Showing 54001 words to 57000 words out of 65264 words

Chapter 19 - IZZAR SARAUTA BOOK COMPLETE BY Aunty Baby Ummu Irfan .txt

alkhairin"






Tsaddadan murmushi ya sakan mata sannan yace, "ai tukucin ki ma tukun na ma dan wannan babban albishir kika sanar min" ita dai Deeyana na zaune sai murmushi take nan ya kama mata hannu suka fita direct part d'in Ammi suka shiga, da murnar shi ya fara Kiran "Ammi Ammi".






Ammi da ke bedroom ta fito da sauri tana cewa "lafiya?" rungume ta yayi da sauri sannan yace, Ammi burin ki ya cika Deeyana "is pregnant" Ammi rasa abinda zata ce tayi sai sakin shi da tayi ta Isa gun Deeyana ta rungume tana share kwallan farin ciki.






Kunya ya kama Deeyana, Ammi ta fara cewa "Allah ya sauke ki lafiya Deeyana nayi farin ciki sosai na rasa ma mai zance miki Deeyana" "ameen" Dameer yace, yana murmushi kafin dan wani lokaci har zancen cikin ya bade masarautar mure kowa farin ciki yake har yar k'aramar walima aka had'a kowa yana mata fatan Allah ya sauke ta lafiya.






Amma tana jin dadin yanda ake ba Deeyana kulawa ita ko kallon Deeyana ma bata yi, haka Dameer ma kulawa yake bata ta musanman ya mayar da ita kaman kwai, zancen makaranta kuwa cewa yayi sai cikin ta yayi kwari ko kuma ma Sai ta haihu ita ce ma take cewa bata yarda ba.






Mai-martaba sarki Fahad Abdullah da sarki na yanzu Abba sunyi farin ciki sosai sai fatan Allah ya sauke ta lafiya, wata rana mai-martaba sarki Aliyu yaje zagayan gidan kurkuku duk wanda yake da k'aramin laifi a cire shi a mai afuwa yaci Karo da jakadiya ta zama wani iri dan bai ma gane ta ba sai da fadawa sukai mai bayani.






Tausayi ta bashi sosai na yace, "a fito da ita yayi mata afuwa" kuka sosai jakadiya ta fara tana Kara bashi hakuri haka yayi ta zagaye yana fito da duk wasu masu k'aramin laifi, dan shima sarki Aliyu ya cigaba da duk wani abun alkhairi na masarautar shiyasa mutane suke son shi.






Dameer da Deeyana suka shirya suka tafi Saudi Arabia dan sun dan kwana biyu Basu je ba gashi jaddah na san ganin Deeyana tunda taji ance tana da ciki take ta kofarin tana son ganin ta d'aga nan har Dubai zasu wuce gurin Al'mustapha, sun sauka lafiya Jadda taji Dadi sosai da ganin Deeyana ta k'ara kyau abun ta dan cikin ba k'aramin Kyau ya mata ba gashi ya d'an fara fitowa dan k'arami da shi.






Ayusha da taga Deeyana ba k'aramin hauka tayi ba dan har Jadda ta fad'a wa ita fa son Dameer take, Jadda tace, ba ruwan ta tasan Dameer ba abunda zai sa shi ya k'ara aure kuma ita baza ta sa shi ba, haka ta samu Dameer da maganar ita tana so ya aure ta murmushi Dameer yayi sannan yace, "Ayusha kenan yanzu baki ganin ba'a ma Deeyana adalci ba in dai na aure ki".




Haushi ma da ya ishe ta rasa bakin magana tayi wato ba'a ma Deeyana adalci ba lallai Dameer, tashi tayi tayi tafiyar ta tana jin haushin abun da Dameer yake mata dan yaga tana son shi.






Sunyi wata daya a Saudi Arabia sannan suka shirya zasu tafi Dubai lokacin cikin Deeyana ya shiga wata hudu dan cikin ba mai laulayi bane ba abunda baya barin ta yanzun ma Dameer yana so ta fara zuwa awo ne hospital da a Saudi Arabia d'in yake so ta dunga zuwa sai Ammi tace "mai gwara su dawo Nigeria".






Ranar da zasu tafi Ayusha ita ma ta shirya zata bisu dan tana son zuwa Dubai ita ma dan bata ga amfanin zaman ta a Saudi ba tunda shi Dameer d'in baya ta tata ita dai Deeyana ba abun da ya shafe ta dan ko kallon ta ma batayi dan ba k'aramin haushi take ji ba in taga tana shigema Dameer.






Su Jadda ne suka raka su har airport sai da suka ga sun shaga jirgi tukun suka tafi gida gurin zama ma a cikin jirgin sai da Ayusha tayi fada dan kusa da Dameer ta zauna Deeyana tace, ita kam ana take san zama Ayusha Bata Isa ta zauna a kusa da shi ba Dameer ya rasa abin yi dole sai tsakiyar su ya zauna dan shi baya son fitina.






Ba k'aramin haushi Deeyana taji ba daman ita ce ta kusa da window ta ko mayar da kanta wanjan window tqna kallon gari, Ayusha kam dadi kaman ya kashe ta har kwqntar da kanta tayi jikin Dameer ta sakala hannun ta cikin nashi haka har bacci ya dauke ta ita kam Deeyana ko kallon su bata yi ba dan haushin Dameer take ji.






Sun Isa lafiya Dameer yaga Deeyana bata kallon shi da zasu fito a jirgin ya rik'e ma Deeyana hannu sabida cikin ta dayan hannun shi kuma ya sanya kasan maranta sai bige mai hannu take tana dalla mai harara, Al'mustapha da matar shi suka zo daukan su nan suka tafi gidan.






An had'a musu kayan ciye-ciye kala-kala matar Al'mustapha sai kula da Deeyana take nan ta kaita bedroom d'in ta tayi wanka D'akin da aka basu su zauna kiri da muzu Deeyana tace, baza ta D'akin ba wai nan fushi take da Dameer.






Satin su biyu suka shirya zasu koma Nigeria ranar da zasu tafi Ayusha tasha kuka wanda har ta ba Dameer tausayi yasan Ayusha tana mutukar son shi amma bazai tab'a iya auran ta ba dan yama Deeyana alk'awari haka yayi ta lallashin ta da zasu tafi harda ita a raka su a cikin mota ta kwantar da kanta kan kafad'ar shi shi kuma sai lallashin ta yake.




Suna Isa airport Deeyana tayi saurin fita daga motar dan gani take kaman da gayya Dameer ke mata wani abun tunda tun da suka je Dubai d'in bata tab'a sakin mai fuska ba wai tana fushi da dashi, Dameer da Ayusha suka fito a motar ya rungume ta sosai yana k'ara bata hakuri nan yake ce mata abokin shi mus'ab na sonta tayi hakuri ta so shi tace sai tayi shawara.






A kan idon Deeyana Ayusha ta sakin ma Dameer kiss shima kuma ya mayar mata, sai da cikin Deeyana ya murd'a d'an dafe shi tayi da hannun ta tana runtsa Ido dan wani irin zafi take ji a zuciyata, sukai sallama da kowa da kowa sannan suka shiga jirgi, kamo hannun ta yayi yana mata k'ayatatcan murmushi amma Ina ji yayi ta kafe mai hannu.






Suna zama a kujera ya daura hannun shi saman cikin ta yana shafawa haba nan ma ta kafe mai hannu wannan karon yaji zafi sosai haushi ya k'amshi ya juya fuskan shi ma haka kowa ya juya fuska bamai ba dan uwan shi magana har suka Isa Nigeria, da zasu fito a jirgi ma ya d'an tallafo ta sabida cikin ta cike da masifa tace, "malam in kana da zuciya karka kara tab'a Ni".




Tab'e Baki yayi sannan yace, "kina da jikin da zan tab'a ki ne ciki na nake k'arewa dan haka tunda bake na tab'a ba karki Kara min magana" taji zafin maganan shi sosai hakan na ta juyar da kan ta nan suka shiga mota dan fadawa ne suka zo daukan su har suka Isa gida ba wanda ya kalle wani tana fitowa a mota direct ta huce part d'in Ammi.






Shi kuma part d'in su ya huce zuciyar shi cike da K'una wato yariyar nan dan taga yana lallabata shine zata dunga kawo mai raini to zai barta ya gani, haka tunda suka je Dubai ko kallon shi bata yi har message ya tura mata na bada hakuri amma ko dubawa batai ba to zai saka mata ido haka dai yayi ta magana da zuciyar shi har ya shiga bedroom d'in shi.






Tana shiga part d'in Ammi ta tatda ta kuyangu suna matsa mata k'afa tana ganin ta ta tashi tana murmushi sosai Ammi ta fara kulawa da ita can dai Ammi tace, "Ina yayan naki?" tace, "yana part d'in su" sannan ta shiga daya daga cikin bedroom d'in Ammi tayi wanka tayi sallah sannan ta kwanta Idon ta na hasko mata Ayusha da Dameer na kiss.






Kusan k'arfe tara na dare Dameer yazo gaishe da Ammi ko tambayan Deeyana bai yi ba suna gama fira da Ammi ya tashi zai tafi wannan abun ba k'aramin kuntatawa Deeyana yayi ba dan tana jin shi har ya fita, kifa kanta tayi jikin pillow ta fashe da kuka sai da tayi mai isar ta sannan ta tashi ta shiga toilet ta wanke fuskan ta.






Ammi shuru taga Deeyana bata fito ta tafi part d'in su ba tashi tayi taje ta samai ta tayi mata magana akan ta tashi ta raka ta sai cewa tayi ana zata kwana, Ammi bata kawo komai a ranta ba ta mata addu'a ta fita, bacci take so tayi amma Ina ta kasa dan ta saba kwana jikin Dameer hakan nan ta rungume pillow har bacci ya kwashe ta.








Shima Dameer yana can sai juye-juye yake kan bed ya kasa bacci can dai yayi addu'a ya kwanta cike da mafark'in Deeyana nan shi, washe gari wajan karfe takwas ya shigo dak'in Ammi samun su yayi suna break Ammi da Deeyana kusa da Ammi ya zauna sannan ya gaishe ta amsawa tayi tana mai ya gajiyar hanya.






Kanta a kasa tace, "ina kwana" tab'e baki yayi kaman be jita ba sai da Ammi tace, "hala baka ji ana gaishe ka bane?" "Oh sorry lfy" ya fad'a yana basarwa sosai abun ya bakan ta mata rai tashi tayi da sauri ta bar kun.






Da kallon Ammi ta bita sannan ta dawo da kallon ta gun Dameer ta fara mai kallon tuhuma kasa da kai yayi ya fara sanya kwai a bakin shi, "kai menene ya had'a ka da matar ka?" Ammi tayi maganar fuskan ta ba alaman wasa, shuru yayi sai da Ammi tace, ba magana nake ma ba.






"Ba komai Ammi" "ni zaka mayar karaman yariya jiya ina kallon ka da ka shigo har ka fita baka nemai ta ba yau gashi ta gashe ka kayi mata banza Dameer wai mai yake damun ka ne, yariyar nan zaka fara k'unsa mata bakin ciki ko zaka fara nuna mata halin ku na maza ko kayi shine zan san kai namiji ne Allah ya baka sa'a" tana gama fadar haka ta tashi ta far gun.






Shuru yayi yana k'ara mai-maita maganar Ammi tashi yayi shima ya fita dan ji yayi ma ya kasa cin abincin, Deeyana tana shiga bedroom kuka ta fashe da shi ko a mafarki aka fad'a mata Dameer zan canja mata zata ce karya ne amma shi yake mata wannan wulak'anci to ko dai ya daina sonta ne shine tambayar da take ma kanta.






Kwanciya yayi kan duguwar kujera tunani kala-kala a ran shi tashi yayi ya kunna wayan shi number Deeyana ya nema ya danna ya fara kira, tana kwance taji wayan ta ya fara ringing tashi tayi ta duba mai kiran tana ganin Dameer ne ta katsa wayan tanq hararan wayan.




Ganin ta katse sai ya tashi ya tafi dak'in Ammi direct bedroom d'in da Deeyana take ya shiga kwance ya samai ta tayi ruf da ciki saurin isa gunta yayi yana juyar da ita dai-dai, saurin ture shi tayi tana kuka "ni ka rabu dani maci amana kawai".






Saurin rufe mata baki yayi da nashi ya fara kissing d'in ta sai da ya kaita karshe sannan ya sake ta yana mai da numfashi, "haba Deeyana kin san fushin ki ila ce a gare ni pls kiyi hakuri ki yafe min laifin da na miki duk da dai ni ban san laifin da na miki ba".






Fashewa tayi da kuka sannan ta fad'a kirjin shi ta fara cewa, "ai sai gaje gun Ayusha d'in tunda yanzu naga ita kafi danuwa da ita wato ni tunda ka gama cutata ka durka min ciki shine zaka daina kula dani to kaje amma ka sani sai ka fara raba ni da wannan cikin da ka dura min tukun"






Murmushi ne ya subuce mai sannan yace, "kai Deeyana ashe haka kike da rigima to kiyi hakuri ni ba wani abu tsakani na da Ayusha ita da aure ma zatayi yanzu wato shine kike kishi ko to ko kin manta alkawari da na miki ne".






Girgiza kai tayi sannan tace, "to ai zaka iya karyawa ai nasan halin ku na maza" kumatun ta ya kama Sannan yace, "halin mijin ki na da ban ne kinji" daga kai tayi alaman eh nan da nan suka shirya har sun manta sunyi wani fada ko sallama basu ma Ammi ba suka huce part d'in su.








Bayan wata uku.






Cikin Deeyana ya shiga wata na bakwai yayi girma sosai, kowa addu'a sauka lafiya yake mata kayan baby's kuwa ai ba'a magana dan Ammi London taje duk tayo siyayan kayan baby's dak'i guda haka Dameer ma yana ta siyo nashi kayan.




Dameer da Deeyana suna zaune lafiya abin su, cikin ta baya hana ta kyautatawa mijin ta shima haka ba wai ya cika takura mata bane haka dai suke rayuwar su gwanin ban sha'awa.




Cikin Deeyana na shiga wata tara ta koma bangaran Ammi dan Dameer da kan shi ma ya mai da ta sabida Ammi zata fi bata kulawa, kullum sa ran haihuwa ake yau ko gobe hakan nan ita ma kullum cikin addu'ar Allah ya sauke ta lafiya take.






Yanzu satin ta biyu da shiga wata tara shuru dai ba wani bayani hankali kowa ya fara dawowa kanta gimbiya mabaruka kullum sai tayo mata rubutu ta kawo mata tasha haka mai-martaba ma, har ta shiga wata goma da kwana biyu shuru nan ma shima dai Dameer hankali shi ba karamin tashi yayi ba.




Dan yanzu abun ya fara bashi tsoro, wata ranar Friday da daddare sun gama firan su ya tafi part d'in su Ammi ta bata rubutun da gimbiya mabaruka ta kawo mata tasha taji fitsari ya kama ta tashi ta shiga toilet dan tayi kawai taji maran ta ya rike ga wani irin ruwa da ya fara zuban mata.






Sallati ta fara yiiii.






*To ko dai abun yazo ne😹😹😹😹ni dai bance komai ba in akwai likitoci a Izzar sarauta fan's sai ku kawo ma Dameer a gaji🀣 Allah sarki gimbiya Haleematun-Sa'adiya ba rabon taga... nayi shuru daiπŸƒπŸΏβ€β™€πŸƒπŸΏβ€β™€*




*VOTE*
*COMMENT*
*&*
*SHARE*






*Aunty baby ce*✍
[1/6, 10:37 PM] Mum Irfaan🀱🏻: 🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚
🦚🦚
🦚










🀴🏻 *IZZAR SARAUTA*🀴










🌐
*_ALHERI WRITER'S* *ASSOCIATION_* ✍
*~[ Alheri danko ne, duk inda kayi shi zai dawo gare ka, burin mu mu ribantu da alherin da ke cikin wannan harka]~*








*ALHERI SAI DAN AlHERI* πŸ‘Œ












*Story*
*&*
*written*
*By*
*Aunty baby* ✍








*DEDICATED TO..*
*AMEER*
~Ubangiji Allah ya baka lafiya~ πŸ‘πŸ˜’






*Sadaukarwa ga UMAIMA ALIYU*








*BISMILLAHIR RAHMAIR RAHIM*










πŸ“ *page* 6⃣3⃣⏩6⃣4⃣












________πŸ“–Sallati ta fara yi tana kiran sunan Allah ta rike maran ta kuma, nan da nan zufa ya jika mata jiki Ammi da taji kaman alaman nishi a toilet ta shiga da sauri, durkusha ta samu Deeyana ta tara uban zufa.






A rude Ammi ta iso gun Deeyana tace, "Deeyana haihuwar ce Allah ya sauke ki lafiya diya ta" saurin riko Deeyana tayi dan su tafi hospital rike mata hannu Deeyana tayi da karfi tana rintsa ido nan kuma sai nishi da karfi faya ce ta fashe ruwa ya fara zuba duk da azaban da Deeyana take ji bai hana ta kiran sunan Allah ba.






Ammi dai banda aikin sannu ba abunda take mata dan jikin ta rawa yake ta rasa ma mai zatayi tunda ta san haihuwar ce tazo kafin ta gama tunanin ta ma taji kukan jariri ya fadu da sauri tayi kasan Deeyana tana jinjina kokari irin na Deeyana.






Saurin duba saman mirror tayi taci sa'a akwai sabuwar reza ta yanke cibin ita kam Deeyana matsawa gefe tayi tana fitar da numfashi a hankali, dauke yaron Ammi tayi sannan ta nade shi a towel kallon Deeyana tayi sannan tace, "sannu Deeyana Allah ya baki lafiya kinyi kokari".






Jin Dameer tayi yana kiran ta "Ammi Ammi" shigowa bedroom d'in yayi yaga toilet a Bude kuma kaman Ammi na magana lekawa yayi ganin Deeyana durkusha jariri kuma na hannun Ammi tana kara nada mai towel, wayyo kara goge idon shi yayi sannan yace, "Ammi Deeyana ce ta haihu".




Dagowa Ammi tayi sannan tace, "yauwa Dameer zo ka rike min yaron in gyara Deeyana amma fara kiran Dr tukun" da sauri ya afka toilet d'in, yayi kan Deeyana ita kuma Ammi ta fito tana k'ara gyara mai towel d'in da ta rufe yaron da shi dan sai carkada kuka yake.






Daukar ta yayi cak ya sanya ta kan kujeran da ke bedroom d'in yana sanya mata albarka yanzu Deeyana ce ta haifan mai d'a shi kam mai zai mata a duniya wanda zai biya ta, dafe kai ta tayi da hannun ta tana cewa "washhhhh" "oh sorry habibaty sannu" ruwa ya diba ya wanke duk wani jinin toilet d'in sannan ya koma kan Deeyana ya cire mata kayan jikin ta ya dauraye mata jiki sannan ya daura mata towel ya dauke ta cak ya fito da ita.






Ammi har ta dauki waya ta kira Dr dan tazo ta duba ta sannan ta kira gimbiya mabaruka da sauran ta sanar da su Deeyana ta haihu, ba'a fi minti goma ba sai ga Dr ta shigo nan ta shiga duba Deeyana ta Bata wasu magunguna sannan ta duba yaron duk lafiyar su lau.






Gimbiya Mabaruka ce ta fara shigowa cike da murna yau ta samu da sannan mutanan gidan suka fara zuwa Nan da nan masarautar mure ta san an samu k'aruwa, gimbiya mabaruka ce tayi ma yaron wanka gimbiya Aisha kuma tayi ma Deeyana, nan aka shirya su cikin kayan sarauta masu kyau da tsari jariri sai shan pic yake sabida kaman shi sak da uban shi Dameer.






Komai nasu iri daya ne ba abun da ya dauko na Deeyana komai na Dameer ne Amma ma tayi murna amma ko idon ta Ba'a gani ba a dak'in nan aka fara shagulgulan haihuwa iri-iri, Dameer ai rasa in da zai saka Deeyana yayi dan murna nan da nan ya fita ya siyo mata zinare mai masifar kyau wanda zata saka kafin suna.






Abinci aka ma Deeyana kala-kala na mai jego, gata dai Deeyana tana shan shi yan uwan Amma ma duk sun zo amma ai su sai suka je gefe dan yanda suka ga kowa na faran ta mata,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login