Showing 12001 words to 15000 words out of 65264 words
Chapter 5 - IZZAR SARAUTA BOOK COMPLETE BY Aunty Baby Ummu Irfan .txt
kuka.
"Innalillahi wa'inan ilaihir rajiun" shine kawai abunda babanta yace zufa ne ya fara zubo mai lallai yaron nan ya cika maci Amana yanzu duk irin sharudan da suka kafa mai sai da ya musu wannan abun.
Rungume ta maman ta tayi tana kara lallashin ta akan haka Allah yaso basu da yarda zasu yi kuma insha Allah sai Allah ya saka mata.
Washe gari.
Ko da Dameer ya tashi ya ganta yayi murna sosai sai tambayar Ina Abban shi yake kawai yake yi, sai tace Mai zai zo ya gan shi har yaron ya manta da abun.
Haka ta saka kanta a damuwa Bata cin abinci bata wal-walan ko yan uwan ta sun zo bata sakin jiki da su kullum cikin kuka take, gashi yanzu wani irin so take Mai da shi yake wahalar da ita.
Maman ta da baban ta burin su ta manta da komai ta barshi ta raini yaron ta Amma Ina abun yaci tura, har Al'mustapha ya dawo ganin gida ko da yaji abunda ya faru cewa yayi bazai yarda ba sai ya dau Mata fansa tunda shi ba Dan halak bane tunda har yayi wa khaujut wannan rashin mutuncin.
Iyayan su ne sukai ta bashi hakuri akan ai aikin gama ya gama ya barshi kawai zai girbi abunda ya shuka, hakan nan yayi hakuri ba dan son ranshi ba.
Ita kuma khaujut yace ta shirya su tafi Dubai d'in tare ko acen ta cire damuwar da ta daura wa ranta da da farko cewa tayi baza ta ba Dan bata son tayi nisa da yaron ta Amma daga baya da aka Mata mgn sai tace to.
Haka nan suka shirya suka tafi aka bar Dameer a hannun iyayan ta yaci gaba da zuwa makarantar shi, Daman ba wani Sabawa yayi da ita ba shiyasa be damu ba.
Yarima Aliyu kon ko da ya fita daga masarautar be San in da zashi ba tafiya kawai yake har Allah ya Kai shi wata kasuwa, nan ne da yaga mutane ya zauna a wata yar runfa mutane sai kallon shi suke tunda sanye yake da kayan sarauta.
Da yaga kallon yayi yawa sai ya shiga wani shago a kasuwar ya siyo wasu k'ananan kaya da yan kudin da ya fito da shi a jikin shi sannan ya cire wannan kayan sarauta da ke jikin shi ya sanya wannan wanda ya siya, ragowar kudin kuma ya siya abinci.
Haka ya koma rufar nan ya zauna har dare kowa ya ta tashi a kasuwar sabida dare yayi ya tafi gida shi kon bashi da in da zashi sai kawai ya jera kwali a runfar yayi kwanciyar shi.
Haka ya kwana a nan sai da asuba ya tashi ya alwala yayi Sallah sannan ya k'ara zaunawa a cikin runfar, haka har mutane suka fara zuwa kasuwar kowa na siyar da abunda yake siyar wa har dai yamma ta k'ara yi.
Ga wata irin yunwa da yake ji bashi da ko sisi haka ya kwanta yana tuna irin rayuwa da yake da, a kwai wani mutumi da tun jiya yake lura da shi ya kasa dauke ido a kanshi gani tunda ya shigo kasuwa yana zaune a runfa kuma shi ba wani abu yake siyarwa ba.
Kau da idon shi yayi a kan shi yaci gaba da kasuwanci shi har dare yayi zai tafi gida, runfar ya k'ara lekawa har lokacin Yana kwance sai yaji bazai iya tafiya ba tare da ya tambaye shi menene yasa yake zaune tun jiya a runfar ba.
Sallama yayi mai yarima Aliyu da ke kwance yaji ana mai sallama sai ya tashi zaune yana kallon wqnnan bawan Allah, hannu ya Mika mai suka gaisa sannan mutumin yace,
"Dan samari lafiya kuwa kike zaune anan tun jiya ko bata kayi ne? ".
Girgiza Kai yarima Aliyu yayi sannan yace, "ba Bata nayi ba kawai Ina zaune ne kafin na samu warin zama".
Kallon shi mutumin yayi sannan yace, "wurin zama kuma Dan samari Kai bako ne kenan? ".
Kai ya d'aga Mai alamar eh, mutumin yace, "in ba damuwa ka taso in Kai ka gida na wala Allah ko gobe sai ka tafi Amma kwana a kasuwa ai hadari ne".
Girgiza Kai yarima Aliyu yayi sannan yace, "ai bansan yaushe zan samu gidan ba na gode kawai baba sannan ya juya ya kwanta".
Tsayawa mutumin yayi tsaf yana kallon shi kaman yana cikin damuwa Amma zai taimaka mai tunda duk Wanda ya taimake wani Allah zai taimake shi, sannan yace, "dan samari akwai wani Abu da yake damun ka ka fada min insha Allah Zan taimake ka".
Hakan nan yarima Aliyu yaji mutumin ya kwanta Mai kawai sai ya tashi zaune wasu zafafan hawaye suka wanke mai fuska sannan ya fara ba mutumin labari Wanda ya boye Mai abu daya cewa shi d'in Dan gidan sarauta ne cewa yayi kawai matar yayan shi ta mai Sharri shida amaryar matar yayan nashi.
Mutumin ya tausaya mai sosai sannan yace insha Allah zai taimake shi ya dauke shi kamar uba shi kuma zai dauke shi d'a yana da Mata daya da yara biyu duka Mata in zai Iya zama da su to bashi da matsala kuma yasan matar shi ma haka.
Daga Mai Kai kawai Aliyu yayi sannan mutumin ya rik'e Mai hannu suka fita a runfar mashin din mutumin suka hau daga Nan suka wace gidan shi.
Ko da suka je gidan mutumin ya shedawa matar shi halin da yaga yaron ita ma ta tausaya mai sosai sannan tace, "insha Allah zasu rike shi hannu bibiyu shima ya dauke su iyayan shi ya zama Yaya kuma a gurin 'ya'ya su" yace, "insha Allah" sannan aka Kai shi daki aka bashi abinci.
Washe gari haka aka kawo Mai abin Kare sannan yaran Mata suka shigo suka gaishe shi baban yace, ga yayan su nan su shima aka nuna Mai su akan ce ga kannin shi nan.
Tun daga lokacin ya saki jikin shi dasu Mariya wacce suke ce ma mama tana bashi kulawa sosai da sosai haka shima yana ba Yan yaran kulawa da babban mai suna fateema sai k'aramar mai suna Faiza.
Fateema shekaran ta sha-bakwai sai k'aramar Faiza shekaran ta sha-hudu, Nan da nan suka saba sosai da sosai.
Ya fara bin baban kasuwa, a hankali ya fara koya mai kasuwanci har ya saba, suna dawowa daga kasuwa zasu zube parlour suyi ta hira wani zubin hiran duk fad'a ne shida fateema mama tayi ta musu dariya.
Haka Yarima Aliyu yake ta rayuwa a gidan be tab'a nuna musu daga in da ya fito ba, shakuwa na Kara shiga tsakin su da fateema, wanda daga gani kasan soyayya ce.
Tunda mama ta fahince da kwai soyayya a tsakanin su sai ta sanar da baba yayi farin ciki sosai da jin haka dan D'an zaman da yayi da Aliyu ya karanci halayan shi mutun ne Mai son ibada sannan kuma ga amfani dashi.
Haka ya tara Aliyu da fateema ya tambaye su ko suna son junan su k'asa Aliyu yayi da Kai Dan har cikin zuciya shi yake son fateema nan baba ya fahinci shi kunya yake ji itama fateema haka ne tana masifar son Aliyu shiyasa ita ma ta k'asa da Kai harda boye fuska a hijabi.
Mama da baba duk duka sa ta dariya nan baba yace, "ya tsayar da ranar aure wata daya tunda duk gida ne ba sai anyi wani Abu ba".
Farin ciki da Aliyu ya shiga ciki ba'a magana kuka kawai ya fashe da shi yana k'ara gode ma baba akan dawainiyar da yake da shi.
*************
Masarautar mure kuwa tun daga wannan lokacin mai-martaba sarki Fahad Abdullah ya canja gaba daya, duk wani adalci da yake ya daina duk wata makaranta da ya bud'e sai da ya maida ta ta kudi.
Islamiyya da ya bud'e ya maida ta ta kudi asbitocin shi komai dai mulkin shi ya koma IZZAR abu kad'an zakai a yanke ma hukunci.
Gaba daya yanzu garin tsoron shi ake da mulkin shi kuma kwata-kwata besan adalici ba IZZAR SARAUTA kawai ya sa a gaba.
Bayan wata daya da yin wannan abun aka daura Mai aure da Mata biyu gimbiya Marwa da gimbiya Aisha, ya mance shafin wata khaujut ko D'an shi ma Sai wata ran ne yake Tina wa yana da d'a Amma kwata-kwata yaji baya son shi.
Jin tsanar yaron kawai yake shiyasa ya yanke ma Kan shi hukunci ya bar Mata Dan tayi duk yanda take so da shi, gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta zama hamshakiya a masarautar mure sai abunda tace ayi ake yi.
Gimbiya Mabaruka nata Ido bata cewa hmmm Bata cewa ummmmm sai yanda sukai, gimbiya Marwa ta samu ciki Amma shima be zauna ba ya zube ita kam gimbiya Aisha bata tab'a ko batan wata ba.
******
Shirye-shiryan biki ake fateema da Aliyu Wanda ba wani bidi'a zasu yi ba walima ce kawai bayan daurin aure, haka kon aka yi an daura aure lafiya an tashi lafiya.
In da akai walima kowa ya tafi cikin farin ciki, wani dan matsakaicin gida baba ya gina musu Wanda ya ba Aliyu halak malak, Aliyu har rasa bakin godiya yake Dan abun da baba yake Mai ko mahaifin shi sai haka.
An Kai amarya fateema gidan ta lafiya Wanda aka barta daga ita Sai mijin ta Aliyu, nisiha Aliyu ke Mata sosai Mai ratsa jini da jijiya sannan suka gabatar da Sallah bayan sun idar suka ci kaza daga nan Aliyu ya mori amarcin shi.🙈
Alhamdulillah komai Yana tafiyar musu dai-dai Aliyu Yana da Dan rufin asirin shi haka yake taltalin fateeman shi har Allah ya basu rabo, baba da mama sunyi farin ciki sosai da addu'ar Allah ya sauke ta lafiya.
Wata Tara cif Allah ya sauke ta lafiya ta samu yarta mace, wacce aka sa mata sunan mama suna mata lakabi da Deeyana, Aliyu ya dauki san duniya ya daurawa Deeyana .
Deeyana nata girma Masha Allah ga shegen wayyo, har aka yaye ta suna ta rainon yarsu ciki so da Kauna har ta kai shekara uku Aliyu ya sanya ta a mkrt yariyar ta taso da wayyo da kok'ari kowa burge shi take.
Deeyana tun tana karama kyakyawa ce sosai fara ce sol ga gashi Dan komai uban ta ta biyo Aliyu..
*****
Dameer yayi girma ya zama kyakyawan saurayi jinin larabawa ajin karshe ga kyau ga ilimi lokacin da ya Kai shekara 20 a duniya ya matsa ma kakan nin shi akan sai sun kaishe Nigeria yaga mahaifin shi.
Haka nan khaujut ba yanda ta iya ta shirya suka tawo Nigeria hotel suka fara sauka sannan washe gari ta Kai shi har kofar Gate d'in masarautar mure, tace, ya shiga ita baza ta shiga ba.
Haka nan ya shiga kowa binshi yake da kallo bayi da fadawa, sunga balarabe a gidan su nan da nan zance ya karade masarauta balarabe ya zo, da zance ya je gun mai-martaba sai yace, aje a kawo mai shi.
Daman Dameer neman shiga yake ko da fadawa suka zo sai ya bisu har fada, Yana shiga yayi ido hudu da mahaifin shi kallon kallo kawai suke ma juna.
Mai-martaba yana gani Dameer ya Mike da sauri yaje ya rungume shi yana fad'i, "sai yau taga Daman kawo min kai" .
Da Ido kawai Dameer yabi mahaifin nashi Dan wani irin takaici ya bashi, kujera aka bashi a fada ya zauna mai-martaba yace, "kaine dai baka sannin ba Amma duk shekara sai naje na ganka Amma kai da mahaifiyar ka baku tab'a ganin na ba".
Tabe Baki kawai Dameer yayi Dan shi ba mai son yawan magana bane yanzu sai kanshi ya fara ciwo.
Haka sarki Fahad Abdullah ya dunga ba Dameer labari harda ya kwana a masarautar washe gari aka had'a shi da fadawan shi Wanda zasu dunga tsaron shi.
Tunda gimbiya Haleematun-Sa'adiya taji zuwa shi hankali ya kai koluluwar tashi, wani sabon tashin hankali ma Sai da ta ganshi gaban ta sai da ya Fadi.
Satin su biyu a Nigeria suka koma saudiyya tare da fadawan da mahaifin shi ya bashi, tun daga lokacin baya shekara be zo Nigeria ba ganin mahaifin shi.
Haka nan kuma wani zuwa da yayi yaga mahaifin nashi ya canja mai kwatakwata ba kamar yanda da yake rawar jiki da shi ba.
Gimbiya Haleematun-Sa'adiya tana nuna tana masifar son shi har mamaki take bashi, lokacin ya Dan fara sakin jiki da ita wani zuwa da yayi kawai sai yaji suna magana da jakadiya akan yanda za'a gama da shi tun daga lokacin ya daina sakin mata fuska.
*Wannan ne labarin masarautar mure*
*CIGABAN LABARI*
*VOTE*
*COMMENT*
*&*
*SHARE*
*Aunty baby ce*✍
[1/6, 10:37 PM] Mum Irfaan🤱🏻: 🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚
🦚🦚
🦚
🤴🏻 *IZZAR SARAUTA*🤴🏻
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }
🎐 ```G•W•A```🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼
*Story*
*&*
*written*
*By*
*Aunty baby* ✍
~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@ Gaskiya writer's Asso~
*DEDICATED TO..*
*UMAIMA ALIYU*
{ *golden girl} wannan littafin sadaukarwa ce gare ki gaba daya bani da bakin gode Miki Allah ya bar kauna nagode sosai da irin comment d'in ki da addu'ar da kike* *min* 😻😻
*BISMILLAHIR RAHMAIR RAHIM*
📝 *page* 2⃣1⃣⏩2⃣2⃣
*____________*📖 *CIGABAN LABARI*.
Haka Dameer ya gama zaman shi a Nigeria ba tare da ya saka mahaifin shi a Ido ba har ya koma saudiyya.
Ya cigaba da harkogin shi kaman yanda yake Amma in ya tuna mahaifin shi abun na damun shi, sai mahaifiyar shi ce ke kwantar Mai da hankali.
Watan shi uku a Saudi Arabia ya k'ara shiryawa ya taho Nigeria sabida Kiran shi da akai akan plazan shi da yake da ita ta Nigeria tana buk'atar manyan ma'aikata.
Ko da yazo kaman kullum haka Amma wannan zuwan ya samu ya gana da mahaifin nashi sama-sama,
Tafiya suke ita da k'awar ta suhaema suna tattaunawa akan walimar makarantar islamiyyan da zasu yi suheema ta Kalle Deeyana tace,
"Mtss My dear wallahi Ni yusuf ya matsa min akan maganar Auran mu Amma ni ina ga kamar sai mun kammala waec zance ya turo, Amma naji kamar Baffan mu na cewa ko bamu gama waec ba indai ya shirya kawai ya turo"
Deeyana tace, "Ni dai a yanzun gaskiya ba Aure bane a gabana insha Allah abbana ma University zai saman min".
Murmushi suheema tayi sannan tace, "hmm ai wallahi ba ruwan na da wani zan ce University na karashe a gida na".
Dariya Deeyana ta tun tsire dashi sannan tace, "hehe my dear Allah ya kaimu musha biki".
Haka dai suka cigaba da firan su har suka k'ara sa gida, daman kusa suke ga gidan su Deeyana ga gidan su suheema Deeyana ce ta fara shiga gidan su.
Tana shiga gida ta tatda Amma na kitchen, kitchen d'in ta shiga tana sallama sannan tace, "Amma sannu da gida ya kike ya aiki?".
D'agowa Amma tayi tana murmushi sannan tace, "Deeyana kin dawo daga makarantar?".
Tace, "Eh na dawo ".
"Toh ya makarantar? ".
Tace, "Amma Alhamdulillah kin san ma muna ta shirin walimar mu".
Amma tace, "Allah ya kaimu ranar" haka dai suka zauna suna hira irin ta uwa da y'a gwanin ban shi'awa, suna cikin hirar sai ga Abban Deeyana ya shigo.
Yace, "A'a Deeyana yan makaranta an dawo?".
Murmushi tayi sannan tace, "Abba sannu da shigo wa".
Yace, "Yauwa Deeyana ya karatun?".
Tace, "Alhamdulillah Abba ranar juma'a ma za'a yi waliman mu".
Yace, "Toh shikenan Allah ya Kai mu, ai ina jin dad'in yarda kike nuna kwazo a makaranta Allah ya miki albarka"
Ita dai Deeyana murmushi kawai tayi tace, "ameen", sannan ta tashi ta shige d'aki, su kuma suka cigaba da zancan su, kan Deeyana akwai k'okari masha Allah.
Haka dai suka cigaba da shirya-shiryan walimar su daza suyi ranar juma'a, dan gangarumin walima za'a musu na saukar Alqur'ani,
Ita da suheema komai nasu iri daya sukayi, walimar na gaiyatar manya malamai da dama irin su, Shek Malan jubirl, Shek Malan Abdulra'uz, da dai sauran manya manya malamai.
Yau ta kasance ranar juma'a duk wani Wanda ke cikin yan walimar ya hallara suna zaune guri da aka ware musu Masha Allah sunyi kyau ba karya , tare da iyayyan su da kuma abokan Arziki,
A cikin manya bakin da aka gayata harda daya daga cikin matan Sarki, wato gimbiya Haleematun-sa'adiya, tazo tare da fadawanta haka shugaban makarantar da sauran malaman suka ringa Kai gaisuwa tare da samun tarba Mai kyau,
Haka aka cigaba da gudanar da walimar cike da tsari da burgewa, haka aka cigaba da k'iran yan walima dan gabatar da karatu,
Haka har Aka zo kan Deeyana Masha Allah duk Wanda ke gurin sai da Deeyana ta burge sa, sabida yarda take fitar da harafin koh wanann karatu, bayan ta gama ta koma bangaran Hadisa shima, sannan ta dawo kan tarbiya ta fara bayani kamar haka,
( Dan Allah iyayye mu kula da karatun yaran mu, yanzun wani zamani yazo da zaka ga wata Sam bata damu da yaran ta suje islamiya ba, Amma fi d'auka ka school akan islamiya, ba'a ce kar yaron ki yaje school ba, Amma dan Allah ki nusar dashi mahimmancin duka biyun, wani yaron ma baya zuwa makaranta sai a gida ake koyar dashi ba'a ce gidan baya shiga ba Amma idan so samu ne ki tuzashi can zefi saurin mayar da hankali sabanin yana cikin gida malami ya biya Mai karatu be iya ba Sam bazai damu ba, Amma idan acikin makarntane fa yau antashi ka tashi ka karanta, ban iya ba, gobe an kuma shima ban iya ganin yarda ake mai dariya da kuma irin kallan da suran yara ke binsa dashi a Karo da uku wallahi zaka ga yaro
ya mayar da hankalin dan bazai so kullum a ringa mai dariya ba Allah yasa mu gyara)
Tunda gimbiya Haleematun-sa'adiya taga Deeyana taji ta burge ta, take ta saka abu a ranta,ko dan ta b'ata mai rai sai tasa ya aure ta.
Abu na biyu kuma taga daga ganin yariyar yar talakawa ce ko dan haka dole sai ta had'a wannan aure, wani makirin murmushi ta saki.
Haka aka gama taron walima lafiya an raba kyututuka masu yawa, Deeyana ita tazo ta daya sosai aka bata kyauta, kowa ya tafi yana murna.
```Koh``` ```ya``` ```abun``` ze ```kasance``` ```muje``` ```zuwa```
*VOTE*