube shi shekeKe da alamun har ta mance irin marin da ya yi mata dazu ta ce, “Wallahi ba zan je ba. Ni lokacin nawa ai ba wata ta kirawo ni ba, ni na kai kaina da kaina. Kuma ina zaton ko za ka yi kwanakinka ai sai ka jira Umma ta tafi ko? Ko kuwa a gabanta za ta dinga tsallake Umman tana zuwa wurin miji?� Shikam Sultan kansa ciwo yake yi, amma duk da hakan sai da ya ba Zakiyya amsarta, “Kin ga bambancin Zakiyya da Nasreen ko? Kin kawo kanki wurin miji ba tare da ya neme ki ba, babu aji ko kadan, dole miji ya dinga yi maki kallon wacce bata kai ba, ita kuma saboda kunya ba za ta iya kawo kanta wajen miji ba. Ina gaya maki ki dinga sanin irin maganar da za ki gaya min, idan ba haka ba jikinki ne zai dinga gaya maki, daga Karshe ki bar min gida, domin ba ayi yarinyar da zan auro ta zo har cikin gidana tana gaya min abinda ranta ke so ba, ya zama dole ki koyi ladabin magana.� Ya shige dakinsa yasa dan makulli.


Zakiyya ta je ta taso Umma tana gaya mata tana kuka. Nasrcmeen dai tana kwance a gado tana jin su tayi shiru, da farko tana zaton Sultan hasashe yake yi akan abinda Umma take nufi, a yanzu kuma ta fahimci da gaske Umma take yi ta shirya rabata da Sultan. Hawaye kawai ke sauka a idanunta, domin a zahirin gaskiya tana buKatar ko babu abinda zai hadata da Sultan ta kwana a gefensa suna hirarsu da baya gundurarta. Umma ta fito tana kwankwasa Kofar Sultan, kamar ba zai bude ba, jin muryar Umma yasa ya bude fuskarsa babu ko alamun fara’a.


Umma ta dubi Zakiyya ta ce, “Maza shiga gun mijinki. Me yasa ka rufe Kofa ka bar matarka?� Kamar ya ce mata wancan ba matarsa ba ce? Sai kuma ya share kawai. Ya bar Kofar a bude ya shige. Zakiyya ta kutsa kai. Da taga ba zai bata hadin kai ba, sai ta koma ta sanya wannan turaren ta dawo. Babu shiri ya amince ya aikata abinda take so ba tare da natsuwar zuciyarsa ba, Warin nan nata yana nan har yanzu babu canji. Ganin ta kwanta tana shirgar barci


yasa ya bubbugeta yace sai ta tashi ta je ta yi wanka, sannan zai kwanta gado daya da ita. Bayan ya fito wankan tana kallonsa ya zauna gaban madubi ya matso wannan turarcn ya matso wancan. Sai da ya tabbatar da Kamshinsa ya saje ko ina na jikinsa sannan ya saki ajiyar zuciya. Ya koma ya haye gado, tunanin Nasrcen kawai yake yi. Kwanaki biyar a tsakani Sultan ya shirya yaje aka daura auren Abba, wanda shi ya bayar da sadaki akayi komai. Hajiya Gwaggo ta ji dadin wannan auren don haka ta hada su ta yi � masu fada. Mairo mace ce mai alkunya da kawaici, . haka ansha wahala matuka kafin Mairo ta amince da auren da take ganin tsabar cin amana ne ta auri mijin uwar dakinta. Ita kuwa Umma ta kafe ta tsare, ta hana Sultan Karasowa kusa da matarsa. Shi kuwa iya haKurinsa ya kai Karshe don haka yau ya yi rantsuwa sai ya san yadda zai yi ya shaki Kamshin matarsa. Yana shigowa falon ya same su gaba daya suna kallo ya duba ko ina babu Nasreen, don haka ya mike ya kama hanyar dakinsa. Zakiyya ta shigo ta sami har ya fara barci don haka ta koma suka ci gaba da hirar su.


A hankali ya fito babu wanda ya ankare da shi ya shige sashen Nasreen, Tana _tsaye hannunta dauke da turaren wuta da mai aikinta ta kawo mata tana turara dakin. A hankali ya shigo kawai ya tsaya yana kallonta.


Ga mamakinsa sai yaga tana murmushi, har ya sha jinin jikinsa ko dai idanunta sun bude ne? “Barka da shigowa Deena. Nayi matukar kewarka ta yadda baki ba zai iya fadin iya adadin kewar ba.�


Sultan ya ce, “Oh ya akayi kika san na shigo?� Sai da tasa bakinta ta hura masa hayakin � turaren sannan ta bashi amsa, “Ashe dai ba gaskiya ba ne da ake cewa idan har jini ya hadu wuri guda rabuwarsu abu ne mai matuKar wahala? Ina da tabbacin idan jini ya hadu bin ilahirin jiki yake yi yana kaiwa da komowa alamun ya riga ya hade da dukkan sauran jinin da ke jikinka. Ka ga kuwa mai iya raba wannan jinin sai ya zo da shiri ba na wasa ba.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login