Showing 6001 words to 9000 words out of 65264 words

Chapter 3 - IZZAR SARAUTA BOOK COMPLETE BY Aunty Baby Ummu Irfan .txt

ta cikin farin ciki duk wani bakin ciki sai taji ya gushe.






Jakadiya tana kallon kyau gimbiya khaujut ta fita parlour da sauri har tana tuntube part d'in gimbiya Haleematun-sa'adiya ta shiga cikin rawan jiki irin na munafukai.






Gimbiya Haleematun-sa'adiya tana kwance bak'in ciki duniya ya ishe ta Dan anyi anyi da ita taje tayi ma mai-martaba sarki Fahad Abdullah sannu da zuwa tak'i.




Jakadiya ta shigo ta same ta cikin rawan Baki ta fara magana, "barka da hutawa uwar gijiyata uwar gida gun sarki Fahad wacce Babu kamar ki, in kin bani dama nazo Miki da wani labari".




Tashi tayi zaune tana kallon jakadiya sannan tace, "fad'i Ina sauraran ki".




K'asa da murya tayi sannan tace, "Allah ya taimake ki mai-martaba Ashe balarabiya ya auro yanzu na ganta da Ido na kyakyawar gask.." bata k'arasa ba sabida wani gigicacan Mari da taji saman kuncin ta.




"Wannan bak'in labarin kike gaya mai to Wallahi Bari kiji duk lokacin da kika k'ara zuwa min da irin wannan labarin sai kin fuskan ci hukunci Mai tsauri" cewar gimbiya Haleematun-sa'adiya.




Shuru jakadiya tayi dafe da kuncinta sannan tace "a min afuwa ya sarauniyar kyakyawa uwar gidan da Babu kamar ta zan iya tafiya? ".




Daga Mata Kai tayi kawai sannan jakadiya ta fita tana data sanin zuwa,




Shagali ake sosai sun nuna farin cikin su da zuwan ta duk wata al'ada da suke in an kawo amarya gidan sai da sukai Mata shima mai-martaba sarki Fahad Abdullah ba k'aramin Dadi yaji ba ganin yanda suke murna.




Yarima Aliyu k'anin sarki Fahad Abdullah sosai yake nuna ma gimbiya khaujut kauna ganin ta yake kaman k'anwar shi, ita ma tunda ta fuskanci Yana kula da ita sai take sakin mai fuska.




Haka masarautar ta kasance har na tsawon kwana biyu ana shagulgula, duk wannan shagalin da ake gimbiya Haleematun-sa'adiya bata tab'a zuwa ba, sarki Fahad Abdullah kon ko a jikin shi be nuna ya damu ba shi ta khaujut kawai yake dan ya sama ranshi insha Allah baza ta tab'a kukan yan uwan ta ba.






Bayan an gama duk wani shigali da ake komai yayi dai-dai sarki Fahad Abdullah ya had'a gimbiya khaujut da gimbiya Haleematun-sa'adiya yayi musu nisiha sosai yace khaujut ta dunga girmama gimbiya Haleematun-sa'adiya kowa dai ya gimama dan uwan shi.




Duk suka ce insha Allah sannan kowa ya tashi ya tafi part d'in shi, tun daga ranar gimbiya Haleematun-sa'adiya bata kara saka gimbiya khaujut a Ido ba dan ko ganin ta bata son yi so da dama tana zuwa gaisheta sai tace ace tana bacci.






Haka zaman nasu ya kasance sarki Fahad Abdullah yana kokarin ganin yayi adalci a tsakanin su dun da haka dai yafi son gimbiya khaujut dan kullum ya ganta sonta k'aruwa yake a zuciyar shi.




Rayuwar gimbiya khaujut a masarautar mure tana jin dadin shi sosai Amma Abu biyu ne kawai yake damunta na daya iyayan ta da kullum sai tayi kuka in ta tuna yanda suka rabu Amma.




Sarki Fahad Abdullah yana lallashin ta akan tayi hakuri insha Allah zai kaita ta gansu ko lokacin zuciyar su tayi sanyi.




Na biyu kuma shine yanda kishiyar ta take nuna Mata tsana wani abu da ta lura da shi shine in a gaban mai-martaba ne tana janta a jiki sosai Amma in ita da ita ne ko kallo bata ishe ta ba.




Cikin gimbiya Haleematun-sa'adiya nata girma yanzu har ya shiga wata tara addu'a kawai take Allah yasa namiji ne duk hankalin ta yanzu a tashe yake burin ta kawai ta haife namiji.




Lokacin kuma gimbiya khaujut take dauke da cikin wata uku sarki Fahad Abdullah yayi murna sosai haka masarautar mure cike take da murna.




Ranar wata alhamis gimbiya Haleematun-sa'adiya ta tashi da nakuda mahaifiyar ta kawai ta kira nan da nan tazo suka tafi asbitin cikin masarautar.




Ba'a fi awa biyu ba Allah ya sauke ta lafiya, tana haihuwa bata tsaya komai ba ta fara duba abunda ta haife Kash mace ce kuka ta fashe da shi, wani irin bakin ciki ya rufe ta kaman ta kashe jaririyar taji.






Nan da nan aka gyara ta da jaririyar ta, mai-martaba yana fada aka Kira shi aka gaya mai murna sosai yayi Nan fada ma ta cika da farin ciki.






Tun daga ranar kullum cikin bakin ciki take ita taso ta haifi namiji tasan dai shi zai gaji masarautar mure amma bashi ta haifa ba gashi ta lura khaujut ciki gare ta sai ta k'ara shiga cikin damuwa kar ita ta haife namijin dole kon ta san yanda za'a yi.






Haka akai suna yariya taci sunan matar mai-martaba tsuhon sarki gimbiya Maimunatu, anyi shagali k'ala-k'ala.






Bayan wata hudu lokacin cikin gimbiya khaujut watan shi bakwai a lokacin kuma sarki Fahad Abdullah ya shirya musu tafiya zuwa saudiyya dan ziyaran Yan uwan ta.






Gimbiya Haleematun-sa'adiya ki yarta tana da wata hudu tayi bul-bul abinta,




Ranar da zasu tafi har airport gimbiya Haleematun-sa'adiya ta raka su sai da taga jirgin su ya tashi sannan ta koma gida, suna Isa saudiyya masaukin su suka huce.




Wanka suka yi suka huta sannan suka huce Haram Dan sauke umrah bayan sun sauki sai sarki Fahad Abdullah ya Kira abokin shi Al'mustapha Dan ya fad'a Mai sun zo.




Amma wayan baya shiga haka yayi ta kira a kashe sai kawai suka huce gidan su khaujut d'in, shiko Al'mustapha yayi tafiya ne zuwa Dubai shine yasa ba'a samu wayan shi ba.




Bayan sun Isa gidan sarki Fahad Abdullah da gimbiya khaujut suka shiga gidan, jikin ta ne yayi sanyi sosai Dan bata San da wani Ido zata kalle iyayan nata ba.




Noking suka fara yi da sauri wani yaro yazo ya bud'e yana ganin khaujut ya juya da gudu cikin gidan yana fadin, "khaujut ga khaujut ta dawo".




Maman tane ta fito da sauri tana tambayan yaron "wata khaujut d'in?" Kafin yaron ya bata amsa su khaujut sun shigo.






Da sauri khaujut taje ta rungume mahaifiyar ta tana kuka itama rungume ta tayi tana shafa kan ta, tsawan da suka ji ne yasa ta saki khaujut da sauri ita kam khaujut sai da cikin jikin ta ya murd'a.






BABAN ta ne fuskan Nan nashi a daure ya matso kusa da mahaifiyar ta kamar zai bige ta yace, "bana ce Karta k'ara zuwa min gida ba menene dalilin da ta zo kika kulata? ".






Kasa magana ma maman nasu tayi sabida ita a ganin ta be kamata suyi musu wannan tarba ba, kama hannun khaujut yayi ya fara tafiya da ita dai da ya kaita har kofar Gate d'in gidan sannan ya saki ta.




Sarki Fahad Abdullah yana tsaye Yana kallon ikon Allah nuna Mata waje yayi yace, "kin ga kofar gidan Nan na kara ganin ki a wajan Wallahi sai na kusa kashe ki kije can wajan Wanda suka daura miki auran Ni yanzu na tashi a uban ki ban sanki ba Baki sanni ba".






Kuka khaujut ta fashe da shi sannan tace, "ya Kai mahaifina ka yafe min laifin dana ma Allah ya riga ya tsara wannan abun bazan iya jure fushin ku ba" ta k'arashe maganar tana zubewa a gaban shi.




Juyawa yayi yayi shigewar shi ciki ko kallon ta beyi ba, da sauri sarki Fahad Abdullah ya karaso ya rik'e Mata hannun ta mik'e sabida cikin da yake jikin ta.




Kanta ta daura a girjin shi ta saki kuka Mai tsuma zuciya, mota ya shigar da ita Yana lallashin ta Nan direba ya tada motar suka tafi masaukin su.






Haka suka zauna a k'asa Mai tsarki har na tsawon sati biyu, sun je gidan uncle ya amshe su da farin ciki da murna har ta kwana.




Kullum sai taje gidan su Amma baban su ya Hana ta shiga ranar da zasu koma Nigeria ma Sai da taje Amma ko kallon ta beyi ba.






Haka suka komai Nigeria duk wal-walan ta ya ragu duk in ta tuna fushin da iyayan ta suke da ita, kullum Yana k'ara kwantar Mata da hankali akan tayi hakuri komai zaiyi dai-dai.




Haka take ta rainon cikin ta har yanxu ya Kai wata Tara cib kullum jiran haihuwa ake, gimbiya Haleematun-sa'adiya kuwa ta gama shirya duk wani abu da zata ma duk Dan da ta haife shiyasa yanxu Bata gaban ta.






Wata safiyar juma'a gimbiya khaujut ta tashi da nakuda Wanda tun shida na safe aka kai ta asbiti har kusan sha-biyu tana Abu daya.




Hankalin kuwa na masarautar ya tashi dan mai-martaba ya kasa zauna ya kasa tsaye, jakadiya ce ta shigo D'aki nashi da sauri tace.......








*Vote*
*Comment*
*&*
*Share*








*Aunty babyn ku ce* ๐Ÿ˜‰๐Ÿ˜‰โœ
[1/6, 10:37 PM] Mum Irfaan๐Ÿคฑ๐Ÿป: ๐Ÿฆš๐Ÿฆš๐Ÿฆš๐Ÿฆš๐Ÿฆš๐Ÿฆš๐Ÿฆš
๐Ÿฆš๐Ÿฆš๐Ÿฆš๐Ÿฆš๐Ÿฆš
๐Ÿฆš๐Ÿฆš๐Ÿฆš
๐Ÿฆš๐Ÿฆš
๐Ÿฆš








๐Ÿคด๐Ÿป *IZZAR SARAUTA*๐Ÿคด๐Ÿป











ยฎโ˜„
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATIONโœ*
{ _Gaskiya ษ—aya ce daga ฦ™inta sai ษ“ata, burinmu mu faษ—akar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }




๐ŸŽ ```Gโ€ขWโ€ขA```๐ŸŽ
*_GASKIYA DOKIN ฦ˜ARFEโ€ข_*๐Ÿ‡๐Ÿผ










*Story*
*&*
*written*
*By*
*Aunty baby* โœ






*DEDICATED TO..*
*MOM AYSAR*
*Masoyiya Allah ya huce zuciyar ki* ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜






~VOTE & FOLLOW 4Wattpad @ GaskiyaWritersAsso.~








*BISMILLAHIR RAHMAIR RAHIM*










๐Ÿ“ *Page* 1โƒฃ5โƒฃโฉ1โƒฃ6โƒฃ








*___________*๐Ÿ“– Gimbiya Haleematu-Sa'adiya kuwa tunda taji ance gimbiya khaujut ta haihu ta bazama asbiti, lokacin tuni an huce da gimbiya khaujut gida.






Taji haushi sosai da Dan ba Haka ta so ba, sai a lokacin ta tambaya mai gimbiya khaujut ta haifa aka ce Mata namiji cikin tashin hankali ta furta, "namiji? ".




Sai da kanta ya sara jiri ya fara d'ibar ta da k'yar ta iya Kai kanta cikin part d'in ta tana zuwa kuwa ta zube kan Bed tana kuka Bata San ma wani irin bakin ciki take a lokacin ba, "shikenan wannan matsiyaciyar zata gaje masarautar Ina bazai tab'a yuhuwa ba" Haka take fad'a sai kace wacce ta haukace.




Masarautar mure kuwa ta kid"e da bushe-bushe da kid'e-kide kowa murna yake, mai-martaba sarki Fahad Abdullah da Kan shi ya bud'ewa talakawa D'akin abinci kowa ya d'ibi yanda yake so.






Matan tsohun sarki rabon atamfa da shadda kawai suke Yarima Aliyu kuma ragona kawai yake fitarwa ana yanka wa.




Haka dai masarautar mure ta cika da shagulgula har ranar suna, ai ranar ba'a magana, yaro yaci sunan tsohun sarki Abdallah, gimbiya khaujut take kiran shi da Dameer wato( *heart* , *conscience* ).




Gimbiya Haleematun-sa'adiya kuwa tun da gimbiya khaujut ta haihu so daya taje ta ganta ko jaririn ma bata iya Bari ta gani ba sabida bak'in ciki da take ciki,






Anyi taron suna na lafiya an tashi lafiya, Bayan suna gimbiya khaujut taci gaba da rainon Dan ta Dameer cikin kwanciyar hankali Wanda a duniya ba Wanda take so a yanxu barin shi.






Hmmmmm Daman larabawa ba dai na son 'ya'ya ba a gaban kowa nuna Mai so da kauna take, haka ma ta fannin mai-martaba sarki Fahad Abdullah sosai yake nuna Mai so har fada yake zuwa dashi.




Wannan soyayya da yake nuna Mai sai ya dasa wa gimbiya Haleematun-sa'adiya tsanar yaron kwata-kwata a duniya taji Bata da mak'iyi kamar shi sabida tana ganin ai 'yarta ita ce babba Amma ba'a nuna ma 'yarta so kaman yanda ake wa wannan yaron.




Haka Nan sai ta aiko a Kai Mata shi ta nunawa kamar tana son yaro, Amma Ina ba Haka bane ana Kai Mata shi zata Fara gana Mai azaba yaro yayi ta kuka a rasa Mai ke damun shi.




Har dai gimbiya khaujut ta fara ganewa sai ta daina Bata shi kwata-kwata nan ma Sai da tayi ta bala'i gimbiya khaujut tayi kamar Bada ita take ba.




Kwance tashi ba wuya yanzu Dameer har yayi wata shidai a duniya lokacin yayi masifar wayyo, kyawun shi ya k'ara fitowa irin na jinin larabawa kowa son yaron nan yake sabida wayyon shi.




Sarki Fahad Abdullah ya dau son duniya ya daurawa wannan yaron ko kukan shi yaji ko d'aga Ina ne sai ya bar fada ya tafi gurin shi, Haka ma k'anin shi Yarima Aliyu yana bala'i son yaron.




Ya shiga wata na bakwai mai-martaba sarki Fahad Abdullah ya shirya Mata tafiya k'asar saudiyya wannan karon ita daya zata tafi banda shi sabida suna da wani gaggarumin taro a masarautar shiyasa.




Har airport ranar da zata tafi mai-martaba ya raka ta da kuyangun ta, sai da yaga jirgin su ya tashi sannan suka koma gida cike da k'ewar matar shi da d'an shi.




Ita ma haka tana jin kewar mijin nata haka suka Isa saudiyya sai a lokacin kuma tsoro da fargaba abunda iyayan ta zasu Mata yazo Mata Dan yanzu ma Bata San da wani Ido zasu kalle ta ba.








Jiki a sanyaye su kama hanyar gidan su, suna Isa bak'in Gate d'in gidan kuma sai ta kasa shiga nan dai jikin ta a sanyaye suka shiga hayaniya taji a babban parlour gidan alaman duk Yan gidan suna parlour.




Sallama tayi sannan ta fara noking d'in kofar a hankali wani Dan k'aramin yaro ne ya fito yana ganin ta ya rungume ta yana murna, ita ma rungume yaro tayi sannan suka shiga parlour.




Maman ta dake zaune kan kujera ta fara araba da Yar tata da sauri ta mik'e tana murna ganin ta itama gimbiya khaujut da sauri ta Isa gare ta ta rungume tana kuka.




Baban da yake zaune yana kallon su abunda zai Mata kawai yake rayawa, gaba daya yan uwan ta da suke zaune suka tashi suka rungumeta.




Kukan jariri da suka ji ne ya katsa musu murna da suke yana hannun daya daga cikin kuyangun ta ita ta manta da shi ma Sai murnar ganin Yan uwan ta da take.






Kallon yaron kawai suke sai tsala kuka yake da sauri mamanta taje ta amsa yaron tana kallon shi kama da ta gani da khaujut ya bata tabbacin jikan ta ne.




Rungume yaron tayi a jikin tana hawaye tasan rabon yaron nan ne yasa Allah ya k'addara aure tsakanin khaujut da sarki Fahad, baban su da yaga yaro sak shi da sauri ya tashi yana kallon khaujut d'in.




Mik'a mai yaron maman khaujut tayi tana murmushi, amsa yayi shima yana kallon yaron dariya kawai yaron yake sakan mai sai abun ya burge baban ya rungume yaron a jikin shi.




Gimbiya khaujut na ganin haka ta Isa gare shi da sauri ta rungume shi tana kuka, shafa kanta baban yayi sannan yace, "tayi shuru ta daina kuka" zubewa gimbiya khaujut tayi a k'asa ta rik'e k'afar shi tana kuka ta k'asa magana.




D'ago da ita yayi sannan ya rungume ta yana sanya mata albarka, maman taji Dadi Sosai sai ta rungume su gaba daya tana ma Allah godiya.




SOSAI gimbiya khaujut ta rok'i gafaran su, baban yace, "shi daman burin shi ya ganta cikin farin ciki tunda tana lfy kuma ai magana ya huce".




Haka suka kasance cikin farin ciki da annashuwa da murnar ta ta Kira sarki Fahad Abdullah ta fad'a Mai shima yaji Dadi Sosai yace, "ma shi zai zo ya tafi da ita sai ya k'ara basu hakuri".




Dameer kam kaman zasu had'iye shi suke ji sabida farin cikin, a Haka har sukai sati biyu nan sarki Fahad Abdullah ya zo tafiya dasu shima sunmai tarbar mutuncin sosai baban yace, "ai komai ya huce sai dai ya kara rik'e musu 'ya da Amana".




Kwanan shi biyu da zuwa suka shirya suka dawo Nigeria, cikin farin ciki wannan dawowar da tayi tafi jin dadin ta akan duk tafiyan da suke sabida iyayan ta sun daina fushi da ita, haka taci gaba da kula da yaron ta.






Wata safiyar juma'a gimbiya Maimunatu da gimbiya Ameena suka shirya zasu tafi can wani kunye ziyara sunje lafiya hanyar dawowa Allah ya had'a su da hadari Wanda duk sun biyun ba Wanda ya rayu har uku daga cikin musu tsaran su ma.




Mutuwan ya girgiza duk masarautar mure, kowa yaji mutuwan Nan barin ma mai-martaba sarki Fahad Abdullah yafi kowa shiga tashin hankali.




Haka aka musu sutura aka kaisu gidan su na gaskiya,






Tun daga ranar mai-martaba ya kasa samu sukuni kullum cikin tunani yake gimbiya khaujut ta tambaye shi menene damuwar shi amsa daya ce ba komai ta rasa gane Kan shi.






Lokacin kuma gimbiya Haleematun-sa'adiya ta yaye yarta tana dauke da wani cikin fad'an farin ciki da take ciki ai ba'a magana addu'ar ta kawai Allah yasa namiji ne.






Sai kuma wani makircin da suke had'awa ita da jakadiya Wanda take ganin duk in tayi wannan abun to zaman gimbiya khaujut a masarautar mure ya Kare..






********


Bayan shekara daya




Gimbiya Haleematun-sa'adiya ta haihu lafiya ta k'ara samu 'ya mace wacce kaman ta kurma ihu da aka ce mata mace ta haifa ta k'ara daukar aniyar fansa akan gimbiya khaujut Dan a haukarta gimbiya khaujut ce ke hana ta haihuwar mace.๐Ÿคฃ




Dameer yayi girma sosai yayi wayyo har ya iya tafiya ma lokacin kuma gimbiya khaujut take Shirin yaye shi sai kawai maman ta tace ta Kai shi gunta ta yaye shi haka kon aka yi suka shirya suka kai shi saudiyya.




Bayan sun dawo ne befi da sati uku ba gimbiya khaujut ta fara laulayin ciki murna gurin mai-martaba sarki Fahad Abdullah ba'a magana yaji Dadi Sosai Dan be cire Rai Allah zai k'ara bashi namijin ba.




Tunda gimbiya Haleematun-sa'adiya ta lura tana da ciki ta fara had'a yanda zatai ta zubar da shi, sai jakadiya ta Bata wata shawara cikin sauki kuwa tabi shawaran nan.






Sai dai kawai gimbiya khaujut ta tashi taji jini na zuba ba'a Dadi ba cikin ya fita gaba daya, sarki Fahad Abdullah beji dadin zubewar cikin Nan ba amma ba yarda zaiyi tunda haka Allah ya nufa.




Ba'a fi wata biyu ba ta k'ara samun wani cikin nan suka fara tattalin shi kaman kwai, shima tana fahintar tana da ciki ba'a fi sati ba ta k'ara zubar da shi.




Nan fa abun ya fara damun gimbiya khaujut sai ta nemi shawaran mai-martaba sarki Fahad Abdullah akan tayi family-planing ko in ta huta cikin zai dunga zama.




Nan ya nuna mata bacin ran shi akan be yarda ba k'ila in ta kuma zamu ba zai zube ba d'in, hakan nan ta hakura Bata yi ba d'in.




Shima bata huce wata hudu ba ta k'ara samun wani cikin, shima dai watan shi daya ya zube Nan abun ya fara ba mai-martaba sarki Fahad Abdullah haushi.




Sai wata zuciyar na cemai Anya kuwa ba zubar da cikin nan take ba ya za'a yi ciki su uku yana zubewa cikin yarda da abun da zuciyar shi tace mai ya tashi ya tafi gun gimbiya khaujut cikin fushin da bata tab'a ganin shi da shi ba....










Vote
Comment
&
Share










*Aunty baby ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login