Showing 18001 words to 21000 words out of 65264 words
Chapter 7 - IZZAR SARAUTA BOOK COMPLETE BY Aunty Baby Ummu Irfan .txt
kuma".
Murmushi gefen baki tayi sannan tace, "zaka iya tafiya" tashi yayi ya fita jakadiya ce ta kalle ta sannan tace,
"Ya uwar gijiyata wannan yariyar da kike son hada yarima Dameer da ita talakawa ne iyayan ta nasu da komai da zaki lura lokacin da muka je makarantar su ko kayan jikin ta na matalauta ne..".
"Ya isa ni zaki gaya min abunda ya dace ni nasan dalilin da yasa zan had'a auran nan sabida Dameer ya kask'anta ai abun bakin ciki ne kaman Dameer ya aure yar talakawa sannan daga yau duk abunda zan aiwatar karki saki saka min bakin ki tashi ki fita ki bani waje" gimbiya Haleematun-Sa'adiya tayi maganar cikin matsanecin fushi.
Jikin jakadiya na rawa ta zube gaban ta tana bata hakuri, "kiyi hakuri ya uwar gijiyata wallahi ban san wannan maganar zai bata miki rai ba Allah ya huci zuciyar ki".
Ko kallon ta gimbiya Haleematun-Sa'adiya bata yi ba tace, "tashi ki fita nace" da sauri jakadiya ta fita tana kara bata hakuri.
Washe gari.
Su waziri sun shirya komai da zasu tafi gidan su Deeyana dashi sannan suka tafi sallama sukai da Abban Deeyana daman ya had'a yan uwan shi da kuma wani makocin shi wanda yake kaman dan uwan shi sannan kuma Baba yazo shima.
Yana jin sallaman su suka fito shi da abokin shi suka musu iso har dak'in nan na zauran gidan, daman Amma ta had'a musu dan abun taran baki.
Sannan sukai dan gaishe-gashe sannan waziri ya fara magana, "malam daman yau mukai da kai akan zamu dawo muji shawaran da ka yanke to muna sauraran ka".
Abokin Abba ne ya fara magana, "to a gaskiya mun gode sannan kuma mun amince da neman wannan aure Allah yasa alkhairi aka had'a".
Murmushi waziri yayi sannan yace, "ai mune da godiya malam yanzu to daman munzo da komai na saka rana sai ku yanke mana sadaki".
Baba yace, "shikenan na yanke dubu dari Allah yasa ma auran albarka".
Godiya malam fada suka fara yi daya daga cikin malaman ya amso kudin gun waziri ya bada dubu dari sai kuma dubu dari biyar dukiyar aure, gaba daya su Baba suka ce baza su amsa dubu dari biyar ba ai aure albarka ake so ba kudi ba ba yanda su waziri basuyi su amsa kudin ba suka ce baza su amsa ba.
Haka nan su waziri suka hakura, nan waziri yace, "mai-martaba yace, sati biyu kawai yake so a daura aure ranar juma'a sannan kuma basai sun ma yariya komai ba shi sarki ya dauki nauyin komai".
Baba yace, "Aa dole a matsayin su na iyaye su mata kayan dak'i amma baki a sati biyu yayi kad'an su kara ko wata daya ne".
Waziri yace, "Aa haka al'adan gidan su yake su suke ma yariya kayan dak'i sannan sati biyu nan haka mai-martaba sarki Fahad Abdullah yace".
Haka nan zuka amince a satin biyun sannan suka gama komai suka tafi, nan Baba da Abban Deeyana suka fara tattaunawa akan yanda bikin zai kasance.
Ko da su waziri suka koma gida komai suka sanar ma mai-martaba sarki Fahad Abdullah komai da saka ranar da akai da komai da komai dai, Allah ya kaimu yace, sannan yace, "mq waziri su fara shirye-shiryen had'a babban biki" waziri yace, shikenan komai za'a yi yanda yake so.
Dameer ya had'a komai nashi na komawa Saudi Arabia sannan ya shiga fada dan sallama da mahaifin shi, zaunawa yayi a gaban shi sannan yace, "insha Allah yau zan komai Saudi Arabia Allah ya kara ma lafiya da nisan kwana".
Fadawa suka amsa da ameen sannan suka fara mai kirari "an gaishe ka yarima Dameer da guda tamkar da dubu".
Daga kai sarki Fahad Abdullah yayi fadawa na ganin haka suka fara fita a fadan dan daga ganin haka sun san mai-martaba zai gana da d'an shi kenan.
Kallon Dameer yayi sannan yace...
*VOTE*
*COMMENT*
*&*
*SHARE*
*Yar autar gaskiya writer's ce*😉✍
[1/6, 10:37 PM] Mum Irfaan🤱🏻: 🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚
🦚🦚
🦚
🤴🏻 *IZZAR SARAUTA*🤴🏻
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }
🎐 ```G•W•A```🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼
*Story*
*&*
*written*
*By*
*Aunty baby* ✍
~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@ Gaskiya writer's Asso~
*DEDICATED TO..*
*JUYIN RAYUWA FAN'S*
*Sadaukarwa ga UMAIMA ALIYU*
*BISMILLAHIR RAHMAIR RAHIM*
📝 *page* 3⃣1⃣⏩3⃣2⃣
*_____________* 📖yace, "ai ina ga ba sai ka koma Saudi Arabia ba ka bari in ma komawan zakayi ka tafi da matar ka, insha Allah juma'a ta sama za'a daura ma aure!".
Da sauri Dameer ya dago kan shi ya kalle mahaifin nashi bakin shi na rawa ya furta "aure!!?" ciki da dinbun mamaki da tashin hankali.
Mai-martaba sarki Fahad Abdullah yace, "kwarai kuwa aure, sai ka bari sai an gama bikin ka dauki matar ka ka tafi da ita yanzu kaje gun mahaifiyar ka fulani ku shirya abinda kake so".
Dafe kan shi yayi dan ji yayi ya sara mai, sannan ya daure yace, "shikenan Abba nasan baza ka taba min abinda zai cutar dani ba Allah yasa hakan shi yafi zama alkhairi nagode sosai Allah ya kara ma lafiya da nisan kwana".
"Ameen" yace, sannan yace, "zaka iya tafiya" tashi yarima Dameer yayi a hankali dan gaba daya baya jin karfin jikin shi komai nashi ya saki bayi da kuzari ko kad'an.
Yana fitowa a fada tunani ya dunga yi yasan ba wanda zata hada mai wannan abu sai gimbiya Haleematun-Sa'adiya amma zai nuna mata shi dan halak ne dan bazai taba nuna mata yaji haushi ba bare tayi farin ciki ta saka shi a cikin damuwa.
Part din shi ya koma bedroom ya huce ya kwanta ana Bed tare da dafe kan shi ji yake kaman ya fashe da kuka, wayan shi ya jawo ya fara kiran Ammin shi dan ita daya zata iya share mai hawaye, sai da tayi ringing uku sannan ta daga cike da farin ciki tasan yau zai koma Saudi Arabia.
Tace, "hello Dameer".
Kuka ya fashe mata dashi kawai ya kasa magana sai kace wata mace🤣.
"Hello Dameer kana lafiya kuwa kamin magana mana wallahi har kasa zuciya ta ta tsinke" cewar Ammi da duk ta rud'e.
Cikin kuka ya fara magana, "Ammi Ammi mai nayi ma gimbiya Haleematun-Sa'adiya da take son kashe ni duk abinda take min be ishe ta ba Ammi wallahi in na koma Saudi Arabia ni da Nigeria har abada".
Murmushi wanda yafi kuka ciwo Ammi tayi sannan cikin lallashi da kwantar da murya tace, "haba Dameer yanzu kuka kake akan matar mahaifin ka? nasha gaya maka komai na rayuwar nan dan hakuri ne yanzu menene haka ka tayar min da hankali kayi hakuri insha Allah komai zai yi dai-dai".
"Ammi wai sai kace wata mace wai aure Abba zai min nan da sati biyu Ammi guda nawa nake da za'a ce za'a min aure yanzu" yayi maganar cike da damuwa.
Hmmmmm kawai Ammi tace, sannan tace, "aure to Allah yasa hakan shi yafi zama alkhairi kayi ma mahaifin ka biyayya insha Allah zaka ga ribar shi gaba kuma Allah ya kaimu sati biyun".
Ji yayi zuciyar shi tayi sanyi sannan yace, "ameen" ta dade tana lallashin shi sannan sukai sallama tace "kuka ko da wasa karya taba nuna baya son auran" yace, "insha Allah".
Abban Deeyana ne da Amma suke maganar yanda za'a yi su gayawa Deeyana wannan aure da zasu mata ba yarda ta har ga Allah Abba Deeyana har yanzu hankalin shi yaki kwanciya akan wannan aure amma ya zaiyi tunda abun ya riga yayi nisa.
Amma da taga yayi shuru ta tabo shi tana cewa, "haba Abban Deeyana tunanin mai kake haka mu muka haife Deeyana dole ta bimu ba mu zamu bita ba sannan kuma Deeyana tana da tarbiya baza ta taba watsa mana kasa a ido ba".
"Hmmmmmm" kawai Abban Deeyana yace, shigowar ta kenan ta dawo daga makaranta taji abinda Amma take fad'a dafe kirjin ta tayi nan da nan lokaci daya hawaye suka wanke mata fuska.
"Innalillahi wa'ina ilaihir rajiun mai yake shirin faruwa da rayuwar ta kenan!!!?"....
*(To fa ko ya Deeyana zata yi*🙆)
*VOTE*
*COMMENT*
*&*
*SHARE*
*Aunty baby ce*✍
[1/6, 10:37 PM] Mum Irfaan🤱🏻: 🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚
🦚🦚
🦚
🤴🏻 *IZZAR SARAUTA*🤴🏻
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }
🎐 ```G•W•A```🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼
*Story*
*&*
*written*
*By*
*Aunty baby* ✍
~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@ Gaskiya writer's Asso~
*DEDICATED TO..*
*MY ZEE*💞
*Sadaukarwa ga UMAIMA ALIYU*
*BISMILLAHIR RAHMAIR RAHIM*
📝 *page* 3⃣3⃣⏩3⃣4⃣
*____________* 📖 "innalillahi wa'ina ilaihir rajiun mai yake shirin faruwa da rayuwa ta kenan!? Ko dai banji da kyau bane bani Deeyana ba nasan iyaye na na sona baza su taba min aure yanzu ba" ta karashe magana kaman wata zararriya.
Shiga parlour tayi da sallama a bakin ta sannan ta gaishe da iyayan nata, Abba ne yace, "kin dawo Deeyana ya karatun?".
Murmushi karfin hali tayi sabida har lokacin jikin ta rawa yake dan addu'ar ta Allah yasa ba dade taji maganar ba, tace, "Alhamdullh Abba" sannan tayi hanyar shigewa bedroom d'in ta har ta kusa shiga Amma tace,
"Deeyana in kin gama cin abinci kizo muna san magana da ke ni da mahaifin ki".
Gaban Deeyana ne yace, ras ras sannan bakin ta na rawa tace, "to Amma" sannan ta shiga bedroom d'in ta jikin ta duk a sanyaye.
Bata wani bata lokaci ba ta canja kaya ta fito ko abinci bata ci ba, ta zauna k'asan kujeran da iyayan nata suke kai ta kasa da kanta sannan tace, "Abba Amma gani".
Amma ce ta kalle Abba shima kallon ta yake sannan ta d'aga mai kai alaman ya fara mata magana, gyaran murya yayi sannan yace, "Deeyana".
D'ago kanta tayi sannan tace, "Na'am Abba".
Yace, "Deeyana a rayuwa ta ina burin kiyi karatu kaman yanda ke ma kike buri amma Allah be tsara hakan ba komai kika gani ya faru da mutum daga Allah ne sannan kayi hakuri da duk kaddara da zata zo maka ka amshe ta hannu bibbiyu sai kaga Allah ya dafa maka".
Zuwa lokacin kwalla ya cika idon Deeyana hakan nan ta d'aga kai alaman haka ne, nan Abba ya bata labarin komai tun daga zuwan su waziri har ranar bakin da aka saka sati biyu sannan ya cigaba da cewa, "kiyi hakuri Deeyana ba haka raina ya so ba Deeyana".
Fashewa tayi da kuka sannan tace, "Abba yanzu dan wannan abun ne kake bani hakuri ku fa iyaye na ne ko bansan da wannan auran ba kaini kawai akai wallahi bazan damu ba nasan kun isa dani ne Allah yasa hakan shi yafi zama alkhairi a rayuwata nagode sosai iyaye na Allah ya baku abinda kuke nema a duniya da lahira".
Murmushi Abba yayi sannan yace, "naji dadi sosai Deeyana Allah yayi Miki albarka yasa ki gama da duniya lafiya insha Allah biyayan nan da kikai mana sai kinga rabar shi gaba".
"Ameen" Amma tace, sannan ta rungume Deeyana tana kara sanya mata albarka, tashi Deeyana tayi ta shiga bedroom d'in ta Bed d'in ta ta fad'a ta saki wani irin kuka mai ban tausai, yanzu duk mafarki da take na ganin tayi karatu ya tashi a banza kenan wa zata aure ya mijin yake duk bata sani ba tasan ita kuma jin dadin ta na rayuwa ya riga ya k'are.
Washe gari, Deeyana ba wani bacci tayi ba gaba daya tunani ya hana ta bacci haka ta shirya makaranta dan Abba yace, daga wannan satin baza ta kara zuwa ba tunda wani satin zai shiga na bikin ta.
Dameer ne sanye da kayan Ball ya fito daga bedroom d'in shi hannu shi rike da key d'in motar shi da alaman fita zaiyi dan ya saba kullum da safe sai ya fita buga Ball, parking space ya huce motan shi ya shiga sannan ya fita daga masarautar.
Yau ita daya ta kama hanyar makaranta sabida suheema baza ta samu zuwa ba tun jiya daman ta gaya mata, tafiya take a hankali tana tunanin wai yanzu nan da sati biyu za'a daura mata aure.
Dai-dai wani dan kwalbati zata tsallaka mota da tazo hucewa ta fallatsa mata ruwan wajan gashi fararan kaya ne a jikin ta dan-danan suka canja kala, tsayawa kawai tayi tana kallon jikin ta ganin yanda kayan jikin ta yayi duk ya b'aci.
Da sauri yayi parking ya fito a motar ganin yanda kayan ta duk ya b'aci kuma daga ganin alama makaranta zata tafi sai yaji duk b'aji dadi ba, zuwa yayi dai-dai in da take cikin muryan shi mai sanyi yace,
"ma'alashin yan mata ban sani bane".
Wani k'ulolin bakin ciki ne ya rufeta ji tayi kaman ta zazzage shi amma sai kawai ta juya ta fara tafiya, da kallo Dameer ya bita be dai ga fuskan ta ba Amma sai yaji beji Dadi ba tunda yasan yanzu sai ta koma gida ta gyara jikin ta.
Hakan nan ya shiga mota, ji yayi kaman ya bita ko kaita gidan su yayi, fitowa yayi a motar Yana duba hanyan da tabi amma be ganta ba sai kawai ya koma motan shi ji yayi ma bazai iya zuwa Ball din ba kawai sai ya koma gida.
Hakan nan Deeyana ta koma gida cike da haushi sabida uniform d'in daya gare ta kawai, Amma da ta tambaye ta Mai yasa maita ta fad'a mata wani ne be sani ba ya watsa mata wannan ruwan hakan Nan ranar ta hakura bata je makaranta ba.
Bayan sati daya..
*VOTE*
*COMMENT*
*&*
*SHARE*
*Aunty baby ce*✍
[1/6, 10:37 PM] Mum Irfaan🤱🏻: 🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚
🦚🦚
🦚
🤴🏻 *IZZAR SARAUTA*🤴🏻
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }
🎐 ```G•W•A```🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼
*Story*
*&*
*written*
*By*
*Aunty baby* ✍
~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@ Gaskiya writer's Asso~
*DEDICATED TO..*
*MOM ABDULLAH And MMAN MEENERHT*
~To Alhamdulillah insha Allah yanzu zaku dunga jina maybe kullum Amma banyi alk'awari ba, nagode sosai da kulawar da kuke bani masu kira na Ina godiya sosai masu message ma dai duk nagode~ ~Allah ya bar kauna~
*Hmmmmm Ashe haka masoyan IZZAR SARAUTA suke da yawa😻 nayi mamaki sosai, to ina godiya🥰 aunty baby ta kuce👌*
*BISMILLAHIR RAHMAIR RAHIM*
📝 *page* 3⃣5⃣⏩3⃣6⃣
*___________* 📖 Bayan sati daya, shirye-shirye masarautar mure take na biki ba kama hannu yaro, Dameer kuwa ko da gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta Kira shi akan mai da mai yake buk'ata na biki ce Mata yayi.
"Karta wahalar da Kan ta ai ko matar da ta nemo Mai ma tayi Mai babban abu a duniya to dan haka ba sai ta k'ara mai komai ba shi zaiyi da Kan shi".
Mamaki sosai ya kamata bata tab'a tunanin zai ce Mata Haka ba sannan wani Abu da ya k'ara Bata mamaki shine jiya da ya shigo da dank'ara-dankaran akwatuna kusan dozin uku yace, na amarya ne, abun ya bata mamaki sosai ji tayi kaman taje tace, ma mai-martaba sarki Fahad Abdullah a fasa auran sabida taga murnar da Dameer yake ta faskara.
Ko yanzu ma zaune take a kilisar ta sai murza zuban hannun ta take tana tunanin yanda zata bullo wa al'amarin cizan labb'an bakin ta tayi da k'arfi tana K'ara Jin tsanar Dameer zuciyar ta.
Jakadiya ce ta shigo tana kirarin ta amma taji shuru Dan gimbiya Haleematun-Sa'adiya tayi nisa gurin tunani Bata Jin komai, zama jakadiya tayi a gaban ta sannan tace,
"Ya uwar gijiyata menene Naga kaman kina cikin damuwa, kiyi hakuri ki fad'a min insha Allah zan Miki maganin shi koma menene Dan bana so na ganki cikin damuwa".
Lalkwasa yan yatson hannun ta tayi da karfi sannan cikin karad'i tace, "na gaji na gaji naji da ganin yaron Nan a duniya so yake ya haukata Ni na had'a wannan aure ne Dan ya shiga bakin ciki da damuwa Wanda zaiyi sanadiyar mutuwar shima amma Ina, sai yafi Ni murna ma da auran to zan kashe shi in wuta".
Da sauri jakadiya ta rufe Mata Baki tana waiga bayan ta ko wani najin su taga ba kowa sannan tace, "haba gimbiya Haleematun-Sa'adiya uwar gida fulani wacce Babu kaman ta a masarautar mure har akwai yaron da Zaki dunga fushi akan shi Wanda bamu aika shi lahira ba ki tuna fa kakanin shi ma mu muka aika su lahira to shi menene k'aramin gwaro kawai lokaci muke bashi".
"Ke jakadiya wannan yaron ya huce in da kike zato duk wayyon mu sai yayi yanda yayi ya bar tarkon mu yanzu so nawa Ina sa ana kwance burgin motar shi amma be tab'a samun wani abu ba ko abinci in aka aika mai baya ci toooo mai yake so muyi Mai" ta k'arashe maganar tana buga hannun ta akan ta sannan ta rik'e Kan dan wani Sara Mata yayi.
Shuru jakadiya tayi tana tunani can sai tayi murmushi tace, "ga shawara uwar gijiyata kawai da matar da aka aura Mai da ita zamu kashe shi kinga su talakawa ne sannan kuma talaka akwai kwad'ayi mu Mata barazana da kudi har a samu ta aika shi lahira kinga shikenan sauran batu kuma Sai ta gama mana komai".
"Hhhhhhhhhh lallai kuwa in haka ya faru zan k'ara Miki girma a masarautar mure gaskiya jakadiya kina da kwakwalwa ai banyi wannan tunanin bama" gimbiya Haleematun-Sa'adiya tayi maganar cike da murna da farin ciki.
Murmushi jakadiya tayi ganin maganar ta ta amsu sannan tace, "yauwa uwar gijiyata yanzu ki kwantar da hankalin ki ayi bikin nan a gama sannan mu fara Shirin mu komai zai tafi dai-dai".
Dariya gimbiya Haleematun-Sa'adiya tayi sannan suka ci gaba da kitsa abun su.
Dameer kuwa mahaifiyar shi na k'ara kwantar Mai da hankali sannan kuma wasu daga cikin Yan Uwanta zasu zo bikin Dan yanzu ya kasance sauran kwana shida.
Duk da wani lokacin in ya tuna auran gaban shi na faduwa Amma hakan nan yake daurewa yana abubuwa, mai-martaba sarki Fahad Abdullah ya Kira shi ya tambaye shi nawa yake buk'ata kudi ya k'ara hidiman biki sai Dameer yace baya buk'atan komai kudi kuma Yana dasu alhamdullh.
Haka nan mai-martaba yace, "duk da haka dai sai ya k'ara wani abun" sannan ya bashi kudi masu yawa, hakan nan