Showing 81001 words to 84000 words out of 123375 words

Chapter 28 - RUBUTACCIYA BOOK 1-2-3-4 Complete Document by Fatima Dan Barno.txt

yadda kika ci nasarar jefa shaidan a zyciyata, Allah ya rama min. Me kike fada ne? Abban Sultan� Har abada ‘babu wanda zai danganta Abban Sultan da abinda kike fada in gasgata shi koda Kuwa Wacce ta tsuguna ta haife nine ta kirawoni tana gaya ‘min mdganar nan bazan amince ba Bare Kuma ké da kika Kware wurin‘makirci. Ta yaya ma zuciyata zata Aminta dake? ‘Yaushe� ya fara aikata masha’a bayan Shekarun da yayi a turai, inda ya hadu da mata masu jida kansu ya kaucewa sharriin su Saida ya dawo kasata� Najeriya, da girmansa, zai aikata hakan? Kuma agun mai aikina? ‘Ki dai tuna ‘abinda’Kika gan shi ‘yana aikatawa ba� abinda Zuciyarki ta Sanar dake ba� Hajiya Ladidi -tayi ‘rantsuw tana -yi_ tanta sakewa, *don haka ‘Hajiya Salma ta fara� jin zuciyarta� tana ‘rawa yar yardar data bashi ta nemi fizge abinta da Karfin tsiya jin tayi shiru yasa Hajiya Ladidi ci-gaba da’yi mata famfo,-har sai da jikinta ‘ya kama rawa‘ta datse waydr tana ‘jin ’wani irin� Kunci a ranta� ji take! har abada ba *zata iya zama da miazinaci ba haka ko ranta za,a ‘zare ba za ta iya rabuwa da� soyayyar� Alhaji Lukman’ba� da tayi mata rassa! Ta hade da jinin jikinta.“Ta -‘rasa me take ji a ranta ‘a tsakanin tsanarsa� da� tausayinsa� da “Kuma: kishinsa da � sonsa? Ta tafi ta bar shi ne saboda tana tsoron Nasreen ta ci galaba akan danta, haka kuma tana da tabbacin Sultan ba zai iya kwatanta adalci a tsakanin Zakiyya da Nasreen ba. Kankat! Ta zo nan ne domin ta sake raba Nasreen da zuri’arta. Can daki ta shige yadda babu mai iya jinta, sannan ta kira Alhaji Lukman a waya. A lokacin yana zaune tare da Mairo fuskarsa da alamun damuwa, Mairo ta yi magana cikin sanyi, “Abba me yasa za ka damu da maganar Hajiya Ladidi? Kafi kowa sanin duk a cikin zancenta babu gaskiya. Na zauna da Umma nasan halinta, nasan abinda za ta iya aikatawa nasan wanda ba za ta iya ba. Maganar mallaka kuma da take yi Karya take, ita ce ta yaudari Hajiya ta ce, akwai wani malami a cikin Alqur’ani yake ciro addu’a ya yi idan ya yi addu’ar sai ta sha mamakin irin yadda za ka koma tamkar yaron Umma. A kunnena na ji Umma tana cewa ita idan har ta tabbatar da babu kaucewa za ta iya yi, saboda kana yawan yi mata gardama akan kome ta gaya maka. Ka ji ta inda ta yi wa Umma dabara kenan, kasancewar ta san Umma ta tsani shirka. Haka maganar bin maza duk Karya ce, ina ji wasu lokutan Umman ke yi mata fada akan rayuwarta, har ma tana nuna Kyama ga Hajiya Ladidi. Don haka ka daina damuwa.� Abba ya saki ajiyar zuciya, “Lallai sun yi hakan kuma sun sami nasara akaina, ba wai don bana ibada ba, sai don Allah ya aiko min da jarabawa kuma na karbeta. Maryama ba maganar Hajiya Ladidi ya sanya ni damuwa ba, don bana jin akwai abinda za ta fada akan Salma har ya dameni, nasan wacece matata tun Kuruciya, na santa da zafafa kiyayyarta akan abinda ta furta ta ce ta tsana bata so. Kawai-ina jin damuwar yadda Salma ta yi zamanta a gidan danta ta nuna bata damu da ni ba, duk irin son da take gwada min.� Ya Karashe cikin damuwa, sai -kuma ga kiran wayarta, don haka jikinsa na rawa ya dauka, domin ji yake kamar ana Kara masa sonta. Yana yin Sallama ta kasa jurewa, sakamakon wani kishi da ya tokareta, ta fasa kuka. Iya gigicewa Alhaji Lukman ya gigice, tambayarta kawai yake waye ya mutu? Cikin kuka take cewa, “Abban Sultan yau ni za ka yi wa haka? Duk yadda na baka kulawa na hana kaina kwanciyar hankali don in kyautata maka, yau kuma dan bana nan shi ne za ka kasa jure wa har sai ka aikata Barna?
6/11/22, 17:43 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 3🦚*




CHAPTER 9




*BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO*





MUN TSAYA


Haka maganar bin maza duk Karya ce, ina ji wasu lokutan Umman ke yi mata fada akan rayuwarta, har ma tana nuna Kyama ga Hajiya Ladidi. Don haka ka daina damuwa.� Abba ya saki ajiyar zuciya, “Lallai sun yi hakan kuma sun sami nasara akaina, ba wai don bana ibada ba, sai don Allah ya aiko min da jarabawa kuma na karbeta. Maryama ba maganar Hajiya Ladidi ya sanya ni damuwa ba, don bana jin akwai abinda za ta fada akan Salma har ya dameni, nasan wacece matata tun Kuruciya, na santa da zafafa kiyayyarta akan abinda ta furta ta ce ta tsana bata so. Kawai-ina jin damuwar yadda Salma ta yi zamanta a gidan danta ta nuna bata damu da ni ba, duk irin son da take gwada min.� Ya Karashe cikin damuwa, sai -kuma ga kiran wayarta, don haka jikinsa na rawa ya dauka, domin ji yake kamar ana Kara masa sonta. Yana yin Sallama ta kasa jurewa, sakamakon wani kishi da ya tokareta, ta fasa kuka. Iya gigicewa Alhaji Lukman ya gigice, tambayarta kawai yake waye ya mutu? Cikin kuka take cewa, “Abban Sultan yau ni za ka yi wa haka? Duk yadda na baka kulawa na hana kaina kwanciyar hankali don in kyautata maka, yau kuma dan bana nan shi ne za ka kasa jure wa har sai ka aikata Barna?


ZAMU TASHI


To ya yi kyau sosai, ina tabbatar maka ba zan koma gidanka ba, sai ka bani takardata.� : Alhaji Lukman ya _ yi kasake’~ yana Saurarenta, “Me nayi maki kuma Salma? Me yasa za ki jefe ni da irin wannan kalaman?� . Ajiyar zuciya ta yi tana Kokarin share hawayenta, “Hajiya Ladidi bata kama ka da mairo ba? Bata kama ka ba? Me yasa za ka wulakanta ni a idon mai aikina? Ban ga laifin Mairo ba, laifin wanda ya bata fuska ne, amma na gama zama da mazinaci. Tsawa ya daka mata jikinsa yana rawa, “Ya isa Salma! Haba!. Me ke damunki ne? Za ki iya jifana da ko wacce kalma amma banda Kalma mafi muni da Kazanta. Har kullum ku mata Karamin tunani ke gareku, namiji zai iya kare martabarki a ko ina, ko da kuwa kin sauya, amma ku babban burinku a gaya maku zunubin mazajen ku, ku fita duniya kuna ihu kuna fadin ba a kyauta maku ba, kuna fadin a sake ku. Na ji ciwo da Salmar da nake yi wa irin wannan son ne take gaya min maganganu masu dacin nan, nayi tur da wannan halin da kika ara kika dora wa kanki. Idan aka bani AlKur’ani zan iya dafa wa matata ita ce za ta bayar da shaidan Kwarai




akaina, sai dai abin takaicin yau da raina nake jin Kazaman kalamai daga bakin wacce na mallakawa zuciyata. Gara ki ce min ba zaki dawo ba, sau dubu da ki ce min mazinaci. Ki dinga bincike kafin yanke hukunci, idan ba haka ba za ki yi ta samun matsala da jama’a da dama daga Karshe ki rabu da mutanen kirki ki kama na banza.� . Abba ya kashe wayar yana jin zuciyarsa babu dadi. Ita dai Mairo tagumi ta yi ta zuba masa idanu, tana kallon son uwargidansa a idanunsa, ita dama tasan ya dai aureta ne kawai, ba dan tana burge shi ba. Sai yanzu ta sake gazgata abinda bahaushe yake cewa, tsohuwar zuma da ita ake magani, haka duk kyan amarya da yadda take ganin mijinta yana sonta, har abada uwargidansa daban take a cikin zuciyarsa, domin kuwa ita ce Mafarinsa. Don hakane take taya duk macen da ta zama Uwargida murnar samun sarauta mai girma a zuciyar mijinta. Zuciyar Mairo ta nemi ta fara zafi, saboda wannan halittacen kishin da ke maKale a zuciyar kowacce mace, sai ta yi saurin karanta A uzubillahi. Ta kori shaidan, domin idan har ta yi kishi da matar da ta zauna a KarKashinta bata yi adalci ba. � Ba za ta iya yi masa magana a irin yanayin nan da yake ciki na halin bakin ciki ba, dole ya na buKatar zama shi daya don haka ta mike za ta fice, ya kirawo sunanta_ cikin natsuwa, “Maryama zo ki zauna.� Babu musu ta dawo ta zauna, ya dubeta cikin kulawa, “Na ga fuskarki ta sauya ina fatan ba ni bane na bata maki?� Girgiza kai ta yi, tana murmushi hakan yasa ya gyada kai, suka kuma yin shiru, domin ya rasa me zai ce mata. Ita kuwa Umma ji ta yi danasani yana shigarta, ta san halin Hajiya Ladidi ta hada fada, amma kuma ta kasa gano irin ribar da za ta ci idan har ta hada ta fada da mijinta. Zuciyarta ta kasu gida biyu, sai dai yarda da mijinta ya fi yawa a cikin zuciyarta, tana jin ta amince da shi, ba za ta taba yarda a ce wai Alhaji Lukman zai iya zama kujera daya da Mairo ba, “Lallai da sai na kasheta idan ya so nima a kasha ni.� Ta fada a sarari tana huci. Sultan da Hafsat suka dubi juna, kafin suka dawo da kallon su gun Umma. Sultan ya ce. “Wa za ki kashe Umma?� Tana ganin su ta mike sai kuma ta fara kuka, ta dubi Sultan ta ce, “Ka ji Hajiya Ladidi wai Abbanku yana neman Mairo mai aikin mu.� Gaban Sultan ya fadi, lallai yasan akwai yaki a nan gaba. Ya kasa magana sai dubanta kawai yake yi. Hafsat ta dora hannu a kai kamar wacce aka yi wa mutuwa, “Umma mun shiga uku! Kai Karya ne Abba ba zai taba duban wacce ta fi Mairo ba, bare kuma Mairo. Gidanmu cike yake da ma’aikata maza da mata, babu yadda za ayi Abba ya wulakanta kansa a cikin su. Mun bani Yaya Sultan ka kira Abba baya boye maka komai za ka ji gaskiya a bakinsa.� .
Umma ta kamo hannun Sultan suka zauna, ta ce, “Gaskiyar Hafsat ce, na kira shi yana ta min wasu maganganu wai anyi masa sharri, amma yanzu kira shi ka Kara murya sai mu ji abinda zai ce ta hakanne kadai ragowar zuciyar da bata amince da shi ba, za ta Karasa yarda da shi. Sultan na gigice da yawa, nasan halin Abbanka ba zai aikata hakan ba.� Sultan da gabansa ke fadi ya dubi Umma ya ce, “A’a Umma ba sai na kira shi ba, ni na yarda da mahaifina babu abinda zai aikata da ake zarginsa. Kawai sharri ne.�
Umma ta share hawayenta, “Eh na sani Sultan kai dai ka kira shi.� Nasreen ce ta shigo tana lalube, ran Umma ya sake baci ta daka mata tsawa, “Ke! Fice ki bamu wuri muna tattauna abinda ya shafe mu ne, ban ga dalilin shigowan bare ba.� Nasreen ta gigice sosai ta yadda har ta taba hannun da aka yi gyara, ta sake komawa da baya ta kusa faduwa, Sultan ya mije da sauri zai iso wurinta, Umma ta sake riKe hannunsa tana harararsa dole ya koma ya zauna yana dubanta. Zakiyya da har ta sawo kai ta ji irin tijarar da aka yi wa Nasreen sai ta koma gefe, ta labe tana sauraran su. Nasreen kuwa ta yi matukKar daurewa bata yi kuka ba, har sai da ta samu isa dakinta sannan ta fasa kuka mai Karfi. Gabadaya Sultan ya daina fahimtar mahaifiyarsa hankalinsa ya koma kan Nasreen, ya san cewar tana can tana kuka, don haka ne yake jin damuwa a ransa. Babu shiri ya fitar da wayarsa ya danna lambar wayar Abba gabansa yana ci gaba da fadiwa, ya tabbata idan Abba ya dauka asirinsa da na Abbansa ya gama tonuwa, yana da tabbacin tsine masa kawai za ta yi. Cikin ikon Allah aka sanar da lambar Abba 2 kahe take, hakan yasa Umma ta sake gigicewa. Sultan ya tattaro natsuwarsa sannan ya yi magana, “Ki kwantar da hankalinki Umma gobe insha Allahu zan je Kadunan za ki ji komai.� Umma ta yi hamdala ta kuma ba shi Karfin guiwar ya tafi ba tare da ya sanar masa da zuwansa ba. Da Kyar ta sallame shi yana fitowa kai tsaye dakin Nasreen ya shige ya same ta tana kuka, ya jawota jikinsa yana share mata hawaye, sannan ya rungume ta yana bubbuga bayanta, “Na taba gaya maki na tsani in ga kina kukan nan? Haba Nasreen yaushe za ki saba da halin Umma? Tana cikin bacin rai ne, maganar nan ne na Mairo aka gaya mata sai dai cewa aka yi Abba yana nemanta, kin dai san Umma da kishi shi ne yanzu duk ta tashi hankulan mu. Don Allah ki daina kukan nan.�
Nasreen ta yi luf a jikinsa, tana jin ba za ta iya magana ba, domin da gaske kalaman Umma sun yi mata ciwo, tana son sanin su waye danginta? Duk lalacin su za ta iya zama da su. Sultan ya ji duk zuciyarsa ta jagule. Ya rasa me zai ce mata, kawai sai ya kafe ta da idanunsa. A lokacin ya sami kiran gaggawa, za su fita wani aiki. Cikin gaggawa ya mike zai fita, sai kuma
ya dawo, ba zai iya barinta a cikin wannan halin ba. “Babyna ta shi ki raka ni wajen aiki. Zan siya maki babyn roba ki dinga wasa da ita.� Murmushi cikin kuka ya subuce mata. Hakan yake son gani don haka ya ji sanyi a zuciyarsa, haka yana da tabbacin zai sami natsuwa wajen fitar. Hannunta ya dauka yasa a kansa, “Yi wa mijinki addu’a zai fita gun aiki. Addu’arki za ta taimaka in je lafiya in dawo lafiya. Ki kauda damuwa a fuskarki idan kika yi haka mijinki zai kwantar da hankalinsa a cikin jama’arsa.�
Nasreen ta shanye kukanta ta yi magana cikin sanyi, “Ya Allah ga mijina, yana da . kamanta gaskiya, ya hana kansa cin haram, ya tsarkake zuciyarsa ta hanyar neman halak! Ya goya marayu, ya inganta karatunsu, ya hana su kukan maraici, ya Allah ka taimake ni ka kare min shi, ka bashi sa’a a dukkan lamuransa, ka makantar da idanunsa a lokacin da aka kusance shi da haram, ka Kara masa hasken idanu a lokacin da Halak take tunkaro shi. .Allah ya tsareka Dee, ya baka nasara akan dukkan abinda ka sanya a gaba.� Sultan ya tsinci kansa da jin dadin addu’ar Nadsreen, duk da ta Karashé muryarta tana rawa, hakan bai hana shi sumbatarta ba, ya dubeta “Kin yi min alqawarin in tafi in kwanta da hankalina ba za ki yi kuka ba? Idan kin san za ki yi kuka in fasa fita in zauna ina renon hawayenki don ganin na hana su zubo wa.� Murmushi ne shimfide a fuskarta, za ta so ta iya kallonsa a lokacin da yake wannan maganar, don haka ta daga kanta, “Nayi maka alKawari.�
Cikin sauri ya shafi Kanta ya fice. Bai ga ‘Umma ba, bare Hafsat, hakan ke nuna masa lallai yau Umma tana cikin damuwa. Zakiyya tana ganinsa ta biyo bayansa, bai ce mata komai ba, ya fitar da uniform dinsa ya sanya, ya dauké takalmansa da safa ya zura, ya dauki ‘hula ya sanya. Zakiyya ta bude baki tana kallonsa, zata iya rantsewa bata taba ganin mutumin da Unifoam yake yi masa kyau ba, kamar Sultan gaba daya kayan sun Kara haskaka shi. Shi Kansa. ya gamsu kayan sun karbe shi. Duban ta yayi lokacin da yake gyara zaman hularsa yace, zanje Office.�Zakiyyatace,“To.�Ya dube ta kamar zai yi magana sai kuma ya fasa ya kama hanyar fita. Ba zai iya wucewa. bai sake zuwa ya duba Nasreen ba, yana komawa dakin ya same ta zaune ta yi Shiru.Tun kafin ya yi magana ta fara murmusho “Ka yi kyau tamkar dawisu Mayar da kanta tayi ta kwanta a gadon tare da rigingine, “Dee kullum idan na yi Sallah ina sake gode wa Alla da ya bani kai a matsayin mijin aure, tabbas ita din ta daban ce a cikin ‘mata. Ban taba ganin mutumin da yake kyau-da kaki ba, sai akanka.� � Sultan ya zaro ido sosai yana dubanta. Yadda ta kwanta tana kallon sama, yasa ya Karaso ya hada kansa da nata suna shakar Samshin juna, “Anya baki ganin komai Nasreen? Abubuwan da kikeyi suna yi min kama da macen da take gani, ba makauniyar dana sani ba.
Nasreen ta yi murmushinta dake Kara kawata fuskarta ta ce, “Babu makauniya a duniyar nan, musamman akan wanda takeso. Makantar zuciya ita ce Makanta, ba ta idanu ba, zuciyata tana ganinka, tana jinka tana iya siffantaka, tana iya idan kana wuri Zuciyata za ta makance ne Kawai a duk ranar da ta daina son ka, hakan kuma ba zai faru ba, ko da kuwa an dauke numfashina daga jikina.�
Sultan ya nemi ya mance abinda ke gabansa, sai da ya fara KoKarin cikuikuye unifoam din da ya sha guga, sannan ta ankarar da shi. Jiki a mace ya mike ta yi masa sai ya dawo ya fice. Ajiyar zuciya ya Kwace mata, tana son jin Naufal a kusa da ita, Kila hakan zai kwantar mata da hankali, da gaske ta yi kewarsa tana son jin dan uwanta a kusa da ita. Zakiyya da bakin ciki ya isheta ta rasa me za ta yi? Sai kawai ta fice ta dawo ta ajiye ruwan zafi a dai-dai hanyar da Nasreen za ta wuce ta koma dakinta.
Nasreen cikin ikon Allah da ta tashi fitowar sai ta zagaye ta wuce ruwan zafin. Sai kuma ga Umma ta fito tana tafe kamar bata gani ta buge ruwan zafin, ya zubar mata a Kafafu. Ta fasa Kara wanda ya jawo hankalin dukkan mutanen da ke cikin gidan. Zakiyya ta rude iya rude wa musamman da ta ga Kafar Umma ana taba wa tana sabulewa. Hafsat ta gigice ta rike Umma tana kuka. “Wa ya ajiye ruwan zafi a kan hanya?� Zakiyya ta fara kame-kame.
Hafsat ta mike a fusace ta shaKo ta, “Gaya min waye ya ajiye wa Umma ruwan zafi? Ba ki isa ki ce Nasreen ba, domin kina sane da makauniya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login