Showing 27001 words to 30000 words out of 123375 words
Chapter 10 - RUBUTACCIYA BOOK 1-2-3-4 Complete Document by Fatima Dan Barno.txt
daya ya yi mata ya dauke kansa gabansa yana fadiwa. Babu laifi yarinyar tana da kalar tata kyan, sai rashin kamun kai da ke dawainiya da ita. Jikinsa ta Karaso tasa hannu ta rungume shi. Kamshin maganin da ta yi amfani da shi, ya yi ta dawainiya da shi, don haka ya fara mayar mata da martani, da taimakon tsaftace jikinta da ta yi. Ba shi ya farka ba, sai da asubahi. Ware idanunsa ya yi yana duba irin barnar da ya yi wa ‘yar mutane. Mamakin samunta a budurwa yafi komai tsaya masa a rai, domin yadda yaga bai taya taba, ita ta fara kawo kanta yasan da matsala. Haka wannan budurcin da ya samu ya sanya ya Kara ganinta da girma da mutunci a idanunsa. Gabadaya zanen gadonsu ya lalace da uban jini. Tana nan kwance kamar kayan wanki tana shakar barcinta. Mamaki ya sa ya kafe ta da ido, yaushe za a yi wa mace hakan ta kwantar da hankalinta? A hankali ya zame kansa ya shiga bandaki ya tsaftace jikinsa, kafin ya sa hannu ya tasheta, tana bude idanu ta fara magana cikin magagi, “Bilal ka rabu da ni barci nake ji.� Sultan ya zaro idanu yana sake dubanta, “Bilal kuma? Waye Bilal?� Ware idanunta ta yi gabanta ya fadi da Karfi, sai yanzu ta tuna abinda ya faru, don haka ta fara raki, “Wash! Don Allah ka taimaka min ba zan itya tashi ba.� Sultan dai kallon ta kawai yake yi, haka kuma zai iya makara yin Sallar asuba, don haka yace “Ki yi haKuri Zakiyya zan makara.� Ya sa kai ya fice abinsa. Yana fita ta mike ta shige bandaki ta gasa jikinta, sannan ta cire zancn gadon ta shimfida masa wani ta sake hayewa gadon tana shaKar barcinta. Babu Sallah bare Salati. Yana dawowa ya dube ta yana tantaman anya ta yi Sallah? Sai kuma ya kau da wannan tunanin a cikin ransa, ya yi tagumi. Wannan ranar ya tanadarwa Nasrcen dinsa, sai ga shi a lokaci guda Allah ya yi ikonsa, wanda babu wanda ya isa ya yi jayayya da yinsa. Shirin zuwa office ya fara, yana tunanin dole sai an samo ma’aikata sun yi masa gyaran gidansa domin har yanzu wari yakeyi sosai. Tashinta ya yi yace ta koma dakinta zai rufe Kofarsa. Ba ta yi mamakin rashin mutuncinsa ba, domin tuni ta fara haddace su. Tana dingishi ta fice.
Faruwar wannan lamari tsakanin Zakiyya da Sultan ya sanya mata wani irin sonsa, a cikin zuciyarta kamar ta mutu. Tana jin bata taba mu’amala da wani namijin da ya gigita tunaninta irin Sultan ba. Duk inda ake neman namiji mai mantar da mace damuwarta, Sultan ya hada abubuwan nan. Tana jin ko dukanta zai dinga yi kullum ba za ta rabu da shi ba. Haka ta raina iyawar Bilal duk yadda take yabonsa kuwa. Shi kuwa ya kasa farin ciki da irin sabon lamarin da ya shiga, abin ya kasa burge shi, haka shi bai san yadda budurwa take ba bare ya fahimci abinda Zakiyya ta yi. Yan sandan ya basu umarnin su samo masu aiki a tsaftace masa cikin gidansa, a fitar da dukkan abubuwan da suka lalace.. Jaridar da ya samu a cikin motar ya dauka yana dubawa. Gabansa ya fadi da ya ga hotonsa hade da na Zakiyya. Cikin sauri ya ware ya fara karantawa. Ya gigita iya gigita, don haka ya ce wa direba ya juya gidan. Yana fitowa daga mota ya dubi-~daya daga cikin ‘yan sandansa yana tambayarsa yaushe akayi wannan hirar? Cike da tsoron yadda ya ga yanayin Ubangidansa ya gaya masa komai. Sultan ya daga hannu ya wanke shi da mari, ya sake daga hagunsa ya dauke shi da mari yana huci. “Ashe baka san aikinka ba aka kawo min kai? Ashe idan kashe ni za a yi zaku iya ba barawon hanya? A cikin gidana zaku bar ‘yan jarida su shigo har falona? Wannan wani irin shirme ne� sandan ya ce, “Sorry sir! Mun so mu hana su, madam ta fito ta zage mu ta ce su shigo.� Sultan ya daka masa tsawa, “Ka yi min shiru bana son bayanin nan. Ita kuke yiwa aiki a gidan nan ko kuwa ni? Daga yau babu wata mace da za ta sake sa doka wani a cikin ku ya bi, ba tare da ya tuntubeni ba. Saboda kune sakarkaru har ayi wannan abun tsawon kwanaki babu wanda ya taba gaya min? A kan me?� Ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, za su iya rantsewa tunda suka fara aiki da shi, ko tsawa babu wanda ya taba yiwa, amma yanzu harda mari, lallai ankai shi Karshe kenan. A fusace ya taka ya shige dakin Zakiyya. Tana zaune tana waya tana bada labarin yadda suka kasance da Sultan, wanda karaf a kunnensa. A duniya ya tsani mace mara sirri, ji yake kamar ya shaketa ya huta. Tana ganinsa ta cire wayar tana zare idanu. “Ke ashe baki da hankah? Da izinin uban wa kika je kika yi hira da ‘yan jarida? A ina kika sami lambarsu da har kika gayyato min su cikin gidana?� Yadda ya harde hannayensa ya kafeta da idanu ta gane amsar kawai yake buKkata, ta ce, “Wata Kawata ce da ke aiki a gidan jarida, ta hada ni da su, shine suka zo. Kayi haKuri bansan zai bata maka rai ba.� Sultan mutum ne mai son
6/5/22, 10:28 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 1 KARSHE🦚*
CHAPTER 10
*BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO*
A JIYA MUN TSAYA
sandan ya ce, “Sorry sir! Mun so mu hana su, madam ta fito ta zage mu ta ce su shigo.� Sultan ya daka masa tsawa, “Ka yi min shiru bana son bayanin nan. Ita kuke yiwa aiki a gidan nan ko kuwa ni? Daga yau babu wata mace da za ta sake sa doka wani a cikin ku ya bi, ba tare da ya tuntubeni ba. Saboda kune sakarkaru har ayi wannan abun tsawon kwanaki babu wanda ya taba gaya min? A kan me?� Ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, za su iya rantsewa tunda suka fara aiki da shi, ko tsawa babu wanda ya taba yiwa, amma yanzu harda mari, lallai ankai shi Karshe kenan. A fusace ya taka ya shige dakin Zakiyya. Tana zaune tana waya tana bada labarin yadda suka kasance da Sultan, wanda karaf a kunnensa. A duniya ya tsani mace mara sirri, ji yake kamar ya shaketa ya huta. Tana ganinsa ta cire wayar tana zare idanu. “Ke ashe baki da hankah? Da izinin uban wa kika je kika yi hira da ‘yan jarida? A ina kika sami lambarsu da har kika gayyato min su cikin gidana?� Yadda ya harde hannayensa ya kafeta da idanu ta gane amsar kawai yake buKkata, ta ce, “Wata Kawata ce da ke aiki a gidan jarida, ta hada ni da su, shine suka zo. Kayi haKuri bansan zai bata maka rai ba.� Sultan mutum ne mai son mutumin da
ZAMU TASHI
zai aikata kuskure ya kuma amsa ya aikata har ya bada hakuri. Don haka ya sassauto, “Ki kiyaye kanki, ki kiyaye mutuncinki, matar aure ce ke, bai kamata ace kin fito a haka a gidan jarida ba, kamar ba matar aure ba. Idan kin siya min mutunci kanki kika siyawa. Daga Karshe kada wani ya sake shigo min gida ba tare da izinina ba, yin hakan zai jawo maki tarin matsalar da baki taba tunani ba.� Ya juya abinsa cike da takaici. Ashmaan ya kira shi a waya, sun jima suna tattaunawa, sannan suka yi Sallama. Yana isa office yaga babu wani aikin kirki, ya shirya motar ‘yan sanda suka kama hanyar Kaduna. Nasreen tana zaune ta hada kai da wani abun, gaba daya ta yi baki, ta rame ta sauya daga Nasrcen din Sultan ta koma Nasrcen Kankia. Nawfal ya koma kamar mai sana’ar bola, haka duk inda ake meman dan uwa Nawfal ya wuce hakan. Hakika da babu Nawfal da rayuwar Nasrecn ya zama abar Kyama. A zaman su maza sun sha kawo mata farmaki, Nawfal ke tsayawa kai da fata wajen ganin ya kareta. A Kalla da zuwansu garin nan, sun yi sana’a yafi kala ashirin. Haka sun
kwana a wurare mabambanta, A yanzu haka ma Kosai ya siyo mata ya ajiye a gabanta tana ci, sai da ta gama sannan ta fara shan kokon, idanun Nawfal suka hasko masa hoton Sultan. Ya yi saurin dauka yana dubawa. Hotonsa ne tare da matarsa. Nawfal ya kafe su da idanu, ya gama karantawa yana al’ajabin irin wannan matsayin da Sultan ya samu, wanda a yanzu wane su su iya tunkarar gidansa? Bakinsa ya subuce ya ce, “Nasreen Deedinmu ya tare da matarsa yanzu ya zama A.I.G Kin ga yadda ya Kara kyau kuwa? Sai dai matar ko lullubi babu a jikinta.� Nasreen ta gigice iya gigicewa ta hau lalube, “Nawfal a ina ka gani? Ya zan yi in gani ni ma?� Bai dube ta ba ya ci gaba da duban jaridar Kosan, “A jarida na gani, wanda a ka Kunsa maki Kosai. Nasreen ke da ba idanu gareki ba ya za a yi ki iya gani?� Nasreen ta goce da kuka. Hakan yasa Nawfal ajiye jaridar ya kafeta da idanu ya rasa me zai ce mata kawai sai ya zuba mata idanunsa wanda shima hawayen ke zuba daga kwarmin idanunsa. A hankali ya fara magana, “Kin gani ko? Deedi ya fi Karfinmu a yanzu. Dole zamu ci gaba da zama a nan, domin gujewa abinda zai sa hankalinsa tashi. Na san soyayyar da zamu nuna masa kenan mu yi nesa da su. Ki kwantar da hankalinki akwai ranar da wahalar nan za ta zama labari.’� Muryar wani suka ji yana cewa, “Alhamdulillahi gasu can a lungun can.�
Nawfal duba Nasreen yace, “Mun shiga uku, waka gani waye?� , ne Mansur ya Karaso yana kwasar dariya, “Nasreen ni ne nan mijinki Mansur. Zuwa nayi insauya maku rayuwa inkuma ajiyeki ki zama matata.� Nawfal zai yi magana, wasu suka kama shi suka tura cikin mota, haka ita ma Nasreen din aka dauketa sai mota. Lalube ta shiga yi tana neman Nawfal, hakan yasa ya kama hannayenta, ta shafa fuskarsa zuwa kansa ta tabbatar da shi ne, don haka ta saki ajiyar zuciya. Ta riga ta sadakar mutuwa za ta yi, ta fi son idan za a kasheta Nawfal ya kasance yana kusa da ita. Sai da suka yi tafiya mai nisan gaske, kafin suka sauka a wani Kauye. A kuma Kofar wani gidan Kasa. Haka suka sauka suka shiga ciki Mansur ya umarci mutanansa da a shigar da su. Nawfal ya ce, “Dakata! Za mu iya shigar da kanmu ba sai wasu sun sake taba mu ba. Ya kamo hannun Nasreen suka shige ciki. Mansur ya nuna masu daki ya ce su shiga zuwa anjima zai zo. Haka suka shiga suka dunKule wuri guda daki komai sai ledan Kasa. Aka kawo musu abinci maradadi, haka suka tuttura suka sha ruwa
Mansur bai bata lokaci ba ya dawo hannunsa dauke da kwanon sha cike da fura yana isowa gabansu ya dubesu duba a tsanake sannan ya fara magana, “Na sha matuKar wahala wajen nemanki Nasreen. Hajiya Salma ta bani aiki akanki, domin in aureki in wahalar da ke, a lokaci guda kuma sai na ji ina son ki da gaske. Da naje gidanku sai Sultan ya watsa min Kasa a idanu, ya wulaKanta ni, ya shake ni yana neman ya kai ni inda ban shirya zuwansa ba. Ina cikin shirya wa Sultan kawai naji labarin Hajiya Salma tasa a sace ku saboda wasu dalilanta marasa tushe. A ranar da na sami labarin nan na yiwa Hajiya Salma gargadi akan duk abinda ya sameki ita ta siya da kudinta dan sai na fanshe bacin raina akanta. Hakan yasa ta tsorata ta gaya min inda aka kaiku. Daga Karshe take sanar min ashe kece matar da aka daura maki aure da Sultan. Bacewarki ya sa mahaifinsu gaya masu gaskiya, Sultan mijinki ne.� Nasreen da Nawfal suka ji dirar maganarsa kamar wani labari wanda ba zai taba faruwa ba. Ta gigice, ta shiga rudu, tana son ta Karyata shi domin Nawfal yaga jarida dauke da matarsa. Don haka ta girgiza kai tana kuka, “A’a ni ba matarsa ba ce, matarsa a yanzu haka tana gidansa.� Mansur ya kafe ta da ido, duk da ta lalace, amma har yanzu yana sonta, kuma da gaske yake ya shirya fuskantar kowacce irin matsala akanta. Zai jure koma menene yaga ya mallake ta. Girgiza kansa ya yi yana murmushi, “Ke ce matar Sultan ta farko, daga baya ne da aka yi ta jiran dawowarki aka ga shiru sai Hajiya Salma ta shiga ta fita ta mallake Abbanku, daga nan aka hada aurensa da Zakiyya ‘yar wajen Hajiya Ladidi, ba tare bada saninsa ba, sai ganin mata ya yi. Ya so ya ci musu ya Ki karbanta a matsayin mata, sai mahaifinsa ya yi masa nasiha, kasancewarsa mutum ne mai jin maganar mahaifinsa shi ne ya karbi Zakiyya a matsayin mata. Allah kadai ya sani ko suna zaman lafiya ko basa zaman lafiya. Amma tabbas ke matar aure ce, matar Sultan, Zakiyya ita ce matarsa ta biyu. Ni kuma ina son ki a yanzu haka, na shiryawa mutuwa akanki. Ki yi tunanin mafita, ina sonki babu idanun zan iya zama da ke. Zuwa anjima zan dawo in ji shawarar da kika yanke, ko aurena, ko kuma ki zama dadirona.� Mansur ya miqe ya fice, ya barsu cikin tashin hankali mara yankewa. Nasreen ta labubo hannun Nawfal ta ce, “Nawafal saita ni gabas don Allah.� Nawfal ya saita ta ta kai goshinta Kasa ta yi sujjada, “Allah na gode maka. Allah kai ne Allah, Allah ka bamu ikon bauta maka a bisa hanya madaidaiciya. Allah kai ka shirya wannna lamarin ka kawo min Karshensa. Allah na gode maka da ka amsa addu’ata a lokacin da ban za ta ba. Allah ka nuna min ranar da mijina zai dawo gareni.�
Farin ciki ya kama Nawfal ta yadda bakinsa ya kasa rufuwa. Haka ya shiryawa komawa ya damKawa Sultan matarsa. Ya kafe Nasreen da idanu yana kallon yadda take cikin farin ciki da annashuwa, wanda rabon da ya ga hakan tun suna gidan su Sultan. Daga baya kuma ya ga ta fara kuka tana magana cikin kuka, “Me muka yi wa Umma haka? Me yasa za ta sa rayuwar Abbanmu a cikin matsala? Duk Kokarin da Abba yake yi don yaga ya faranta mata sai da ta kai shi mahallaka? Me ya sa Deedi zai auri Zakiyya? Umma da kanta take siyo masifa tana kawowa cikin gidanta da sunan gyara? Rayuwar Abba a yanzu shi yafi bani tausayi. Yanzu tuntuni ni matar aure ce? Dama goron da Abba ya kawe min cikin farin ciki na daurin aurena ne? Me yasa Abba bai gaya min ba? Ina tafe da igiyar aure akaina ban sani ba? Allah ka sake hada idanuna da suke rufe da mijina ko da sau daya ne. Nawfal yanzu za ka daina nesanta ni da mijina? Yanzu ka amince son da nake yiwa Deedi a cikin jinina yake? Ka amince Allah ya riga ya hada jinin mu da su Umma? Abu daya ya rage mana shi ne mu gano su waye danginmu? A ina suke? Waye zai gano mana su? Deedi kadai yake da amsar wannan tambayar.�
Nawfal yasa hannu ya goge mata hawayen fuskarta, “Nasreen ba wannan ne a gaban mu ba, abinda ke gabanmu yafi Karfin wannan. Ta ya ya zamu iya rabuwa da mutumin da ya kira kansa da Mansur? Yanzu yafi Umma zama matsala a cikin rayuwar mu.�
Cak! Ta daina kukan, ta yi shiru kamar mai tunani, “Nawfal tunani ya Kare min, ban san ya zanyi ba. Mu ci gaba da addu’a kawai.� Dakin ya yi shiru Kowa da irin tunaninsa. A haka Mansur ya dawo ya same su, ya yi maganar duniya babu wanda ya iya ce masa ko zo ka c1 kanka. Sultan ya iso Kaduna cikin awannin da basu gaza biyu ba, ya wanzu a Kofar gidansu. Kallo daya ya yi wa gidan Nasreen ta fado masa a rai. Har ya juya ya ji muryar mahaifinsa yana masa sannu da zuwa. Ya dubi mahaifinsa sosai, a irin wannan lokacin kamata ya yi ace yana Office.
Tare suka shiga ciki suna rike da hannun juna. “Abba barka da gida.� Bai amsa ba, sai da ya dire shi a falon, sannan suka zauna. “Sultan idonka kenan?� Kafe hoton Nasreen ya yi da idanunsa har yanzu ba a cire hoton ba. “Abba ka yi haKuri na kasa . mance Nasreen. Abba komai ya sauya a rayuwar gidanmu abin yana ba ni tsoro. Ina Umma?� Abban ya dan yi shiru kafin ya ce, “Bana dan jin dadi ne shi ne na turata Office din taje ta sallami mutanen da suka yi Order tasa hannu.� Sultan ya girgiza kai yana al’ajabin yadda Umma za ta shiga harkar da ba nata ba. Haka kuma duk tsauri irin na Abba yau shi ne yake ba Umma izinin tafiya Office dinsa? Hafsat ta shigo ya kafeta da idanu, ta yi wani irin haske ta rame. “Barka da zuwa Yaya.� Murmushi ya yi ya mika mata hannu ta Karaso kusa da shi tana sunkuyar da kal, “Hafsat babu abinda ke damunki ko?� Girgiza kai ta yi tana sake duKar da kai. Sallamar Umma da Hajiya Ladidi yasa duk suka bi su da kallo. Hajiya Ladidi tana shigowa ta kwaye lullubnta tana satar kallon Abba. Ta jima tana kwadayin Alhaji Lukman a matsayin miji, amma bai taba kallonta ba. Sultan ya dan rankwafa ya gaida su, suka amsa cike da farin cikin ganinsa. Hajiya Ladidi ta ce, “Oh ashe kai ne a tafe? Shi ya sa muka ga garin hadari ya hadu. Ya su Zakiyyan? Ai mun ga � hira a jarida hira ta yi kyau sosai.� Sultan ya kauda kai kamar bai ji ba, ya dubi mahaifiyarsa ya ce, “Umma daga ina haka?� Tana shirin yin magana Haidar ya