Showing 63001 words to 65264 words out of 65264 words
Chapter 22 - IZZAR SARAUTA BOOK COMPLETE BY Aunty Baby Ummu Irfan .txt
samu nan kuma Deeyana ta farka kowa na mata sannu da ya jiki aka kira nurse ta kara duba ta sannan ta mata wasu alluran, had'a mata tea gimbiya Aisha tayi sannan ta zuba mata farfesun kayan cikin da aka yo mata, ta dan ci ba laifi sannan aka mika mata jaririn da sai yanzu ma ta dauke shi.
Kallon shi tayi kaman shi daya da Dameer shima murmushi tayi sannan ta fara bashi nono nan kuwa ya cafke kaman jira yake ya fara sha sosai, murmushi gimbiya Aisha tayi sannan tace, "wai acici kenan wannan ai yafi kowa ci cibi daga bashi nono ya cafke kaman jira yake?".
Ita ma gimbiya marwa murmushi tayi sannan tace, "ba komai dai ai wayewar kenan" haka dai sukai ta caftar su suna dariya ita dai Deeyana murmushi kawai take musu.
Sha-biyu dai-dai Dameer ya Isa airport Dan ya kosa yaga Deeyanar shi da kuma baby boy d'in shi nan da nan jirgin su ya tashi sai Nigeria, Deeyana Kam tana zaune sai tunanin Dameer d'in ta take ko ya sani oho Bata sani ba ita da badan su gimbiya Marwa ba tambayar Ammi zata Yi.
Dr ya shigo ya k'ara duba su lafiyan su lau ita da jaririn ta sannan yace nan da two hours zasu iya tafiya, k'arfe hudu dai-dai jirgin su Dameer ya sauka Daman fadawa suna airport d'in suna jiran shi direct hospital d'in yace a huce da shi sabida hankalin shi gaba daya na kan Deeyana nan shi.
Lokacin su Deeyana kuma sun gama had'a komai zasu tafi gida har ma sun fito daga hospital d'in zasu shiga mota shi kuma Dameer d'in ya fito, da sauri ya k'ara su gurin su da murmushi a fuskar shi, k'amshin turaren shi kawai Deeyana taji tasan shine da saurin ta ta juya bayan ta.
Nan sukai ido hudu sakan mata wani shu'umin murmushi yayi ita ma murmushi tayi, Ammi tace, "Aa Dameer Ashe kun sauka" "eh Ammi tafiya gida zakuyi haka? " yayi maganar yana kallon Deeyana.
Gimbiya Marwa tace, "eh tafiya zamuyi an duba su Alhmdllh basu da matsalan komai" jinjina kai yayi Ammi ta kama hannun Deeyana suka shiga mota gimbiya Aisha da babyn yake hannun ta ta shiga dayan motar gimbiya Marwa kuma motar da su Ammi suke ta shiga shi kuma Dameer ya shiga motar da aka kawo shi suka tafi.
A hanya gimbiya Marwa take tambayar Ammi Ina za'a huce da Deeyana Ammi tace, gidan ta sai a Kai mata ko wanda zata dunga mata wanka ne, gimbiya Marwa tace, "Aa gwara a kaita masarauta sabida gida daga ita sai shi akwai matsala".
Ammi tayi murmushi dan tasan halin y'a'yan nata sai tace, "ai Deeyana yanzu ba yariya bace tasan yanda zatayi ta kula da kanta" to gimbiya Marwa tace, kawai nan aka drive ya huce dasu gidan su Deeyana, tana jin su addu'a take Kar Allah yasa Ammi tace, za'a kaita masarauta sabida tasan halin mijin ta gwara in a gidan su ne tasan yanda zata tafiyar da kayan ta.
Suna isa gida duk suka fito a motar suka shiga cikin gidan bedroom d'in Deeyana suka huce tana shiga kwanciya tayi sabida cikin ta da ke matsa mata nan kuyangu suka fara daura abinci gimbiya Marwa kuma ta shiga toilet ta had'a ma Deeyana ruwan wanka sannan tace ta tashi tayi mata ko jinin ya sauka na in yaji ruwan zafi tunda shi yake sata ciwan cikin.
Dameer kam ko da suka iso yaga motocin su Ammi ba k'aramin dadi yaji ba sabida bai tab'a zaton Ammi zata bari a kawo Deeyana gidan su ba ai kon part din Deeyana ya shiga lokacin har an ma jararin wanka an shirya shi cikin kayan shi masu Kyau da tsari, da murnan shi ya dauka yaron.
"Woow Masha Allah" kawai yace sannan ya fara mai addu'a, "wannan ma kamar mu daya" shine kawai abunda Dameer ya maimaita yana kissing d'in jararin haka Deeyana ta fito daga toilet ta samai shi ya manne shi a k'irjin shi sai murmushi kuma yake.
Zaunawa tayi bak'in Bed tana goge ruwan jikin ta da towel, kuri ya mata da ido yana jin wani irin sonta na kara shiga ko wani bargo na jikin shi, turo baki tayi sannan tace, "kallon fa? " tasowa yayi daga inda yake ya matso kusa da ita sannan yace, habibaty bani ma da bakin gode miki Wallahi kin bani duk wani farin ciki na duniya Allah ya miki albarka ya raya mana yaran mu".
Murmushi Deeyana tayi sannan tace, "Ameen hayatee Ashe kana hanya ya jikin Jadda? " "Hmmmmm ko ban tashi dawowa ba ai dole na dawo kuma daman yau zan dawo nayi ta Kiran wayan ki ashe lokacin ma kina hospital" yayi maganar yana gyara ma jararin hular kan shi.
Haka dai sukai ta firan su har aka kawo ma Deeyana abinci dan Ammi ma ta tafi gida sai gimbiya Marwa da gimbiya Aisha kawai aka bari, ai kam tare suka ci abincin suna ta hiran su har aka kira maghrib Dameer ya tashi ya tafi dan yayi wanka yayi Sallah.
Bayan kwana shida yau ya kama ana gobe suna sai shirye-shirye ake yan uwa da abokan aziki duk sun zo dan tunda Deeyana ta haihu gimbiya mabaruka ta dawo gidan gaba daya sai kuma kuyangu manya masu manyan shekaru da aka kara kawowa dan su dunga kula da Deeyana da kuma baby boy d'in ta.
Mai-martaba ya kira Dameer ya tambaye shi sunan da za'a sama jaririn yace, Aliyu shima ba k'aramin murna mai-martaba yayi ba dan yaji dadin yanda Dameer d'in ke mai kara nan aka sanar a masarautar kowa ya shiga murna sarki Aliyu kuwa ai baki har kunne haka akai ta saka ma jaririn albarka.
Washe gari ya kama suna anyi shagali kala-kala sannan an rada ma yaro sunan shi Aliyu za'a dunga kiran shi da jenior sosai Deeyana tayi murna da farin ciki dan b'ata kawo sunan Abban ta za'a saka ba haka aka yi taron suna lafiya aka tashi lafiya.
Bayan wata biyar Deeyana da jenior sunyi Kyau abin su har yanzu Abdul na hannun Ammi yana samun kulawa sosai Deeyana har ta cigaba da zuwa makarantar ta dan jenior bashi da rigima a gida take barin shi, shima Dameer kasuwancin shi yaci uban na da dan sosai kudi ke shigo mai sai abun alkhairi da yake ta ma talakawa.
Watan jenior goma sha-daya Deeyana ta daina ganin period d'in ta tun da taga haka ta san ciki ne kuka kan tasha shi ba adadi har rama tayi sabida damuwa da ta saka ma ranta shi kam Dameer bai sani ba amma shima yaji ta canja mai ta ko ina ma kullum tambayar ta yake tace lafiya.
Akwai wata rana da ya kusance ta kwata-kwata manta kan shi yayi sai santi yake zuba mata yana tambayar ta wai menene sirrin ta zama kaman wani zuma baya gajiya da ita sai dai tayi murmushi kawai, haka har jenior ya shiga shekara daya cif lokacin ba in da baya zuwa sannan tace ma Dameer zata yaye shi.
Da farko kin yarda yayi wai bai isa yaye ba tace, "Abdul ma isa yayan yayi aka yaye shi to shima wannan hakan nan za'a yaye shi" tun da tayi wannan maganar ya gane ashe ciki gare ta yayi murna sosaii dan har mota ya siyo mata akan tukuici Allah ya sauke ta lafiya kuma zata ga babban kyautar da zai mata.
Nan suka had'a kayan jenior gaba daya rabar jumm'a suka shirya suka kai shi gun Amma ita ma fad'a ta fara musu sai daga baya ta fahince kaman ciki Deeyana take dashi sai tayi shuru kuma, Ammi kam tun da taga sun kawo jenior tace, "Allah ya sauke ki lafiya dan tasan ciki ne".
Haka kam Deeyana tayi ta rainon cikin ta har Allah ya sauke ta lafiya ta k'ara samun danta namiji wanda aka saka mai sunan mai-martaba tsohun sarki Fahad wayyo shima anyi shagali har ake ce mata uwar maza su uku duk maza Abdul jenior sai kuma Fahad shi Ba'a boye sunan shi ba.
Shekaran shi daya da wata uku ta samu wani cikin wannan karon ko hmmmm bata ce ba a zuciyar ta tace ba wanda zata kaima yaye ai sai a gaji da ita ma ko Dameer ta kasa gayawa tana da ciki dai rainon abinta take kuma tana ba Fahad nono har ya kai wata biyar lokacin Dameer ma ya riga ya sani.
Ayusha ta haihu xasu tafi suna anan ne Ammi ta san Deeyana nada ciki fasa zuwa sunan tayi ta amsa Fahad d'in tace, "a yaye shi haka tunda yanxu shekaran shi daya da wata bakwai ai ya isa yaye kar shan cikin da yake kuma ya saka mai wani cutar".
Nan Dameer da Deeyana suka tafi Saudi Arabia satin su biyu suka dawo Nigeria, Dameer ba k'aramin kulawa yake da Deeyana ba dan gani yake kaman rabin ran shi ce duk ranar da aka ce ba Deeyana to yana ji bazai tab'a kara numfashi a duniya ba ita ma haka ko tafiya Dameer yayi bata iya bacci shiyasa yanxu baya tafiya ta kwana ko da kuwa kasashan waje ne.
Cikin ta har ya shiga wata goma shuru kullum cikin addu'a ake Allah ya sauke ta lafiya in ta zauna tayi shuru tace, "to ko dai mutuwa zatayi" haka dai har wata ranar talata Allah ya sauke ta lafiya ta samu yaran ta twin's duka mata masu kama da juna gashi komai na Deeyana suka yo.
Fadan irin farin ciki da masarautar mure ta shiga baya musaltuwa tun da ta haihu kullum sai an yanka ragona da shanu har ranar suna ranar irin kyautar da mai-martaba tsohun sarki da sabon sarki sukai baya faduwa, haka uban gaiyar ma yarima Dameer.
Haka dai akai suna lafiya aka tashi lafiya yara sunci sunan Ammi da Amma wanda za'a dunga ce musu Nihal da Nayal, Abdul da Fahad suna gun Ammi jenior kuma na gun Amma.
Dameer aje komai nashi yayi ya dawo gida gaba daya yana kula da habibaty shi da yan twins d'in shi wanda suke ta girma abin su, yayi yayi ma Deeyana ta koma makaranta taki sabida tace, bata ga amfanin karatun ta ba tunda ko ta fara ciki zai tsayar da ita, murmushi Dameer yayi sannan yace, "hakan nan zaki daure ki cigaba da zuwa bana so kiyi ta wasting time d'in nan a banza".
"Hmmmmm hayatee kenan to ya zanyi tunda haka Allah ya tsara min ciki da goyo sai dai fatan Allah ya shirya mana su cikin tafarkin islama" Deeyana tayi maganar muryan ta a raunane.
Rungume ta yayi sannan yace, "Allah ya miki albarka Deeyana ina son ki ina sonki Deeyana Allah ya barmu tare har a aljanna" ita ma Deeyana rungume shi tayi tana sakan mai zafafan kiss shima ya fara mayar mata daga nan suka cilla wata duniyar.ππΏββ
Bayan shekara biyar.
Zaune na hango sarauniya Deeyana a tafkeken parlour ya tsaru iya tsaruwa yara ne wanda baza su wuce shekaru biyar ba su biyu duk mata daga gane dai twins ne Nihal da Nayal sanyi cikin uniform din makaranta sun dawo da gudu suka rungume "Deeyana suna cewa Momy Momy mun dawo".
Ita ma rungume su tayi tana murmushi sannan tace "wow twins d'in Momy sannun ku da dawowa ya school d'in anyi karatu da kyau dai ko?".
Daga kai sukai sannan suka fara cire duguwar rigar tasu kuyangu ne suka shigo da sauri suka gaishe da Deeyana sannan suka kama hannun yaran suka tafi dasu dan su shirya su su baau abinci, Abdul jenior Fahad duk suna gurin su Ammi, tun daga kan twins Deeyana bata Kara haihuwa ba ta cigaba da karantun ta har yanxu ta kammala.
Amma Dameer ya hana ta zuwa aiki wai aikin jarida bai dace da ita ba dan ta matsa ne ma yasa ya barta ta karanta miss communication d'in.
Da daddare misalin takwas Dameer ya dawo cike da daukin ganin tauraruwar shi ai kam ta tare shi da murnar ta ita ma tayi mai shiri sosai ga abinci da ta had'a mai kala-kala wanka ma ita tayi mai bayan sun fito ta shirya shi kaya ta fito mai dashi mara su nauyi wanda baza su takura mai ba sannan ta riko hannun shi sukai wajan dining table.
Sai da yaci ya koshi sannan su twins suka zo wajan shi nan suka fara wasa yana ta biye musu sai gurin goma na dare sannan yaran suka tashi suka ce "Momy Daddy bye good night".
Hannu Dameer ya d'aga musu sannan yace, bye twins d'in Momy ayi addu'a in za'a kwanta" suka ce to sannan suka tafi tashi Deeyana tayi ta bisu sai da taga ko wacce fa hau Bed d'in ta sannan ta musu addu'a duk ta shafa kan su sannan ta fito daga dak'in nasu ta dawo gurin oga Dameer.π€
Tun kafin ta karaso ya taso ya sure ta sai Bedroom d'in shi yace, "yau sai sun saman ma twins k'ani ko kanwa".
To ni kam aunty baby nace a buga kwallo da kyau har aci sa'a ta fad'a ragaπ€©.
*TO ALHAMDULILLAH A NAN NA KAWO KARSHEN WANNAN LITTAFI NAWA KUSKURAN DA NAYI A CIKI YA ALLAH KA YAFE MIN ALLAH YASA SAKON DA NAKE SON ISARWA YA ISA KAMAN YANDA NAKE SA RAI*
~Godiya ta musanman gare ku masoyana Allah ya bar kauna nagode sosai da irin kulawar da kuke bani Allah ya bani ikon fadakar da ku dai-dai, sai kun sake jina a sabon littafai na kamar haka *MIJIN FATIMA* and *NAHEEDARH* ku dai kuci gaba da kasancewa tare dani *NAHEEDARH* labari ne mai ban tausayi soyayya da kuma nishadi insha Allah first January zan fara suburbudo muku Allah dai ya k'ara min lafiya~
*Naheedarh*
*MIJIN FATIMA*
*Coming soon*π
*Aunty baby ce*β