Showing 33001 words to 36000 words out of 123375 words

Chapter 12 - RUBUTACCIYA BOOK 1-2-3-4 Complete Document by Fatima Dan Barno.txt

Nawfal ya za mu yi? Ni na tsani Mansur dinnan duk wani mummunar labari daga bakinsa muke fara ji. Don Allah kada ka dauki lokaci wajen nema mana mafita, kuma Nawfal tuntuni kana da lambobin su Abba ka kasa kiran su?�


Nawfal ya dan yi shiru kafin ya ce, “Kuskure ne anriga anyi Nasreen sai mu tari gaba.� Bata ce komai ba, ta kwantar da kanta a jikin bango kawai tana jin sanyin simintin yana shigarta.


Sultan ya yi bala’in daukewa Zakiyya wuta, ta yadda ya rage zaman gidansa, kullum yana cikin aiki. Yau Lahadi, sanye yake da wando iya guiwarsa sai t shirt mai ° dauke da sunansa a baya. Shigar ta yi matuKar dacewa da shi, fatan jikinsa ta sake laushi sai walKiya take yi, kallo daya za ka yi masa ka fahimci yana cikin natsuwa, sai dai a zuciyarsa ba haka abin yake ba. Yana zaune a cikin garden dinsa ya_ harde Kafafunsa a kan wani yana karatun jarida. Wayarsa ce ta dan yi Kara hakan yasa ya fahimci kira ne, don haka ya dauka ya manna wayar a kunne.


Ashmaan ya ce, “Ka jira mu sati mai zuwa zamu zo gidanka. Na samo wasu bayanai akan Saudat bayanan suna da mahimmanci, don haka ne nake son mu
hadu mu dukka domin ganin yadda zamu bullowa abin.�


Sultan ya rasa bakin magana, ya rasa yadda zai fara godewa abokansa, da suka hana kansu barci saboda shi? Kafin ya yi magana har Ashmaan ya datse wayar.


Murmushi ya yi ya ce, “Girman kai a wurinka Ashmaan abin ba a cewa koma. Ibtihal ce kadai ta isa ta yi min
* maganinka.� Zakiyya da ta dade tsaye akansa tana � Kare masa kallo, ta lumshe idanunta tana jin waye ya kaita sa’an miji? Dogo ne tsayayye mai faffadar Kirji. Yana da haske irin hasken nan mai kyau da daukar hankalli. Hancinsa ya dace da bakinsa.


A hankali ta Karaso tana washe hakora. “Ina son magana da kai.� Ta fada masa tana tsaye a kansa tana yi masa wani shu’umin kallo wanda yasa ya tamke fuska. “Ina jinki. Kuma ke baki iya gaisuwa bane? Menene na tsaya min akai haka?� Zagayowa ta yi sannan ta gaida shi, bai amsa ba, haka bai daina kallon ta ba. Shi tunda yake anya ma ya taba ganinta babu kwalliya? Har yanzu ba zai ce ya taba ganin asalin fuskarta ba. “Dama ina son ingaya maka ne, ni ba zan iya jure rashin kusanto ni da kake yi ba, sai ka dinga ja baya da ni sai kace ba matarka ba. Ina da buKatar mijina.� Sultan dai yana ganin abin al’ajabia_ � duniyarsa, “To na ji ki shiga ciki zan zo.� Babu musu ta mike tana tafiya tana » yanga, abinda bata sani ba, ko daga kansa bai yi ba, bare har ya dubi 1rin takun da take yi. Tunani ya yi tunda yarinyar nan ga kalarta gara ya yi iya yinsa ya sauke hakkokinta tun kafin watarana ta kawo masa Kato cikin gida. Rintse idanunsa ya yi kasancewarsa namiji mai tsananin kishi musamman a kan abinda ya shafi iyalansa. “Ta kawo min wani gidana? Ashe da na kashe ta kowa ma ya huta.� Yana jin dadin yanayin wurin don haka ya kasa tashi yana nan zaune har sai da ta sake dawowa. Babu shiri ya mike sam ba ya jin sha’awar komai, haka ya same ta. Maganin da ta shafa a jikinta shi ya rinjaye shi har ya aikata abinda take so.


Wani abu da Sultan ya gama fahimta da Zakiyya shi ne ba ta Sallah kwata-kwata hakan ya tashi hankalinsa har ta kai yau ya yi mata magana, “Wai ke me yake hanaki Sallah ne? Kina nufin in zauna da kafira a


� cikin gidana? A’a ba za a yi hakan da ni ba, idan baki iya bane zan tattaraki da direba ya * kai ki gidanku ki koyo yadda ake ibada, kafin mu iya zaman aure. Domin bana jin ko wankan tsarki kin iya yi.� .


Idanun Zakiyya ya raina fata sai � girgiza kai take yi alamun babu inda za ta je. Tsaki ya ja ya fice daga dakin kawai. Washegari ya gama shiryawa zai wuce aiki, yana fitowa Zakiyya ta fito da gudu kamar mahaukaciya ta kama _ Kafar wandonsa. Kunya ya kama shi, ya kafeta da ido kawai. Yau babu kwalliyar a fuskarta, hakan yasa ya fahimci dalilin da yasa take kwana da kwalliya. Kallon ‘yan sandan shi kawai ya yi gaba daya suka watse. Dubanta ya yi cike da takaici ya ce, “Me yake damunki ne Zakiyya? Baki ganin ina gaban yarana ne? Me kike tunanin abinda kika yi zai jawo min? Kada ki sake yi min haka.� Kin sakinsa ta yi tana magana cikin kuka, “Wallahi zan dinga yin Sallah kada ka ce inkoma gidanmu.� Sai yanzu ya fahimci dalilin haukan da take yi, “To koma ciki.� Sakinsa ta yi ta kama hanyar cikin gida, ya bi bayanta da ido. Ya tsani ya ga mace tana sanye da riga daban zani daban, amma Zakiyya kamar hakan ya zame mata jiki, za ta yi kwalliya yadda ya kamata ta dauko riga daban zane daban ta sanya, ita kuma ba ‘yar kauye ba. Tunda tazo gidan bai taba cin wani abu da ya shafi girkinta ba, ita kanta baa bin arziki take dafawa ba, wataran kuma ta ba masu gadi kudi su yo mata order. Shi ya sa yake ta tunanin yadda zai yi da su Ashmaan da suke shirin zuwa


gidansa, kuma ya tabbata za su zo ne daga nan su ci abincin amarya. Ya zama dole yasan yadda zai yi kafin ranar tazo idonsa ya raina fata. Yana kan hanya ya kira mahaifinsa a waya suka fara tattaunawa akan matsalar su Nasreen. Abba ya nisa ya ce, “Sultan mutanen da suka bace menene amfanin bin diddigi akan Saudat?� Sultan ya shaki iska ya fesar, “Abba
“na yi wa Anti Saudat alKawarin zan Kwato mata ‘yancinta. Ko su Nasreen suna nan, ko basa nan, sai na nemo wanda ya kashe Anti Saudat na hada shi da hukuma ta hukunta shi dai-dai da irin laifinsa.� Abba ya gyada kai ya ce, “Idan kuma mutumin ya mutu fa?� Sultan ya ce, “Irin wadannan azzaluman Allah yana jinkirta mutuwarsu domin suga ishara tun a gidan duniya. Abba ka bari duk yadda al’amuran suka kasance zan sanar da kai insha Allahu.� Suka yi Sallama ya ajiye wayarsa. Duban yaransa ya yi ya ce, “Ranar Lahadi insha Allahu za ku nemo min ma’aikata masu aikin abinci za su kawo mana lunch, ina da baki.�
Da girmamawa suka amsa masa.


. Sultan ya Kurawa gefen titi idanu, har yanzu yana nan da halayyarsa na son kallon gefen titi. Haka abubuwan da suka faru shekarun baya suna nan manne a ransa sun Ki gogewa. Yana jin yanzu ne zai dauki fansa akan koma waye ya ingiza rayuwar Saudata ° cikin Kunci.


Nasreen tana zaune a gaban Mansur ° ya ajiye mata nama zuciyarsa cike da farin cikin yadda Nasreen ta kwantar da hankalinta. Doguwar riga ya kawo mata ya ce ta sauya wanda za ta yi zaman takaba da ita. Yana fita ta rungume doguwar rigar ta shaki kukanta yadda ranta ke so. Sannan ta sauya kayan kamar yadda ya buKata. Bata san ya shigo ba, sai muryarsa ta ji, “Kin yi kyau sosai. Bari ki gama takabanki za ki ga yadda zan mayar da ke Nasreen. Idan har za ki dinga bani hadin kai ni kuma zan mayar
6/5/22, 10:47 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 2 CHAPTER 2🦚*






*BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO*






A JIYA MUN TSAYA


Ranar Lahadi insha Allahu za ku nemo min ma’aikata masu aikin abinci za su kawo mana lunch, ina da baki.�
Da girmamawa suka amsa masa.


. Sultan ya Kurawa gefen titi idanu, har yanzu yana nan da halayyarsa na son kallon gefen titi. Haka abubuwan da suka faru shekarun baya suna nan manne a ransa sun Ki gogewa. Yana jin yanzu ne zai dauki fansa akan koma waye ya ingiza rayuwar Saudata ° cikin Kunci.


Nasreen tana zaune a gaban Mansur ° ya ajiye mata nama zuciyarsa cike da farin cikin yadda Nasreen ta kwantar da hankalinta. Doguwar riga ya kawo mata ya ce ta sauya wanda za ta yi zaman takaba da ita. Yana fita ta rungume doguwar rigar ta shaki kukanta yadda ranta ke so. Sannan ta sauya kayan kamar yadda ya buKata. Bata san ya shigo ba, sai muryarsa ta ji, “Kin yi kyau sosai. Bari ki gama takabanki za ki ga yadda zan mayar da ke Nasreen. Idan har za ki dinga bani hadin kai ni kuma zan mayar


ZAMU TASHI


da ke bin alfahari a idon duniya. Ki kwantar da hankalinki zan nuna maki ba Sultan ne kadai mai Kaunarki ba.�


Kuka ya taho mata da gudun gaske ta shanye kukanta tana sakin ajiyar zuciya. Tana jin dadi ne idan ta tuna bata da idanun da za ta dube shi bare har bakin cikinsa ya kasheta. Shi dai Nawfal yana nan daga waje, yaki amincewa ya yi nisa da inda suke, gani yake yi kamar Mansur zai iya cutar da ita.




Mansur ya fahimci abinda Nawfal yake nufi don haka ya yi masa wani inn kallo kafin ya bushe da dariya ya Kara da cewa, “Ji dan tatsitsin yaron nan! Wanda baka wuce in fyato ka daga hancina ba, wato ka tsaya kai a dole ga mai gadin ‘yar uwarsa. Idan wani abun zan yi mata tuni zan sa a banKare min kai a wancan bishiyar.� Ya nuna wata bishiya dake tsakar gidan. Nawfal ya dube shi ido cikin tdo babu wata alama ta tsoro, ““Ni ma ban ce maka ina gadinta ba. Haka baka isa ka yi mata abinda Allah bai tsara zai faru da ita ba.�
Mansur ya sake bushewa da dariya, hakan yasa Nawfal wuce shi ya afka dakin da Nasreen take. Ya rada mata a kunne ta yi wata magana da za ta nuna alamun tana son Mansur. Nasreen ta cije lebbanta tana jin daci a wuyanta sannan ta daure ta fara magana muryarta tana rawa, “Nawfal me ya sa za ka gayawa Mansur magana? Ka mance shi yake shirin taimakona ya aure ni duk da bana gani? Ka mance shi ya rabo mu da zaman KasKancin da muke yi a Kankia ya kawo mu nan? Ba mu da matsalar abinci, haka shi yake bamu dukkan abinda muka buKata. Ka daina gaya masa magana ka ji Nawfal?�


: Mansur da ya labe yana sauraransu farin ciki ya kasa barinsa har sai da ya bayyana a gabansu. “Nasreen za ki ji dadina fiye da tunaninki. Zan mayar da ke tauraruwa a cikin gidan nan. Kai kuma kayi min biyayya.�
Nawfal ya hade rai yana dubansa, “Babu biyayyar da zan yi domin ban gama yarda da kai akan ‘yar’uwata ba. Idan da gaske kana son ta me zai sa ni ma ka dinga takura min kana hanani yin abinda nake so? Idan ita mace ce ai ni namiji ne, a bar ni infita in nemo gumina saboda ban saba da zama ba.� Mansur ya dan yi shiru, “Za ka iya sana’ar fashi da makami?� , Nawfal ya zaro idanu, “Allah shi kyauta ya tsareni. Ce maka na yi zan je in nemi halalina ba hakkin wasu ba.� Mansur ya yi murmushi ya fice yana jinjina Karfin taurin kai irin na Nawfal.


Yana fita ya dubi Nasreen ya ce, “Kin gani ko? Sai kin dinga daurewa idan kina son mu fita daga gidan nan lafiya lau. Bana son koke-koken nan da kike yawan yi bana jin dadi. Ki daurewa zuciyarki za ki iya Nasreen.� Gyada kanta kawai take yi, amma ita kadai tasan menene a can Kasan zuciyarta.


Ashmaaan ne zaune a cikin mota a unguwar Magajiya da ke Kaduna. Idan bai yi Karya ba nan ne gidan su Kawar Saudat da aka nuna masa, wanda aka tabbatar masa a nan gidan take aure da ‘ya’yanta. Ya rasa ta yadda zai yi ya sami shiga cikin gidan ba tare da wata matsala ba, kasancewarsa musulmi. Dole ya aika yaro a yi masa kiran mai gidan. Aka tabbatar masa da baya nan .. yaje gona, sai dai matarsa. Idan lissafinsa ya yi dai-dai zuwansa na shida kenan yana . neman gidan bai taba cin sa’a ba, sai yau da aka tabbatar masa da nan ne gidan Nora. Haka hoton Saudat da ya nuna angane ta har aka furta sunanta da Justina. Yana nan zaune har Allah ya fito masa da matar da yana ganinta ya gane ta, ita ce ta cikin hoton nan. Fitowa ya yi daga motarsa ya Karaso kusa da ita, “Sannu madam.� Ta dube shi da tsoro a idanunta ta ce, “Yauwa sannu.�


Bakinsa ya rufe ne sakamakon yadda take tafiya tana waiwayarsa, alamun ba za ta tsaya ba. Da sauri ya taka ya biyo a, “Madam ina neman gidansu Justina ne.� Ya fada hakan ne domin ya sa mata razana a jikinta, kuma ya ci sa’a domin kuwa jikinta yana kyarma ta dawo da baya, tana dubansa. “Ka ce kana neman waye? Justina?� Ashmaan ya daga mata kai alamun haka ne.


Matsowa ta yi daf da Ashmaan sannan ta ce, “Justina ta dade da mutuwa, ba mu ga


; gawanta ba, ba mu san inda take ba. Amma ta mutu. Ni ban santa sosai ba, a unguwa kawai mun tashi.�


Ashmaan ya zaro idanu, “Ta mutu? Ina neman ta ne in bata kudadenta miliyan biyu da ta taba ba Babana aro, shi ne ya ba ni hotonta ya kwatanta min unguwar nan ya ce duk ranar da na dawo Kasar nan in neme ta in ba ta saboda ta taimake shi.� Nora ta zaro idanu kasancewarta mayyar abin duniya, “Miliyan biyu? Waye ne zai ba Justina miliyan biyu? Ina ganin Alhajin nan ne zai bata, ita kuma saboda
tsoro za ta bada aro. Ka yi haKuri mu koma inuwa, nice babbar Kawarta bata da Kawa kamana a nan unguwar.�


Ashmaan ya saki ajiyar zuciya ganin abinda yake nema zai same shi ba tare da yasha wahalar da yake tunani ba. “Tunda ke babbar Kawarta ce na san kin san family dinta sosai, zan iya ba ki kyautar dubu dari biyar ki hada ni da iyayenta domin in ba su _ � kadarorinta.� Nora ta rufe ido ta sake budewa. � Tunda take bata taba ganin ko da dubu hamsin ba, amma yau gashi ance za a bata dubu dari biyar domin kawai ta fada inda gidan su Justina yake. Tuni ta sauke daron da -ke kanta tana dubansa, “Babu komai Alhaji.� ; Ashmaan ya dan saita abin daukar maganarsa, ya ce, “Amma me ya kashe ta ne?�
A nan kuma sai Nora ta yi sit! Domin ba ta mance irin gargadin da aka biyo ta har gida aka yi mata ba,
kasancewarta wacce tasan komai akan rayuwar Justina. Girgiza kai ta yi, “Ban sani ba woo.. Ka ba ni kudin in kai ka gidan da kake so ka sani, ba mu da nisa.� Ashmaan ya rikKe kansa, ya san zai sha wahala a gun Nora matuKkKa. “An ce an kashe ta ne?� Nora ta yi wani irin zabura, sannan ta dauki daronta ta aza a kai ta yi gaba abinta, tana tafe tana sake waiwayo Ashmaan, sai kuma ta yi kamar za ta dawo idan ta tuna makKudan kudaden sai kuma ta tuna da rayuwarta tana gaba da komai, don haka ta hakKura ta ci gaba da tafiyarta. Mutuwar Justina ta dawo mata sabuwa, tana son Justina fiye da tunanin mai tunani.


Ashmaan ya rikKe kansa, dole ya tattara ya koma Hotel din da yake ya kwanta shiru. Kewar Ibtihal dinsa yana sake damunsa, dole ya jawo waya ya kirata. Sai dai ‘yan tagwayensa ne suka dauki wayar, hakan ma ya yi masa dadi, domin sun taimaka masa wajen rage masa dukkkan damuwar sa yake
dauke da ita. Sai wajen yamma, a lokacin wurin ya yi sanyi, don haka ya fito cikin shigar Kananan kaya. Abin mamaki Sultan ya gani, shima cikin shigar kayan gida, yana daga zaune yana latsa waya. Har zai yi masa magana, ya Kyafta masa idanu, don haka ya basar kawai. Wannan karon mai gidan ne ya fito da kansa, Sultan ya ba shi hannu suka gaisa. “Ba ka gane ni ba ko? Ni abokin Samuel ne. Ina neman gona ne shi ne ya ce min in zo wurinka za ka taimaka min.�


Daniel ya cika da farin ciki, ya san zai dan sami wani abu, don haka ya washe bakinsa suka sake gaisawa. Ashmaan yana daga nesa yana mamakin irin salon Sultan.


Zama suka yi yana bashi labarin yadda wuraren suke da kuma irin amfanin da zai samu. Sultan ya aikawa Ashmaan text a kan ya zo ya aiwatar da aikinsa,. Ashmaan ya Karaso ya ba su hannu duk suka gaisa. Sultan yana yi masa wani irin kallo kamar bai taba ganinsa ba.


Nora ce ta fito da nufin zubar da shara, tana ganin Ashmaan ta zaro ido tana nunawa Danicl ta ce, “Daniel ga mutumin nan shi ne.�


Daniel ya ce, “Sannu. Ka yi haKuri ba mu San mene ne ya samu Justina ba.�


Sultan ya dube su ya ce, “Wace ce kuma Justina? Ko matar nan da ta mutu shekaru kusan ashirin baya?�
Gabadaya suka kafe Sultan da ido. Ashmaan ya dubi Sultan, ya riKe shi, “Don Allah kana da labarinta ne?�


Sultan ya fizge kansa, “Sake ni mana malam. Na sani lokacin ina yaro Karami.� Ya fada tare da kawar da kansa. Ashmaan ya ce, “Zan ba ka miliyan daya idan har za ka gaya min labarinta. Kawai abinda nake son naji kenan, sannan ka dauke ni ka kai ni gidan iyayenta.�* Jin miliyan daya ya sake kidima Nora da mijinta. Sultan ya ware idanunsa ya ce, “Miliyan daya? TirKashi! Ni yanzu ma sai in gaya maka. Justina an kashe ta ne, saboda tana da cutar Kanjamau, shi ne wasu suka sassare ta suka kashe ta. A kan idona abin ya faru. Da farko ma ana tunanin tana da ciki ne, ashe duk sharrin mutane ne, bata dauke da komai. Nora da Daniel suka zaro idanu jin Sultan yana ta sakin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login