Showing 36001 words to 39000 words out of 123375 words

Chapter 13 - RUBUTACCIYA BOOK 1-2-3-4 Complete Document by Fatima Dan Barno.txt

Karya kuma hankalinsa a kwance. Yana gamawa ya ce, “Sai muje innuna maka gidansu ka bani kudina.� Ashmaan ya ce, “Amma na gode abokina. Nayi maka alKawarin inhar _ maganganun da ka gaya min gaskiya ce, zan daukeka har Kasar nan ka bari. Kai musulmi ne?� Sultan ya kalle shi ya ce, “A’a ni _ inyamuri ne.� Ashmaan ya yi murmushi, “Kayi haKuri ba fada bane.� Daniel ya ce, “Wannan labari akan Justina ba gaskiya bane. Mune munsan gaskiya.� Nora ta ware � idanunta ta ce, “Daniel! Ka zo mu yi shawara ya dawo gobe.�


Sultan ya ware idanu, “Au labarin da zaku bayar ne sai kun yi shawara? Ga kudi har miliyan daya? Wanda za ku iya yin shekaru goma kafin ku same su. Ni babu
ruwana ka Kyale su kawai ka zo mu je ingaya maka komai.�


Daniel da ya kidime ya ce, “Pls ka dawo gobe zamu san abin yi, har ka ji yadda akayi Justina ta mutu.� Ashmaan ya yi masu sallama ya wuce.


Yana tafiya Nora ta dubi Daniel gaba daya ta mance Sultan yana wurin, kuma ko ta tuna ba za ta kawo komai a ranta ba, kasancewar tare da mijinta ta gan _ shi. “Daniel kasan mutumin nan a lokacin irin wahalar da ya dinga bamu saboda kawai yana tunanin zamu je mu tona masa asiri? Ni ina jin tsoro kada ya kashe mu.� Daniel ya girgiza kai, “Yanzu mutumin ya mance � da mu, yasan kowa ya manta da maganar mutuwar Justina, don haka babu idon kowa akanmu ki yarda da ni.� Sultan ya rufe idanunsa ya nausa duniyar tunani, “Waye wannan mutumin? Me yasa yake bin duk wanda yasan yana da alaKa da _ sanin mutuwar Justina? Insha Allahu komai ya kusan zuwa Karshe.� Nora ta koma ciki Daniel kuma ya dubi Sultan yana harararsa, “Kai ina tunanin wani Alhaji ne mai kudi, da kazo maganar gona, sai gashi kana jin ance miliyan dayaka gigice. To noman nawa za ka yi?� Sultan ya dube shi yana sake nazarinsa, “Dubu hamsin gareni na kawo a bani gona muyi noma.� Daniel ya zaro ido, “Duk a dubu hamsin din?� Sultan ya ware idanunsa yana gyada kansa domin kan yana matuKar sara masa, ji yake kamar ya shake su. Daniel su gaya masa komai._ Daniel yaja dogon tsaki, “Ka tafi kawai. Ban san inda za ka sami wadannan � � abubuwan ba.� Sultan ya wuce abinsa yana taka Kasa kamar mai tausaya mata. Kansa a Kasa yake tafiya tunani ne kala-kala a cikin kwanyar kansa. “Sai ka zo mu tafi.� Muryar Ashmaan ya ji, don haka ya waiwaya, ya Karasa tare da bude motar ya shiga. Duk kwanar da suka zo sai Sultan ya ce su dakata, abin mamaki duk inda suka tsaya ‘yan sandansa ne cikin shigar fararen kaya. Ashmaan duk yadda yake tunanin lamarin Sultan ya wuce hakan. Sun nausa titi babu wanda ya iya cewa_ uffan! Ashmaan ya yi magana ba tare da ya dube shi ba, “Zamu wuce wurin da aka kashe Saudat!� Sultan idanunsa suna kafe a bisa titin kamar mai son sanin yawan motocin da ke wuce wa. “� Yan sandana suna wurin. Na sa daya aikin faci a wurin, na kai daya koyon kanikanci na babbar mota, daya _ _kuma yana can ya zama mahaukaci bashi da wurin zama da ya wuce wurin da akayl kisan nan. Suna nan dai sun mamaye wurin.� Ashmaan ya gyada kai, “Da haushi kake bani da nake zaton baka dauki abin da mahimmanci ba, amma yanzu na gama ganewa kalar naka daban ne. Ya akayi ka gano su Nora? Bayan komai yana hannun mu?� Sultan ya dan waiwayo ya dube shi, ‘Na gano ta ne, a dalilin C.1.D na, su suka yi min wannan KoKarin.� , Babu wanda ya sake cewa uffan, har suka iso Hotel din da Ashmaan ya kama Hotel. Ashmaan ya zauna a falo yana mayar da ajiyar zuciya, Sultan kuma ya wuce ciki ya watsa ruwa. Abincin da aka jere masu babu wanda ya dubi abincin. Sultan ya mike ya dauki Power Horse ya kai bakinsa, yana jin yadda sanyin ruwan ke sauka a cikin maKoshinsa. Yana nan tsaye a _ windo yana duban waje, sannan ya saki labulan ya dawo yana magana, “Ashmaan matar nan tana da shegen kafiya, da wahala ko goben ka koma ta saki jiki ta bamu_ .abinda muke so. Ya zama dole mu nemo mafita, domin ita ce take dauke da dukkan .bayanan da muke nema. Ina son sanin waye mahaifin Nasreen! Ko ma waye mahaifin Nasreen akwai wani boyayyen lamari a tsakani mai girman gaske. Ashmaan ko ban sake ganin Nasreen ba, zan_ sauke alKawarina da na dauka! Ni zan zama gatan Anti Saudat, ko da kuwa yin hakan zai iya sawa inrasa aikina, inrasa iyalaina, inrasa mutuncina, in rasa dukiyoyina. Zan aikata hakan da Karfin guiwana. Ashmaan mu nemo abin yi tun kafin wannan damar ta kubuce mana.�


Sultan ya yi nisa, sannan ya ce, “Zan tura ma’aikata su kwaso min ita da mijinta, ba tare da sanin kowa ba. Yin hakan zai taimaka mana wajen sanin abinda ya kamata mu sani. Lokaci baya jiranmu, yau idan mutumin da ya aikata wannan laifin ya mutu ba tare da ya san da akwai Kwansa a duniyar nan ba, ba zan yafe wa kaina ba, zan kalli kaina a matsayin mutum mai sakaci da rashin mayar da hankali a kan abu mai mahimmanci.�


Ashmaan ya gyada kansa, “Hakan zai iya yuwuwa. Amma Sultan baka ganin idan aka kama su ta Karfi za su iya botsare mana su hana mu jin abinda muke son ji? Kasan ita Nora tana da kafiya, duk baKar talaucin da suke ciki hakan bai sa ta saki jiki da mu ba.� Sultan ya sake kai Power Horse bakinsa ya zukKa, sannan ya dawo da dubansa ga Ashmaan, “Dan sanda yana sa Shugaban ‘yan daba ya yi bayanin da kudi basu isa su sa shi ba. Muna da abin da za mu jona masu suyi bayani ko basu yi ninya ba.� Ashmaan ya yi murmushi, “Kada ka wahalar da su, na tabbata za su yi bayanin.� Zakuda kafadunsa ya yi, “Kada ma su yi. Idan miliyan daya bata sanya su bayani ba, ina tabbatar maka batir da wayan wuta za su kawo bayanai dalla-dalla.�


Sultan yana nan zaune, yana jin yadda Ashmaan yake soyyaya da matarsa kamar yau aka daura masa auren. Sai da ya sauke wayar Sultan ya dan dube shi ya ce, “Kasan wani abu ne? Wallahi ina mancewa ina tare ~ da wata mata a cikin gidana. Abinda ke daga min hankali yarinyar nan duk abinda muka yi sai ta gayawa mahaifiyarta? Kai ranar da naji da kunnena ban iya barci ba.�


Ashmaan ya shafi kansa ya ce, “Mahaifiyarta fa ka ce? Wannan kam yafi Karfina. Wayewar ta yi yawa.� Sultan ya ce, “Yauwa kasan Allah? Idan ka sake ce min ni musulmi ne sai nasa anboye min kai, inga yadda Ibtihal za ta yi . Baka san dazu
6/9/22, 09:25 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 2🦚*




CHAPTER 3




*BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO*




A JIYA MUN TSAYA


Dan sanda yana sa Shugaban ‘yan daba ya yi bayanin da kudi basu isa su sa shi ba. Muna da abin da za mu jona masu suyi bayani ko basu yi ninya ba.� Ashmaan ya yi murmushi, “Kada ka wahalar da su, na tabbata za su yi bayanin.� Zakuda kafadunsa ya yi, “Kada ma su yi. Idan miliyan daya bata sanya su bayani ba, ina tabbatar maka batir da wayan wuta za su kawo bayanai dalla-dalla.�


Sultan yana nan zaune, yana jin yadda Ashmaan yake soyyaya da matarsa kamar yau aka daura masa auren. Sai da ya sauke wayar Sultan ya dan dube shi ya ce, “Kasan wani abu ne? Wallahi ina mancewa ina tare ~ da wata mata a cikin gidana. Abinda ke daga min hankali yarinyar nan duk abinda muka yi sai ta gayawa mahaifiyarta? Kai ranar da naji da kunnena ban iya barci ba.�


Ashmaan ya shafi kansa ya ce, “Mahaifiyarta fa ka ce? Wannan kam yafi Karfina. Wayewar ta yi yawa.� Sultan ya ce, “Yauwa kasan Allah? Idan ka sake ce min ni musulmi ne sai nasa anboye min kai, inga yadda Ibtihal za ta yi . Baka san dazu


ZAMU TASHI


naji haushi ba? Ashe haka mutum yake ji yana da addininsa a cire masa da Karfi da yaji?� Ashmaan ya yi murmushi har sai da hakoransa suka bayyana, “Kawai a lokacinne sai ka juye min sak!� Kafin ya Karasa Sultan ya jefe shi da gwangwanin Power Horse kuma ya ci sa’a ya same shi. Ko waiwayarsa bai yi ba ya tunkari Kofar fita yana cewa, “Zanje ingaida ‘yan gidanmu. Ashmaan ya mike, “Jirani mana malam. Kai kadai za ka kwashi ladan? Nima zan je.� Sultan da kansa yake janmotar, Ashmaan yana gefensa. A tsakiyar titi yaja burki da Karfi, sakamakon ganin wani a gefen titin yana wankawa mace da namiji mari, haka kowa ya tsaya yana kallo babu wanda ya iya cewa komai. Da Karfi ya ce, “Nasreeen!!� Ashmaan ya ware idanu, “Kashe mu za ka yi ne? Wacce Nasreen kuma?� Bai bashi amsa ba, sai balle belt din da ya yi ya fito yana Karasowa ya dinga wanke mutumin da mari yana Karawa. Ashe wai


soja ne, yaran sun kusa sanya shi ya yi hatsari shi ne ya dage yana hukunta su. Yaso suyi dambe da Sultan amma ina� Karfin ma ba daya ba. Ashmaan yana tsaye yana kallon wanda ya fi shi zafi da zuciya. Daga baya ya Karasa ya finciko yaron daga hannun Sultan yana dubansa, “Kai baka da hankali da A.I.G za ka yi fada?�� Tsoro da firgici suka shige shi, a take ya sara masa yana mazurai. Sultan ko dubansa bai yi ba, ya Karaso gurin yaran yana duban su. Ko alamar kama basu yi da Nasreen ba, idanunsa kawai ke gizo yana nuna masa wasu mutanen daban a matsayin Nasreen. Sultan ya basu kudi yasa su a dai-daita sahu, sannan ya fincike Id card din gaban rigar mutumin ya gama dubawa, sannan ya. jefar masa. Har bakin mota mutumin ya bi su yana bashi hakKuri, Sultan ya dube shi sosai ya ce, “Kunsa ana zagin kaki, kunsa ana yiwa Soja kallon mara hankali, mara sanin ciwon kansa. Kun sa tsofaffi, yara, malamai, da ‘yan iskan gari, da zarar suka ji


fadi sunan hukuma sai su kama tsine mana, wanda bamu san bakin wasu ba, kai tsaye tsinuwar ke isowa garemu ba tare da wani shamaki ba. Kuna sa kaki kuna wulaKkanta duk wanda tsautsayi yasa ya biyo ta layinku, wai a ganinku wani matsayi gareku. Kun mance idan za a kaiku lahira kwaye kakin za a yi a ajiye a gefe. Mutum baya taba tafiya da muKaminsa lahira iyakarsa a duniyar nan da ya samu, sai dai ya je can ya dibi dukkan zunuban da ya kwaso wa kansa. Ni zan yi maganin irinku sannu a hankali. Bana zalunci ban yarda a yi ba!� Sultan ya jawo Kofar motarsa suka wuce. Sannan ya shafi kansa ya ce, “Kasan wani abu ne? Bana tuki saboda idan har nayi sai idanuna sun hasko min Nasreen. Hakan yake sawa nake take burki a ko ina ba tare da nayi la’akari da motar da ke bayana ba.�




Ashmaan ya ware idanu, “Da gaske kake wannan maganar? Dan tsaya a nan akwai abinda zan yi.�


Sultan bai kawo komai ba, ya ja ya tsaya. Ashmaan ya fito daga motar ya zagaya ta wajen zaman direban ya ce, “Fito! Ka fito mana.� Sultan ya fito yana dubansa.


Ashmaan ya shige mazaunin direba ya yi wa mota key, sannan ya ce, “Zagaya ka zauna mu tafi. Ina da mata da ‘ya’ya uku, idan na mutu Ibtihal za ta iya haukacewa, kai kuwa baka ma san zaKin macen ba. Ka . bari in lallaba rayuwata mu tsufa tare. Ta ya ya zan zauna kana jana a mota kana taka � burki a tsakiyar titi saboda soyayya? Ko zamanin nawa soyayyar a hankali na dinga bi da kaina, har na samu na mallaketa.�


Sultan ya yi murmushi abinsa, ya wuce suka ci gaba da tafiya. Sun iso cikin gidansu sun kuma sami Abba, don haka ya yi ta basu shawarar yadda ya kamata su yi. Ashmaan ya ji dadin kasancewarsa a cikin gidan su Sultan domin yaga kara da karramawa.


Gabadaya suna zaune a Katon falon kowannen su gabansa dauke yake da laptop Kanana masu tsada da kyau. A tsakiyar falon Nora ce da Daniel jikinsu babu inda baya rawa. Sun gama sakankancewa Alhaji ne ya turo mutanen nan domin ya ji ko sun mance labarin, sai aka yi rashin sa’a kwadayin abin duniya yasa suka furta wasu kalaman da yake nema ya jawo masu masifa.


Sultan ya ba yaransa umarnin su fice daga falon, sannan ya dawo da kallonsa a kan Nora, “Sunana Abdullahi Lukman, wanda aka fi sani da Sultan wato S. Lukman. Ni jami’in ‘yan sanda ne, a tare da ni kuma akwai abokaina. Ina nufin a nan akwai Soja, akwai Dan jarida, ga kuma Barrister da likitoci. Ina nufin bamu neman wasu ma’aikata a waje, shi ya sa muka hada kawunan mu domin duk irin taimakon da muke nema a cikin mu akwai masani akan abin. Ku saki jikinku, bamu cutarwa, amma idan ka yi mana gardama ina da kayayyakin


aikin da za su sanya a yi maganar gaskiya.


Ina son sanin tarihin Justina, da kuma dalilin da yasa aka biyota cikin dare aka sassareta da ciki. An tabbatar min kina da masaniya akan komai. Shi wancan barazana ya yi maki zai kashe ki ko? Ni kuma bana barazana, sai dai insa bakin bindiga indauke numfashinki.� Yana maganar yana shafa mata bindiga a hanci.


Nora ta kidime iya kidimewa. Daniel kuwa tuni ya yi alKawarin bayar da wadannan amsoshin domin gujewa tarin masifar da mutanen nan masu kwarjini suke dauke da shi. Kafin ya yi magana Nora ta fara magana, “Mu ba mu san komai ba, a kan mutuwar Justina, ku yi haKuri kada ku kashe mu.�


Sultan ya dubi Ashmaan, sun tabbatar da kafiyar matar nan ya wuce tunanin su, haka za ‘ta yi wahalar shigowa cikin musulunci, saboda irin kafewarta. Sam Sultan baya son taba lafiyarsu, yana son yadda aka dauko su salin alin a mayar da su


Don haka dabara tana neman ta Kwace masu. Khamis ya mike ya kama dan yatsan Nora ya yi mata wani irin izaya da yasa ta bude bakinta tana magana cikin wahala da tashin hankali. “Zan gaya maku komai zan gaya maku.�


Ya sake ta yana murmushi, sannan ya jawo Stool ya zauna kusa da_ ita. “Dukkanmu nan muna da abubuwan yi, ki yi maza ki gaya mana abubuwan da muke son ji. Idan kika yi mana Karya, akwai


littafin da ta yi rubutu zamu gane gaskiyar ki ne idan kina magana muna duba littafin. Khamis ya ware littafin wanda rubutun ba ta yi su a bude ba, bayanai ne dai irin wanda zai iya sa ka isa ga inda kake da_ buKata. Daniel ya dubi Nora ya ce, “Nora ki gaya masu, yaranmu suna buKatarmu a raye.�


Nora ta dago kanta tana son Kare masu kallo, amma kwarjininsu ya wuce dukkan yadda take tunani. “Sunana Nora, sunan Kawata Justina, mun taso a unguwar


Magajiya. Justina yarinya ce mai kyau da ilimi, yanayinta yafi kama da Fulani, shi ya sa mutane daban-daban suke cewa suna sonta, tun tana ‘yar Karamarta. Abin mamaki harda hausawa. Hakan yasa iyayen Justina suka dage akanta, kasancewar suna sonta kamar su kashe kansu. Komai suka samu ita suke siyowa. Justina ‘yar gata ce da ta taso cikin so da Kaunar iyayenta. Sun ci buri akan iliminta, haka kullum sai sun kaita wajen addininmu an yi mata addu’a saboda suna ganin idon mutane yana kan yarinyarsu. Asalin su ‘yan Zangon kataf ne, . amma an ce asalin Mamanta ‘yar Adamawa ce.


Watarana muna hanyar dawowa daga Makaranta, wani saurayi ya tare mu ya ce yana son magana da Justina, ta Ki tsayawa. Haka saurayin nan kullum idan muna hanyar dawowa sai ya biyo mu, tun ba ma tsayawa har ta koma tana saurarensa. Na yi mata magana na ce, “Justin ba addininki daya da mutumin nan ba, me zai sa ki tsaya


kina kula shi? Kin san halin iyayenki idan suka ji duk yadda suke sonki sai sun bata . maki rai.�


Ba ta ba ni amsa ba, amma na ga tana ta murmushi. Sai daga baya nasan sunan saurayin Sani, haka Justina bata da hira sai na Sani, daga baya ma ta gaya min tana son Sani. Na damu sosai haka ina tsoron kada iyayenta su sani, shi ya sa nake basu wajen


hira daga nesa da gidajenmu. Sani ya nunawa Justina yana son ya aureta, amma yana son ta musulunta ita kuma ta gaya masa gaskiya addinin shi baya burge ta ba za ta musulunta ba. Idan Justina za ta kama hannun Sani sai ya gaya mata addininsa ya hana hakan, haka ya ta6lba yin tafiya ya dade bai dawo ba, ranar da ya dawo ta ruga za ta rungume shi saboda farin ciki, amma sai ya dakatar da ita, ya gaya mata shi addininsa bai amince masa da aikata hakan ba. Da haka ya fara jawo hankalinta, har ta fara zama tana jin abubuwa akan addininsa. Ya ci gaba da ce mata, “Addininmu addini ne


mai sauKi, a wajen jarabawa ce kadai mutane suke fadiwa imaninsu yake rauni.� Bayanan nan nasa yasa ta koma gida tana ta tunani, da naje gidan su take bani labari, nayi mata fada, na jawo hankalinta akan kada ta yarda iyayenta su ji.


““A hankali shigarta ta fara komawa ta addinin musulunci, tun iyayen basu kula har hankalin su ya dawo kanta. Babu Bata lokaci suka dauketa suka kaita wajen addu’a ° a ganinsu wani abu ne ya shiga kanta. A maimakon abun ya ragu sai ya cigaba da � Karuwa. Hakan yasa suka tsananta bincike suka sa aka kama Sani har tsawon kwana biyu yana kulle. Justina ta yi kuka ta Ki ci ta Ki sha, shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login