Showing 72001 words to 75000 words out of 123375 words

Chapter 25 - RUBUTACCIYA BOOK 1-2-3-4 Complete Document by Fatima Dan Barno.txt

Umma ta tabe baki, “In banda iyayi wai * tashin shan tea a daddare, da a can gidan matsafan waye yake kawo maki tea cikin dare? Ke ni bari in gaya maki ba na son tashin dare, ki daina bana so. Wannan iskancin ba zan taba daukarsa ba.�


Sultan ya kafe mahaifiyarsa da idanu yana jin dacin abubuwan da take fada akanta, sai dai ba shi da daman hanawa, da yan. dama da bai bari har abin ya yi nisa haka ba. Ya dube ta yadda ta yi shiru ya ce, “Gobe zan kai ki asibiti a sake duba idanun nan, kafin tafiyarki London ya tabbata. Sai ki shirya da wuri in kai ki in dawo in mayar da ke gida.�


Umma ta dubi Zakiyya sai kuma ta ce, “A‘a bai kamata ka je kai ta asibits ita kadai ba, kamar babu mutine a gidan. Ke Zakiyya da Hafsat ku shirya goben ku raka su.�


Dukkansu suka amsa, shi kuwa kallon mahaifiyarsa kawai yake ransa a Bace. yanzu ba shi da halin fita da matarsa har sai an hada shi da ‘yan rakiya? Shi kenan tsakaninsa da matarsa an sa Hijabi kenan? Rintse idanunsa ya yi yace. “Hafsat, kama hannunta ku koma ciki� ~


Umma ta ce, “A kama hannun wa? ~ Yarinyar da ta iya zuwa kitchen, ta iya shigowa nan, ita ce yau saboda gulma za a kama ~~ hannunta? Ban yarda ba, ban amince ba_ Ta tashi ta lalubi bango ta koma inda ta fito. Ke hafsat wuce ki bar ta.�


Nasreen ta yi saurin miKewa tana dan rintse idanu, “Deedi ka bari zan iya tafiya da kaina ba sai an kai ni ba. Mu tashi lafiya�™ ta yi gaba abinta.


Da idanu ya rakata yana jin tausafiitta, ana cin zarafinta a wurin da aka fi Karfinsa;Saboda bakin ciki a nan falon ya kwanta, musamman da yaga Zakiyya ta ki tafiya don haka yake zargin idan ta bi‘shi za ta gane Nasreen ta shiga dakin


don haka yaki amince mata ya kwanta a nan falon. Sai da asuba ya koma ciki, a nan ya ga ribom dinta haka gadon gaba daya a yamutse yake. Murmushi ya Kwace masa, ya shinshini ribom din ya tura shi cikin kayansa sannan ya yi alwala ya wuce .


Da safe ya gama shirinsa tsaf! Ya fito zuwa dakin Zakiyya, abin mamaki ba ta nan, don haka ya wuce dakin Nasreen. A nan ya sameta ita da Hafsat sun caba kwalliya kamar wadanda za su je gun biki. Gaishe shi suke yi, ya kasa amsawa saboda mamaki,


“Ina za ku je haka kuka yi wannan kwalliyar?� Gaba daya jikin su ya dan yi sanyi, don haka suka hau kame-kame. “Asibiti da Umma ta ce za mu raka ku.�


Mamakin fuskarsa ta Karu. Ya waiwaya yana duban Nasreen, tana zaune daga ita sai doguwar riga, hannunta rike da dan Karamin carbi tana ja. Ya sake waiwayawa yana duban . Umma da ke zaune tana karyawa hankalinta kwance. Ya ce, “Amma dai kuna da Karfin hali, ita wacce za a kai ta asibitin ba ta shirya ba, sai


ku ne iyayen iyayi ko? To babu inda zaku je.Tunda baku da lissafi.�


Umma ta karkace bayan ta danna dankalin turawa a baki ta kurbi ruwan tea sannan ta ce, “Babu abinda zai hana su, zuwa Asibitin nan. Karyar banza kake yi Wallahi. Ai ba sai ka zo gabana kana kushe su ba, na sani sarai ban isa da kai ba, amma ina tabbatar maka duk abinda ka shuka a gidan duniya sai ka girbe shi.�


Sultan ya shafi kansa, “Umma ki yi wa Allah kada ki yi min baki akan yaran nan. Ni abin ne ya bani mamaki, ta yadda daga zuwa Asibiti sai ayi kwalliya, sai ka ce wanda na gaya masu za mu je gidan biki. Ke me ya hanaki . shiryawa?��


Kafin ta yi magana Umma ta yi carab, “Gulma mana! Wai ita mai addini ta tsaya tana jan carbi kamar sabuwar tuba. Ko da yake menene ma..�


Sultan ya yi saurin taran numfashinta, “Umma ki barta a haka za ta tafi kin san ita bata kwalliya.�


� Umma ta tabe baki, “To ina makauniya ina kwalliya? Ai ko ta yi sai dai ta bata fuskarta, tunda ba kallon madubi za ta yi ba.�


Sultan yana kallon yadda fuskar Nasreen ta sauya, bai ce komai ba, ya dubeta, “Nasreen tashi ki dauko Hijabinki.� Babu musu ta tashi ta nufi dakinta. Tana shiga ya bi bayanta.


Umma ta saki baki tana kallonsa. Abinda ya yi zato shi ya tarar, tana share hawayenta wasu suna sake zuba.


Jawo ta ya yi jikinsa hakan yasa ta fashe da kuka. “Bana son kuka Nasreen, idan kina kukan


nan sai in ga kamar baki dauki Umma a matsayin uwa a gareki ba. Ya kamata a ce kin saba da dukkan irin wannan halayyar na Umma.�


Nasreen ta ce a zuciyarta, shi cin mutunci ba a sabo da shi, domin kullum danye yake sake komawa, a maimakon a barshi ya bushe har ganyen ya kakkabe. A zahiri kuma sai ta shiga goge hawayenta yana taya ta. Ya dauko hijabin ya sanya mata, sannan ya dube ta ya ce, “Baki ga yadda hijabin ya yi maki kyau ba.� Ya sumbaci goshinta sannan ya kamo hannunta suka fito. Suna kawowa falon ya saki hannun ya Karasa gun Umma ya ce, “Za mu tafi sai mun dawo.� Ta amsa da a dawo lafiya.


A hanya babu wanda ya cewa wani zo ka ci kanka, kowannen su da irin tunaninsa. Shi Sultan


tuni ya gama kissima dukkan abubuwan da zai yi.


Suna isa Asibitin ya ajiye su a Receiption Ya jawo hannun Nasreen ya ce su zauna anan, su za su je su ga Dokto. Ya zagaya ta baya, ya shiga mota Nasreen ma ta shiga, duk basu sani ba, dan sanda ya ja mota suka fice. Kai tsaye babban Hotel ya wuce da ita, ya kama daki ya shige abinsa.


Nasreen dai binsa take yi bata san inda suka shiga ba, har sai da ta ji sanyin A.C. bayan ta zauna a bisa shimfidadden gadon, “Dee ina ne nan kuma? Wurin wa muka je? Dee ina tsoro kada su Hafsat su ankare bamu nan. Don Allah mu koma.�


Sultan ya rage kayan jikinsa ya zauna kusa da ita tare da cire mata Hijabin, gashinta da yake ta walKiya suka zubo kafadunta. Ya _ tura hannunsa yana yi mata susa, “Nasreen ina shan wahalar rashinki a kusa da ni, Umma kuma ta kafe ta tsare. Bansan ya suke son in yi da rayuwata bane. Yanzu kin ga Hotel muka zo zan samu in yi barcin da na rasa zuwa anjima sai mu je mu dauke su. Karki damu idan suka sha wahala gobe ba za su sake cewa za su biyo mu


ba. Ita Zakiyyan duk irin dadewar da muka yi tare, ai ya kamata ta daga min Kafa tunda babu laifi na sauke dukkan hak KoKinta.�


Nan take fuskar Nasreen ta sauya, da gaske take jin kishinsa akan Zakiyya, ta fi son abinda bata sani ba, akan alaKarsu ta boye sirrin su, idan ya bari tana jin irin wannan kalaman za ta iya shiga wani hali na kishin da halitta ce a jikin mace, sai dai kowa da irin yanayin danne kishinsa. Sultan ya Kura mata ido yana murmushi, bai taba sanin tana da kishi ba sai yau, dama kuma abinda yake son ya gani kenan.


“Kishi kike yi ne?� Ya tambaye ta cikin zolaya.


Sake Bata fuska ta yi ta ce. “Dee ni tsoro nake ji me zai kawo mu Hotel? Bai kamata ba, ga gidanmu na sunna sai mun je wani Hotel? Dee gaski…�


Ba ta samu daman Karashe abinda take son Karasawa ba, ta hadu da zazzafar soyayyar Sultan da take kashe ta a kowani irin lokaci. Dole ta sakar masa jikinta, ba don ta so ba, sai dan salon soyayyarsa daban yake. Sun jima a wata duniyar da bata san wacce ce ba, daga bisani ya Kyale ta dan kansa, domin bai mance
6/10/22, 10:06 - Ummi Tandama😇: *🦚RUBUTACCIYA BOOK 3🦚*




CHAPTER 6




*BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO*





MUN TSAYA






Sultan ya rage kayan jikinsa ya zauna kusa da ita tare da cire mata Hijabin, gashinta da yake ta walKiya suka zubo kafadunta. Ya _ tura hannunsa yana yi mata susa, “Nasreen ina shan wahalar rashinki a kusa da ni, Umma kuma ta kafe ta tsare. Bansan ya suke son in yi da rayuwata bane. Yanzu kin ga Hotel muka zo zan samu in yi barcin da na rasa zuwa anjima sai mu je mu dauke su. Karki damu idan suka sha wahala gobe ba za su sake cewa za su biyo mu


ba. Ita Zakiyyan duk irin dadewar da muka yi tare, ai ya kamata ta daga min Kafa tunda babu laifi na sauke dukkan hak KoKinta.�


Nan take fuskar Nasreen ta sauya, da gaske take jin kishinsa akan Zakiyya, ta fi son abinda bata sani ba, akan alaKarsu ta boye sirrin su, idan ya bari tana jin irin wannan kalaman za ta iya shiga wani hali na kishin da halitta ce a jikin mace, sai dai kowa da irin yanayin danne kishinsa. Sultan ya Kura mata ido yana murmushi, bai taba sanin tana da kishi ba sai yau, dama kuma abinda yake son ya gani kenan.


“Kishi kike yi ne?� Ya tambaye ta cikin zolaya.


Sake Bata fuska ta yi ta ce. “Dee ni tsoro nake ji me zai kawo mu Hotel? Bai kamata ba, ga gidanmu na sunna sai mun je wani Hotel? Dee gaski…�


Ba ta samu daman Karashe abinda take son Karasawa ba, ta hadu da zazzafar soyayyar Sultan da take kashe ta a kowani irin lokaci. Dole ta sakar masa jikinta, ba don ta so ba, sai dan salon soyayyarsa daban yake. Sun jima a wata duniyar da bata san wacce ce ba, daga bisani ya Kyale ta dan kansa, domin bai mance


ZAMU TASHI


alKawarin da ya yi ba. Nasreen tana gigita shi ta yadda yake jin kansa kamar sabon Sarki. Yana sonta ya shirya fuskantar kowani irin Kalubale ne akanta.


Tana kwance a gefensa barci ya kwasheta, shima a nan ya sami natsuwa har barcin ya kwashe shi, cikin kyakkyawan mafarki mai cike da natsuwa. Zai iya rantsewa bai taba samun irin wannan barci ba kamar yau. A Kalla sun kwashi awa biyar suna barcin sannan Nasreen ta fara farkawa, ta lalubo shi tana bugunsa a hankali. “Dee ka tashi mu tafi bansan Karfe nawa ne . yanzu ba.� Sultan ya sake jawota jiki ya rufe su da bargo ya ce, “Yanzu Karfe goma sha daya na safe, sai Karfe daya zamu koma.�


Bata da yadda za ta yi dole ta koma ta kwantar da kai. Irin abubuwan da yake yi mata ne, yasa ta riKe hannunsa tana girgiza masa kai kamar za ta yi kuka. Yana son salon shagwabar yarinyar. Karfe daya ya fada bandaki ya watsa ruwa, ya taimaka mata itama ta yi wankan, duk da bata iya yi a gabansa ba har sai da ya fice saboda kunya. Alwala suka yi, sannan ya ja su Sallah suka gabatar da Sallar azahar, sannan ya rike hannunta suna jerowa. Duk wanda ya zo




wuce Wa Sai ya sake waiwayowa ya dube su, sun yi matuKar kyau, haka sun dace da juna.


Suka fito suka koma Asibitin, ta inda suka bi ta nan suka sake biyo wa suka dawo inda suka bar su Hafsat. Gaba daya kwalliyar nan da suka sha, ta watse, fuska sai maiko take yi saboda wahala. Sun gaji da zama, har sun siya maltina sun sha, amma duk da hakan sai mita suke yi. Suna ganin sun iso, kowacce ta ja bakinta ta yi shiru. Yadda Zakiyya ta kafe su da ido yasa Sultan daure fuska sosai, ya kuma kamo hannun Nasreen ya ce, “Mu je cikin mota.� �


Babu musu ta biyo shi, sauran ma suka mara masu baya. A mota kowacce tambaya ce cike da cikinta, amma babu fuskar aiwatar da hakan. � ,


Bayan sun iso gida ne, Umma ta ce, “Ya na ganku duk kun sha wahala?� Hafsa ta hada rai ba tare da ta ce komai ba, sai Zakiyya ce ta ce, “Umma tunda suka shiga cikin asibitin babu wanda ya sake sanya su a idanunsa. Muna zaune duk mun sha wahala mun lalace.�


Umman ta dubi Sultan, wanda tuni ya kama hanyar barin falon. Umma bata iya cewa komai ba, har ya bacewa ganinta. Juyo wa ta yi gun


Nasreen tana harararta, wai aikin banza a harara a duhu, domin kuwa Nasreen bata san ma tana yi ba. Ta antayo mata tambayar da ya gigita ta, “Ke Nasreen ki gaya min gaskiya tun kafin in yi Kasa-Kasa dake wani lungun kuka shige a asibitin? Ina ya kai ki?�


Nasreen ta dan diririce, hakan yasa Umman ta sake hasko wani abin, ta gyara zama, “Ina takardun da Doctor ya baki? Me ya ce akan idanun?� Nasreen ta rude ta kasa magana, sai muryar Sultan suka ji yana magana, “Doctor ya ce mu dawo gobe za su sake gwada idanun, daga nan kuma sai su bamu result


Umma ta Harare shi, a lokaci guda Nasreen ta saki KaKarfar ajiyar zuciya. Bata kallon Umma, amma jikinta yana bata tana shan uwar harara. Umma ta zame mata kishiya, ta hanata sakat! Ta Ki amincewa ta barta da mijinta, ta amince ta kashe nata auren ta zo ta zauna tana zaman kashe auren danta. Da za ta iya da ta baiwa Umma shawarar auren Sultan Kila ta sami natsuwar irin wannan dakon da take yi


Ita kuma Zakiyya da ta zama bita zai-zai da za ta iya da ta bata shawarar ta koma ta nemi dukkan abubuwan da za ta gyara kanta, domin
dawo da martabarta agun miji, a maimakon zaman sa ido da take yi masu, da kuma kasa Kyale su su zauna su biyu. Sai dai duk wayonta, duk irin gadin da take yi wa mijinta, duk irin matakan tsaron da take sakawa, hakan bai hana mijinta nuna mata cewar shi namiji ne mai cikakken wayo da dabara ba.


Ya nuna mata har yanzu mata basu yi wayon da za su iya gwada wayon su da na mijin su ba. Ya nuna mata ita Karamar ‘yar sa ido ce, sai dai idan bai yi ninyar aikata abu ba, amma da gudu zai aikata ba tare da wata ta taka masa burki ba. Suna ta gadinta, shi kuma yana daukarta a duk lokacin da ya so ya maidota lokacin da yake so. Da za su gane da sun daina wahalar da kansu wajen sanya masu idanu a cikin rayuwar amarcinta.


Umma ta dube shi rai a Bace, “Wai shin kai na tambaya ne? Kana bani mamaki idan kana da gaskiya menene naka na tsoma min baki? Ka barta mana ta yi magana da bakinta, ai makauniya ce kawai ba kurma ba. Kar ko ka dauki mataki akanta tana son raina ni ina magana ta yi banza da ni? Jiya-jiya na gaya maka matar nan taka yawon banza take fita,


amma ka yi min kunnen uwar shcgu, kai a dole baka son laifinta ko? Wallahi ba baki nake yi maka ba, jiki magayi, lokacin da za ta nuna maka asalin kalarta, nawa idanu.� Nasrcen ta dafe Kirjinta tana cewa a zuciyarta, “Insha Allahu, babu ranar da Dee zai yi danasanin aurena, babu ranar da zai kamani da ha’intarsa. Allah ka raba ni da hada aurena da zina, idan nayi hakan me zan gayawa Mahallicina? Da wasu idanun zan dubi mijina in ce ya yafe min?�


Tuni hawaye suka tsinke mata, idan da abinda ta tsana bai wuce a hada ta da sharrin zina ba, da a ce Zakiyya ta yi wannan maganar, da har tashin dare sai ta yi ta roki Allah ya saka mata wannan Kazafin, ta tabbata Allah ba zai jinkirta amsar addu’arta ba. Sai dai wacce ta yi wannan addu’ar ta fi Karfinta, hasalima a matsayin uwa take kallonta. Sultan ya shafi kansa yana satan kallon Nasreen tana kuka, duk sai ya ji babu dadi, ya tsani a taba masa Nasreen, baya son ganin hawayenta tun tana Karama bare kuma yanzu da ta girma.


“Ki yi hakuri.� Ya fada yana duban Umma, wanda a zahiri da Nasrcen yake yi, yaci gaba da cewa, “Bana son in zama ni ne sanadin zubar da hawayenki, ki dinga yi min addu’a ne watarana sai labari.�


Nasreen da maganganunsa suka shigeta, ta ji wani irin sanyi yana shigarta, tabbas saKon da ya aika mata sun iso har cikin kunnuwanta zuwa zuciyarta, da ke narkewa da wani abu mai sanyi, sabanin dazu da yake tafarfasa saboda bacin rai.


Umma kuwa sai ta sakankance da ita yake yi, don haka ta ji sanyi a ranta. Sultan ya juya kawai yana cewa, “Allah na gode maka. Nayi amfani da kalamai masu Karanci, na wanzar da farin ciki a zuciyoyi biyu masu matuKar_. mahimmanci a zuciyata. Allah ya saka maki Umma, ke kika kawo ni duniya kika rene ni, har na girma na ga mahaifiyar Nasreen na zama silar taimakonta. Da baki haifeni ba, Umma da ban zama abinda na zama ba. Allah ya saka maki mahaifiyata, Allah ya haskaka maki duk wani abu da kike ganinsa a cikin duhu. Har abada ke nake fara yi wa addu’a kafin kowa ya biyo baya.�


Kai tsaye Office ya nufa, yana jin nishadi idan ya tuna kasancewarsa da Nasreen dinsa. Yana tashi daga office kai tsaye ya nufi gidan �


Yumnah ya sameta da mijinta a falo suna shan hirar su. Ya shigo suka zauna yana cin abinci suna dan taba hira.


Yumnah ta mike za ta basu wuri domin taga sun dauko maganar case din su. Sultan ya dube ta ya ce, “Kanwata zo mana, wurinki na zo.�


Yumnah ta dawo da baya ta zauna tana dubansa. Ya tashi zaune ya ce, “Don Allah wannan Kamshin da na ji a wurin Nasreen, da yadda fatarta ta yi kyau gashinta ya sake wani tsawo da sheki, a ina kika samo wadannan abubuwan ne? Da gaske nake yi, da kaina zan je innemo mata kayayyakin nan. Ni kadai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login