Showing 30001 words to 33000 words out of 65264 words

Chapter 11 - IZZAR SARAUTA BOOK COMPLETE BY Aunty Baby Ummu Irfan .txt

wannan abun da yake shirin faruwa be ishe ki ishara ba yaron da kikai sanadiyar fitar shi a masarautan nan shi kuma yanzu a rashin sanin ki da muguntar ki kika kara shigo da shi..".






"Dakata! Dakata!! Wallahi in dai ina raye Aliyu bazai tab'a kara shigowa masarautar nan ba" Gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta fad'a tana shiga bedroom d'in ta fuuuuuu, Hmmmm kawai gimbiya mabaruka tace sannan ta fita a dak'in, jakadiya na tsaye sororo ta kasa tafiya! tana shiga bedroom d'in ta ta fara zagaye dak'in tana zantuka.








"Ni gimbiya Haleematun-Sa'adiya zan saka abu a gaba ban cin ma buri na ba wallahi karya ne" shigowa jakadiya tayi da sauri sannan ta tsugunna gaban ta tace, "kiyi hakuri ya uwar gijiyata Allah ya huci zuciyar ki in dai ina raye baza ki tab'a shiga damuwa ba".








"Huuuuuummm jakadiya wani bala'i ne yake shirin tinkaro ni yanzu y'ar Aliyu tana cikin masarautar nan komai na ya gama lalacewa ya zanyi yanzu?" ta fada tana zauniya a bakin Bed d'in ta dafa kanta tayi dan ji take kaman zai fashe, jakadiya ta gyara zaman ta sannan tace,








"Ummmmm uwar gijiyata sai kace ba ke ba wannan Dan matsalar har zata kwance miki kai abu mai sauki" matsowa tayi kusa da gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta fara gaya mata magana a hankali sannan ta kare da cewa, "haba uwar gijiyata ai ki daina damuwa wannan shine hanya mafi sauki da zamubi".








Daga kai gimbiya Haleematun-Sa'adiya tayi sannan tace, "shikenan kuwa jakadiya shiyasa nake sonki wallahi sabida k'wak'walwar ki" murmushi kawai jakadiya tayi.










Ko da su Dameer suka fita dak'in da jaddah take suka shiga ita ma ta saka musu albarka sannan ta k'ara musu nasiha ko da taga Deeyana tayi mamaki sosai amma bata ce komai ba dan ita a zaton ta duk yan uwa ne gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta had'a, sosai taji Deeyana ta shiga ranta nan dai ta dunga tsokalan su irin na jika da kaka ita Deeyana ba wani fahimta take ba dan larabcin Nigeria da Saudi ba iri daya bane shiyasa sai dai tayi ta murmushi.








Sai bayan sallah Asr suka tafi nasu part d'in, Deeyana tana shiga bedroom d'in ta alkebba ta fara cire wa sannan ta cire kayan jikin ta ta shiga toilet wanka tayi sannan ta fito kaya mara su nauyi ta sanya sannan ta zauna bakin Bed tana tunanin iyayan ta dan wani irin kewar su take gashi bata da waya bare ko Amman ta ta kira.






Shima dai Dameer wanka yayi sannan ya sanya jallabiya ya fito parlour ya zauna yana danna waya tunani yake gobe kawai zasu wace saudi amma mai-martaba kuma shine ko zai bari su tafi a gobe oho, kiran Ammin shi yayi ya sanar da ita cewa yana so su taho gobe amma yana tunanin ko mai-martaba zai bari, Ammi tace, ya gwada tambayan shi yaji amma barin masarautar nasu shine mafita tunda duk ya bata labarin yanda sukai da gimbiya Haleematun-Sa'adiya.








A haka dai suka tsaya zaije yama mai-martaba magana, tashi yayi ya shiga bedroom d'in shi ya canja kaya sannan ya shiga na Deeyana tana kwance kallon ta yayi ganin yanda tayi shuru, dan sosa giran shi yayi sannan yace, "akwai abinci a Parlour ki fita kici".








"Bana jin yunwa" shine kawai abunda Deeyana tace, tayi kasa da kanta lumshe kyawawan idon shi yayi sannan yace, "hhh ina ga d'ure kike son na miki d'aga kafadun shi yayi sannan yace, "in hakan kike bukata dan Allah ki bari na dawo baki ci abincin nan bq kiga yanda zan miki" yana gama fadar haka ya fita a dak'in.






Kwalla ta share sannan a hankali tace, "wayyo Allah na wai dan mugunta yace zai min dure wannan daman daka ganin shi bashi da imani" tashi tayi a hankali ta fita a bedroom d'in ta huce parlour, abincin ta taran a cikin basket an rufe shi da farin kyalle mai Kyau zaunawa tayi sannan ta bude flast daya ta bude sannan ta dauke plate ta dan zuba abincin kad'an sannan ta koma kan kujera ta fara ci kaman tana cin magani.






Yana fita fada ya huce lokacin ana kokarin sallahn maghrib shima alwala yayi sannan yabi jam'i ana idarwa sarki ya huce kilisar shi dan ana sallah maghrib zaman fada ya k'are kuma sai gobe, jakadiya yasa tayi mai iso mai-martaba yace, ya shiga sannan ya shiga cikin ladabi da biyaya ya gaishe shi sannan ya fara mai bayanin abun da ya kawo shi.








Sarki yace, "be kamata ace daga yin biki jiya ba gobe su tafi wata kasan amma tunda shi hakan ya zaba shikenan sai ya sanar ma fulani a shirya musu tafiyan sannan kuma ya kai yariyar gidan su tayi sallama da iyayan ta" sosai Dameer yaji dadi dan be tab'a zaton mai-martaba zai amince ba nan ya mai godiya sannan ya tashi ya fita.






Kilisar fulani ya huce dan yasan iyanzu tana can yana shiga ya tatda ta ita da jakadiya suna firan su tashi jakadiya tayi tana mai fadanci sannan ta fita dan ta dan basu guri su zanta, zaunawa yayi kusa da gimbiya Haleematun-Sa'adiya da ke kishingid'e tana cin tufa lokaci zuwa lokaci kallon ta yayi sannan yace, "Momma na sannu da hutawa".








Murya a had'a tace, "yauwa" murmushi yarima Dameer yayi sannan yace, "Momma na insha Allah gobe tare zamu huce da jaddah Saudi Arabia" washe Baki tayi dan azaton ta zai bar Deeyana ana sai tace, "to madallah amma my daughter zatayi kewar ka amma ai ba wani Abu tunda gani".






"A Momma na tare zamu tafi daga jiya zuwa yau nayi sabon da bazan iya rabuwa da ita ko na minti daya ba" ya fad'a tare da basarwa kaman bashi yayi maganar ba, zaro Ido gimbiya Haleematun-sa'adiya tayi sannan tace,






"Dameer yariyar da aka kawo ta jiya kace zaka tafi da ita wata k'asar ai be dace ba kuma kasan a k'aidar masarautar nan ba'a fita da yariya har sai tayi shekara amma ita jiya jiya ai sai kaja mana zage ace dan ita ba Yar kowa bace shiyasa".






Kallon ta yayi ganin yanda ta dage tana magana sai kace da gaske sannan ya cizai labb'an bakin shi na k'asa yace, "Momma na pls kiyi mana addu'a kawai amma naga ai ba komai bane dan na tafi da ita tunda duk gida ne kuma yanzu na sanarwa da Abba yace, ba komai".






"To bazai tab'a yuhuwa ba kuwa dole ka barta ana ka tafi kai daya" "hmmmmm Momma kenan to ai Naga dai matata ce kuma Ni ke da iko da ita dan haka ni dai tare zamu tafi".




Huci ta fitar Mai zafi sannan tace, "wato Dameer ban san ranar da raini ya shiga tsakanin mu ba ni da Kai na daya dai ni ba wasa nake da Kai ba, ba wani abu ba kuma ko da uwarka ban taba wasa balle Amma Ina daga maka kafa baka sanni ba ko hhhhhhhh Dameer kenan to Wallahi ka kiyaye kanka sannan kuma matar ka ce baza ka tafi da ita d'in ba sai Naga yanda za'a yi".








Tashi yayi sannan ya zuba hannun shi cikin aljihun wandon shi ya fara takawa a hankali sai da ya kai bakin kofa sannan yayi dariya mai sauti yace, "hmmmmmm Momma na kenan" sannan ya fita a kilisar.






Ajiyar zuciya ta sauke mai karfi jakadiya ce ta shigo da sauri jikin ta har rawa yake gurin zubewa gaban gimbiya Haleematun-sa'adiya tace, "Allah ya huci zuciyar ki Dan nasan wannan shegen yaron sai da ya Bata Miki rai ya fita Amma ki kwantar da hankalin hakan mu ta kusa cin ma ruwa".






Shuru gimbiya Haleematun-sa'adiya tayi dan ko kalma daya baza ta iya fad'a ba tashi tayi da sauri ta fita fuuuuuu kilisar mai-martaba ta huce ko iso bata nema ba ta shiga, kallon shi tayi sannan tace, "Allah ya baka yawan rai Dameer ya zo min da wata magana wai gobe zai tafi da yariyar nan kasar su baka ganin da cutarwa a ciki ai ba'a mata adalci ba".






Shayin da ke hannun shi ya kurba sannan ya kalle ta sai huci take sannan yace, "fulani ki barshi ya tafi tunda hakan yaga yafi mai kila uwar shi ce take son ganin ta" kallon mai-martaba tayi sannan tace, "lallai sai yau na tabbatar Daman in dai ba Kai ka haifi d'a ba to baka da iko da shi in ba Haka ba duk abunda nake ma Dameer baza Yi abunda na saka shi ba sannan har ka goya mai baya".






Murmushi su na manya yayi sannan yace, "to yanzu na riga nace mai ya tafi hakan nan za'a barshi ya tafi d'in dan kin san bana magana biyu sai a kori gaba kuma" hawaye ta fara sharewa "shikenan, dan ban haifi da namiji bane shiyasa da Ina da d'ana Nima ai ba Wanda ya Isa ya mai wani abu a kan shi bazan Kara shiga shirgin dan ka ba" tana gama fadar haka ta fita fuuuuuu.








Girgiza Kai kawai mai-martaba yayi yaci gaba da shin shayin shi, tana shiga D'akin ta ta fara zagaye shi tana tunanin mafita wata zuciyar tace, kije ki samu yariyar kice karta amince ta bishi wata kuma tace la karki haka za'a gano ki da wuri rasa ma wani tunani zata yi tayi.








Yana fita daga kilisar fulani part d'in shi ya shiga parlour ya zauna duguwar kujera yana ta tunanin maganar gimbiya Haleematun-sa'adiya ciza labb'an shi yayi sannan yace, "Wallahi Momma baki san Dameer bane Ina ga lokaci yayi da zan nuna miki real color na".






Deeyana tana zaune a kan Bed d'in ta tunanin Amma da Abba sun damai ta ta rasa yanda zatayi tayi magana da su tunda dai ita ba waya gare ta ba tashi tayi a hankali ta leka parlour kwance ta samai shi a duguwar kujera idon shi lumshi da alaman bacci yake a hankali ta lallaba ta fito tana tafiya a hankali har ta k'arasa kujeran da yake dubawa tayi ko zata ga wayan shi bata gani ba ta lika bayan shi ana ta hango duk wayoyin nashi.




Ta bayan kujeran ta sak"ala hannun ta zata dauka daya daga cikin wayoyin nashi zurun ya rik'e mata hannu, kulle idon ta tayi gam sabida ba k'aramin kunya taji ba kallon ta yayi sannan ya dawo da ita ta gaban shi ya zaunar da ita kan kujeran sannan ya shima ya gyara zaman shi, Kara kallon ta yayi a karu na biyu ya kafe ta da lumsassun idon shi.






Kaman tasan yana kallon ta ta k'ara kulle idon murmushin gefan Baki yayi sannan yace, "Kai wannan yariyar akwai wayyo mai zakiyi da waya?" Toro baki Deeyana tayi sannan tace, "ai Abba da Amma zan Kira".




Shima kwaikwayan muryan ta yayi sannan yace, "shine kuma baza a gaya min ba kawai za'a kwashi min waya" kara tura bakin tayi sannan tace, "ka matsa to in tashi" "Aa an fasa kiran Abba da Amma ne?" Ya fad'a yana lakatan hancin ta sauri tashi tayi a zuciyar ta tana cewq "shi wannan baya jin kunyar taba mata".






Kaman yasan tunanin da take kenan ya mika mata wayan a hannun ta sannan ya dauka sauran ya tashi ya shige dayan part d'in, tabe Baki Deeyana tayi sannan ta mik'e ta shiga bedroom d'in ta, sai da ta zauna a kujeran bedroom d'in sannan ta sanya number Abba ta fara Kira, ringing kusan uku sannan Abba ya dauka.




Cike da murna Deeyana ta fara gaishe shi yana jin muryan Deeyana yayi murmushi sannan suka fara gaisawa yace, Ina ta samu waya sai tayi shuru ta rasa abunda ma zata ce can dai tace, "na na hmmm ynnn yaya ne" murmushi Abba yayi sannan ya k'ara mata nasiha sosai nan dai sukai Sallama.




Murmushi tayi sannan ta fara kiran Amma ringing daya Amma ta dauka cike da murna Deeyana tace, "Amma na" Amma tana jin muryan Deeyana tace, "Deeyana kece ya kike" "lafiya lau Amma na ya gida ya kuke Ina su aunty Faiza da suheema" Amma tace,






"Lafiyan su lau Deeyana duk sun koma gida" murmushi Deeyana tayi sannan suka cigaba da firan su kusan minti ishirin sannan sukai sallama, wani irin dadi Deeyana taji jin muryan iyayan nata tashi tayi zata maida mai da wayan shi da ta fito parlour taga baya nan sai kawai ta aje mai a akan kujera juyawan da tayi zata koma kawai sukai karo.






Taga-taga zata fadi da sauri ya taro ta tare da rungume ta tsam a jikin shi, jinta cikin fad'edan girjin shi sai ta wani lumshi Ido ta manta ma tare dawa take a hankali ya fara lilaya mata kanta a tunanin shi ko ta bege ne hannun shi da taji a kanta yasa tayi saurin barin jikin shi tana shiga bedroom d'in ta da gudu, murmushi gefan Baki yayi dan ji yayi ta burge shi.








Abdul ya Kira akan ya neman musu jirjin hamma na Saudi Arabia Abdul yace, to ba matsala yanzu zai tafi akwai abokanan shi a airport d'in sai dai kuma Deeyana sai an mata passport tunanin yanda zai kaita kawai yake sai kawai yace ya duna wayan shi in akwai pic d'in da aka dauke ta jiya a gun biki ya Kai ayi passport d'in, to Abdul yace sannan ya kashe wayan ya fara duba wayan shi.






Yaci sa'a kuwa ya samu amma ba'a ganin fuskan ta sosai tunda da net a fuskan na ta nan ya Kira yarima Dameer ya gaya mai Dameer yace, ya kai ayi haka kawai ok kawai Abdul yace, kiran jaddah yayi sannan yace, mata insha Allah gobe zasu huce Saudi jaddah tace, to Allah ya kaimu.






*Washe gari*






~Pls kuyi hakuri da wannan~








*VOTE*
*COMMENT*
*&*
*SHARE*
[1/6, 10:37 PM] Mum Irfaan🀱🏻: 🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚
🦚🦚
🦚










🀴🏻 *IZZAR SARAUTA*🀴










🌐
*_ALHERI WRITER'S* *ASSOCIATION_* ✍
*~[ Alheri danko ne, duk inda kayi shi zai dawo gare ka, burin mu mu ribantu da alherin da ke cikin wannan harka]~*








*ALHERI SAI DAN AlHERI* πŸ‘Œ












*Story*
*&*
*written*
*By*
*Aunty baby* ✍








*DEDICATED TO..*
*ALL GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION*




Jinjina da gaisuwar ban girma gare ku.


My aunty miss XerksπŸ‘
Ummu Nabil
My kankanaty maman MuhammadπŸ’˜
My dear friend neat ladyπŸ’”
Masoyiya mom AysarπŸ’ž
Mrs basakwace
My aunty takwara kuma momyn gaskiya writer'sπŸ’“
Ummu Mudassir my daughter
Innaro
Kai aradu kuna da yawa.








*Sadaukarwa ga UMAIMA ALIYU*








*BISMILLAHIR RAHMAIR RAHIM*










πŸ“ *page* 4⃣5⃣⏩4⃣6⃣












___________πŸ“–tunda ya tashi shirye-shiryen tafiyan su yake misalin karfe sha-biyu ya shirya ya tafi plazan shi dan ya dan kwana biyu be shiga ba, ba wani dadewa yayi ba dan ko awa beyi ba ya dawo gida.






Bedroom d'in Deeyana ya huce noking yayi sannan ya shiga ya samai ta zaune kan sallaya tana karatun Qur'an sosai yaji ta bashi sha'awa, a hankali yace, "mata in kin gama ki shirya zamu fita" kai kawai ta d'aga mai sannan shi kuma ya fita.






Tab'e baki tayi a zuciyar ta tana cewa "to ina zamu haka" tashi tayi daman ta gama ta canza kaya sannan ta zauna gaban mirror ta dan shafa powder sama-sama sannan ta sanya gyalen ta ta fito parlour, zaune yake kan duguwar kujera ya daura kafa daya kan daya yana danna wayan shi, a hankali take takowa har ta zo kusa da kujeran da yake kamshin turaran ta ne ya daki hancin shi yasa ya daga kai ya kalle ta wani irin Kyau yaga ta mai dan murmushin gefan baki yayi.




Tashi yayi sannan ya dauka key d'in motar shi ya fara tafiya ita ma binshi tayi a baya har suka fita part d'in su fadawa ne suka taso da sauri daga masu hannu yayi alaman baya buk'atar su sannan suka koma ita dai tana biye da shi har suka iso in da yayi parking d'in motar shi, da hannu yayi mata nuna da ta shiga.




Bude motar tayi sannan ta shiga shima shiga yayi sannan ya tada tuki ya fara cikin kwaraiwa da natsuwa, tunda suka fara tafiya ba wanda yayi ko tari wani babban plaza ya tsaya sannan ya fita shiga plazan yayi be dade sosai ba sai gashi ya fito wasu mutane na bayan shi rike da manya-manyan ledoji bayan motar ya bude musu suka sanya kayan sannan ya rufe motar ya shiga.






Kallon ta yayi ta gefan ido sannan yace, "ina ne hanyar gida?" saurin kallon shi Deeyana tayi dan bata gane mai yake nufi ba, "ko baki san gidan ku ba na tambaye ki kinyi shuru" bakin Deeyana na rawa ta fara mai kwatance shikuma yana tuki har suka isa kofar gidan su Deeyana.






Wani irin farin ciki ne ya baibaye Deeyana dan bata tab'a zaton zata zo gida a wannan lokacin ba ai bata tsaya mai magana ba kawai ta fita motar da sauri, gidan ta shige tun daga bakin kofan gida take kwad'awa Amma kira Amma da take kitchen taji muryan kaman na Deeyana gaban ta yace, rasss da sauri har tana hadawa da gudu ta fito daga kitchen d'in.






Deeyana tana ganin ta ta rungume ta tana murna murmushin karfin hali Amma tayi sannan tace, "Deeyana lafiya na ganki?" turo baki Deeyana tayi sannan tace, "Amma baki murna da gani na bane?" shuru Amma tayi sannan tace, "Deeyana tambayar ki fa nake amma kina min wani zancen da ban".






"Kai Amma tare da shi fa muke gashi can a mota ma" Deeyana ta fad'a tana turo baki, ajiyar zuciya Amma ta sauke sannan tayi murmushi tace, "ja'ira shine kika barshi a waje baku shugo ba gashi Abban ki baya nan ya tafi jana'iza tun safe be dawo ba kije kice ya shigo sai ki kai shi parlour gani nan zuwa".






Duk sai Deeyana bata ji dadi ba taso taga Abban ta amma ba dama "to" kawai tace, sannan ta fita dan ta shigo da yarima Dameer, zaune ta samai shi a mota kunkusa glass d'in motar tayi budewa yayi sannan tace, "wai ka shigo" kallon yanda take turo baki yayi sannan ya mai-maita wai ka shigo ji yayi kaman ya kamo ta ya murde wannan bakin dan yaga alaman ta saba da turo shi ya lura da ita tun jiya take turo mai baki to sai yayi maganin ta in batai wasa ba dan shi baya so ana turo mai baki.




Juyowan da zaiyi yaga har ta kusa shigewa gida bude motar yayi a hankali ya fito sannan ya fara dubawa ko zaiga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login