Showing 24001 words to 27000 words out of 65264 words
Chapter 9 - IZZAR SARAUTA BOOK COMPLETE BY Aunty Baby Ummu Irfan .txt
fara fesa musu tana gama fesa musu tayi murmushin dole dan duk wannan abun karfe hali kawai take tana yi amma da za'a bata huka ace ta kashe su to zata iya.
Sannan tace, "to my son zaku iya fitowa" murmushi yarima Dameer yayi sannan yace, "thinks Momma gaskiya na gode miki sosai Allah ne kawai zai biya ki sabida kin iya zabi ko da banga fuskar wannan sarauniyar Amaryar tawa ba nasan kyakyawa ce ajin karshe shiyasa nake gode ma Allah i love you so much Momma".
Ji tayi kaman ta kurma ihu sabida bakin ciki lallai sai yau take bakin ciki abunda ta haka, shurun da tayi ne yasa yayi murmushin gefan baki sannan yace, "Momma mu tafi ko kar mu fata ma mutane lokaci".
Fuuuuu ta fita bata ko kalle shi ba ita dai Deeyana tana zaune dan bata ma jin abunda suke cewa dan tana can wata duniyar tana tunani, tashi tsaye yayi ya fara tafiya sai da ya kai kofan fita cikin tausansiyan muryan shi yace....
*VOTE*
*COMMENT*
*&*
*SHARE*
*Aunty baby ce*😉✍
[1/6, 10:37 PM] Mum Irfaan🤱🏻: 🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚
🦚🦚
🦚
🤴🏻 *IZZAR SARAUTA*🤴🏻
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }
🎐 ```G•W•A```🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼
*Story*
*&*
*written*
*By*
*Aunty baby* ✍
~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@ Gaskiya writer's Asso~
*DEDICATED TO..*
*MY KHAUSAR* 💋
*Sadaukarwa ga UMAIMA ALIYU*
*BISMILLAHIR RAHMAIR RAHIM*
📝 *page* 3⃣9⃣⏩4⃣0⃣
*_________*📖yace, "zaki iya tasowa" jiki a sanyaye Deeyana ta tashi ta fara takawa a hankali har ta isa gare shi, hannun shi ya zura cikin nata daga ita har shi wani irin shuuu suka ji a jikin su, tafiya ya fara a hankali sannan ita ma ta bishi har suka fita a dak'in.
Lokacin kowa ya isa gurin partyn har yan gidan su Deeyana, wata dalleliyan mota ya hango a can anyi parking din ta da alaman su ake jira karasawa gun motar sukai Abdul na ganin su ya bude ya fito daga cikin motar dan shi zai direving nasu, sakin hannun Deeyana yayi sannan ya bude kofar motar ya sanya ta a ciki murmushi Abdul yayi sannan ya sagaya ya bude ma Dameer.
Shiga yayi ya zauna, ita dai Deeyana gaban ta banda faduwa ba abunda yake sabida bata tab'a zama kusa da wani namiji ba banda yau, Abdul ya shiga motan ya tada sai gurin da za'a gudanar da party d'in, shuru kowa yayi sai zuciyoyin su da ke bugawa Dameer ba abunda yake tunawa sai muryan Abban Deeyana da yake ce mai Deeyana "kanwa ce a gare ka ka riki ta amana" parking d'in da Abdul yayi ne ya dawo dashi daga duniyar tunani da yaje.
Kallon shi Abdul yayi sannan yace "mun iso" kai kawai Dameer ya daga mai alaman to sannan Abdul ya fita a motar, shuru ba wanda ya motsa har kusan minti biyar sai gashi ana k'wank'wasa glass d'in motar glass din ya bude sarauniya maimunatu ce fuskar ta da murmushi ta leko window motar tace, "my bro's ku fito mana".
"Hmmmm" kawai yace sannan ya bude ya fito zagayawq sarauniya maimunatu tayi sannan ta bude ma Deeyana ta kama hannun ta ta fito daga motar sannan ta kaita har in da yarima Dameer ke tsaya ta kamo hannu shi ta sanya a cikin na Deeyana sannan tace, "to mu tafi yan k'anne na".
Murmushi kawai yarima Dameer yayi wanda in baka kula ba baza ka san shi yayi ba sannan suka fara tafiya a hankali, sun zo dai-dai kofar shiga hell d'in kuyangu suka fara zuba musu flawors masu kamshi da kyau, haka suka ci gaba da tafiya a hankali sarauniya maimunatu na bayan su har suka karasa wajan zaman su da sauri gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta matso da murmushi a fuskar ta ta rungume Deeyana da Dameer gaba daya, mutanan gurin suka dau tafi da murna yan uwa Deeyana sai murna suke ganin yanda ake nuna ma Deeyana so.
Shima Dameer rungume ta yayi, tab'e baki gimbiya Haleematun-Sa'adiya tayi tana zagen shi ta bayan shi ta had'e fuska a zuciyar ta tana cewa "kwana kusa ka kusa barin duniya gaba daya kowa ma ya huta" sakin su tayi ta daura hannun ta akan Dameer tana cewa "Allah ya maka albarka Dameer Allah ya sanya muku albarka a cikin rayuwar auran ku".
"Ameen" kowa yace cikin farin ciki wasu suna ganin ai gimbiya khujut haihuwar Dameer kawai tayi amma gimbiya Haleematun-Sa'adiya tafi kowa son shi a duniya, zaunar da Deeyana yayi a hankali a kujeran da aka tanadar musu sannan ya zauna nan aka fara gudanar da abubuwa cikin nishadi.
Ita dai Deeyana tana zaune shuru ko motsi k'wak'wara bata yi DJ ya fara kiran ango da Amarya su dan taka amma Deeyana taki tashi sabida ita bata ko sha'awan waka balle rawa sai da aunty faiza ta rike mata hannu ta kaita sannan Dameer ya taso nan aka fara zuba musu kudi duk da ba wanda yayi rawa a cikin su amma sai zuba musu kudi ake.
Gimbiya Aisha da gimbiya marwa da gimbiya Haleematun-Sa'adiya ai Ba'a magana gurin zuba kudi sai abun ya zama ma kaman gasa ita dai Deeyana baya ma taja ta tsaya tana ganin ikon Allah kudi sai kace paper haka dai sukai ta zuba kudi har DJ yace Amarya da ango su koma.
Ba'a dade ba aka kira su yanka cake dan lokaci ya fara tafiya gashi a yau duk za'a komar da mutane gidajan su, rike mata hannu yayi a hankali suka taso suka tsaya yanka cake wanda sai ya bude ma Deeyana fuska tukun zai bata gimbiya Haleematun-Sa'adiya ce ta sanya hannun ta a saman nasu sannan suka fara yanka cake d'in suna yankawa aka tafa musu sannan aka ce ya bude fuskan Amarya.
Daga shi har Deeyana sai da gaban su ya fadi ita tunda aka had'a su ma bata ko kalle fuskan shi ba balle ta ga kallan shi ta san dai muryan shi mai dadi ne dan in yayi magana kaman kar ya daina sabida yanayin yanda yake maganar, ta b'ata da yayi ne tayi saurin dawo wa daga duniyar tunani da ta tafi a hankali yasa hannun shi ya fara yayi mata net din da ke fuskar ta har yazo dai-dai hancinta bata san lokacin da ta rike mai hannu da sauri ba.
Murmushi kowa na gurin yayi sannan DJ ya fara cewa "to dai amarya bata so a ga fuskar ta Dan haka bari kawai ango ya bata cake a hakan nan ba sai an bude mana fuskar sarauniyar ba" sa a lokacin ta saki hannun shi da sauri tana dan ja da baya kad'an, sarauniya maimunatu ce tayi murmushi sannan ta jawo hannun Dameer ta gutsira cake d'in ta matso da Deeyana sannan ta mai alama da ya sanya mata a baki.
Hakan kuwa yayi ta cikin net din ya shigar da hannun shi ya sanya mata sannan itama sarauniya maimunatu tayi mata kaman yanda tayi ma Dameer d'in daga ganta tayi ganin ya fita tsaho kawai sai ta tsaya cak ganin haka Dameer sai ya dan rank'wafo dai-dai tsahun ta ya dan turo bakin shi kad'an, gaba daya mutanan gurin ya basu dariya hannun ta na rawa ta fara kokarin sanya mai a baki sai da ta kulle idon ta gam sannan ta sanya mai a baki.
Amsa shima yayi ya fara taunawa a hankali idon ta da yake a rufe shiyasa bata san ko ya gama amsar cake d'in ba shi kuma ganin bata cire hannun ta daga bakin shi ba kawai sai ya fara tsoste hannun ji da tayi ana tsotan mata hannu yasa ta cire da sauri tana bude idon ta, duk abunda suke gimbiya Haleematun-Sa'adiya na kallan su sai taji wani irin bakin ciki ya kamata da dunkule hannun ta tana jin zuciyar ta na masifar zafi.
Haka dai akai ta shagali har kusan goma sannan aka tashi motar da aka sanya Deeyana a ciki nan yan uwa ta duk suka zo suna mata sallama dan ance daga nan gida za'a kai su suheema kam ta fashe da kuka tana ganin shikenan ta rabo da kawarta ita ma Deeyana kuka ta fashe da shi sai da aunty faiza ta dunga lallashin su da taga abun ba na kare bane kawai sai raja suheema ta sanya ta a mota sannan ta zo motar da Deeyana take ta kara mata nasiha sannan ta mata sallama ta fita a motar.
Gaba daya yan uwan Deeyana sai da kowa ya shiga mota sannan sarauniya maimunatu ta ja Dameer da ke tsaya gun abokanan shi suna sallama ta sanya shi a motar sannan tace Abdul ya kai su gida dan tasan sun gaji da yawa, sautin kukan tane kawai yake tashi a motar kad'an-kadan ba komai take tunani ba sai irin rayuwa da zata tsinci kan ta a yanzu.
A rayuwar shi baya son kukan mace dan shi mutum ne mai rauni sai yaji duk mugun tausayin ta ya kama shi ji yake kaman ya rungume ta yayi ta lallashin ta amma ina bazai iya ba kuma, a haka Abdul har yayi parking a wani dan-fareran part wanda ko shi Dameer d'in be san da shi ba ashe sarki Fahad Abdullah yasa a gina mai fita Abdul yayi sannan ya bude ma Dameer yace, "ango sai ka fito ai"
Mamaki ne ya kama Dameer sannan ya fito a motar yana kallan in da aka kawo su cikin mamaki yace, "Abdul wannan gurin fa?" Abdul yace, "gidan ka ne malam kaji dadin ka kawai mai-martaba ne yasa a gina ma nima jiya na gan shi".
Tab'e baki kawai yayi sannan ya zagaya ya bude ma Deeyana a hankali ta fara fitowa hannun shi kawai taji cikin nqta sannan taji yana cema Abdul sai da safe ya nufi wannan part d'in da ita, bude kofar yayi parlour ne danfatsetse wanda ya gaji da jin kayan alatu suka shiga sanyi da kamshi turare musu dadi ne suka fara musu sallama a hankali yake addu'a a wanda bata san mai yake cewa ba ta dai ji kawai yana addu'a.
Wasu dakuna ne guda kusan hudu da ban da ban na tsakiyan ya shiga bedroom ne kunna gaba daya wutan yayi sannan ya sakin mata hannun ta ya jata har bakin Bed ya zaunar da ita sannan ya fita, shuru Deeyana tayi dan wani bala'in tsoro ne ya kamata kaman ace mata ar ta ruga sai kankame jikin ta take, kusqn minti goma tana zauna a bakin Bed d'in sai can dai ta tashi ta cire net d'in da ke fuskar ta sannan ta fara kare ma bedroom d'in kallo.
Gaba daya komai na bedroom d'in fari ne da dan ratsin ja ji tayi ya burge ta sosai har Bed d'in italiyan Bed ne shima dai ja da fari ne sai yan kujerun da aka sa a gaba Bed d'in masu masifar Kyau, taba baki kawai tayi ta koma bakin Bed d'in ta zauna tana tunanin iyayan da da yanzu tana tare da su.
Yana fita daga bedroom d'in da ya aje Deeyana dayan dak'in ya shiga wanda shi kuma parlour ne fitowa yayi ya kalle shi sannan ya shiga dayan shima dai parlour ne sai wata kofa daga can kofar ya nufa yana shiga wasu daguna ne guda uku na farkon ya shiga bedroom ne fitowa yayi ya shiga dayan parlour ne sai ya kara shiga dayan shima dai bedroom ne murmushi yayi wato kowa da nashi d'akunan kenan sai ya fito ya dawo kusa da bedroom din da Deeyana ke ciki ya kunna wutan bedroom ne shi kuma komai na cikin shi pink ne har Bed d'in amma shi wannan ba italiyan bane gadon sarauta ne.
K'arasawa yayi bakin Bed d'in dan yasan wannan shine bedroom d'in shi abun da ya gani ne yasa shi zare ido farin kyalle murmushi yayi sannan yace, "lalle duk wanda yasa wannan abun ma zai zo ya dauke abin shi jahlcin banza kawaii mtsww" yaja dan karamin tsaki.
Bacci taji ta fara ji gashi kayan jikin ta wani k'aik'ayi ma yake mata gashi Ba'a zo mata da kaya ba sai ta tashi ta fara duba wardrobe ko zata samu kayan da zata da, akwai ta samu wardrobe d'in cike da kaya, wasu riga da wando ta fito da shi sannan ta shiga toilet ta tayi alwala sannan ta canja kayan ta fito, bacci ne sosai yake damun ta sai kawai ta hau Bed tayi kwanciyar ta.
Gimbiya Haleematun-Sa'adiya tunda suka dawo daga gurin party ta kasa zaune ta kasa tsaye sai safa da marwa take tana da ta sanin wannan aure, tashi tayi ta tafi sasan jakadiya ta taso ta suka fito sannan tace, "yauwa jakadiya yaron na zaki leka min ki gani dak'i daya suka kwana ko kuwa dan in dak'i daya suka kwana to ba abunda zai hana shi kusantar ta in ko ba daki daya suka kwana ba kinga kenan gobe mun samu damar watsa wannan aure dan wallahi ni yanzu hankali na be kwanta da wannan aure ba sai gaba da yayi ta faduwa".
Mitsike idon ta jakadiya ta fara yi sannan yace, "to uwar gijiyata an gama yanzu zan dubo miki" murmushi gimbiya Haleematun-Sa'adiya tayi sannan tace, "to ina jiran ki" part d'in su yarima Dameer jakadiya ta nufa tana yi tana waige-waige sabida in wani ya ganta ta san ta shiga uku a masarautar mure.
Dai-dai window bedroom d'in da ta san na Dameer ne ta tsaya kollon window tayi ba yanda za'a hango mutum sai ta fara kokarin bude window, yarma Dameer da yana kan sallaya ya idar da sallah kenan yaji kaman motsin wani abu a jikin window sai ya natsu tsam dan yaji ko wani abu ne motsin ya k'ara ji wanda yafi na d'azu ma sai ya tashi ya dan leka.
Kaman mutum ya gani sai ya tsaya tana tunani to mai mutum zai zo yi wajan window nan da daran nan haka, gimbiya Haleematun-Sa'adiya ce ta fadu mai a rai murmushi yayi sannan a hankali ya fara takawa har ya fita a bedroom d'in, rasa ina zaiyi ma yayi sai kawai ya shiga na Deeyana.
Yana shiga ya fara tunanin to ina zai kwanta yasan dai gimbiya Haleematun-Sa'adiya ce zata yi mai wannan aikin wato a zo a duba su dak'i daya suka kwana ko kuwa, Bed d'in ya kalle kwance take cikin bargo ta kudundune har kanta sai kawai ya haye Bed d'in ya kwanta a dayan gefen.
Jakadiya kuwa duk iya yin ta ta bude window ta kasa kuma bata hango komai hakan nan ta koma ta sanar da gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta kara da cewa amma tana tunanin dak'i daya suka kwana kuma gobe zata tabbatar dan ita zata tashe su bacci ma da sassafe zata shiga part d'in nasu ta amso wannan farin kyalle, a haka zuka rabu a gobe da sassafe jakadiya zata je part d'in su yarima Dameer d'in.
Washe gari kiran sallah farko a kunnan yarima Dameer dan ba wani bacci yayi ba tashi yayi a hankali yanda Deeyana baza ta ji shi ba ya fita a dak'in bedroom d'in shi ya shiga yayi wanka sannan yayi alwala ya fita masallacin masarautar.
Bayan ya dawo ya shiga bedroom d'in Deeyana yaga ko ta tashi amma bata tashi ba sai ya fara tunanin to ya tashe ta ko ya barta can dai ya fara tashin ta hannun shi ya daura akan pillow din da take kwance ya dan girgiza shi kad'an bude ido tayi dqn Deeyana bata da nauyin bacci.
"Tashi ki sallah" kawai yace sannan ya fita a bedroom d'in tashi tayi sannan ta shiga toilet tayi wanka sannan ta fito ta bude wardrobe ta dauko hijab ta shinfida sallaya ta data sallah, ko da ya fita bedroom d'in shi ya shiga ya kwanta sabida bacci yake ji.
Ita ma tana idar da sallah bed ta koma ta kwanta, misalin karfe bakwai na safe yaji ana buga musu kofa tashi yayi yana tsaki sannan ya fito parlour ya bude kofar, jakadiya ce jiki na rawa tashi "barka da safiya yarima kaya kuri na tashin ku daman gimbiya fulani ce tace, wai na zo na dauke abunda ta ta ajiye jiya".
"Wani abu ta ajiye kuma?" cewar Dameer dan yaji abunda jakadiya zata fad'a dan yasan abunda suke nufi, murmushi jakadiya tayi sannan tace, "hmmm ummm farin kyalle".
Murmushin gefan baki yayi sannan yace, "kece zan kawo mata" kallon shi jakadiya tayi da sauri shima kallon ta d'in yake sai kawai tace, "to bari in je ranka ya dade sannan an jima za'a zo a shirya gimbiya dan za'a zagaya da ita masarautar mure gaba daya" kai kawai yarima Dameer ya daga mata, fita tayi a dakin part d'in gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta huce tana shiga ta tatda ita gimbiya Haleematun-Sa'adiya ma take jira.
Da sauri gimbiya Haleematun-Sa'adiya tace, "ya bangan ki da kyallen ba?" duk abunda yace, mata haka ta gaya ma gimbiya Haleematun-Sa'adiya girgiza kai ta fara tace, "lallai Dameer yana wasa dani to wallahi sai na nuna ma yaron nan shi ba komai bane kuma yanzu nan dole kije ki kira min shi".
"To" jakadiya tace, sannan ta fita, Dameer kuwa har ya koma bedroom sai kuma ya fito ya tafi part d'in gimbiya Haleematun-Sa'adiya shiga yayi da sallama lokacin kuma jakadiya zata kiran shi sai kawai ta huce bata ce ma komai ba, samun gimbiya Haleematun-Sa'adiya yayi tana zagaye dak'in sallama yayi be bari ta amsa ba ma yace, "Momma lafiya kuwa?".
Murmushin dole ta k'ak'alo sannan tace, "ina fa lafiya my son na aika a amso min abu kace zaka kawo min to yanzu ina yake kasan dai wannan abun yana da babban muhimmanci dan za'a fi ganin matar ka da mutunci a wannan gida namu".
Dariya yayi har hakuran sa na beyana sannan yace, "haba Momma ai wannan ba matsala bane tunda ba adini bane ai ba dole bane sai kowa yasan sirrin ka da matar ka".
Hadiya wani miyau tayi dan taga in ta tsaya tana mai magana a hankali zai raina mata hankali sai kawai tace, "wannan abun fa Dameer dole ne in kuma bata kawo maka budulcin ta bane kawai