Showing 42001 words to 45000 words out of 65264 words

Chapter 15 - IZZAR SARAUTA BOOK COMPLETE BY Aunty Baby Ummu Irfan .txt

kije ki kaima mahaifin ki dan shine ya cancanci kyauta ita ma mahaifiyar taki insha Allah akwai nata amma mahaifin shine gaba" shuru Deeyana tayi dan Bata san ma mai zata ce ba da k'yar ta iya budan baki tace, "Allah anfana".






Tashi gimbiya Haleematun-sa'adiya tayi sannan tace, "bakomai Deeyana ai ke y'ata ce" da Ido ta bisu har suka fita a D'akin, ledan hannun ta ta k'ara dubawa to menene wannan?? dashi kenan take so ta kashe mahaifin ta lallai wannan matar ta cika makira tashi tayi zata shiga bedroom d'in ta Dan tana so ta Kira Abban ta yanzu, yana tsaye ya sakala hannun shi cikin k'irjin shi, tun shigowar gimbiya Haleematun-Sa'adiya yake tsaye amma basu gan shi ba.






Kallon ta yayi sannan ya duba ledan da ke hannun ta, hannun shi ya miko alaman ta bashi mik'a mai tayi tana kallon shi yana amsa ya fara duba ledan yana duba abin da ke ciki girgiza kai kawai yayi sannan yace, "da mai zaki da ita ya kamata duk abinda zakiyi ki dunga sanar min".






Dafe Kan ta tayi da hannun ta sannan tace, "nasha baka nan ne shiyasa!! hmmmm yanzu da gaske dai kashe mahaifina take son yi? ". murmushi Dameer yayi yana cizan baki shi sannan yace, "insha Allah komai nata ya kusa zuwa karshe" "hmmmmm Allah yasa" Deeyana ta fad'a sannan ta shiga bedroom d'in ta.






Kitchen ya shiga ya hadu β˜• coffee sannan ya fito ya zauna kan kujera ya daura laptop d'in shi yana dan wani aiki, ita ma Deeyana fitowa tayi ta zauna tana buga game a wayan ta shuru kusan minti goma can dai Dameer ya aje laptop d'in ya dawo kujeran da Deeyana ke zaune ya daura Kan shi kafad'an ta ya fara danna waya shuru Deeyana tayi mai dan tasan tsokana yake nema can dai yaji tak'i kula shi sai ya dawo da kan nashi cinyarta.






Tab'e baki Deeyana tayi sannan ta cigaba da abinda take dan kwatakwata tunanin gimbiya Haleematun-Sa'adiya yak'i barin ta shiyasa baza ta iya biye mai ba shi kam Dameer so yake su saba Sosai yanda son shi zai shiga zuciyar ta lokaci daya, kallon ta yayi sannan yace, "wai menene?" Aje wayan tayi sannan tace, "to yanzu ya zamuyi da wannan matar ni gaskiya tsoro nake ji".






D'ago Kan shi yayi sannan yace, "tsoro kuma hhhhhh ki cire komai a ranki anjima zamu fita kaman gidan Abban muka je dan nasan yanzu idon ta na kanki zaki fita ko baza ki fita ba to in muka fita shikenan mun gama da game d'in yau" "hmmmmm" kawai Deeyana tayi ta kwantar da kanta Kan saman k'irjin shi.






Tunda gimbiya Haleematun-sa'adiya ta koma D'aki take ji yau kaman ta taka rawa sabida tasan ta gama da Aliyu a duniya sauran Deeyana kuma dan ita ma bata barta bane tana nan dawowa kanta sai an gama da mutuwar Aliyu kuma, jakadiya dake kusa da ita zaune ta washe Baki sannan tace, "Allah ya taimake ki yau mai kike ji akan wannan Abu da zai faru ace Aliyu zai mutu ai gobe sai kin had'a mana party".






"Hhhhhhh karki ji komai jakadiya ai abunda yafi party ma zan had'a ke dai Allah yasa muji alkhairi" gimbiya Haleematun-Sa'adiya tayi maganar tana wani kafirin murmushi.






Alhmdllh mai-martaba sarki Fahad Abdullah Allah ya bashi lafiya ya dan samu sauki dan har fada ya fito Amma abunda yanzu ke damun shi shine tunanin Aliyu da gimbiya khaujut da baya bace Mai ko na minti daya ko wani lokaci cikin tunanin halin da suke ciki yake.






Wajan karfe biyu Yarima Dameer ya fito fada ya shiga ya duba jikin mai-martaba yaga yaji sauki sosai, sai da sukai sallahn asr sannan ya koma part d'in shi Deeyana ta shirya suka fita, gidan da Ammi take suka nufa Deeyana ba k'aramin Dadi taji ba suna Isa Ammi ta fito ta tare Deeyana ita ma Sai murna take Dan tayi missing d'in ta haka sukai ta fira sannan Ammi ta shirya itama dan zasu gidan su Deeyana.








A mota Dameer ke ba Ammi labarin zuwan da gimbiya Haleematun-Sa'adiya tayi gun Deeyana murmushi Ammi tayi sannan tace, "hmmmm Allah sarki duk wani makirci nata yazo karshe da yarda Allah" haka sukai ta tattaunawa har suka Isa gidan su Deeyana, a tare Deeyana da Ammi suka shiga gidan sallama sukai Amma najin muryan su Deeyana ta fito da sauri tana musu sannu da zuwa.






Parlour ta kai su tana ta kallon Ammi gaisawa sukai cikin mutunci kaman sun San juna Amma sai haba haba take da su ta kawo musu wannan ta kawo musu wancen haka dai sosai Ammi ta zage suna ta firan su Dan Dameer da Deeyana ma D'akin Deeyanan na da suka shiga suma suna nasu firan haka har Abba ya dawo beyi mamakin ganin Ammi ba sai ma murna da yayi.






Nan Abba ya zaune suka fara gaisawa da Ammi, "Abba yace, "abun mamaki ko a mafarki ban tab'a zaton zan k'ara ganin ki ba Bari kuma d'ana Dameer Allah mai iko!!!;" "hmmmmm Allah kenan ai nima Wallahi ban tab'a zaton zan dawo Nigeria ba gashi wacce ta raba ta k'ara had'awa".






Shuru Abba yayi sai yake jin kaman yanzu abun ya faru to ba yanda zasuyi haka Allah ya tsara nan dai suka fara tattaunawa yanda zasu tona ma gimbiya Haleematun-Sa'adiya duk wasu makirici da take kullawa, Ammi ta gayawa Abba abunda ta kawo ma Deeyana d'azu akan ta kawo ma mahaifin ta, nisawa Abba yayi Sannan ya tashi da kan shi ya Kira Dameer da Deeyana ya fara magana kaman haka.....










*AFUWAN AFUWAN kuyi hakuri masoyana nasan na muku laifi rashin jin IZZAR SARAUTA kwana biyu tafiya ce ta kamani shiyasa Amma kuyi hakuri nima ba Haka Raina yaso ba insha Allah yanzu zaku dunga jina kullum*












*VOTE*
*COMMENT*
*&*
*SHARE*








*Aunty baby ce*✍
[1/6, 10:37 PM] Mum Irfaan🀱🏻: 🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚
🦚🦚
🦚










🀴🏻 *IZZAR SARAUTA*🀴










🌐
*_ALHERI WRITER'S* *ASSOCIATION_* ✍
*~[ Alheri danko ne, duk inda kayi shi zai dawo gare ka, burin mu mu ribantu da alherin da ke cikin wannan harka]~*








*ALHERI SAI DAN AlHERI* πŸ‘Œ












*Story*
*&*
*written*
*By*
*Aunty baby* ✍








*DEDICATED TO..*
*MISS XERKS*❣








~Happy birthday πŸŽ‚πŸŽˆπŸŽ‰ to meπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒam +1~






*Sadaukarwa ga UMAIMA ALIYU*








*BISMILLAHIR RAHMAIR RAHIM*










πŸ“ *page* 5⃣5⃣⏩5⃣6⃣












________πŸ“–"da farko dai Allah ya sanya ma auran ku albarka Dameer Deeyana wannan aure naku had'in Allah ne dan mutum bazai tab'a had'a wannan abu ba to Allah ya baku hakurin zama da juna" gaba dayan su suka amsa da Ameen.






Abba ya cigaba da cewa yanda zamu billo ma wannan matar shine a mai-makon gobe taji mutuwa ta kaman yanda take zato sai kuma mu, mu shirya mu tafi masarautar mure masarautar da ban tab'a zaton zan k'ara shigan ta ba Amma yanzu k'addara ta saka zan shiga dan in kawo k'arshan gimbiya Haleematun-sa'adiya".




Murmushi Ammi tayi sannan tace, "gaskiya ne wannan shawaran naka yayi insha Allah gobe zamu kawo k'arshen gimbiya Haleematun-sa'adiya sai tayi danasanin rayuwar ta tunda dai ita kullum burin ta ta saka mutum cikin damuwa da bak'in ciki insha Allah ita ce zata dauwama a haka".






Haka Dameer ma ya d'aga kai yace, "eh Abba yayi Allah ya Kai mu goben" Ameen suka ce sannan suka fara tsara yanda zasu shiga masarautar mure gobe in Allah ya Kai mu,.




~Ni kam aunty baby nace gobe akwai cakwakiya a masarautar mureπŸ™†~






Kusan bakwai na dare sannan suka bar gidan su Deeyana kowa fuskar shi cike da farin ciki, sai da Dameer ya fara sauke Ammi a gidan ta sannan suka huce nasu, tunda suka Isa Deeyana jikin ta a sanyaye yake Bata san dalilin ba Dameer ya fahinci haka har bedroom d'in ta ya biyo ta ya tambaye ta menene tace bakomai.




Kusan karfe goma gimbiya Haleematun-sa'adiya sai sagaye bedroom d'in ta take bata san mai yake mata Dadi ba da har tayi tunanin ko taje taga su Deeyana ko har Aliyu ya mutu ne amma wata zuciyar tace ta Bari sai gobe, hakan nan ta kwanta zuciyar ta na bugawa sabida Bata so a samu matsala yazo be mutu ba.






Yana idar da sallah ya huce bedroom din Deeyana Dan yaga ya take yana shiga ya tatda ta Kan Bed idon ta biyu batai bacci ba matsuwa yayi ya hau Bed d'in sannan ya cire mata hannun ta da tayi tagumi da shi, d'an firgita tayi dan bata tsanmaci zai shigo D'akin a wannan lokacin ba.






Kallon juna suka fara Ido da Ido sun kusa minti uku a haka sannan tayi sauri tsaida idon ta kasa tana runtse idon, kwanto da ita yayi jikin shi ya fara shifa bayan ta a hankali kaman yana mata tafiyan tsutsa can dai ta dan matsa jikin shi.






Kara mannota yayi jikin shi murya a sanyaye ya fara magana, "Yar k'wan wata lafiya kuwa tunda muka dawo naga baki da walwala menene pls ki gaya min" girgiza Kai Deeyana ta fara yi sannan tace, "ba komai kawai dai ji nayi gaba na na faduwa".




Shafa kanta yayi sannan yace, "oh my God yar k'wan wata dan gaban ki na faduwa sai ki kasa bacci to ya kamata in kika ji haka sai ki tashi kiyi sallah sannan ki dauki Qur'ani ki karanta sai kiji komai na zuciyar ki ya fita kin daina jin wani faduwar gaba da sauran su" d'aga kai Deeyana tayi alaman haka ne sannan tace, "to zanyi hakan".






"To tashi kije kiyi alwala" yarima Dameer ya fad'a yana kallon Deeyana, k'asa da Kai Deeyana tayi dan kunyar tace mai Bata sallah take ji sai da ya k'ara maimaita wa tukun, matsa hannun ta ta fara yi a hankali can dai tace, "to ka tafi zanyi" girgiza Kai yayi sannan yace, "A'a kije yanzu Ina jiran ki ki fito" k'asa da kai tayi tana mai jin kunyar ta sanar da shi bata sallah.






Kallon ta yayi ganin tayi shuru can dai ya lakaci hancin ta sannan yace, "ko dai.." kasa k'arasawa yayi dan ya gano ta, turo baki Deeyana tayi sannan tace, "ko dai mai?" "baki yi" shine kawai abunda ya fad'a yana murmushi k'asa-k'asa.






Da sauri ta sanya kanta cikin girjin shi tana mai jin kunya, shima sanya hannun shi yayi ta bayan ta ya rungume ta kam kaman za'a k'wace mai ita, nan da nan bacci ya kwashe su rungume da juna.






Washe gari sai kusan shida saura Dameer ya farka har lokacin Deeyana tana manne a girjin shi kallon fuskan ta yayi yana jin wani irin sonta na shiga ko wani sako na jikin shi a hankali ya zamai ta a jikin shi ya tashi ya shiga toilet d'in ta yayi alwala sannan ya wuce bedroom d'in shi yayi sallah.








Deeyana bata farka ba sai kusan takwas da rabi da sauri ta tashi ta shiga toilet tayi wanka sannan ta fito ta fara shiryawa yau kawai taji tana sha'awan kwalliya nan ta zauna ta fara tsarawa tana gamawa ta fito da kayan ta swiss lace mai Kyau da daukar ido nan ta shirya tayi kyau sosai dan ita ma da ta duba kanta a mirror sai da tayi murmushi dan tasan tayi kyau.






Bed d'in ta ta fara gyarawa sannan ta shiga toilet ta wanke ta gyara dak'in sosai ta sanya turaran wuta masu kamshi sannan ta fita parlour dan ita sam bata so kuyangu su gyara mata dak'i tunda tazo gidan ita ke gyaran komai nata sai dai d'an abun da baza a rasa ba suke kama mata tana gama gyara parlour ta shiga kitchen.






Flour ta fito da shi dan fankasau take sha'awa nan da nan ta kwafa ta aje sannan ta fara had'a kayan miya hanta ce kawai zata yi miyan da ita, nan da nan ko ina ya dau kamshi girkin dan Deeyana bada ganan ba wajan girki dan Amma tun tana yar karamar ta ta fara koya mata girki dan girki shine mace☺






~Yes yan mata a dage a koya girke dan yanzu maza ba wai mace mai Kyau suke buk'ata ba A'a wance ta kwarai wajan iya girki da kwalliya su ake yayi dan haka a aje girman kai a koya girke-girken zamani shawara ce~ πŸ‘Œ






Shirye yake cikin kayan sarauta black and White sai yar hula da ya saka a saman lallausan gashin shi yayi kyau sosai sai ya fito a asalin balaraban shi kuma jinin izzar sarauta🀴kamshin da ya fara sallama da shi ne yasa ya dakata yana jin kamshin girkin har miyan shi ya sinke kitchen d'in ya shiga arba yayi da ita tsaye tana juya miyya.






Tsayawa yayi kawai yana kallon kyakyawan suran da Allah yayi mata kaman ita tayi kanta gashi kayan sun dan matse ta komai na jikin ta ya fito ji yayi kaman ya hadiye ta dan so gaba daya ya manta waye shi jin sonta yake yana bin duk wani jini na jikin shi ya saka ma ranshi insha Allah yau zai baiyana mata son da yake mata dan ji yake anya zai iya zama ya dau wani lokaci kuwa.






Kusan minti biyar yana tsaye yana kallon ta can dai ya fara tafiya a hankali har ya isa gare ta a hankali ya sanya hannun shi saman wuyan ta, bata ji shigowar shi ba ko kad'an sai kawai jin abu tayi saman wuyan ta da sauri ta juyo tana dafa wajan sabida bata san ko menene ba tayi mugun firgita, Allah yaso ma yana tsaye a bayan ta da zubewa zatayi a kasa saurin taro ta yayi ta fad'a fadedan girjin shi.






K'ank'amai shi tayi tana sauke ajiyar zuciya d'an shifa bayan ta yayi yana kallon fuskan ta dan ta firgita sosai, itama kallon shi take ganin tayi be tab'a mata Kyau kaman yau ba ji tayi kaman ta rungume shi tayi ta aika mai da kiss, ta masifar shagala da kallon shi shima haka kallon ta yake sun kusa minti goma suna kallon juna can dai Deeyana tayi saurin tsaida idon ta kasa dan wani irin haushin kanta taji tasan Dameer bazai tab'a sonta ba amma ita wacce irin zuciya gare ta da take tsanmanin a yanzu ta fad'a son Dameer.







Kwalla ce ta cika mata ido bata san lokacin da hawaye suka fara zuban mata ba, d'ago fuskan ta yayi da hannun shi biyu yana kallon ta hawaye yaga ni a idon ta jikin shi yayi sanyi sosai dan bai san mai ya saka ta zubar da hawaye ba a hankali ya sunkuyo dai-dai fuskan ta ya sanya harshan shi ya fara lashe mata hawayan kusan minti goma yana abu daya dan ya shagala gurin lashe mata fuska, can yaji miyya kaman yana konewa da sauri ya sake ta yayi wajan gas din.






Kashe gas din yayi sannan ya dawo gurin ta da take tsaye kallon ta yayi sannan ya sakin mata murmushi saurin kasa da kanta tayi sannan ta matsa ta gefen shi ta wuce gurin gas d'in miyan ta duba taga yayi dai-dai sai kawai ta sauke sannan ta daurawa Dameer d'in shaye dan tasan ba cin abinci yake da safe ba, yana tsaye ta gama had'a komai na breakfast sannan ta saka a babban tire zata dauka kenan ya dauka ya fita da shi da kallon kawai ta bishi har ya fita sannan tabi bayan shi.




A kasa taga ya aje zaunawa tayi kaman yanda ya zauna sannan ta fara had'a mai shayi tana gamawa itama ma ta zuba nata fankasau ta fara ci gani yayi abun ya bashi sha'awa sannan kuma kamshi da ke tashi kawai sai taga ya saka hannu nan suka fara ci, can dai ya fara tambayar ta menene wannan dariya ta dunga yi haka suka cinye harda kari ranar Deeyana tayi mamakin cin abincin shi.




Gimbiya Haleematun-Sa'adiya ko break ta kasa yi dan jiya ko bacci mai dadi batai ba jakadiya na shigowa da kayan motsa baki ita da kunyangu ta tare ta suka fara magana, gimbiya Haleematun-Sa'adiya tace, "jakadiya yau kinji sanarwan mahaifin Deeyana ya mutu ko kuwa?" tayi maganar alaman hankali ta a tashe.






Gyara zama jakadiya tayi sannan tace, "haba uwar gijiyata ki daina tashin hankali ki ai mutuwa fa ya mutum ke dai ki bari zuwa anjima sai musan mai zamuyi" girgiza kai gimbiya Haleematun-Sa'adiya tayi sannan tace, "A'a jakadiya baki san mai nake ji bane a zuciyar nan tawa yanzu bari in shirya inje gurin mai-martaba je ki min iso".






"To an gama ranki ya dade" jakadiya ta fad'a tana tashi da sauri, nan jakadiya taje tama gimbiya Haleematun-Sa'adiya iso gun sarki Fahad Abdullah ba'a dade ba sai gashi ta dawo tace ma gimbiya Haleematun-Sa'adiya zata iya zuwa.






Suna gama break yarima Dameer ya tashi yace ma Deeyana zai tafi gun mai-martaba daga nan zai huce ya taho da su Abba sai kuma Ammi Deeyana tamai sai ya dawo sannan ta shiga kitchen gyara in da ta bata dan yau ranta fes, yqna isa yace jakadiya ta mai iso sai da ta sanar mai gimbiya Haleematun-Sa'adiya na nan yace eh zai shiga, nan ta mai mai-martaba yace, ya shiga nan ya shiga bakin shi da sallama.






Amsawa su kai gimbiya Haleematun-Sa'adiya sai da taji gaban ta ya fad'i dan daman in dai zatai ido hudu da Dameer sai taji gaban ta ya fadi dan yana mata kwarjini wanda ko zata mai wqni abun a gaban shi sai taji ta kasa, zaunawa yayi gaban mai-martaba sannan ya gaishe shi yana mai ya jiki kuma, gyara zama yarima Dameer yayi sannan yace,






"ABBA insha Allah yau akwai taron da nake so ayi a fada jiya naga ka shiga fada nasan jikin naka yayi sauki to yau a had'a duk wasu manya na wannan masarautar ta mu mai albarka da duk ma yan wannan masarautar namu harda su sarauniya maimunatu" gyaran murya mai-martaba yayi sannan yace, "ya za'a yi a had'a wannan duk wanda kace nan ba'a sanar da su abunda za'a yi ba kasan Ba'a tab'a haka ba ko?".




"Abunda zan fad'a kenan mai-martaba ka riga ni" gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta fad'a tana hararan Dameer ta bayan ido, murmushi Yarima Dameer yayi sannan yace, "ayi hakuri Momma bansan hakan zai b'ata rai ba amin afuwa" ya fad'a yana dan rausaya kan shi, kallon mai-martaba ya k'ara yi sannan yace, "ABBA wannan taro yana da mahimmaci sosai Amma in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login