Showing 60001 words to 63000 words out of 65264 words
Chapter 21 - IZZAR SARAUTA BOOK COMPLETE BY Aunty Baby Ummu Irfan .txt
Deeyana wato ma tafiya zaiyi ya barta tana kuka saurin fita tayi a motar tayi hanyar parlour su lokacin da ta shiga har ya aje Abdul yana had'a mai madara dan ya dan fara kuka, zuwa inda yake tsaye tayi ta rik'e mai riga "wai Dameer baka ji abinda nace bane zaka mayar dani mahaukaciya ka tafi ka gyale ni"
Mamaki da al'ajabi gaba daya sun rufe Dameer abunda be tab'a ji ta Kira ba kenan Dameer yau ita ke rik'e mai riga take mai wannan rashin kunyar lallai yanzu yasan mace komai k'ank'antar ta karka Raina ta Dan in ta maka wani rashin mutunci ko dan shekara hamsin Albarka.
Kallon ta yake da raunannin idon shi da suka rine suka jajir ya kama hannun ta ya cire rigar shi a hankali sannan ya dauki Abdul ya fara bashi madaran, fincike fidan bakin Abdul d'in tayi ta fadi kasa sannan tace, "Wallahi baka Isa ka Mai dani mahaukaciya ba ka dauki danka dole kasan yanda zakai da cikin nan sabida akan cikin ka bazai tab'a daina karatuna ba.
"Deeyana Deeyana ki kiyaye kanki bana son hauka in kina rashin mutunci ki kiyi Dani kawai karki tab'a min yaro kinji na gaya miki" yana gaya mata haka ya tashi ya dauki Abdul ya bar mata gun.
Bin bayan shi itama tayi...
*VOTE*
*COMMENT*
*&*
*SHARE*
*Aunty baby ce*β
[1/6, 10:37 PM] Mum Irfaanπ€±π»: π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦
π¦π¦π¦π¦π¦
π¦π¦π¦
π¦π¦
π¦
π€΄π» *IZZAR SARAUTA*π€΄
π
*_ALHERI WRITER'S* *ASSOCIATION_* β
*~[ Alheri danko ne, duk inda kayi shi zai dawo gare ka, burin mu mu ribantu da alherin da ke cikin wannan harka]~*
*ALHERI SAI DAN AlHERI* π
*Story*
*&*
*written*
*By*
*Aunty baby* β
*DEDICATED TO..*
*MY MOTHER β€οΈ*
*~Hmmmmm Allah sarki rayuwa wato ba dan wani abu nace na mayar da buk d'ina na kudi ba Sai dan wulak'ancin da kuka min, na zauna na bar duk wani abu da nake yi na muku typing har two page amma kuka nuna min halin ko in kula ba Wanda ya min comment ko wani abun ban damu da godiyar ku ba Dan dan Allah nake komai ba dan mutum ba kaman wata da tace, komai mutum zaiyi yayi dan Allah to ta sani ni fateemah aunty baby dan Allah nake komai sannan kuma ta kiyaye bakin ta tomπkuma da nace na mayar da buk d'ina na kudi Kun san kudin ku ba abunda zai k'ara min to Ni ma zanyi da shi to Ni bama a k'asar nake ba bare in ce zanyi wani abun da shi, wasun ku da yawa sun min magana tun shekaran jiya akan nawa ne kudi bani ce musu komai sai dai nayi dariya tom masu zagina ma can ta matse musu sabida Ni nake da ikon nayi duk abunda naga dama kuma badan mutum daya ba Wallahi sai ka biya kudi zaka karanta ko kuwa kudin bazai amfane ni ba, π
gama my jika sai in bud'e mai account ana zuba mai ko ya kika ce my daughter.~ *
*Sadaukarwa ga UMAIMA ALIYU*
*BISMILLAHIR RAHMAIR RAHIM*
π *page* 6β£7β£β©6β£8β£
_______πbin bayan shi itama tayi, lokacin ya fara had'a ma Abdul kaya a dan k'aramin akwatun shi tana shiga D'akin ta matsar da akwatun sannan tace, "wallahi ba abunda zakayi baka tsaya ka saurare Ni ba ka gama cutar dani a duniya ta sanadiyar ka na rasa karatu na yanzu kuma na fara dan rashin Imani ka durka min ciki dan in daina zuwa ko to baka Isa ba".
Kulle idon shi yayi Yana karantu duk wata addu'a da tazo bakin shi, can yaji Abdul ya fara dan kuka ya dauke shi dan yaje ya had'a mai madara yaji ta kwace yaron da badan ya rik'e shi da kyau ba da faduwa zaiyi.
Haushi da ya kama shi besan sanda ya dauke hannu ya watsa mata mari ba, daga ita har shi sai da suka dauke wuta na yan mintina dafe wajan da ya mare ta tayi sannan ta kafe shi da ido har na tsawan mintina biyar, saurin dafe kan shi yayi yana ma kan shi tuhumar mai yasa ya mare ta innalillahi shi basan ma lokacin da ya mare tan ba.
Kallon ido cikin ido suke ma juna har lokacin Abdul na hannun Dameer bata san lokacin da tayi kukan kura ta cakumai shi ba har Abdul na faduwa kan Bed rike mai riga tayi tam sannan tace, "Dameer ni ka saka hannu ka mara ni ka mara wallahi sai ka sake ni bazan tab'a zama da namijin da zai duke ni ba, kuma ciki a gaban ka zan zubar da shi na tsane ku kai da Abdul ko ganin ku bana son yi wallahi sai ka sake ni" duk maganar nan da take tana kuka tana jinjiga mai rika kuma idon ta a rufe gam.
"Innalillahi wa'ina ilaihir rajiun" kawai Dameer yake mai-maitawa yau da wace irin tashin hankali ya tashi yanzu shi ya dauke hannu ya mare macen da yafi so a duk duniya mai Deeyana ta mai da bazai iya hakuri ba har ya d'aga hannu ya mare ta, saurin rungume ta yayi cikin kirjin shi sannan yace, "wayyo Allah Deeyana dan Allah ke yafe min wallahi ban san na mare ki ba tsakani na da ke ba zancen saki auran mu hadin Allah ne dan Allah kiyi hakuri".
Dukan kirjin shi take iya karfin ta tana cewa "na tsane ka bana son ganin ka ka mare ni akan danka wallahi sai ka sake ni" zubewa yayi a kasa ya rike kafar ta ya fara kuka wewe yana bata hakuri "Deeyana zan iya mutuwa mudin ban tare da ke dan Allah kiyi min rai kiyi hakuri ki dau duk matakin da kika ga ya dace a kaina amma banda zancen saki".
Zubewa tayi saman bed ta saka kuka mai cin rai shima Dameer d'in fashea yayi da nashi kukan yana jin kaman yayi ta dungan kan shi Abdul da ya ji duk suna kuka shima sai ya fashe da nashi kukan sabida yaji dak'in duk ya barke da kukan su, rasa Wanda zai dauke shi akai ita kuka shima Dameer d'in kuka.π€£ππππ
```Abdul sai dai Kai hakuri dan iyayan naka duk shagwa'ba ta musu yawa ace uwa kuka uba kuka to Ni dai aunty baby naga tab'ara sai yan IZZAR SARAUTA FAN'S su zo su lallashe ka``` π€£π
Kusan minti goma suna a haka Abdul kon sai K'ara sautin kukan nashi yake ya rarrafo ya zo gun Deeyana ya dunga d'aga hannu alaman ta dauke shi amma shuru dan ita Bata San ma yana yi ba saurin tashi Dameer yayi ya dauke shi ya fara lallashin shi, fita yayi a D'akin yaje had'a mai madara.
Tana jin ya fita ta tashi ta saka ma kofar key, ta k'ara fashewa da kuka yau ita ce Dameer ya mare ta lallai sai yanzu ta tuna da maganar Ammi namiji ba dan goyo bane, zaunawa yayi Kan kujera ya fara bashi madaran yana yi yana jinjiga shi har yayi bacci sannan ya tashi ya koma D'akin da Deeyana take ya murd'a kofar yaji ta rufe gam.
Bubbugawa ya fara yi Yana rokan ta dan Allah ta bud'e kofar amma Ina yaji shuru Ashe ma har tayi bacciπdayan bedroom d'in ya shiga ya kwasu ma Abdul duk kayan shi sannan yaje yasa a mota yazo ya dauka Abdul ya fita.
Direct masarautar su ya huce, yana parking ya fito ya Kira fadawa su dauke kaya sannan ya dauke Abdul ya huce part d'in Ammi fadawa na biye da shi da kayan shi da sallama ya shiga Ammi na zaune kuyanga tana yanke mata kunfa amsawa tayi tana murmushi sannan ta Mika hannu ya saka mata Abdul.
Amsan shi tayi lokacin har ya tashi a bacci yana ta wankale Mata Baki fadawa ne suka shigo da kayan sannan suka aje kunyangu kuma suka dauka suka kai D'akin Ammi sannan suka fita, kallon mamaki Ammi ke bin shi da shi idon shi yayi jajir sannan kuma duk beda wani kuzari.
A hankali Ammi tace, "Dameer lafiya kuwa na ganka da kaya haka?" Sosa kai yayi sannan yacr, "eh Ammi kayan Abdul ne kawai tunda ba shan nonon yake ba a yaye shi", "yaye kuma" Ammi ta maimaita.
Daga kai yayi sannan yace, "Ammi ba shan nonon yake ba fa kuma gashi yawan ci a gida take barin shi tunda tana zuwa makaranta" "to shikenan amma gaskiya yayi k'ank'anta da yawa ni da zaka bari ko wata biyar ya kara Amma yanzu fa ya shiga shekara daya dan dai ku y'ay'an zamani kun cika fitana ne amma ai Abdul be isa yaye ba komai shan nonon da bayayi".
Shuru yayi dai yana jin Ammi dan bata san matsalan da yake ciki bane tashi yayi sannan yace, "Ammi ni na tafi sai gobe kuma" "to Allah ya bamu alkhairi" Ammi ta fad'a tana gyara ma Abdul riga.
Yana fita gidan su ya koma har lokacin bata bude kofan fa zaunawa yayi a Parlour yana tunanin abunda ya faru d'azu, har dare yana zaune a Parlour ko abinci ya kasa ci sai kai kawo yake kuma ya buga kofar har ya gaji tki budewa.
Misalin karfe sha-biyu na dare ya gaji ya tashi ya tafi part d'in shi nan ma ya kasa baccin alwala yayi yazo yayi ta sallah yana rokan Allah ya dai-dai ta shi da matar shi farin ciki shi, ita kam Deeyana tana can tana aikin kuka da k'yar ta tashi tayi wanka tayi sallah ta dauke Qur'ani ta fara karantawa.
Nan taji zuciyar ta tayi mugun sanyi duk abunda ya faru d'azu yayi ta dawo mata dafe kanta tayi yanzu duk wannan rashin mutunci tayi ma mijin ta innalillahi mai ya rufe mata ido haka tayi ta mai wannan rashin kunyar, fashewa tayi da kuka tana rokan Allah ya yafe mata tashi tayi a hankali ta bude kofa ta duba baya parlour.
Tasan yana part d'in shi nan ta huce part d'in nashi a hankali ta fara kwankwasa kofa, yana zaune kan sallaya yaji kaman ana k'wank'wasa mai kofa tashi yayi ya isa gun kafar ya bude idon shi na kan kofar Deeyana ya gani kan ta a kasa tsaye yayi yana kallon ta da raunannin idanun shi.
Da gudu taje ta rungume shi tana kuka mai ban tausayi shima rungume ta yayi yana goge kwalla da ta cika mai ido, sun kusa minti biyar a haka can dai ta sake shi ta saka gwaiwar ta a kasa ta fara mai magana.
"Hayatee dan Allah dan girman Allah kayi hakuri wallahi lokacin idona ya rufe ban san nayi ma wannan abun ba dan Allah ka yafe min wallahi fushin ka kaman wuta ce a zuciyata" saurin mikar da ita yayi sannan ya rungume ta ya sanya ta cikin kirjin shi yana cewa,
"Har abada na yafe miki ke ma ki yafe min Marin da na Miki kiyi hakuri" girgiza Kai Deeyana tayi da sauri sannan tace, "Wallahi baka da laifi ko daya insha Allah kuma zan raina cikin nan kaman yanda na Raina na Abdul" .
Shafa kanta yayi sannan yace, "yawa Allah ya miki albarka" "ameen" Deeyana tace tana mai murmushi, daukan ta yayi cak ya kaita bedroom d'in shi ya daura ta saman bed nan da nan bacci ya dauke su.
Haka Deeyana ta cigaba da rainan cikin ta cikin kwanciyar hankali Dameer na taya ta sabida kuyangu da da yace baya so yanzu duk ya dibo su, ko makaranta ma Deeyana ta daina zuwa Dameer yace ta dunga zuwa tunda dai cikin bamai laulayin bane tace, "Aa in ta haihu ta dunga zuwa" .
Abdul sai wayyon shi yake kara yi yana samun kulawa sosai gun Ammi dan yanzu kowa yasan Deeyana nada ciki sai fatan Allah ya sauke ta lafiya kuma.
A kwana a tashi ba wuya yanzu cikin Deeyana ya shiga wata tara kullum sa ran haihuwa suke komai sun tana ja na haihuwa, tafiya ta kama Dameer zuwa Saudi Arabia jaddah bata da lafiya dole sai yaje sabida yaga jikin ta.
Dole sai manyan kuyangu aka dauka suna kula da Deeyana sabida kar haihuwa ta kamata ba wani babban a gidan, kwana uku kawai zaiyi a can ranar da zai tafi Deeyana tasha kuka wai sai dai ya tafi da ita da k'yar dai ta barshi ya tafi.
*Kuyi hakuri da wannan*π
*Aunty Baby ce*β
π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦
π¦π¦π¦π¦π¦
π¦π¦π¦
π¦π¦
π¦
π€΄π» *IZZAR SARAUTA*π€΄
π
*_ALHERI WRITER'S* *ASSOCIATION_* β
*~[ Alheri danko ne, duk inda kayi shi zai dawo gare ka, burin mu mu ribantu da alherin da ke cikin wannan harka]~*
*ALHERI SAI DAN AlHERI* π
*Story*
*&*
*written*
*By*
*Aunty baby* β
*DEDICATED TO..*
*MY MUNAT*
*EESHAA*
*MAMUU*
*MINAT SS*
*AUNTY SARAH*
*Sadaukarwa ga UMAIMA ALIYU*
```My fan's ku taya ni murna da godiya gurin my khausar ta sadaukar da littafin ta gare ni, ya Allah ka sakawa wannan baiwar taka da alkhairi a gaskiya naji dadi Wanda bazai tab'a musaltuwa ba ace littafin ta na farko ta sadaukar gare Ni ai ban san ma irin godiyar da zan mata ba naji dadi sosai Allah ya bar zumunci Allah ya daukaka wannan littafi nake ya kuma baki ikon isar da sakon da kike son isarwa amma naji dadi sosai nagode kuma kin nuna min kin san mutunci wasu ko hmmmm ba'a magana ai.```
*Wannan littafin nawa gaba dayan shi tukuici ne ga neat lady da miss Xerks Allah ya bar kauna da zamunci nagode sosai da irin gudunmawar da kuka bani a rayuwata gaba daya ku ne sanadiyar fitowa ta social media bazan tab'a mantawa da ku ba Allah ya bar kauna har abada muna tare ya Allah ya bamu miji na gari dukan mu, d'an halak baya manta alkhairi komai k'ank'antar shi kuwa*
ππππππππππ
*BISMILLAHIR RAHMAIR RAHIM*
π *Page* 6β£9β£β©7β£0β£
________πtun ranar da ya tafi take dan jin yanayin ta ya canja kullum da ciwan mara take kwana haka dai take daurewa sai ranar da ya cika kwana biyu da tafiya ranar bata iya bacci ba nan ta tashi tayi ta zagaye dak'in har dai kusan asuba sannan ta fito parlour.
Daya daga cikin kuyangu ta farka fitsari ta ganta sai zagaye dak'in take matsowa tayi ta fara tambayar ta ko lafiya cike da dauriya ta fara magana "je ki kira min driver kice ya fito da mota zai kani hospital".
Da sauri ta tafi ta taso driver ya fito da mota nan ta sanya hijab ta fito ta shiga motan ita ma kuyangan ta shiga suka tafi hospital d'in, tun a hanya ta fara zubar da farin ruwa suna isa hospital d'in kuyangan ta fita da sauri ta kira nurses.
Suka tawo da sauri suka dauke ta sai cikin labour room ko minti goma batai da shiga ba Allah ya sauke ta lafiya, ta samu dan ta namiji nurses d'in suka gyara ta da baby boy d'in ta sannan suka kaita dak'in hutu lokacin har an idar da sallah asuba.
Kuyangan ce ta shigo dak'in ta tatda ta zaune saman bed ta dafe cikin ta da yake murda mata kad'an-kadan, cikin ladabi tace, "barka da sauka lafiya uwar dakina" murmushi Deeyana tayi mata dan bata jin zata iya magana, can dai kusan minti goma ta samu ta Mik'a mata wayan ta tace, "ta kira Ammi da Amma ta gaya musu" .
Wayan ta amsa sannan ta fara kiran Amma ta gaya mata cewa suna hospital sarauniya Deeyana ta sauka lafiya nan Amma tayi murna sosai, nan sukai sallama ta kira Ammi ai ko aje wayan basu ba Ammi ta fara shirin tawo wa hospital d'in, kafin kace mai har zancen haihuwar yq badai masarautar mure.
Ammi ce ta fara zuwa hospital d'in lokacin Deeyana ta samu bacci, bed d'in da jaririn yake taje daukan shi tayi da addu'a a bakin ta "masha Allah" tace, ganin irin Kyau jaririn shima dai kaman su daya da Dameer dan kaman yayi kaki ya zubar ko kad'an baya kama da Dameer murmushi ta dunga yi sannan ta dauke waya ta fara mai pic ko hmmmm bata ce ma Dameer ba ta fara tura mai ta WhatsApp.
Wajan karfe takwas sai gasu gimbiya Aisha da marwa, sunyo breakfast har lokacin Deeyana bacci take sai jariri da ke ta wutsi-wutsin din shi, gimbiya Aisha da ta dauka yaron sai ta fara mai tsiya wai Abdul ya fishi kyau ita kuma gimbiya marwa tace, shine mijin nata yafi Abdul kyau haka dai sukai ta musu Ammi na musu dariya dan tace, ita ta yarta take.
Jikin jaddah yayi sauki sosai shirin dawowa ma Dameer yake dan ya gama komai karfe sha-biyu jirgin su zai tashi zuwa Nigeria, wayan shi ya dauka ya fara kiran Deeyana dan yau basu waya ba amma a kashe yaji wayan sai kawai ya fara kiran Ammi, Ammi da ke zaune bakin Bed d'in da Deeyana take taji wayan ta na ringing dauka tayi tana murmushi dan tasan Dameer ne.
Gaishe ta ya fara yi sannan ta tambaye shi jikin jaddah yace, alhamdllh taji sauki har dai suka gama wayan Ammi bata ji yayi maganar haihuwar Deeyana ba sai tace, "hala dai baka duba WhatsApp d'in ka bane?" murmushi yayi sannan yace, Ammi yau tun safe ban duba wayana ba ma sbd tafiyan nan gashi jaddah ta matsa sai munji siyan wasu kayan baby's shiyasa".
"Ohh to ka duba zaka ga sakon da na turo ma" to kawai Dameer yace, sannan sukai sallama, WhatsApp d'in ya shiga nan ya fara cin karo da dunbin mutane suna turo mai pic d'in baby boy ana mai barka duk be duba ba dai na Ammi da ya shiga nan ya fara ganin pic din baby boy kallon pic d'in yake cike da murna Deeyana ta haihu kenan allahu akbar nan yayi sunjada yana nuna godiyar shi ga Allah da ya bashi komai na rayuwa yanzu yaran shi biyu kenan Allah kenan.
Da sauri ya fito daga dak'in ya isa su jaddah da ke parlour ya fara nuna musu pic din yaron nan murna ya barge ai ji yayi kaman ya jawo sha-biyu sabida kosawa da yayi yaje yaga Deeyana nar shi da kuma sabon babyn da tayi mai.
Sosai mutane suka cika a hospital d'in kowa na murnan sabon baby da suka