Showing 36001 words to 39000 words out of 65264 words
Chapter 13 - IZZAR SARAUTA BOOK COMPLETE BY Aunty Baby Ummu Irfan .txt
daya ilahirin gidan suna break harda Deeyana tana zaune kusa da Ammi kallon ta yayi sanyi take da atamfa ba wata kwalliya tayi a fuskan ta ba amma yaga ta mai Kyau sosai zaunawa yayi kusa jaddah sannan ya lankwasa kan shi jikin jaddah ya fara cewa "ku baku jiran mutum sai kawai ku fara break ku kad'e".
Cire mai kai jaddah tayi sannan tace, "tashi ga uwar ka can ka hau jikin ta ba dai ni ba kuma kana can gurin Ball d'in ka ina zamu tsaya wani jiran ka" murmushi yayi sannan ya saka hannun shi a plate d'in da jaddah ke cin nata abinci ya fara ci, kallon shi Ammi tayi sannan tace, "yau ka jima a gurin Ball d'in lafiya dai ko?".
Sai da ya sanya kwai a bakin shi sannan yace, "lafiya lau Ammi muna tare da mus'ab ne shiyasa" "ok" kawai Ammi tace suka cigaba da break d'in su Deeyana ce ta fara tashi tace ta koshi gaba daya Ammi da jaddah suka fara tambayar ta ko abincin ne bata jin dadin shi shiyasa bata ci da yawa ba tace A'a ta koshi ne kawai, jaddah tace to shikenan anjima zasu fita da Dameer a siyo mata kayan abincin Nigeria tunda ciman su da nata ba daya ba.
Ayusha kon ta k'ulu ji take kaman ta shag'e Deeyana sai wani lallabata suke ita mantawa ma suke da ita hmmmm kawai tace a zuciyar tana jin tsanar ta a ranta, Deeyana na shiga dak'i wayan da Dameer ya siyan mata ta dauka budewa tayi sai kuma ta tuna bata da sim d'in Saudi a wayan tana budewa kuma sai taga akwai zain a ciki na kasar kenan bata san ma lokacin da Dameer d'in ya saka mata ba, number Amma ta saka sannan ta fara gwadawa ko zai shiga, tana kira kuwa ya tafi taji dadi sosai nan Amma ta dauka tunda taga number waje tasan Deeyana ce shiyasa tana dauka cikin murnar ta suka fara gaisawa.
Ammi ce ta kalle Dameer sannan tace, "in anjima ka dauki matar ka kuje ta sauke umrah jibi kuma ku tafi madinah tayi ziyarah" "hmmmm Ammi ki bari sai gobe mana yau ina son fita wani waje" girgiza kai Ammi tayi sannan tace, "yau zaku je tazo kasar mai ya kamata ai da jiya da huri kuka zo sai ta fara sauke umrah ma kafin ta zo nan gidan" "to Ammi shikenan zamu je insha Allah" tashi yayi yace, "Ammi bari naje na watsa ruwa" "to" kawai Ammi tace ta tashi ta shiga kitchen.
Yana shiga ya samai ta tana waya da su Amma har lokacin sai murmushi take tab'e baki yayi sannan ya shige bedroom zaunawa yayi a bakin Bed sannan ya daura laptop din shi a ciya yana dannawa aje ta yayi akan bed d'in sannan ya shiga kitchen d'in dak'in dan ya had'a shaye be dade ba ya fito da d'an karamin tire a hannun shi sai kofin shayin kuma, dai-dai zai shiga bedroom suka ci karo da Deeyana ita kuma zata fito shayin gaba daya ya zuban mai a girji gashi da zafi sakin tire d'in yayi yana yarfe hannu dan zafi da sauri Deeyana tayo kan shi tana zare ido dan bata kula da abu a hannun shi ba shi kuma a zaton shi ya zuban mata shayen be saurara zafin da yak'i ji a jikin shi ba ya surai ta sai toilet.
Ruwan sanyi ya sakan musu dan shi a girji ne ya zuban mai ita kam tsaye tayi ta kure shi da ido can dai ta sanya hannun ta saman girjin shi da taga ya dafe cikin taushashiyan murya yace, "yana miki zafi gurin" girgiza kai tayi a hankali sannan tace, "be zuban min ba Allah yasa dai baka kone ba" lumshi idon shi yayi kawai bece komai ba ruwan kuma nata zuban musu a jiki, jikin ta na rawa ta sanya hannun ta saman singlet d'in shi tana tabawa a hankali sannan tana dan hura mai iskan bakin ta kuri ya mata da ido yana kallon yanda kashin idon ta ya kwanta dan karamim bakin ta da take hure mai iskan sai yaji kaman ya hade da nashi ya tsosa.
Kusan minti goma suna a haka sai can da taji ruwan sanyin ya fara shiga cikin ta ta matsa gefe tana k'ank'amai jikin ta kallon ta yayi da raunannin idanun shi da sauka canja kala yace, "sanyi" d'aga kai tayi alaman eh, towel ya janyo da a jikin kofan bayin sannan ya rufa mata sai ji tayi kawai ya suraita sai kan Bed ya aje ta, juyawa yayi toilet dan ya kara wanke jikin shi tana ganin babu shi ta cire kayan da ke jikin ta ta daura towel d'in sannan ta huce gurin wardrobe ta fara ciro kayan da zata saka.
Doguwar rikan material black ta saka sannan ta zauna gaban mirror ta fara shafa maya-mayan shi masu kamshi tana yi tana dan lumshi ido har dai Dameer ya fito daga toilet ya tatda ta dan murmushin gefan baki yayi sannan yace, "in an gama a bani guri na zan shirya nima" da sauri Deeyana ta juya bayan ta tana zare ido sauri kulle idon nata tayi dan ganin shi da towel daure a kugun shi, takowa yayi har inda take zaune sannan ya sanya hannun shi ya dago ta k'ank'amai jikin ta tayi tana cewa "dan Allah ka barni parlour zan tafi".
"Lallai ma yariyar nan to mai na miki da zaki dunga wannan abun??" ya fada yana cizan bakin shi, turo baki Deeyana tayi sannan tace, "to ka koma toilet na fita a dak'in" "kai in koma kuma yanzu baxa ki iya fita ba sai na koma lallai kam kisha zamanki har in canza kaya ki shirya ma haram zamu tafi zakiyi umrah".
Rufe idon ta tayi da hannun ta sannan ta fara tafiya wai dan karta kara ganin shi a haka sai da ta kai bakin kofa sannan tace, "na shirya" sannan ta fita daga bedroom d'in girgiza kai kawai yayi ya fara shirin shi.
K'wank'wasa kofa akai da sauri Deeyana ta tashi ta bude Ammi ce rike da fararan kaya a hannu ta tana ganin Deeyana ta k'ara murmushi sannan ta mika ma Deeyana kayan sannan tace, "'yata wannan kayan ki ne su zaki saka yanzu in zaku tafi haram da yayan ki kinji" daga kai Deeyana tayi tana murmushi sannan ta amsa kayan tace, "to Ammi nagode sosai".
Ja mata kumatu Ammi tayi sannan tace, "kar na kara jin kin min godiya a duk abinda zan miki in ban miki ba wa zai miki?" Kasa da kai Deeyana tayi tana murmushi kasa-kasa, juyawa Ammi tayi sannan tace, "sai kun fito" har Ammi ta kule Deeyana na tsaye tana kallon ta tana jin wani irin sonta a ranta komawa dak'in tayi sannan ta ake kayan a kusa da ita tana jiran Dameer ya fito in ya shirya sai ta sanya kayan su tafi.
*Nigeria*
Gimbiya Haleematun-Sa'adiya ce zaune a kilisarta ta sai juya tufa take a hannun ta ta kasa ci tunani ne fal ranta ta san ko mujima ko mu dade sai komai nata ya fallasa tunda ta riga da ta kowa Deeyana cikin masarautar yanzu mafita kawai take nema dan bata shirya shan kunya ba a cikin masarautar mure, jakadiya ce ta shigo kilisar kallon gimbiya Haleematun-Sa'adiya tayi da tun dazu aka aje mata abubuwa da ban da ban amma ta kasa cin ko abu daya.
Zubewa tayi gaban ta ta gama kiraye-kirayen ta gimbiya Haleematun-Sa'adiya na jinta dan bata da bakin da zata iya amsa mata, gyaran murya jakadiya tayi sannan tace, "Allah ta taimaki uwar gijiyata a rayuwata abun da na tsana kuma bana so shine shiga tashin hankali ki nima kikan sanya ya ni cikin tashin hankali Allah ya huci zuciyar ki".
Murya a sanyaye gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta fara magana "jakadiya dole in shiga tashin hankali na kawo wukar kashe kaina da kaina cikin masarautar nan yar Aliyu ce fa kin san komai ya ruga da ya gama lalacewa" "Aa uwar gijiyata na samo wani mafita yanzu a shirya miki tafiya saudiyya a zuwan zaki ke kiyi umrah to kinga dole dai ki hadu da su dan zasu zo gaishe ki to ana zamu samu damar aika wannan shigiyar yariyar itama ma" jakadiya ta fad'a tana murmushin mugunta.
Numfasawa gimbiya Haleematun-Sa'adiya tayi sannan tace, "hmmmmmm anya kuwa wannan abun zai yihu ko dai mu canja wata shawaran" daga kai jakadiya tayi tace, "to yanda Kika gani ranki ya dade Amma wannan ita ce mafita" gyara zama gimbiya Haleematun-Sa'adiya tayi sannan tace, "to hakan za'a yi Zan samu mai-martaba nayi Mai magana insha Allah ko zuwa wani satin ne sai mu tafi".
Dariya jakadiya tayi tace, "yauwa uwar gijiyata ki cire damuwa a ranki da anyi wannan kuma shikenan bamu da wata matsala kuma" ita ma gimbiya Haleematun-Sa'adiya dariya tayi tana jin wani nishadi a zuciyar ta.
*Saudi Arabia*
Deeyana tayi Shirin ta cikin fararan kaya sun fito suna sallama da su Ammi zasu tafi shima Dameer zaiyi umrah, har wajan mota Ammi ta rako su sannan suka shiga suka tafi Basu da wani nisa da Haram basu wani Dade a hanya ba suka Isa tunda Deeyana ta fara hango agogon Haram jikin ta ya fara rawa Bata tab'a kawo ma ranta zata zo makka ba tunda tasan uban ta mai k'aramin karfi ne Amma gashi Allah Mai iko Wai ita ce a makka zata sauke umrah kuma jin zuciyar ta tayi fes kaman ance mata ga aljanna.
Suna fitowa daga mota suka nufan babban kofan da zata sada su da ka'aba Dameer ya jawo Deeyana jikin shi ya rungume be San mai yasa ba hakan kurin yaki wani farin ciki ya rufe shi, haka suka shiga suka fara d'awafi addu'a kon Deeyana ba wanda Bata yi har Dameer ma yi mai take dan shine sanadiyan zuwan ta kasan haka suka gama d'awafi suka tafi safa da marwa komai sunyi shi a nutse dan wani abun Dameer d'in ne ke gaya mata sun Sha ruwan zam-zam Sosai a kofi daya ya diba yasha sannan ita ma ya Bata tashi haka suka gama ibadar su sai bayan sallahn Isha sannan suka kama hanyan gida.
Suna Isa gida ko abinci bata ci ba ta kwanta dan ba k'aramin gajiya tayi ba shima dai Dameer d'in hakane wanka yayi kawai ya kwanta ko haduwa da Ammi Basu ba, washe gari Ammi da kanta ta hada ma Deeyana break irin na Nigeria da ta koya su Deeyana basu tashi ba sai kusan bakwai na safe shi yaja su sallah ma duk kunya ya ishe shi be tashi da huri ba.
Sai da sukai wanka tukun suka nufi in da ake cin abinci sai da Deeyana ta gaishe da kowa sannan ta zauna in da take zama kusa da Ammi suka fara break bayan sun gama ne Ammi ta jata zuwa D'akin ki tana ta bata tarihin Saudi Arabia.
Bayan sati hudu Deeyana da Dameer sunje Madina sai da sukai duk ziyara kafin suka dawo makka guraran shak'atawa da dai sauran su kullum sai Ammi ta matsa ma Dameer ya Kai Deeyana a d'an zaman da sukai wata irin shakuwa mai karfi ta shiga tsakani su sun Saba sosai dan yanzu abinci ma in ba tare ba Basu ci kuma wannan Ammi ce ta Saba musu sai ta had'a musu abinci su uku da ita tace suci tunda suka saba ma Sai ya zama su biyu suke abin su.
Nigeria.
Gimbiya Haleematun-Sa'adiya tana ta shirye-shiryan tafiya saudiyya Dan mai-martaba ya barta tunda tace umrah zata to, sati na gaba ne tafiyan nasu sai murna take Dan burin ta ya kusa cika sa'i da lokaci ta Kan Kira Dameer tace ya Bata Deeyana su gaisa haka nan yake Bata ita ma Deeyana ba wani sakin jiki take da ita ba Yana kula da ita duk santa zai Bata waya yace, momma to sai yaga yanayin ta ya canja.
Amma da Abba suna cikin kwanciyar hankali Dan kusan kullum sai sun gaisa da Deeyana Dameer ne ma su biyu suka tab'a magana da Abba amma Amma kuwa kusan duk kwana biyu sai ya Kira ta sun Sha hiran su.
Wata ranar juma'a mai-martaba ya dawo daga sallah juma'a yana zaune a fada aka ga yayi taga-taga zai fadi cikin tashin hankali mutan fad'a da fadawa suka taro shi idon shi yayi sama, malaman fada ne sukayo Kan shi aka fara duba shi addu'a suka fara Mai da suka ga abun bana yi bane sukai part d'in shi da shi zuwa lokacin gaba daya masarautar mure tasan halin da sarki Fahad Abdullah yake ciki.
Gimbiya Mabaruka ana fad'a mata ta tafi part d'in nashi yana kwance Kan Bed har lokacin idon shi na sama kuka ta fashe da shi ta fara tambayan mutan fada mai yasa mai shi, gimbiya Haleematun-Sa'adiya da gimbiya Marwa a tare suka shigo kowa na tamabayan mai yasa mai shi gimbiya Aisha ma ta shigo duk dai suka hadu ana ta jimamin abunda ya samu mai-martaba.
Likitan sarki Fahad Abdullah aka Kira nan da nan kam sai gashi ya hau duba shi kowa yace ya fita a D'akin kusan awa guda yana duba shi sannan ya fito parlour zuwa lokacin kowa ya hadu har su sarauniya Maimunatu da sauran yan uwan ta suna ganin shi suka fara tambayan shi ya tashi, kallon su yayi sannan ya girgiza kai yace,
"Mai-martaba Yana da wata damuwa to gaskiya a tunani na ita ta haifar mai da matsala yanzu haka zuciyar shi tana gab da bugawa amma Alhmdllh yanzu na mishi wasu allurai zuwa gobe Zan k'ara zuwa na duba shi Allah ya k'ara sauki ya k'ara mai lafiya amma gaskiya kusan abun da ke damun shi".
Gaba dayan su juya maganar da likita ya fad'a suke to mai yake damun mai-martaba haka?? fita likitan yayi su kuma suka hau tunani kowa da abunda yake tunani a zuciyar shi gimbiya Mabaruka ce tayi karfin halin shiga bedroom d'in da mai-martaba ke kwance zaunawa tayi dai-dai kan shi sannan ta fara cewa, "abunda ke damun ka be huce tunanin matar ka da kanin ka ba, ga abunda saurin fushi ya jawo ma, ko baka fada cewa kana tunanin su ba Ni nasan haka ne Allah ya baka lafiya amma a tunani k'anin ka na kusa da kai yanzu".
Tana gama fadan haka ta tashi ta fita a D'akin, mai-martaba da tunda ta fara magana ya bud'e idon shi amma ba wani jinta yake Sosai ba dan yana jin jiki sama-sama yaji karshan maganan ta.
Can kuwa har gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta buga waya ta kira yarima Dameer ta sanar mai cikin tashin hankali Dameer yace, Mata insha Allah gobe zai zo, a zahiri gimbiya Haleematun-Sa'adiya kwata-kwata bata ji dadin rashin lafiyan mai-martaba ba tunda a satin zata tafi saudiyya yanzu kam tunda bashi da lafiya ai dole ta jinkirta da tafiyan shiyasa take addu'a Allah yasa Dameer yazo da Deeyana dan in ta ce mai ya taho da ita to zai iya tunanin wani Abu tunani ta fara to yanzu ya zata billo ma al'amarin.
Dameer kam tunda gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta gaya mai mahaifin nashi bashi da lafiya ya kasa tsaye ya kasa zaune Deeyana ma duk ta shiga damuwa sabida ganin shi a haka, Ammi ce ke kwantar mai da hankali cema Deeyana kawai yayi ta shirya gobe zasu tafi Nigeria budar bakin Ammi sai tace, itama zata amma ba masarautar su zata sauka ba kowa yayi mamaki to mai zatayi a Nigeria kuma.
{ ~To nima dai aunty baby tambayar da nake kenan?? My fan's ko Kun san amsan??~ π€}
Washe gari suka shirya sai Nigeria harda Ammi kuma shi dai Dameer kala bace ba dan gaba daya hankalin shi na gun mahaifin shi, sun sauka lafiya In da fadawa suka zo taran su gidan yarima Dameer na can GRA ya kai Ammi Dan can suka fara hucewa ma Deeyana da tace Dameer ya barta a nan yace Aa gwara su tafi tare haka suka bar Ammi a gidan Sai musu kula da gidan.
Suna Isa masarautar part d'in mai-martaba suka huce Dan ko nasu part d'in Basu je ba a parlour duk suka samu mutan gidan sarauniya Maimunatu tana ganin su ta tashi da saurin ta ta rungume su rungume ta shima Dameer yayi a hankali Yana cewa, "ya jikin Abban".
Sakin su tayi sannan ta kama hannun Dameer suka shiga bedroom d'in da mai-martaba yake, kwance yake da sauri Dameer ya saki sarauniya Maimunatu ya tafi gun shi zaunawa yayi a bak'in Bed d'in sannan ya kama hannun shi duka biyun ya saka a nashi sannan yace, "Abba mai yasa mai ka haka?" Sarauniya Maimunatu ta matso wajan Bed d'in sannan ta dafa kafad'ar shi tace, "bro's baya magana tun jiya munyi munyi yayi magana yayi shuru".
Kallon shi Dameer yayi sannan yace, "Abba kana jin mu dan Allah kayi magana" kaman daga sama suka ji yace, "khaujut khaujut" zaro Ido sarauniya Maimunatu tayi sannan tace, "Abba" murmushi Dameer yayi yana Kara had'a hannun shi da nashi sannan yace,.....
*VOTE*
*COMMENT*
*&*
*SHARE*
*Aunty baby ce*β
[1/6, 10:37 PM] Mum Irfaanπ€±π»: π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦
π¦π¦π¦π¦π¦
π¦π¦π¦
π¦π¦
π¦
π€΄π» *IZZAR SARAUTA*π€΄
π
*_ALHERI WRITER'S* *ASSOCIATION_* β
*~[ Alheri danko ne, duk inda kayi shi zai dawo gare ka, burin mu mu ribantu da alherin da ke cikin wannan harka]~*
*ALHERI SAI DAN AlHERI* π
*Story*
*&*
*written*
*By*
*Aunty baby* β
*DEDICATED TO..*
*π€΄IZZAR SARAUTA FAN'SπΈπ»*
*Aradu Ina jin dadin comment d'in ku Allah ya bar kauna aunty baby taku* *ceπ*
*Sadaukarwa ga UMAIMA ALIYU*
*BISMILLAHIR RAHMAIR RAHIM*
π *page* 5β£1β£β©5β£2β£
___________πyace, "Abba ya jikin naka Ammi tana Saudi Arabia amma tana gaishe ka" magana mai-martaba ya fara a hankali irin muryan marasa lafiya yace, "da gaske tace ka gaishe ni? " daga kai Dameer yayi yana murmushi sannan yace, "eh" fita sarauniya Maimunatu tayi tana murna ta gaya ma duk mutanan parlour cewa Abba ya tashi.
Kowa tashi yayi yana murna ya shiga bedroom d'in Deeyana da ke zaune kusa da gimbiya Mabaruka ta tashi ita ma dan taje ta gaishe shi dan yau bata samu fuska a gun kowa ba gimbiya Haleematun-Sa'adiya in banda hararan ta ba abun da