Showing 9001 words to 12000 words out of 65264 words
Chapter 4 - IZZAR SARAUTA BOOK COMPLETE BY Aunty Baby Ummu Irfan .txt
kuce* 🥰🥰🥰✍
[1/6, 10:37 PM] Mum Irfaan🤱🏻: 🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚
🦚🦚
🦚
🤴🏻 *IZZAR SARAUTA*🤴🏻
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }
🎐 ```G•W•A```🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼
*Story*
*&*
*written*
*By*
*Aunty baby* ✍
*DEDICATED TO..*
*IZZAR SARAUTA* *FAN'S 1*
*Inq jin dadin comment d'in ku sosai musanman* *ma*,
*Haleema Adam*
*Khadija*
*Rabi"atul-adawiyya a*
*Mom Abdallah*
*Nafisat Usman*
*Maman khairat*
*Fadimatu*
*Aisha Aliyu*
*Zainab Ibrahim*
*Khadija musbahu*
*Khadija*
*Kai Kuna da yawa da dai sauran Wanda ban Kira sunan ta ba*
*BISMILLAHIR RAHMAIR RAHIM*
~VOTE & FOLLOW 4 Wattpad@ Gaskiya writer'sAsso.~
📝 *Page* 1⃣7⃣⏩1⃣8⃣
*_____________*📖 shigowar shi kawai taji kaman daga sama, sai kuma maganar da ya fara, "wato khaujut zubar min da ciki kike ko to Allah ya toni asirin ki in ma haihuwa ce baki so dani ai ba wannan hanyar zaki bi ba".
Kallon shi kawai ta tsaya yi dan bata fahinci maganar tashi ba sai tace, "Abban Dameer lafiya kuwa Wallahi kwatakwata ban gane zancen ka ba".
Wani irin haushi ta kara bashi wato ma zata mayar dashi be san mai yake ba tunda gashi tana son ta nuna bata san komai ba, fita yayi kawai a D'akin ba tare da ya kara ce mata k'ala ba.
Zaunawa tayi a kan Bed d'in da take kwance ta fad'a duniyar tunani to mai ya faru yake gaya mata wannan maganganun bacin tun da suke ko harara be tab'a mata ba, tashi tayi tsam ta nufi part d'in shi.
Tun da ya shiga bedroom d'in shi safa da marwa kawai yake ya rasa wani abu yake mai dadi a duniya Wai ace yaro daya gare ta har ta fara tunanin zubar da ciki kai da sake sai ta gane ta mai wannan abun.
Shiga tayi bata kan shi a kilisar shi ba sai kawai ta huce parlour ko jakadiya ma batai ma magana ba, sallama tayi sannan ta tako har inda yake ta zube a gaban shi tana kallon shi ko zai Mata magana amma ina ko kallon ta beyi ba.
Magana ta fara a hankali, "Abban Dameer kayi hakuri in wani laifin nama Wallahi ban sani ba karka hukunta ni da fushin ka" ta k'arashe maganar kaman zata yi kuka.
Tausayi yaji kuma ta bashi sai kawai ya d'ago ta ya rungume kuka ta saki mai cin rai, sabida ta san bata aikata lafin da yake zargin ta da shi ba.
Zaunar da I yayi a bak'in Bed d'in shi sannan ya fara mata nasiha mai ratsa jini akan ta daina zubar da ciki ba kyau kuma shi Allah yayi shi mai san 'ya'ya gashi kwata-kwata uku gare shi,
Amsa mai kawai tayi dan bata so tayi jayeya da shi akan insha Allah baza ta kara ba nan da nan kuma ya saki kaman bashi ba suka ji gaba da soyayyar su.
Bayan shekara biyu.
Tun daga wannan b'arin gimbiya khaujut bata saki samun ciki ba, gimbiya Haleematun-Sa'adiya kuwa ta saki haihuwar yarta mace nan ma kaman zatai hauka.
Ya zamo yaran sarki Fahad Abdullah hudu kenan uku mata daya namiji, duk da Dameer na saudiyya baban khaujut yace a gurin su zai zauna.
Mai-martaba sarki Fahad Abdullah be wani damu ba dan yasan zaiyi karatun Arabic sosai nan gaba zai taimakawa kasar sa.
Yarima Aliyu ma yanzu ana ta shirye-shiryan auran shi wanda har an saka rana biki sauran nan da wata uku,
Gimbiya Haleematun-Sa'adiya zaune ita da jakadiya sai maganar su suke daga gani gimbiya Haleematun-Sa'adiya tana cikin farin ciki sai dariya take kaman Wanda aka wa albishir da gidan aljanna.
Tashi jakadiya tayi tana fad'in, "ya uwar gijiyata Bari in je in fara aikatawa yanzu Dan a Bari ya huce shi ke kawo rabon wani".
Dariyar mugunta gimbiya Haleematun-Sa'adiya tayi sannan d'aga mata hannu alaman aikin ki na Kyau jakadiya, fita tayi a D'akin da sauri ta nufi part d'in gimbiya khaujut.
Lokacin da ta shiga gimbiya khaujut bata nan lallek'a window tayi taga ba alaman mutane da sauri ta shige bedroom d'in, duba ko Ina tayi bata ga gimbiya khaujut ba har ta juya zata tafi taji alamar kaman mutum a toilet.
Bak'in toilet d'in ta tsaya lallai mutum ne a toilet d'in kuma ta san gimbiya khaujut ce dan ita daya ce a part d'in nata da sauri ta fita ta huce part d'in Yarima Aliyu.
Jikin ta na rawa ta shiga parlour shi zaune ta same shi yana karatu daga shi sai t-shirt, a rud'e ta shiga tana fad'in, "yarima yarima".
Kallon ta yayi yana jiran yaji menene take Kiran shi haka, jiki na rawa ta fara fad'in "Allah ya taimake ka ya baka nasara gimbiya khaujut ce take Kiran ka tace kazo yanzu yanxu".
"In zo kuma" ya fad'a yana nuna mata kan shi dan shi dai yasan gimbiya khaujut bata tab'a aiko wa yazo ba.
Jingina kai tayi alaman "eh" tashi yayi sannan yace, "muje" tafiya suke jakadiya na gaba shi na baya sai nazarin kiran yake.
Suna Isa part d'in gimbiya khaujut tace, "tana ciki tace in na kira ka naje kitchen na hadu mata shayi".
Kai kawai ya d'aga Mata sannan ya shiga D'akin, ita kuma jakadiya da sauri taje part d'in gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta sanar mata.
Tashi tayi ta sanya alkefba sannan suka fito direct part d'in gimbiya khaujut suka nufa, yana shiga babban parlour ta yaga Bata nan a in da take zaune sannan ba kuyangun ta ko daya sai ya shiga dayan parlour.
Lokacin kuma yayi dai-dai da fitowan ta d'aga bedroom d'in ta zata shiga dayan ta sanya kaya Dan Bata san da mutum a parlour ba ta fito dauri da towel.
Shuguwar gimbiya Haleematun-Sa'adiya kenan da jakadiya, salati gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta rafka tana kuka, "innalillahi wa'inan ilaihir raji'un mai zan gani haka a masarautar mure...... "
Kallon ta kawai yarima Aliyu da gimbiya khaujut suke dan basu gane mai take nufi ba, kuka ta k'ara fashewa da shi sannan tace, "jakadiya je ki kira mai-martaba yazo yaga cin amanar da ake mai wai da k'annin".
Kai kawai jakadiya ta geda ta fita jikin ta na rawa Dan in asirin su ya tonu bata san yanda zata Yi ba yanzu in mai-martaba ya gane ya zata Yi haka take ta magana da zuciyar ta har ta kai part d'in.
Mai-martaba sarki Fahad Abdullah ya fito daga fada kenan jakadiya ta shigo a hargitse, kallon ta yayi sannan yayi gyaran murya yace, "lafiya kuwa jakadiya? ".
Jikin ta ne ya fara rawa ta rasa ma mai zata ce sai kawai tace, "Allah ya taimake ya baka yawan rai gida ba lafiya uwar gida fulani tace, in Kira ka Amma bazan iya gaya maka halin da ake ciki ba dan abun ba dadin ji".
"Wani irin Abu ne wannan to gani Nan zuwa" tashi tayi ta fita, mai-martaba ma tashi yayi ya fito fadawa suna take mai baya.
Ya Isa part d'in gimbiya khaujut, har lokacin gimbiya khaujut da yarima Aliyu da gimbiya Haleematun-Sa'adiya suna tsaye su duk sun kasa fahinta abunda ake ciki.
Mai-martaba sarki Fahad Abdullah ne ya shigo, gyaran murya yayi sannan ya kalle su duk suna tsaye sannan gimbiya khaujut ma be dace ta zauna a yanayin da take ba beyi magana ba dai ya zauna a kujeran zaman shi na parlour.
Yana kallon kowa yana so kuma yaji menene suke tsaye haka kuma harda yarima Aliyu, kuka gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta fashe da shi tana cewa, "ba'a tab'a irin wannan abun ba a tarihin masarautar nan Amma yau gashe..." Bata k'arasa ba.
Mai-martaba sarki Fahad Abdullah yace, "menene aka yi?".
"Ina neman afuwar ka mai-martaba sabida Ina jin kunyar fad'an ma abun da matar ka da k'annin ka suka dade suna aikatawa" cewar gimbiya Haleematun-Sa'adiya.
Kallon rashin fahinta ya mata Yana jiran ta wayar mai da Kai a duhun da ta saka shi, shurun da yayi ne ya Bata damar cigaba da magana.
"Yau naga abun da ya girgiza ni na samu gimbiya khaujut da yarima Aliyu a gadon ka na sunna suna aikata masha'aaaaa" tsawar da taji ne yasa ta k'asa k'arasa wa.
Yarima Aliyu ne yayi tsawan sannan ya tafi gadan-gadan kanta da sauri fadawan suka tare shi rik'e shi sukai Amma Ina yana kwacewa.
K'wakwaran motsi gimbiya khaujut ta kasa, sarki Fahad Abdullah kuwa Yana zaune a inda yake ya kasa furta kalma daya.....
*VOTE*
*COMMENT*
*&*
*SHARE*
*Aunty baby ce* ✍
[1/6, 10:37 PM] Mum Irfaan🤱🏻: 🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚🦚🦚
🦚🦚🦚
🦚🦚
🦚
🤴🏻 *IZZAR SARAUTA*🤴🏻
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }
🎐 ```G•W•A```🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼
*Story*
*&*
*written*
*By*
*Aunty baby* ✍
*DEDICATED TO..*
*MY dear neat lady*
*BISMILLAHIR RAHMAIR RAHIM*
📝 *Page* 1⃣9⃣⏩2⃣0⃣
*____________* 📖juya maganar da gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta fad'a kawai yake, K'ara kallon gimbiya khaujut yayi daure take da towel sai wanda ta yafa akan ta da alamar daga wanka ta fito.
Sannan kuma yarima Aliyu daga shi sai t-shirt da gajeran wando, duba da son da yarima Aliyu ke nuna ma gimbiya khaujut baya nuna ma gimbiya Haleematun-Sa'adiya wannan ma kad'e ya isa ya bashi amsar abun da gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta fad'a.
Tashi yayi ya fara zagaye D'akin, bakin ciki ne ya kama shi da sauri yayi kan yarima Aliyu shag'e shi yayi ya makure shi da bango.
Kakari kawai yarima Aliyu yake kaman wanda zai mutu kuma sarki Fahad Abdullah yak'i sakin shi, gimbiya khaujut na ganin haka ta fasa ihu da gudu ta shiga bedroom d'in ta ta saka kaya sannan ta fito da sauri tayo kan sarki Fahad da har yanzu yak'i sakin yarima Aliyu.
Kok'arin kwatar yarima Aliyu ta fara amma Ina rukon da yayi mai bana wasa bane daga karshe ma tunkud'e ta yayi sannan yace, "ina nan zuwa gare ki bari in gama dashi".
Kuka ta kara fashewa dashi sannan ta fita a D'akin da gudu, part d'in gimbiya Mabaruka taje matar mahaifin mai-martaba sarki Fahad Abdullah.
Gimbiya Mabaruka tana kishingid'e kuyangun ta na matsa mata k'afa, gimbiya khaujut ta shugo a hargitse tana kuka, kallon ta gimbiya Mabaruka tayi sannan tace, "lafiya kuwa? ".
"Abban Dameer zai kashe Aliyu" abunda ta iya fad'a kenan kuka ya kara kufce Mata.
"Subhanallahi" gimbiya Mabaruka tace sannan ta tashi ta fita a D'akin da sauri, ita ma gimbiya khaujut mara mata baya tare sukai part d'in gimbiya khaujut d'in suka shiga.
Nan fa masarautar ta cika da gulme gulme fadawa nayi kuyangu nayi, suna shiga gimbiya Mabaruka tayi kan mai-martaba tana tambayar shi lafiya.
Sakin yarima Aliyu yayi sannan ya kalle wani bafade yace, "yayi sauri ya kira mai waziri da babban malamin fada su hadu duk a fada" da sauri wannan bafadan ya tafi.
Gimbiya Mabaruka tace, "wai lafiyan ku kuwa wannan wani irin tashin hankali ne ka fad'a min abunda ya maka".
Fita kawai mai-martaba yayi a D'akin direct fada ya huce zuciyar shi na soya yanzu duk son da yake mata sai da taci Amanar shi, sannan kuma da k'anin shi wanda yasha nono ya bar mai lallai ita ma sai ta gane kuranta.
Ita ma gimbiya Mabaruka bin bayan shi tayi cike da tashin hankali dan bata tab'a ganin b'acin rai haka ba agun d'an nata, gimbiya Haleematun-Sa'adiya ma haka fada ta nufa jakadiya na mara mata baya.
D'akin ya zama daga gimbiya khaujut sai yarima Aliyu da yake kwance cikin bakin ciki, shi a gurin shi ma gwara mutuwar shi da wannan ranar wai ace yayan shi na zargin shi da neman matar shi wani irin kuka ne yazo Mai mai karfi wanda besan ya sake shi ba.
Waziri na isa fada ya zauna a gurin zaman shi yana kai gaisuwa ga sarki, haka ma malamin fada ya shigo shima ya kai gaisuwa sannan duk suka nutsu suna jiran abun da sarki zai ce dan fuskar tashi ta yau ta basu tsoro.
Magana ya fara cikin IZZA aje a dauko mai yarima Aliyu sannan a kira gimbiya khaujut, jikin waziri na rawa ya fara gayawa fadawa sakon sarki.
Ido kawai gimbiya Mabaruka ta zuba ta kasa cewa hmm balle hummm gimbiya Haleematun-Sa'adiya kuwa murna fal ranta ji take kaman ta zuba ruwa a k'asa tasha.
Duk wani babba na cikin masarautar mure sai da mai-martaba sarki Fahad Abdullah yasa a tara, haka gimbiya khaujut tana zaune guri daya a fadan, ta rasa ma ya zata yi ji take daman Allah ya dau ranta ta huta ko kuka ta kasa.
Kallon kowa na fadan sarki Fahad Abdullah yayi sannan yayi gyaran murya ya fara magana kaman haka,
"Malam ina so ka gaya mun huguncin wa'inda suka aikata zina".
Malam isa muhmud yace, "to hukuncin wa'inda suka aikata zina shine, in namiji ne wanda beyi aure ba za'a mai bulala dari, sannan mace mai aure za'a jefe ta".
Shuru mai-martaba yayi sannan ya kalle gimbiya Haleematun-Sa'adiya yace, "a wani irin Yana yi kika tsince su?".
Gaban gimbiya Haleematun-Sa'adiya ne yayi wani irin fadu wa dum dum dum jikin ta ya fara rawa sannan tace, "ummmmm hummm mmmmm wanka naga sun fito".
Kallon ta yarima Aliyu yayi sannan ya fashe da kuka yace, "insha Allah in Allah ya yarda baza ki gama da duniya lafiya ba wannan sharrin da kikai mana bazai..." Tsawa mai-martaba ya daga mai sannan yace,
"Aliyu a matsayin ka na kanina wanda muka fito ciki daya bazan iya ganin ka shiga wani hali ba amma zabi daya zan baka shine daga yanzu d'in nan da nake ma magana ka tattara duk wani abu naka ka bar masarautar nan daga yau ba kai babu wani a ahalin na masarautar nan".
"Innalillahi wa'inan ilaihir rajiun" shine kawai abunda mutana fadan suke fad'a dan hukuncin yayi tsauri da yawa amma ya zasu tunda mai-martaba ne ya yanke.
Gimbiya Mabaruka tace, "ya kamata kayi binkice ba ka yanke hukunci haka nan ba ko annabi ya hane mu da yanke hukunci cikin fushi".
Girgiza kai yayi be daiyi magana ba sannan ya cigaba da cewa, "ka tashi kafin in sa a fitar da kai".
Kuka yarima Aliyu ya k'ara fashewa da shi sannan ya tashi jiki a sanyaye ya nufi gurin mai-martaba durkusawa yayi a gaban shi sannan ya rik'e k'afar shi yace,
"Ba wai zan fad'a wannan maganar bane Dan kar in fita daga masarautar nan A'a dan in kare mutuncin matar yayana ne gimbiya khaujut, Wallahi Wallahi na rantse da Allah bamu aikata abunda ake zirgin mu ba insha Allah in dai na taba aikata zina ya Allah yasa kar in k'ara numfashi a yanzu nan".
Gaba daya fadan ya ba koya tausayi gimbiya Mabaruka tashi tayi ta rungume shi tana kuka amma shi kon mai-martaba sarki Fahad Abdullah ko a jikin shi.
Zamai jikin shi yayi a jikin gimbiya Mabaruka sannan yace, "dan Allah ki yafe min in na miki laifi dan nasa ni da in k'ara tako masarautar nan har abada" be jira amsar ta ba kawai ya juya ya fita a fadan.
Fada tayi tsit ana jiran hukuncin da za'a yanke ma gimbiya khaujut kuma wacce gaba daya kaman ma batq san mai ake yi ba bata cikin haiyacin ta.
Ko kallon gimbiya khaujut baya son yi shiyasa yace kawai ta tashi ta shirya yau zata koma k'asar ta sannan kuma a bisa alfarmar da yayi mata shine ya sake ta be dai fad'a ko sake nawa bane sannan awa daya ya bata ta gama shirya komai nata.
Kukan da take ta fata yazo shine sai yanzu ya zo ta fashe da kuka mai cin rai sannan ta tashi ta fita a fadan, Nan yace, kowa zai iya tafiya.
Tana shiga bedroom d'in ta kuka ta kara fashewa da shi tana data sanin auran shi har ta rabu da iyayan ta akan shi sannan ya riga da ya gama da rayuwar ta tun tana shekara sha-bakwai.
"Innalillahi wa'inan ilaihir rajiun yanzu ma zata je ta gayawa Iyayan ta zasu barta a gidan su ko zasu kore ta" wannan abu shi yafi tsaya mata a rai ba wani kaya ta d'iba ba kawai ta saka abaya da ta fito.
Part d'in gimbiya Mabaruka kawai ta shiga ta mata sallama kuka sosai gimbiya Mabaruka take yi tana k'ara bata hakuri, haka nan sukai ta kuka sannan gimbiya khaujut ta mata sallama sannan ta fito.
Kilisar mai-martaba ta huce akwai taci sa'a yana nan hawayen da suke zuban mata ta share sannan tace, "Wallahi bazan tab'a yafe ma ba a duniya tun da ka shigo rayuwata ka ruguza min farin ciki na sannan yanzu ka sake ni akan abun da banji ba ban gani ba insha Allah sai Allah ya min sa kaiya" sannan tayi hanyar fita har ta kai kofa ta jiyo muryan shi yana cewa,
"Ki shirya min d'ana Ina nan zuwa amsar shi" ko sauraran shi batai ba ta fita, waziri ya kira sannan yace, fadawa su kaita har airport sai sunga jirgin su ya tashi sannan su dawo yanda yace, kuwa haka akai waziri da kanshi ya kaita airport dan ba k'aramin tausayin ta yake ji ba.
Taci sa'a kuwa ba'a dade ba jirgin su ya tashi, tun da ta shiga jirgin kuka take har dai Allah ya kai su lafiya direct gidan su ta wace lokacin wajan karfe biyu na dare.
Tana isa tayi noking aka bud'e mata sannan ta shiga lokacin Iyayan nata na parlour duk, ganin ta kawai sukai kaman daga sama abun ya Basu mamaki ba waya ba komai.
Yanda suka gan ta ne abun ya basu tsoro idon ta gaba daya yayi ja kuma har lokacin kuka take, da sauri maman ta ta tashi ta rungume ta tana Shafa kanta, kukan ta kara fashewa dashi tana cewa su yafe Mata.
Baban yace, wani irin yafiya kuma ko wani abun ne ya samu mijin nata, shuru tayi kawai tana kara shartar hawaye.
Zubewa kasa tayi sannan tace, "abun da kuke ta nuna min kenan lokacin ban gane ba daman yan Nigeria basu da rokon Amana wai yanzu Abban Dameer ya sake ni" sai ta kara fashewa da