Showing 45001 words to 48000 words out of 65264 words

Chapter 16 - IZZAR SARAUTA BOOK COMPLETE BY Aunty Baby Ummu Irfan .txt

kace be dace ba shikenan Allah ya kara ma nisan kwana da lafiya mai amfani".








Daga hannu mai-martaba yayi sannan yace, "shikenan Allah ya kaimu anjiman amma kasan abunda zakayi mai muhimmanci ne kaman yanda ka fad'a" gaishe shi Dameer ya kara yi sannan ya mai godiya kallon gimbiya Haleematun-Sa'adiya da ta cika tayi fam yace, "Momma na a fito lafiya" kawai ya tashi ya fita.








Direct gidan Ammi ya huce yaje ya dauko ta suka huce gidan su Deeyana daman su Abba sun shirya nan suka huce gidan su Baba, da yake wannan karon da fadawan shi ya fito gaban dayan su dai sun hadu sai masarautar mure abba da baba suna mota daya sai kuma Amma da Ammi suma suna mota daya sai yarima Dameer da mama(kakar su Deeyana kenan).






Haka har suka fara shiga babban gate d'in masarautar mure wanda take da babban tambari baba kallon masarautar kawai yake yanzu Aliyu daga wannan masarautar ya fita kuma d'a a cikin ta Allah mai iko, nan motocin duk sukai parking a babban kofar da zata sadaka da fada, yarima Dameer ne ya fara fita a motan dan yana so ya shiga fada yaga kowa ya hadu.






Shiga fada yayi kowa da ake buk'ata ya ganshi zaunawa yayi kai gaisuwa gurin mai-martaba tukun ya fara bin duk yan fadan da kallon bega gimbiya mabaruka ba gimbiya Haleematun-Sa'adiya ma bata nan amma har su gimbiya Aisha da gimbiya marwa suna nan tashi yayi zai fita nan yaci karo da gimbiya mabaruka sai k'annin shi mata ko kallon shi basi ba haka suka wuce suna kwasar gaisuwa gun mai-martaba.






Fita yayi dan yaje ya tawo da Deeyana sai kuma su Ammi yana isa ya tatda Deeyana daman a shirye take alkebba kawai yace ta sanya sannan suka fito gurin su Ammi ya isa nan duk suka fito a mota suka bi bayan shi bayi da fadawa har sun dan fara gulma dan duk wanda idon shi ya fad'a kan gimbiya khujut sai ya kara kallo suna mamaki dan sun san yau ba zaman lafiya a masarautan mure duk wanda yake da tarihin masarautar.






Gimbiya Haleematun-Sa'adiya tana can kilisar ta dan daman tace, ba inda zata dan wulak'ancin kaman Dameer ne zai sa a wani had'a mai mutune ko uwar mai zaiyi oho mtswwwwwwwww gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta ja tana jin tsanar Dameer na kara shiga cikin zuciyar ta.






*To ni kam aunty baby nace wannan cakwakiya har ina to muna dai zuba ido zamu ga wannan abun* πŸ€’






Dameer da Deeyana suka fara shiga fada su Ammi na daga waje dan ba yanzu ne lokacin shigan nasu ba, har lokacin dai ya kara dubawa bai ga gimbiya Haleematun-Sa'adiya ba kusa da waziri yaje sannan ya mai magana nan da nan sai naga waziri ya tashi ya fita, direct kilisar gimbiya Haleematun-Sa'adiya ya huce yana zuwa ya gaya mata cewa kowa ya hadu ita ake jira Fulani.






Da gimbiya Haleematun-Sa'adiya tace ma waziri a fad'a ma Dameer din baza ta ba sai waziri ya dan lallashe ta da mata kirari nan dai ta tashi suka huce jakadiya na take mata baya har suka shiga fada nan kowa dai ya hadu yarima Dameer ya tashi ya xauna a kujeran shi wanda tashi ce daga ta mai-martaba sai tashi to shi da yake ba zaman fada yake ba shiyasa.






Nan yarima Dameer yayi gyaran murya sannan ya kalle mai-martaba sarki Fahad Abdullah yace, "ya mahaifina wanda babu kaman shi a duniya shekaru ashirin da hudu kenan da faruwan wani babban al'amari a masarautan nan wanda hankali kowa ya tashi duk wanda yake cikin masarautar mure to Alhamdullh yau Insha Allah zan wanke mahaifiyata da Kanin mahaifina wato yarima ALIYU a cikin wannan zargi da basu ji ba basu gani ba".






Ba gimbiya Haleematun-Sa'adiya ba kowa na fadan gaban shi ya fadi mai-martaba kuwa rasa bakin magana yayi lallai yaron nan to mai yake shirin yi kenan kowa gyara zama yayi yana jiran abunda yarima Dameer zai k'ara fad'a, tashi yarima Dameer yayi tsam ya Kira su Ammi da Abba sai baba mama da Amma sai Deeyana kuma da ta cire hular alkebban da ke kanta, saurin tashi mai-martaba yayi yana kallon abun da ke shirin faruwa kaman a mafarki.






Ko kallon shi Ammi batai ba ta samu gu ta xauna haka shima Abba zaunawa yayi mai-martaba idon shi k'yar kan Ammi, gimbiya Haleematun-Sa'adiya kuwa ai Ba'a magana har dan fitsari sai da ya fara zuban mata kanta yayi wani irin sarawa da bai tab'a mata ba a duk tsawan rayuwar ta, yau ta kasance bakar rana a duk ranar kun da take.








Murmushi gimbiya mabaruka tayi tana gode ma Allah da ya nuna mata wannan ranar ashe da rabon zata ga wannan ranar, waziri da malaman fada gaba daya kan su ya kulle kowa jiran karin bayani yake,






Abba ya gyara murya ya kai gaisuwa ga fada kaman yanda al'adan masarautar take sannan ya fara cewa, "shekaru ashirin da wani abu an tozarta mu a wannan masarauta wanda har ya kai an kore mu wanda bamu san komai ba akan wannan k'azafi da aka mana to yau Allah ya bamu ikon kare kain mu sannan kuma mu fallasa duk wani makirci da ake a cikin masarautar nan" jiki na rawa gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta tashi tace, "Kai Aliyu mai ya dawo da kai masarautar nan to tun wuri ka tashi ka fita da kai da wannan bakar masiyaciyar" ta nuna Ammi.








Murmushi Ammi da Abba sukai sannan Ammi tace, "gimbiya Haleematun-Sa'adiya kenan mai kike ci na baka na zuba ai yanzu nan zamu bar muku masarautar ku dan ba zama ya kawo mu ba daman amma sai komai ya fallasu tukun dan haka kija bakin ki kiyi mana shuru" "mai-martaba wai ko baka cikin fadan nan ne da zaka ba.." kafin ta karasa abinda zata ce mai-martaba ya daga mata hannu alaman kar ya kara jin bakin ta.






Mai-martaba bai lura da Deeyana ba sai yanzu da idon shi ya kai kansu baba da suka zaman mai bakuwar fuska bai san ko su suwaye ba shuru yayi dan a zaton shi Ammi ta kara aure ne k'anwar Dameer ce ji yayi zuciyar shi tayi wani baki kaman ta fashe amma kuma yariyar kama take mai da jinin shi shuru dai yayi yana jiran yaji abunda Aliyu zai ce.






Abba yace, "gimbiya Haleematun-Sa'adiya kin dade kina cin karan ki ba babbaka a masarautar nan kin dade kina wulakanta duk wanda kika so kin mayar da masarautar mure kaman masarautar dak'in ki da sai abunda kika ga dama za'a yi kin mana k'azafi mai muni sannan kin saka an kore mu an wulakanta mu duk wannan abun da kikai bai ishe ki ba har gashi Allah ya juya al'amarin shi ta hanyar muguntar da kike so ki had'a kin had'a ruwan dafa kanki shine yanzu da kika gano kuma kike so ki kashe ni ko?"






Zaro ido tayi ganin duk idon yan fadan ya dawo kanta harta mai-martaba kowa kallon ta yake sarauniya maimunatu kuwa kafe ta tayi da ido ko kiftawa, Abba ya cigaba da cewa "jiya kin ba Deeyana abu ta kai min wannan abun ba komai bane face guba kuma in kin musa gashi" Abba ya fad'a yana fito da ledan da gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta bawa Deeyana, waziri ne ya tashi ya amsa ledan dan ya gani sannan sauran mutan fada ma su gani.








Waziri ya mika ma sarkin fada sarki fada ya bude ya fara ma mai-martaba bayanin komai, sannan Dameer yace, "Abba Deeyana y'a ce ga kanin ka yarima ALIYU sannan kuma mata a gare ni".




Waziri da malaman fada duk suka zaro ido suna jin abun kaman a mafarki to ya akai basu gane Aliyu ba wannan abu da mamaki, mai-martaba sarki Fahad Abdullah da shima abun ya bashi mamaki sosai ya kalle gimbiya Haleematun-Sa'adiya da ji take kaman ta nutsai dan kallon da ya watsa mata shi ya saka cikin ta murdawa.






Mai-martaba yace, "Haleematun-Sa'adiya daman kin san yariyar nan yar Aliyu ce shiyasa kika had'a auran" kasa tayi da kai dan tasan yau kam tata da k'are, sai da mai-martaba ya k'ara maimaita abunda yace, sannan bakin ta na rawa tace, "A'a mai-martaba ni ban sani ba sannan ai nasan tabarkazar da uban ta yayi a masarautar nan bazan tab'a yarda na had'a wannan aure ba dan haka ko a yanzu ma zai iya sakin ta".






Mumushi Dameer yayi sannan yace, "shiyasa kike son kashe shi yanzu ko" saurin kallon shi tayi sannan tace, "lallai Dameer zaka iya fada wa uwar ka haka" sosai zuba ke keto ma jakadiya dan ita a yau tasan sarki sai ya kashe ta dan haka gwara tun wuri ta fad'a ma mai-martaba gaskiya ko hukuncin tq yazo da sauki.








Tashi tayi a hankali sannan ta matsa gurin su mai-martaba tace, "Allah ya baka yawan rai ina da magana" mai-martaba yayi alaman zata iya magana, mamaki gimbiya Haleematun-Sa'adiya tayi to mai jakadiya zata fad'a kafin ta fada abunda zata ce taji jakadiya tana cewa.






"Allah ya baka yawan rai kayi hakuri da duk abinda zan fad'a dan ba laifina bane gimbiya Haleematun-Sa'adiya ce ke saka ni, sai da ta share hawaye sannan ta cigaba da cewa, kazafi tayi ma su yarima ALIYU da gimbiya khujut wallahi basu aikata komai ba kuma lokacin da ka yanke wannan hukuncin ba a haiyacin ka kake ba haka ma matuwar su gimbiya maimunatu da sukai hatsari to sawa tayi aka kwance musu burkin mota duk suka mutu sannan kuma ko yarima Dameer da baka kula da shi shima duk aikin asiri ne.."






Tsawa mai-martaba ya daka mata wanda ya razana duk wanda yake cikin fadan, magana ya fara cikin kakkausan murya "Haleematun-Sa'adiya kar kice min wanman duk abunda ta fad'a gaskiya ne yanzu ke kika kashe min mahaifiya sannan ki kullawa k'anni na da matar da nafi so a duk duniya sharri innalillahi wa'ina ilaihir rajiun".




"Kwarai kuwa duk abunda jakadiya ta fad'a gaskiya ne komai da kaji ta fad'a haka yake wani abun ma in aka fadan ma baka san mai zakayi ba" gimbiya mabaruka ta fad'a tana kallon gimbiya Haleematun-Sa'adiya da kallon jakadiya kawai take.






Abba da Ammi kuwa farin ciki sosai suka ji da jakadiya ta fallasa komai, mai-martaba kuwa ji yayi kaman ya kashe gimbiya Haleematun-Sa'adiya da kannun shi yanzu daman yana zaune da makiyar shi ne bai sani ba lallai gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta gama cutar da shi a duniya, gimbiya Aisha da gimbiya marwa kuwa farin ciki fal ransu dan a duniya sun tsani gimbiya Haleematun-Sa'adiya.






Waziri da malaman fada da sarkin fada kuwa magana suka fara "Allah ya huci zuciyar mai-martaba" mai-martaba kallon gimbiya Haleematun-Sa'adiya yayi sannan yacde, "daman haka kike ashe ke kika kashe min mahaifiya hmmmm Haleematun-Sa'adiya ban tab'a zaton kiyayyar da kika min ta kai haka ba amma komai kikai kinyi wa kan ki amma ki sani bazan tab'a barin ki ba Haleematun-Sa'adiya na sake ki saki uku" kallon waziri yayi sannan yace, waziri a dauke ta a tafi da ita gidan kurkuku a yanke mata hugunci mafi kask'anci da tsanani sannan nan da wata shida a kashe min ita dan sai ta girbi duk abunda ta shuka".






"Innalillahi wa'ina ilaihir rajiun" shine kawai abunda sarauniya maimunatu ke mai-maitawa kallon mai-martaba sannan tayi sannan ta fashe da kuka "Abba dan Allah ka sassautawa mahaifiyar mu munsan tai maka lafi amma kayi hakuri dan girman Allah" "wayyo Allah na na shiga uku lallai mai-martaba yanxu ni zaka ce ama wannan hukuncin komai da nayi ai ta sanadiyar sonka ne amma shine zaka min wannan abun?"






Murmushi gimbiya mabaruka tayi sannan tace, komai da karshen shi Haleematun-Sa'adiya yanzu k'in tab'a zaton wannan ranar a gare ki to gashi yau Allah ya nuna miki karshen ki wannan huguncin shi ya dace da ke" mai-martaba yace, "ke kuma jakadiya waziri ka tafi da ita ka yanke mata duk wani hukunci da yayi dai-dai da laifin ta wanda zai sa yan baya suyi izina da ita".






Dan Allah ka min rai mai-martaba ka yafe min gimbiya khujut da yarima ALIYU dan Allah ku yafe min wallahi nayi ladama nayi da nasani" jakadiya ta fad'a tana kuka.




Murmushi Ammi tayi sannan tace, Allah ya yafe mu gaba ki daya, tashi sarkin fada yayi sannan yace, ma jakadiya da gimbiya Haleematun-Sa'adiya su tashi su tafi, da sauri gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta tashi tana cewa "wallahi ba wanda ya isa ya kaini wani gidan kasu kai mai-martaba kama fad'a musu wallahi zan iya kashe kowa a gunnan nan ba wani gidan kasu da za'a kaini"






Dameer ji yayi ba dadi kwalla ya share dan gaskiya ta bashi tausayi tashi yayi daga inda yake sannan ya durkusa gaban mai-martaba yace, "Allah ya kara ma nisan kwana dan Allah a mata afuwa ko dan su maimunatu".






Saurin dagatar da shi mai-martaba yayi sannan yayi ma sarki fada alama da a tafi da su kuka sosai sarauniya maimunatu da kannan ta suke gimbiya Haleematun-Sa'adiya kuwa zama tayi kaman zararriya sai zage zage take a haka aka tasa keyar su aka fita da su jakadiya sai kuka take da danasani.






Nan Ammi ta tashi tana shirin fita a cewar ta an gama kuma mai zata tsaya yi, saurin dakatar da ita mai-martaba yayi sannan yace, yana son magana da su, ko kallon shi Ammi batai ba sannan tace, "sun gama abin da ya kawo su dan haka ko zaman minti daya baza ta k'ara ba".






Tashi gimbiya mabaruka tayi sannan ta dafa kafadar Ammi tace, "haba khujut ban sanki da haka ba tunda har yace akwai maganar da zakuyi ai ya kamata ki zauna kiji" murmushin karfin hali kawai Ammi tayi dan zuciyar ta ba karamin zafi take mata ba sannan tace, "to bakomai" ta kuma ta zauna.






Mai-martaba ya sallama kowa a fadan yace duk zasu iya tafiya kowa ya tashi wasu na farin ciki wasu kuma na kuka kaman su sarauniya maimunatu, nan mai-martaba ya gyara zama sannan yace,






"To Alhamdullh..








~Wayyo na gaji πŸ€•sai Allah ya kaimu gobe~ πŸ’ƒ








*VOTE*
*COMMENT*
*&*
*SHARE*








*Aunty baby ce*✍
[1/6, 10:37 PM] Mum Irfaan🀱🏻: 🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚
🦚🦚
🦚










🀴🏻 *IZZAR SARAUTA*🀴










🌐
*_ALHERI WRITER'S* *ASSOCIATION_* ✍
*~[ Alheri danko ne, duk inda kayi shi zai dawo gare ka, burin mu mu ribantu da alherin da ke cikin wannan harka]~*








*ALHERI SAI DAN AlHERI* πŸ‘Œ












*Story*
*&*
*written*
*By*
*Aunty baby* ✍








*DEDICATED TO..*
*MY NEAT LADY*








*Sadaukarwa ga UMAIMA ALIYU*








*BISMILLAHIR RAHMAIR RAHIM*










πŸ“ *page* 5⃣9⃣⏩6⃣0⃣












________πŸ“–bayan wata daya, mai-martaba sarki Fahad Abdullah da kanshi shi da gimbiya Mabaruka suka shirya suka je gidan Abban Deeyana akan yayi hakuri ya dawo masarauta amma Ina an buga an raya yake sosai hankali mai-martaba ya tashi amma bashi da yarda zaiyi dole sai da yaji gidan baba ya roke shi sosai.






Baba ya shirya suka je gidan Abban Deeyana tare da mai-martaba amma Ina shi Abban Deeyana yace, yayi "alkawari bazai kata taka k'afar shi masarautar ba" sai da baba ya bashi baki sosai sannan ya hakura yace zai kuma kuma mai-martaba ya k'ara rokan alfarmar baba shima ya koma masarautar dan yanzu sun zama daya.






Baba ya amince nan Abban Deeyana ya kira Dameer ya sanar mai Dameer ba k'aramin Dadi yaji ba har da cewa shima zai zo Nigeria dan wannan baban abun farin ciki shi ne, suma Deeyana da Ammi sunji Dadi sosai daman mai-martaba ya dame Ammi kullum waya yaje Saudi Arabia yafi so uku amma taki bashi fuska Dameer ma yace ba ruwan shi in ta yarda ta koma to in Bata koma ba kuma shikenan.






Ranar wata talata gaba daya Abba da baba suka shirya komai nasu suka koma masarautar mure anyi shagali Sosai ranar Amma ai ba'a magana, gashi su gimbiya Marwa suna janta a jiki komai tare ake da ita na masarautar sunje Saudi Arabia ma sun sauke umrah sunyi sati biyu sun dawo.






Yanzu kowa hankali shi ya kwanta sai dai mai-martaba da yake ta fama da Ammi, kunyar zuwa wajan Al'mustapha yake shiyasa, itama Ammin tana son komawa gurin mai-martaba amma su take sai ya gane kuskuran shi tukun.






Gimbiya Haleematun-Sa'adiya tayi baki ta ramai aikin wahala ake sata gashi ba wani abincin kirki sarauniya Maimunatu kon ta gaji da kuka ta daina dan tace ita ta jama kanta amma kullum maganar ta kun mai-martaba ya taimake su ya sakan musu mahaifiya.






Ko sauraran su baya yi, jakadiya ma haka yanzu ko ganin kirki bata yi sabida mugayan Yan D'akin su da suke mata duka azaba iri-iri kwata-kwata bata da hutawa ga aiki Mai tsanani da ake Bata kullum cikin kuka take da tuba ga Allah.








Deeyana da Dameer kam ba'a magana suna bama junan su kulawa sosai Dameer ke son Deeyana baya so ko kad'an yaga bacin ranta yanzu zai zama wani iri ya susuce, haka ita ma ta b'angaran Deeyana tana ba Dameer kulawa sosai dan Bata gajiya da buk'atar shi in dai zai zo mata to sai ta kore ma suna farantawa junan su fiye da yanda ake zato.






Kowa addu'ar shi Allah ya basu zuri'a dan har yanzu shuru ba bayani, yanzu Shirin zuwa Nigeria suke kuma wannan zuwan ne ake sa ran za'a mai da auran Ammi da mai-martaba dan mai-martaba ya matsa hakan nan su Jadda suka ce tayi hakuri ta koma tunda dai kuskure an riga anyi sai dai a kori gaba kuma.






Mai-martaba ya zo Saudi Arabia an k'ara daura musu aure wanda kowa ke farin ciki da murna wannan karon su gimbiya Mabaruka suka zo daukan Ammi nan su Deeyana duk suka shirya suka tafi Nigeria tare, babban part wannan karon aka ma Ammi na gani na fad'a Dan duk masarautar ba inda ya Kai nan Kyau da tsari su gimbiya Marwa da gimbiya Aisha ba ruwan su dan duk sun san irin son da mai-martaba yake ma Ammi shiyasa Basu kishi.








Deeyana na part d'in Amma sai fira suke sai kusan bakwai na dare sannan ta koma part d'in ta lokacin Dameer ya kusa dawowa, kitchen ta shiga ta dan dafa mai abincin da tasan yafi so mai sauki sannan tayi wanka ta tsantsara kwalliya tayi shigan english west musu kyau da daukar hankali








A Kam ba'a wani Dade ba Dameer ya shigo taje da sauri ta rungume shi shima rungume ta yayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login