Showing 117001 words to 120000 words out of 123375 words

Chapter 40 - RUBUTACCIYA BOOK 1-2-3-4 Complete Document by Fatima Dan Barno.txt

girma da ke tsakanin su. �
Murmushi ya Kirkiro mata, “Ki je ki kwanta gobe insha Allahu, za mu je Kaduna.� Kwantar da kanta ta yi a Kirjinsa, dole suka shiga dakin tare, suka kwanta. Kowannen su da irin tunanin da yake yi, haka ko da barci yake barawo bai ci nasarar sace su ba. Da sassafe ya dauki Nasreen ba tare da yayi Sallama da Zakiyya ba, suka wuce Kaduna, da ‘yan sandansa. Umma suka samu tana ba masu_aiki umarmmin abubuwan da za su yi. A lokacin Naural yana zaune ya yi tagumi, idan ka Kura masa idanu zaka ga hawaye kwance a_ fuskarsa. Nasreen ta Karaso gabansa da sauri tana tambayarsa, “Me ya faru? Naufal kai da waye?�
Umma ta dube ta cike da bacin rai, “Shi da uwarki ce, dan ba zan ce ubanki ba, tunda babu uban. Ni ce nan nace ba zan iya zama da kato a cikin gidana ba, ya tattara ya koma Makaranta da zama, ban ga dalilin zama da ‘ya’yan shegu a wuri guda ba. Kai kuma Sultan ka tabbata. Nasreen ta dawo kenan zan san inda za a sama mata ta zauna. Wallahi na tsani yaran nan, ga su kamar mayu, sun Ki barin mu.�
Nasreen tasa kuka, Sultan ya dubeta a lokacin da Abba yake fitowa, domin duk ya ji furucinta. Sultan ya ce, “Ku daina kuka Nasreen, Umma bata tsaneku ba, hasalima ita ce wacce za ta fi son ku fiye da kowa, domin ku din ba dolen Abba ba ne, ba dole na bane, amma dolenta ne.� Umma ta bude baki cike da mamakin furucin Sultan, haka ma Abba ya tsura masa
idanu yana kallon damuwa cike da fuskar Sultan. A lokacinne kuma Hafsat ta fito da gudu tana sheKa amai. Duk suka bi ta da kallo. Tana gama aman, Sultan ya karaso kusa da ita yana mata sannu, ya ce Nasrcmeen ta zo su jesu kaita asibiti. Hakan yasa duk suka zauna cikin zulumi, ita dai Umma bata kawo komai a ranta ba, Sultan ya dauketa sai asibiti.
Suna nan zaune aka fito da sakamakonta tana dauke da ciki. Nasreen ta dora hannu a kai za ta fara kuka, Sultan ya Harare ta, dole ta ja bakinta, amma duk da hakan sai da hawaye suka wanzu a fuskarta. Hafsat kuwa hannu ta dora a baki tana ja da baya tana kuka. Sultan ya rike hannunta da Karfi ya wuce ya jefa ta a cikin mota. Ji yake kamar zuciyarsa za ta faso Kirji saboda azaban zafin da take masa. Kukan su kawai yake saurare ba tare da ya iya furta komai ba. Suna isa gida suka sami Abba Baba Mu’azzam, Baba Sani da Umma suna zaune suna karyawa. A falon ya watso da Hafsat yana yi mata wani duba. Umma ta dube shi cikin rikicewa ta ce. “Lafiya kuwa? Menene?��
Sultan bai yi magana ba, ya dubi Baba Sani, wanda bai ma san ya dawo Kasar ba. A lokacin Naufal ya shigo yana duban Nasreen da ke kuka. Shi kansa Baba Sani kafe su ya yi da idanunsa yana mamakin = irin� wannan kama. Baba Mu’azzam ma yau dai ya Kare masu kallo ba tare da ya furta komai ba.
‘Umma ta dubi su Naufal tace “Yau naga masifa. Tunda nan babu ubanku ko danginsa, sai ku fice ku bar ‘ya’yan dangi muyi magana ko? Yaya ka dai ga abinda nake gaya maka ko? Da kake cewa in barsu tare, in dai Sultan ya zauna da ‘ya’yan mazinaciyar nan babu ko shakka watarana sai sun shafa mana masifa a cikin dangi.�
Abba yai yi magana, Sultan ya dakatar da shi da hannunsa. Yana jin yau zai gaya wa mahaifiyarsa gaskiya sai dai ta tsine masa. Ya waiwayo yana duban naufal da ya kamo.hannun Nasreen suka yi hanyar fita, dukkansu kuka suke yi yace, “Kai Naufal ku dawo, akwai danginku anan, kuma nan gidan gidanku ne, zaku iya sakin Jiki ku y? abinda ‘ya’yan Baba Mu‘azzam za su
Umma ta zabura ta ce, “Karya kake yi Abdullahi! Babu yadda zaka hada ‘ya’yan Kwarai da shegu. Na kula rashin kunyarka sake girma yake yi, ni kuma zan sauke maka.� Sultan ya Karaso gaban mahaifiyarsa ya ce, “Umma ki gafarceni, amma su Nasreen ba su da gidan da ya wuce nan. A yau kuma zagin da kike yi masu akan basu da uba, su je su nemi uban su, mun jajirce Kwarai mun nemo masu_uba. Nasreen, Naufal ku zo Baba Mu’azzam shi ne mahaifinku, shi ne wanda ya yi wa mahaifiyarku fyade, shi ne wanda ya tura a_ kashe mahaifiyarku saboda kada asirinsa ya tonu. Baba Sani shi ya so ya auri mahaifiyarku, saboda
Kaddara ta sameta ya gujeta a lokacin da ya kamata ya kusanceta, ya nuna mata kulawa, ko dan darajar addininmu da ta shiga. Umma kin jima kina tirr da mazinaci, kin jima kina aibata mazinaci, kina kasa yi masa addu’ar shiriya, saboda Baba Mu’azzam malami ne, shima ya tsani mazinaci. Sai ga ‘ya’yan shegu sun zama jininki, Hafsat kuma ta dauko maki abin kunyar da har mu mutu ba zai daina bin mu ba, Hafsat tana dauke da cikin shege a jikinta.�
Baba Sani ya mike zumbur, Abba ma ya mike, haka Baba Mu’azzam shima ya mike. Nasreen da Naufal suka dubi wanda aka kira da mahaifin su duba na tsana, ba su taba jin tsanar mutum kamar mutumin da ke tsaye cikin shigar mutunci da sunan mahaifin su ba. Umma ta daga hannu ta wanke shi da mari, tana dubansa. “Kai har ka isa ka ci mutuncin Yayana uwa daya uba daya? Sultan ka cuceni, ba shi ka ci wa mutunci ba, ni mahaifiyarka ni ka wulaKanta.�
A jejjere su Ashmaan suka shigo, fuskarsu babu wata rahama. Sannu a hankali suka warware masu komai
Baba Sani ya dubi Baba Mu’azzam ya ce, “Yaya ka cuceni, har gobe da soyayyar Saudat nake rayuwa. Na rabota da kowa nata na kawota cikin addinina, shi ne ka zagaya ka wulaKantata, ni kuma na kasa yi mata uzuri. Sultan baka fadi Karya ba, haka dukkan bayananku ya gamsar da ni. Yanzu ‘ya’yan Saudat ne wadannan? Daman cikin jikinta jinina ya yi mata? Datun lokacin ta gaya min da ban barta ta wulakanta ba.� Abba ya dubi Umma cike da fushi ya ce, “Wallahi kin taba fuskar Sultan na Karshe, idan
kika sake Kofarin marinsa, zan nuna maki kuskurenki. Kin ji kunya Salma! Yanzu ne kike girban abubuwan da kika shuka. Mazinaci kika tsana? Ga ‘yarki nan manne da abin kunya. Kin tsani ‘ya’yan shegu? Yayanki ya Haifa maki, sai ki jira haihuwar Hafsaat, domin babu mai zubar da cikin nan. Nasreen da dan uwanta sun sha gori, ashe ke ce kike dauke da abin gorin. Kin wulakanta ‘ya’yanki ba tare da wani daga cikin mu ya tayaki ba. Kin jima kina neman ubansu, to ga uban su nan a gabanki. Malam Mu’azzam ka _bani mamaki. Ban taba tunanin hakan ba, anan har da kai ake haduwa ana zagin mazinaci, a maimakon addu’a da fatan Allah ya shirya. Kun “tsani wadanda suka tuba suka koma addininku, amma baku tsani wanda ya keta haddin wacce ba addininku daya ba. Duniyar nan ina za ki damu? Yau wacce irin rayuwa muke ciki ne?
Sultan da ke jin bakin ciki yana cinsa ya duKar da kai yana magana, “Babu yadda ban yi da Umma ba, akan su Nasreen amma taKi saurarena. Akan ‘ya’yanta ta wargaza gidan, ta ce ba zamu zauna lafiya ba. Bansan su Nasreen jinina bane, na damu sai an taimaka masu. Umma kullum maganganun da kike fada akan su
6/29/22, 21:06 - Ummi Tandama😇: RUBUTACCIYA BOOK 4


CHAPTER 11


BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO






MUN TSAYA


sai ki jira haihuwar Hafsaat, domin babu mai zubar da cikin nan. Nasreen da dan uwanta sun sha gori, ashe ke ce kike dauke da abin gorin. Kin wulakanta ‘ya’yanki ba tare da wani daga cikin mu ya tayaki ba. Kin jima kina neman ubansu, to ga uban su nan a gabanki. Malam Mu’azzam ka _bani mamaki. Ban taba tunanin hakan ba, anan har da kai ake haduwa ana zagin mazinaci, a maimakon addu’a da fatan Allah ya shirya. Kun “tsani wadanda suka tuba suka koma addininku, amma baku tsani wanda ya keta haddin wacce ba addininku daya ba. Duniyar nan ina za ki damu? Yau wacce irin rayuwa muke ciki ne?
Sultan da ke jin bakin ciki yana cinsa ya duKar da kai yana magana, “Babu yadda ban yi da Umma ba, akan su Nasreen amma taKi saurarena. Akan ‘ya’yanta ta wargaza gidan, ta ce ba zamu zauna lafiya ba. Bansan su Nasreen jinina bane, na damu sai an taimaka masu. Umma kullum maganganun da kike fada akan su


ZAMU TASHI


Nasreen ba masu dadi bane. Sai gashi dukka abubuwan sun taru sun dawo cikin gidanki. Baba Mu’azzam you’re under arrest!�
Abba ya gyada kai, “Na ba ka izinin ka hukunta duk wani mai laifi. Bana goyon bayan zalunci, Aikinka ne kayi dukkan abinda ka gadama ba zan hanaka ba.�
Mahbub ya sarawa Sultan sannan ya nufi Baba Mu’azzam. Shi kuwa ido ya raina fata, sai duban su Nasreen yake yana jinjina Karfin ikon Allah. Nasreen da Naufal suka Karaso gabansa suna dubansa, “‘Kai ba mahaifinmu bane, ba zan taba ambaton sunanka a matsayin ubana ba, ba * zan taba kallonka a matsayin mahaifi ba. Sultan shi ne gatanmu,.a duniya, Abba shi ne uban da muka budi ido muka sani, amma ko da alama ba zamu taba danganta kanmu da kai ba. Wayyo rayuwa! Me ya sa


rayuwarmu bata tafi a duhu ba, da in ga wannan mutumin a matsayin uba? Me yasa kuka bari nasan wacece ni?�
Nasreen ta zube Kasa kuka ya ci Karfinta ta daya hannu sama tana magana cikin kuka, “Allah na roKeka, ka hukunta wannan bawa naka tun a gidan duniya, ka hana shi kwanciyar hankali, ka aiko masa da masifu iri-iri ka wulakanta…� Sultan yana jinta ya share ta, sai Abba ne ya hanata Karasa addu’ar da take kwararowa mahaifinta. “‘Nasreen! Uba ubane, ba a taba canzawa tuwo suna. Kada ki sake yi wa mahaifinki irin wannan addu’ar kin ji?�
Nasreen ta girgiza kai tana tsananta kukanta, “Abba! Abba ka daina cewa wannan mutumin ubana ne, ba zan taba yin alfahari da shi ba. Ya wulakanta uwata, ya barta tana kwana a cikin garejin motoci, cikin kwata, cikin Kazanta. Ta kwana bata ci ba, ta tashi duniya suna yi mata kallon karuwa! Suna aibatata. Tana cikin halin wahala, ga yunwa ga Kishin ruwa, ga ‘ya’ya biyu a cikinta, tana magana da Kyar, amma mutumin nan bai tausaya mata? Zai aiko a sassareta? Insha Allahu, Insha Allahu…� Takasa Karasawa saboda kukan da ya ci Karfinta.
Baba Mu’azzam kuka yake yi, ya rasa me ke masa dadi.. Ita kuwa Umma kusan suman tsayé ta-yi: Ta rasa meke yi mata dadi. Nadama ce ta shigéta. Ita dama Mairo tana can dakinta ta nade tana gudun fitowa ta sami dizgi daga Umma. Hafsat kuwa bude baki ta yi tana duban kowa da ke dakin. Naufal sai yanzu ya sami daman yin magana, “Ba ni da uba sai Deedina, shi kadai ne ubana, shi ne wanda ya ganmu a cikin halin matsi da Kazanta ya kusance mu a irin wannan lokacin. Da mahaifiyarmu za ta dawo duniya, babu wanda za ta ba ‘ya’yanta sai Deedinmu. Har in mutu ba zan taba kallonka a matsayin uba ba. Ban taba-jin wata alama a zuciyata da za ta nuna min kai ubana ne ba.� Haka aka tasa Baba Mu’azzam aka fice da shi ba tare da ya samu tausayawan ‘ya’yansa ba. Su Ashamaan gaba daya suka fice bayan sun bada umamin a kamo su Alhaji Kabir. Suna , fita Sultan ya kama Hafsat da wanié irin mahaukacin duka, babu ji babu gani, domin ya fi jin tsanarta fiye da kowa. Umma ta kasa ko daga kai, gaba daya ta muzanta, ta amince laifinta ne, ta kasa yi wa ‘yan uwanta musulmai uzuri, gani take yi duk wanda ya aro addini baya daya daga cikin jerin masu shiga Aljannah, ji take kamar ita ke da ikon sanya mutum a Aljannah ko kuma a wuta, Gaba daya gidan babu dadi haka an rasa wanda zai Kwaci hafsat daga hannun Sultan. Mairo ce ta yi Karfin halin fitowa ta Kwaceta da Kyar. Abba yana zaune ya nuna kamar abin bai dame shi ba, amma acan Kasar zuciyarsa kukan zuci yake yi, yau shi ne ‘yarsa ta cikinsa take dauke da cikin shege. Nasreen kuwa da ita da Naufal suka hada kai suka zauna shiru a waje, ba su cewa um bare um um. Umma tana son yi masu magana tana jin. kunya, ba ta san da wasu idanun za ta kalle su ba. Sultan shi ya kawo masu abinci ya zauna da su, ya tsoma hannun shi, sannan suma suka sanya hannayen su, suna ci fuskar nan babu fara’a kallo daya zaka yi masu baka buKatarn yin na biyu, zaka fahimci ba su jin dadin abinciza. Da daddare Nasreen tana zaune akan dadduma tana roKorwa mahaifiyarta Rahamar Ubangiji, ta ji an turo Kofa. Duba daya ta yi wa Umma ta kauda kanta. Tana jin zafin Umma fiye da kowa, sai dai kuma darajar Sultan ba za ta iya yi mata ko da kallon banza ba.
Umma ta Karaso ta zauna kusa da Nasreen
Sai kuma tasa kuka. Jikin Nasreen yana rawa ta rarrafo jikin Umma ta kwanta kawai tana ci gaba
da kuka. A karo na farko Umma ta rungumeta tana neman afuwanta. Ta kasa magana sai kuka da take yi, Umma tana yi mata nasiha sai daga kanta take yi alamun ta ji. Umma bata bar dakin ba, sai da ta tabbatar Nasreen ta daina kukan, sannan ta koma dakin Hafsat.
Hafsat tana ganin Umma ta durKusa Kasa tana sharar hawaye. Ta ce, “Umma ki yafe min na ci mutuncinku, ban kyauta maki ba, Umma ki yafe min don Allah.� Umma ta shafa kanta kawai ta kasa magana, sai bubbuga bayanta take yi.“Na yarda da Kaddarata. Naga ishara akan Nasreen, na tsane su na wahalar da su, da ga Karshe na makantar da Nasreen, nasa aka kwashe su aka bar garin nan da su, saboda kawai bana son zama inuwa daya da mazinata. Kaicona! Da ban tashi ankarewa ba, sai da ya faru da ni. Allah na tuba. Hafsat gaya min yaushe kika yaudare ni k,’ka je aka yi maki ciki? Yaushe kika fara siyar da ;mutuncinki a kasuwa Hafsat?
Hafsat tana kuka ta gayawa mahaifiyarta yadda Salim ya yaudareta da sunan zuwa gaida mahaifiyars. yasa mata Kwaya a cikin lemu. Tana kuka tana cewa, “Wallahi Umma bana cikin hayyacina ki yarda da ni,� Sultan ya Karasa
shigowa yana duban Umma duba na mamaki. Ya ci alwashin idan ya kama wanda ya aikatawa Nasreen, wadannan abubuwan sai ya dauki mataki, sai dai yanzu ko da shi ne shugabarr masu daukar mataki wannan tafi Karfinsa.
Jiki a sanyaye yake duban Ummansa. Ya ce “Umma� Yanzu ke kika aikatawa Nasreen wadannan abubuwan? Wallahi Umma da a ce ba a bakinki na ji ba, ba zan taba yarda ba.�
Umma ta sunkuyar da kai, hatta danta kunyarsa take ji sosai. Shi kansa Abba ta kasa~ ganin fuska a wurinsa. Sultan ya nemi? wuri ya zauna, duk suka yi shiru a dakin. Ya dubi Hafsat ya ce, “Zan sa a kama Salim, sai ya dandani irin bakin cikin da yasa mu -ciki. Hafsat har yaushe kika yi wayewar bin saurayi gida? Ina. tunaninki yake? Ina iliminki da wayonki? To sai kin haife cikin kuma dole ya aureki, bayan ya gama shan wahala gidan yari.� Ya mike kawai ya fice ‘yana jinjina wai Umma ce ta makantar da Nasreen saboda tsabar Kiyayya.
Washegari Sultan suka wuce Abuja, kasancewar ya sami kiran gaggawa daga office
6/29/22, 21:12 - Ummi Tandama😇: RUBUTACCIYA BOOK 4


CHAPTER 12


BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO






MUN TSAYA


Umma ta sunkuyar da kai, hatta danta kunyarsa take ji sosai. Shi kansa Abba ta kasa~ ganin fuska a wurinsa. Sultan ya nemi? wuri ya zauna, duk suka yi shiru a dakin. Ya dubi Hafsat ya ce, “Zan sa a kama Salim, sai ya dandani irin bakin cikin da yasa mu -ciki. Hafsat har yaushe kika yi wayewar bin saurayi gida? Ina. tunaninki yake? Ina iliminki da wayonki? To sai kin haife cikin kuma dole ya aureki, bayan ya gama shan wahala gidan yari.� Ya mike kawai ya fice ‘yana jinjina wai Umma ce ta makantar da Nasreen saboda tsabar Kiyayya.
Washegari Sultan suka wuce Abuja, kasancewar ya sami kiran gaggawa daga office


ZAMU TASHI


A gida ya ajiye Nasreen ya wuce abinsa. Tana shiga ciki ta kama gyara ba tare da ta duba bangaren Zakiyya ba, komai ta shirya shi a ma’adaninsa tana jin tunanin mutumin da aka kira a matsayin mahaifinta yana ci gaba da addabanta. Har ta gama abincin bata bar tunaninsa ba. Ta rasa a tsakanin tausayi da tsanarsa wannene yafi tasiri a zuciyarta.
Yau shigar Kananan kaya ta yi, kasancewar garin da zafi. Zakiyya ta leKo dakin ta ci burin koma me ke cikin ran Nasreen akan kwana da miji, ita sai ta daKile hakan. Yana dawowa ya fada wanka ya dan kintsa sannan ya shiga bangaren Zakiyya yace ta zauna yana son magana da ita.




Babu musu ta zauna ya dubeta duba na tsanake ya ce, “Zakiyya na zo in yi maki magana ta Karshe daga haka kina iya wuce wa gidanku. Kin ganni nan? Bana son fitina, bana son tashin hankali, idan kika sake zagin yarinyar nan, ko! kika sake gaya mata maganar da Za ta sa ta kuka. Wallahi! Za ki tattara ki koma inda kika fito. Da kike yi mata gorin uba, ke waye yasan naki uban? Zan dauki mataki KwaKKwara akanki. Sai da safe.� Ya mike ya fice abinsa.
Da shigarsa ta tare shi kamar wacce take jiransa. Rungume juna suka yi, ta saki ajiyar zuciya mai Karfi, “Namiji daya ne a gabana, amma yafi maza dubu. Kana da kima a idanuna, ina sonka, ina yi maka irin son da duk wanda ya tsaya kwatanta shi, bai san girman son ba ne. Yau zan yi barci irin wanda na jima ban yi irinsa ba.� Sultan ya shaki Kamshinta yace,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login