Showing 21001 words to 24000 words out of 65264 words
Chapter 8 - IZZAR SARAUTA BOOK COMPLETE BY Aunty Baby Ummu Irfan .txt
Dameer ya amsa ba dai da san ran shi ba, akwatuna kuwa an cika su tam da kaya sosai da sosai dozin uku.
Y'a'yan gimbiya Haleematun-Sa'adiya ma ba'a barsu a baya ba sarauniya Maimunatu tayi nata kokari Dan ita ce babba sannan tana son yarima Dameer sosai sauran k'annin ta ne kawai Basu damu dashi ba Amma sunji bak'in cikin da aka ce Yar talakawa zai aura sannan kuma mahaifiyar su ce ta had'a auran.
Haka kowa na masarautar yake kawo abun arziki komai dai gimbiya Haleematun-Sa'adiya ake ba sabida ganin da mutane suke tafi son shi a duk matan sarki Fahad Abdullah shiyasa komai na gudunmawar biki ita ake ba, gimbiya Marwa ma dai tayi nata kokari haka ma gimbiya Aisha.
Deeyana kam ta cire maganar ma a ranta amma tayi Rama ba karami ba Amma tayi tayi da ita akan ta fad'a Mata abun da ke damun ta amma tace, ba komai tamabayar da Amma take Mata ne ma yasa ta sakin jiki ta.
Sai Dan gyara da k'anwar Amma aunty Faiza ke mata magunguna kuwa Amma ta hana ta sha sai Wanda tasan zai Mata amfani sannan Amma ke bata,sabida tace, shan magani ko wani iri na kawo ma mace matsala baki san ko da mai aka had'a shi ba kawai ki dauka ki zuba ma cikin ki.
suma sai shirye-shiryan ake Abba yana ta Iya bakin kokarin shi.
Yau biki ya kasance sauran kwana hudu nan kuma gimbiya Haleematun-Sa'adiya tace ranar za'a Kai kaya, sarauniya Maimunatu ce da jakadiya sai kuma kad'an daga cikin masarautar sai kuyangu su ne suka shirya xuwa Kai kayan.
Sun shirya kenan zasu fito gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta Basu key din mota tace a ba amaryan motar kaita kunshi kyauta kowa yayi mamaki sosai Amma haka Nan suka amsa.
Gidan su Deeyana an shirya musu tarba ta mutunci dan an san da zuwan nasu, ko da suka isa gidan aunty faiza ce da wata yar uwar Amma suka tare su cikin murna dq farin ciki.
Sarauniya maimunatu taji dadi sosai ganin yanda suka tare su, ita da jakadiya suka fara shiga gidan sannan kuyangu suka fara biyo su da akwatunan parlour su deeyana aka shigar da su nan suka zazzauna aka fara shigo musu da abun da aka tanadar dumin su.
Amma da sai yanzu ta shigo gaishe su bata ga fuskar sarauniya maimunatu da kyau ba sabida ita tana daga can karshen kujera gaisawa kawai sukai ta bar parlour.
Yan uwan ta ne kawai ke dawainiya da su sarauniya maimunatu, kayan da ake shigowa da su ne ya fara ba yan uwan Amma tsoro da kuma mamaki tun mutane na irgawa har suka daina aunty faiza ce ta kasa hakuri ta samu sarauniya maimunatu tace,
"Haj wannan kayan fa duk da munsan daga gidan sarauta ne amma sunyi yawa gaskiya zaku koma da wasu".
Murmushi sarauniya maimunatu tayi sannan tace, "duk na amaryan Dan uwana ne mu da muke ganin ma kaman yayi kad'an Allah dai ya sama auran albarka".
Ameen Yan D'akin suka ce sannan aka ci gaba da ganin kaya ana sa albarka Basu wani Dade ba suka shirya zasu tafi, Abban Deeyana yayi iya kokarin shi ya siyan musu kayan da ake saukan yan kawo laife sannan suka tafi kowa na farin ciki da murna.
Amma da ta ta shigo taga uban tulin akwatuna da kayan da yake ciki kasa magana tayi sai da aunty faiza ta tabo ta sannan tayi murmushin dole tace, "hmmm faiza wannan kayan sun bani tsoro".
Aunty faiza tace, "haba insha Allah ba komai Allah dai ya nuna mana ranar wai ina ma Deeyana take ne?".
"Tana gidan su suheema ai tunda taji yau za'a kawo kayan ta kasa sukuni amma yanzu zan aika a kira ta" Amma ta fad'a tana barin parlour.
Su sarauniya maimunatu sai yabon karamcin gidan su Deeyana suke ko da suka koma masarauta gimbiya Haleematun-Sa'adiya nata tambayan su ya aka sauke su shuru sarauniya maimunatu tayi dan tasan da biyu take tambaya, sigina tama jakadiya sannan ta fita kilisar ta ta shiga tana jiran jakadiya ta zo ta bata rahoto.
Jakadiya na ganin haka ta tashi ta fita da sauri tana zuwa ta zube gaban ta taba kwasar gaisuwa, kallon ta tayi sannan tayi makirin murmushi sannan tace, "jakadiya ya Kika ga talaucin su? ".
Gyara zama tayi sannan ta fara rartafo mata duk yanda aka musu a gidan su Deeyana, girgiza Kai gimbiya Haleematun-Sa'adiya tayi tana murmushi Wanda ita daya ta San ma'anar shi.
**********
Yau ta kama juma'a yau ne kuma daurin auran Deeyana da Dameer, gidajan biyu sai shirye-shirye ake kakan Dameer da k'anwar Ammi sun zo part d'in gimbiya Haleematun-sa'adiya aka sauke su sai hidumomi gimbiya Haleematun-Sa'adiya take musu.
Dameer kam na D'aki a kwance kaman mara lafiya sai tunani yake yanzu shine za'a mai aure be San matar ba bata san shi ba to ko ya zasu kasance, noking d'in kofar bedroom d'in shi yaji ana yi dan k'aramin tsaki yayi sannan ya tashi ya nufa k'ofar.
"Waye" shine kawai abunda yace, daya daga cikin fadawan sarki ne rik'e da wasu kayan sarauta masu Kyau da daukar Ido yace, "nine waziri ne ya aiko Ni" bud'e kofan yayi sannan ya juya a bin shi, shigowa bafadan yayi sannan ya aje kayan a gefen Bed d'in shi yace, "waziri ne yace in kawo ma Wai in lokacin daurin auren ka yayi su zaka sa".
Da hannu yayi Mai alaman zai iya tafiya, rissinawa yayi sannan ya juya ya tafi kallon kayan yarima Dameer kawai yayi sannan ya dau wayan shi da ke gefe ya fara calling d'in Ammin shi.
Deeyana ce zaune a gaban Abban ta nisiha yake mata mai ratsa jiki hawaye ne kawai ke wanke mata fuska tana jin ba dadi a cikin zuciyar ta yanzu yau zata bar iyayan ta zata tafi in da bata san kowa ba, mijin ma da za'a daura mata auran bata tab'a ganin shi ba shima haka maganar Abban tace ta dawo da ita tunanin da ta tafi.
"Deeyana kiyi hakuri da duk abinda zaki taran a gidan auran ki gidan da zaki je gida ne na masarauta mai cike da munafunci da makirci sai kin iya zama da kowa, Allah ya miki albarka sannan dan Allah yanda kikai mana biyaya to kiyi ma mijin ki ma insha Allah gaba zaki ji dadin rayuwar ki Allah ya miki albarka".
Cikin kuka tace "ameen Abba" sannan ta tashi ta ta fita a dak'in, bedroom d'in Amma ta shige tayi kwanciyar ta dan jiya an mata lalle duk wani gyara na amarya da ake yi sai da aka mata.
A babban masallacin taraba za'a daura auran bayan an idar da sallahn juma'a, haka Abba ya tsara abun shi dan su waziri da sunce a masarauta za'a daura auran Abban Deeyana yace, be yarda ba dole a masallacin jumm'a za'a daura haka nan sukai hakuri amma mai-martaba be zai sumu damar halartan masallacin ba sai dai ya nad'a manyan masarautan da zasu halarta.
Kowa na masarauta ya shirya dan wasu ma har sun halarci masallacin Dameer ma ya shirya cikin kayan da aka aiko mai dashi yayi masifar kyau part d'in gimbiya Haleematun-Sa'adiya ya shiga dan yasan ana kakar shi take yana shiga ya tambaye jakadiya ta fad'a mai dak'in da take sannan ya shiga.
Kakan Dameer tayi farin ciki sosai ganin shi d'as dashi be sanya damuwa a ranshi ba sai albarka da ta kara sanya mai, noking d'in dak'in aka gimbiya Haleematun-Sa'adiya ce ta shigo fuskar ta dauke da murmushi ta kalle Dameer tace,
"My son lokaci na gure wa kai ake jira zo mu tafi dan ni ya kamata na sanya ka a mota da kaina" murmushi jaddah tayi duk da bata san abunda gimbiya Haleematun-Sa'adiya tace ba.
Shafa kan jaddah yayi sannan ya mata kiss a goshi ya kalle gimbiya Haleematun-Sa'adiya yace, "muje" rike hannu shi tayi sannan suka fita a dak'in, har bakin motar da aka fito da ita domin yarima Dameer d'in ta kai shi aka bude mai ta sanya shi a ciki sannan ta shafa laulausan gashin kan shi tace, "a daura aure lafiya sannan ka biya gidan Amaryar ka ganta kafin a kawo mana ita".
Murmushi yayi sannan yace, "thanks again nagode sosai" sannan ya rufe motar kawai, had'a rai tayi tana k'ara jin tsanar shi a ranta.
Abban Deeyana yaci kwallyar shi cikin faran shadda mai kyau haka kakan Deeyana ma duk dai yan uwa da abokan aziki sun hallara a babban masallacin, haka ma duk yan masarautan har Dameer ma sun iso, sallah aka fara yi sannan ana idarwa aka gyara zama aka fara daura auran Deeyana da Dameer.
Waziri shi yayi waliyin ango yayan Amma kuma aboki gun Abba shi yayi waliyin Amarya, an daura auran Deeyana da Dameer akan sadaki dubu dari, Dameer da ke gefe yana jin ace ameen wasu zafafan hawaye suka fara zubo mai saurin sharewa yayi dan kar a gan shi Abdul yaron waziri ya matso gun shi ya rungume shi yana bubbuga bayan shi a hankali.
Waziri ya matso kusa da yarima Dameer yace, "ka tashi kaje ka gaida surukin ka mahaifin matar ka kenan gashi can zaune" tashi Abdul yayi ya rike mai hannu sannan suka isa gun Abba.
Dukawa Dameer da yayi sannan ya fara gaishe su, Abba Deeyana na kallon Dameer yaji kwalla na tawo mai Dameer ma kallon shi yake ko kiftawa...
*(😱 To fa ko Dameer zai gane kanin mahaifin nashi wanda yake nema ruwa a jallo to sai dai kun biyo autar gaskiya writer's sannu a hankali 🌷)*
*VOTE*
*COMMENT*
*&*
*SHARE*
*Aunty baby ce😉*
[1/6, 10:37 PM] Mum Irfaan🤱🏻: 🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚
🦚🦚
🦚
🤴🏻 *IZZAR SARAUTA*🤴🏻
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }
🎐 ```G•W•A```🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼
*Story*
*&*
*written*
*By*
*Aunty baby* ✍
~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@ Gaskiya writer's Asso~
*DEDICATED TO..*
*MY HALEEMA ADAM, KHADIJA MUSBAHU And UMMU SAFWAN*
*Sadaukarwa ga UMAIMA ALIYU*
~Mrs basakwace ina taya ki murnar kammala littafin ki da kikai kuskuran da kikai a ciki Allah ya yafe miki fadakawarwa da kikai kuma Allah ya baki lada😻😻😻(muna zuba 👀👀👀👀👀muna jiran sabo)~
*BISMILLAHIR RAHMAIR RAHIM*
📝 *page* 3⃣7⃣⏩3⃣8⃣
*__________* 📖 k'asa da kai Abban Deeyana yayi dan yaga kallon da yarima Dameer yake mai bana k'are bane sannan yace, "Allah ya muku albarka Deeyana kanwa ce a gare ka sannan kuma mata dan Allah ka rike min ita amana".
Wannan kalma ita ta duki kunnan yarima Dameer "Deeyana kanwa ce a gare ka" k'ara maimaita kalma yayi a zuciyar shi sannan ya kalle Abba muryan su daya da Abban shi sannan fuskar su ma haka to mai hakan ke nufi kenan? Dafa shi Abdul yayi sannan yace, "yarima tashi mana tunda kun gaisa".
Murya sarke yarima Dameer ya samu kan shi da cewa "insha Allah Abba" sannan ya tashi suka fita a masallacin mota kawai ya shiga yana k'ara maimaita "Deeyana kanwa ce a gare ka", dafe kan shi yayi sannan yace, "Allah sarki uncle dan na saka ka a raina shiyasa ko da yaushe kake min gizo Allah ya bai yana mana kai".
Abdul yace, "yarima ina muka nufa yanzu gidan Amarya ko masarauta kasan abokan mu suna can suna jira" shuru yayi yana jin shi dan besan mai zaice mai ma ba sabida baya so yace mai be san gidan su Amaryan ba sai kawai yace su huce masarauta, nan direba ya jasu sai masarauta.
Ajiyar zuciya Abba ya sauke yana tuna ran da ya bar masarautar su sannan yanzu gashi yar shi zata shiga, tausayin yar shi ne ya kama shi a zuciyar shi yace, "Allah ya kare min ke Deeyana daga duk kan shirri".
Deeyana kam da k'yar aunty Faiza da suheema suka sata tayi kwalliya dan da tace ita baza tayi ba bata so Amma kam bata san suna yi ba tana can gurin yan uwa da abokan aziki ana shagalin biki, wata dalleliyan shadda da Abba yayi mata ta saka simple make-up aka mata ba wani mai yawa ba amma tayi masifar kyau.
Sannan suka fito ita da suheema dan zuwa gidan su suheema dan duk kawayen su na makaranta na can ai kuwa tana fitowa yan uwa suka rufan mata kowa na fadin tayi kyau Amarya Amarya Deeyana kaman tayi kuka suheema ta janye hannun ta suka fita daga gidan, kawayan su na makaranta suna ta taya ta murna sunji ance dan sarki zata aura.
Can masarauta mure kuwa sai shagali ake irin na sarauta abokan Dameer sun had'a walima a cikin gidan akwai babban hall ana duk suka yi casun su kowa na nuna bajintar shi sai kuma wanda suka shirya bayan an kawo amarya karfe takwas na dare amma shi a waje za'a yi.
Karfe biyar dai-dai yan daukar Amarya suka shirya tafiya wannan karon harda gimbiya Aisha za'a tafi sabida daukar Amarya ne sai sarauniya maimunatu da k'annin ta, motoci ne jere sun kai kusan guda talatin wanda duk za'a tafi dauko Amaryan dasu nan suka fara tafiya a hankali.
Musu busa da yan kid'a ai sun dade da zuwa kofar gidan su Deeyana ana ta kiraye-kiraye, nan yan biki suka fara fitowa kallo sai motoncin da suka fara zuwa kuma a jere kallo ya koma kan motocin.
Deeyana na zaune a bakin Bed d'in su dan tun wajan karfe uku akan kara shirya ta cikin material pink color shima kwalliya aka mata sai ta kara fitowa das da ita aunty faiza da Amma suka shigo gyale aunty faiza ta yana mata a jikin ta har kanta sannan suka fara mata nasiha mai ratsa jiki.
Amma tace, "Deeyana Allah ya miki albarka yasa ki shiga gidan miji a sa'a Allah ya baki ikon yin biyaya kaman yanda kike mana".
Kuka Deeyana ta fashe da shi sannan ta mike ta rungume Amma cikin sheshekan kuka ta fara magana "Amma ki yafe min insha Allah zanyi biyaya kaman yanda kuka ce".
Ita ma Amma rungume ta tayi kwalla ya cika mata ido inna sajida ce ta shigo dak'in ita da inna Sumayya suka ce "to ashe yan daukar Amarya sun zo gasu can ma sun shigo suna parlour baban Deeyana ai sai a gaggauta shirya ta ko sabida kar a bata musu lokaci".
Deeyana na jin haka ta k'ara fashewa da kuka ta rike Amma gam sai da aunty faiza ta rike mata hannu ta babbare ta a jikin Amma sannan suka fita da ita a dak'in, dayan bedroom d'in suka kai ta sannan aunty faiza ta kara gyara mata fuska inna sajida da inna Sumayya suka k'ara mata nisiha sannan inna sajida ta rike hannun ta suka fita a dak'in parlour da aka sauke su gimbiya Aisha suka shiga da da sauri sarauniya maimunatu ta tare ta da murna tana "alhamdullh yau gani ga Amarya Dameer".
Tashi suma su gimbiya Aisha sukai sannan suka masu inna sallama suka ce duk wanda zaije kai Amarya to ga motoci nan ya shiga sarauniya maimunatu taki sakin Deeyana haka ta rike mata hannu suka fita daga parlour har kofar gida ma, suheema daman sun shirya har wasu daga cikin kawayen Deeyana ma duk zasu shiyasa ana fito da Deeyana Suma suka fito.
Wata dalleliyan mota aka sanya ta a ciki wacce duk tafi motoncin gurin haduwa sannan sarauniya maimunatu da gimbiya Aisha sai kuma aunty faiza suka shiga, su suheema kuma duka suka shiga wasu motocin gaba daya yan uwa Amma ba wanda ya zauna a gida har tsofafin Suma sai da suka shiga mota sai sunje, haka motan su Deeyana ta fara tafiya a hankali Deeyana da kanta ke cikin gyale ta ji mota ta tashi ta k'ara sautin kukan ta a hankali.
Shafa kanta sarauniya maimunatu tayi sannan tace, "haba Amarya ki daina kuka insha Allah kin shigo gidan mu a sa'a".
Shuru Deeyana tayi sai ruwan hawaye da ke zuban mata, kowa ya shiga mota sai da suka cika duk motocin nan sannan direbobi suka fara tafiya, kusan minti arba'in suna tafiya sannan suka is babban geta d'in masarauta mure nan suka shiga, busa da K'ara yawa ana ta ma Amarya barka da zuwa.
Motan su Deeyana ta fara yin parking sannan ta sauran fito da ita sarauniya maimunatu tayi ta rike mata hannu suka shiga babban parlour masarauta dan anan ake fara aje amarya in dai an kawo ta masarautan, nan ta samu kowa na parlour gimbiya Haleematun-Sa'adiya da sauri ta tashi ta tare Deeyana ta rungume a jikin ta tana mata barka da zuwa masarautar su Mai tarin albarka.
Wata kujera aka zaunar da ita sannan manyan matan masarauta suka fara zuwa suna mata barka da zuwa, aunty faiza dai tana kusa da ita tana kallon ikon Allah dan yanda suka tarbe su abun ya burgeta, mutan gidan su Deeyana kuwa part d'in gimbiya marwa aka kai su sannan aka fara tarbar su da abinci kala da ban da ban wanda sai wanda mutum yake so ake zuba mai.
Karfe bakwai na dare aka dauke Deeyana aka kaita part d'in gimbiya Haleematun-Sa'adiya dan a shirya ta tayi sallah sannan a tafi gurin da za'a yi partyn, gimbiya Haleematun-Sa'adiya ce ta shigo da wasu kaya na sarauta ta mika ma aunty faiza tace, "yanzu su Deeyana zata saka" amsa aunty faiza tayi lokacin Deeyana tayi sallah sannan mai make-up ta zo ta fara mata.
Yarima Dameer ma shiryawa yayi cikin kayan da aka kawo mai kala daya dana Deeyana yayi masifar kyau waya yake da Ammi sai murmushi yake tana ta bashi labarin haukar da Ayusha take ashe ita son shi take basu sani ba.
Ana gama mata make-up d'in ta sanya wannan kaya da gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta kawo mata hmmmm fadan kyauwan da Deeyana tayi ai bata lokaci ne dan zama tayi kaman sarauniya, kaman ta da yan masarautan mure ya k'ara fitowa wanda da aunty faiza ta kalle ta sai da gaban ta ya fadi.
Karfe takwas nayi gimbiya Haleematun-Sa'adiya da kanta taje ta kira Dameer dan lokacin tafiya yayi, dak'in da Deeyana take ta kai shi wai tare zasu fito zaune ta samu Deeyana an yana mata wani dan net mai sharara wanda Ba'a ganin fuskan mutum sosai, gujeran da Deeyana take ta kama hannun Dameer ta zaunar da shi sannan ta fito da turare ta