Showing 39001 words to 42000 words out of 65264 words
Chapter 14 - IZZAR SARAUTA BOOK COMPLETE BY Aunty Baby Ummu Irfan .txt
take duk sai taji ba dadi a zuciyar ta ta yanke shawaran anjima zata ce Dameer ya kaita gun Ammi.
Haka kowa ya shiga ya gaishe shi suna ta murna ya tashi, sai da suka ji ana kiran sallah Dhuhr sannan kowa ya tafi part d'in shi su Dameer suma suka huce nasu.
Yarima Dameer da ya kula duk Deeyana bata da kuzari sai ya tambaye ta menene tace ba komai kawai ya kai ta gun Ammi tunda dai ta gaishe da mai-martaba dan murmushi yayi sannan yace bazai Kai ta ba abun zai zama magana tayi hakuri kawai ba dan ranta yaso ba hakan nan ta hakura.
Tunda gimbiya Haleematun-sa'adiya ta koma D'aki ita da jakadiya suke shirya yanda zasu cin ma burin su tunda gashi har Deeyana ta zo jakadiya tace, "uwar gijiyata Ina da shawara" kallon ta gimbiya Haleematun-sa'adiya tayi sannan tace, "menene shawaran".
Jakadiya tace, "gobe ki shiga kitchen da kanki kiyi ma Deeyana abinci ki Kira ta taci, Kinga ba Wanda zaiyi tunanin wani abu aka saka a ciki" jinjina kai gimbiya Haleematun-Sa'adiya tayi sannan tace,
"Baza a gane ba kuwa gaskiya a canja wata shawaran Amma wannan daga ji za'a gane in dai ta mutum kin san dole ayi binkice dan haka a canja wata shawaran".
Rik'e baki jakadiya tayi alaman tunani, ita ma gimbiya Haleematun-sa'adiya Kan ta ya kulle tunanin kawai take.
Shiryawa Dameer yayi cikin blue d'in shadda yayi kyau sosai, ya shiga bedroom d'in Deeyana kallon ta yayi sai game d'in ta take a waya cikin nishadi murmushi gefan Baki yayi sannan yace, "ni zan fita bazan Dade ba zuwa anjima kad'an zan dawo".
Shagwa'be Fuska Deeyana tayi sannan tace, "Ni dai wallahi tsoro nake ji sai dai ka kaini gun Ammi amma bazan iya zama Ni daya ba".
Dariya ta bashi sai da ya dara Kam sannan yace, "nace miki baza ki fita daga masarautar nan ba kina son jamin magana ko to shikenan zan turo miki kuyangu sai su taya ki zama Ni in da zani mata basa zuwa da mun tafi tare".
Zaro Ido tayi cike da mamaki tace, "mata basu zuwa to sai su fara zuwa a kaina kawai dai kace min gun budurwar ka zaka shine baka so ka tafi dani".
Matsowa yayi dai-dai inda take sannan yace, "hhhh lallai yariyar nan waya gaya miki Ina da budurwa ni mata basu gaba na ko ke ai k'ak'aba min akai".
"K'ak'aba ma" Deeyana ta mai-maita dan maganar ta dake zuciyar ta, "hmmmm nima haka dan da yanzu Ina karatu na Amma aka k'ak'aba min kai".
Cizan labb'an shi yayi sannan yace, "Ni na tafi" shuru Deeyana tayi Bata ce mai k'ala ba har ya juya sai kuma ya dawo kissing din goshin ta yayi sannan yace, "yar k'wanwata ba dai fushi kikai ba".
Goge in da yayi kissing din nata tayi sannan ta tashi ta bar gun bin bayan ta yayi da murmushi dan duk abinda tayi burge shi take, sannan ya tashi ya fita.
Tana jin fitar shi ta dawo ta saka alkbban ta dan haka kawai taji tana son zuwa part din gimbiya Haleematun-sa'adiya, tazo dai-dai fita daga parlour su ta hadu da kuyangu wai yarima Dameer ya turo su taya ta zama, gyad'a kan ta tayi sannan tace su rakata part d'in gimbiya Haleematun-Sa'adiya.
Tare suka tafi har part d'in sannan suka jirata a waje dan tace ba dadewa zatayi ba, ta kama abunda zata bud'e kofar parlour kenan taji kaman ana anbatan sunan ta tsayawa tayi cak, jakadiya ce tace, "yauwa uwar gijiyata kawai hakan za'a yi in aka kashe uban nata ai shikenan".
Murmushi gimbiya Haleematun-sa'adiya tayi sannan tace, "Allah ya kaimu gobe da Kaina zanje part d'in nasu in bata wannan abun ta kaima Aliyu hhhhh ai Aliyu ka mutu ka gama wato shiyasa da aka je neman auran yace da bazai bayar ba lallai Aliyu".
Jikin Deeyana ne ya fara rawa tana so ta gane maganar da suke Amma ta k'asa ba dai ana nufin mahaifin ta ba to Abban ta Mai ya had'a shi da masarautar nan juyawa tayi da sauri ta fita a D'akin, part d'in su ta tafi jikin ta ba inda baya rawa tana shiga parlour ta zube kan kujera tana nanata maganar da suke yanxu.
Dafe kanta tayi sannan tace, "innalillahi wa'inan ilaihir rajiun mai yake shirin faruwa lallai akwai abunda Abbana yake boye mana to menene had'in shi da masarautar nan?", tunani ta dunga yi to yanzu mai zatayi can dai zuciyar ta ta bata wata shawara.
Tashi tayi ta gyara alkbban ta sannan ta fita gurin motocin gidan ta nufa addu'a take kawai Allah yasa akwai drive a gun tana zuwa ta fara laka D'akin da ta gani jikin motocin wani bafadai ne ya tawo da sauri sannan ya durkusa ya gaishe ta ko amsawa bata iya Yi ba tace, "Ina drive?".
Da sauri mutumin ya tashi tsaye yace, nine ranki ya dade nuna mai mota kawai tayi sannan tace, "zaka kaini wani guri yanzu" to kawai bafadan yace, sannan ya shiga daya daga cikin motacin, ya matso dai-dai in da Deeyana take, shiga tayi zuciyar ta kaman zata fashe sabida tsoro.
Dai-dai ta shiga Dameer ya fito a mota ta glass yaga kaman Deeyana da sauri ya k'ara kallon gurin itace kuwa nan kuma motar ta fita daga masarautar, shima shiga mota yayi da sauri ya fara bin duk inda motar da Deeyana tayi, ita kuma Deeyana tana ta ma driven kwatancan gidan su hardai suka kawo gidan.
Dameer yayi mamaki sosai to mai ya kawo ta gida sannan bata gaya mai ba kafin ya gama tunani yaga har ta fita daga motar ta shiga gidan, shima fita yayi a tashi motar ya bita tana shiga gidan ta fashe da kuka a sakar gida ta tatda Amma da Abba zaune kan tabarma suna fira gaba dayan su suka kalle ta.
Zubewa tayi kan tabarma sannan tace, "Abba Dan Allah ka gaya mana asalin ka Kai waye a gidan su Dameer Abba Mai ya had'a ka da gimbiya Haleematun-sa'adiya da har take son kashe ka Abba Dan Allah ka fad'a mana" daga Abba har Amma gaban su sai da ya Fadi barin ma Abba.
Jikin Amma na rawa ta rungume mai Deeyana sannan ta kalle Abba da yayi shuru tace, "ka gani ko kaga abunda nake gaya maka kullum magana ta ka gaya mana asalin ka amma baka kula zancen gashi nan yanzu ai Sai ka gaya ma Yar ka Dan Wallahi nima na gaji Ina so nasan asalin ka, ko dan kaga mahaifina na da kawaici ya kasa tambayar ka?".
K'ala Abba ya kasa cewa Daman abunda yake gudu kenan shiyasa yaso yak'i auran nan gaba daya dan yasan wannan ranar zata zo gashi kuma, kallon shi Deeyana tayi da Idon ta da yayi jajir tace, "Abba yanzu baza ka fad'a mana ba Abba Wallahi bazan tab'a komawa gidan nan ba in dai baka fad'a mana cewa Kai waye ba..." kasa karasawa tayi ganin Dameer tsaye bakin kofa.
Murya a raurane ya fara magana, "Abba ko dai kaina uncle d'ina uncle Aliyu da Ammi na ta bani labari Abba ko shiyasa ranar daurin auren mu ka fad'a min kalaman da nake ta jimamin su a zuciyata Abba kana nufi yanzu Deeyana k'anwa ce a gare ni Abba ka taimake ni ka bani wannan amsar".
Tashi Abba yayi sannan ya....
_πWayyo Ni aunty baby yau bana jin yin typing kuyi hakuri da wannan to ko mai Abba zaiyi??_ π€π€
*VOTE*
*COMMENT*
*&*
*SHARE*
*Aunty baby ce*β
[1/6, 10:37 PM] Mum Irfaanπ€±π»: π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦
π¦π¦π¦π¦π¦
π¦π¦π¦
π¦π¦
π¦
π€΄π» *IZZAR SARAUTA*π€΄
π
*_ALHERI WRITER'S* *ASSOCIATION_* β
*~[ Alheri danko ne, duk inda kayi shi zai dawo gare ka, burin mu mu ribantu da alherin da ke cikin wannan harka]~*
*ALHERI SAI DAN AlHERI* π
*Story*
*&*
*written*
*By*
*Aunty baby* β
*DEDICATED TO..*
*MAI-GWAZA*
*NEAR LADY*
*MRS BASAkWACE*
*UMMU NABIL*
*UMMU MUDASSIR*
*INNARO*
*MOM AYSAR*
*MOM IRFAAN*
*MOM ABDALLAH*
*UMAIMA ALIYU*
*HALEEMA ADAM*
*KHAUSAR*
*AISHA GAIDAM*
*EESHAA*
*MMAN MEENERHT*
*MMAN ISLAM*
*AMIEENARH*
*MMAN ZEE*
*UMMU SAFWAN*
*MMAN HAYDAR*
*UMMUH FADIMA*
*HANNAH*
*KHADIJA*
```Jinjina da gaisuwar ban girma gare ku masoyana a ko Ina Ina alfahari da ku da bazar ku nake rawa, kuyi min afuwaπkona ta kawo min k'orafin na d'aga muku hankali har kwana shida baku jini ba kuma bana online hakan ya faru ne sanadiyar tafiyar da mukai, sannan kuma an rufe min sim card to na canja sim card ba wanda yake da number shiyasa ko kun kira bazai tafi ba,π
kusan k'asar da ba taka ba dole sai da hakuriπto alhmdllh Allah ya dawo da mu lafiya nagode sosai da kulawar ku Allah ya bar kauna```
*Sadaukarwa ga UMAIMA ALIYU*
*BISMILLAHIR RAHMAIR RAHIM*
π *page* 5β£3β£β©5β£4β£
___________π sannan ya rungume Dameer yana dan bubbuga bayan shi a hankali shima Dameer rungume shi yayi.
Kwalla ce ta ciko ma Dameer sannan yace, "Abba ko baka fad'a ba nasan kaine uncle Aliyu Abba mai yasa ka boye min kan ka? ".
Daga Deeyana har Amma sakin Baki sukai suna kallon ikon Allah, sakin juna sukai sannan Abba ya zauna shuru yayi yana hango ranar da ya bar cikin masarautar su wacce baya fatan ya k'ara komawa.
Murmushi Dameer yayi sannan yace, "Abba ka mana bayani nasan su Amma suna so suji asalin ka to yau gashi Allah yayi saka gaya musu" ya karashe maganan yana murmushi, shima Abba murmushi yayi sannan yace, "sai munje gidan baba tukun Dan shi ya kamata na fara gayawa asalina".
(Mahaifin su Amma kenan)
Murmushi Deeyana tayi sannan tace, "to Abba sai ku shirya ai mu tafi gidan" na su Amma suka tashi suka shirya Dameer da Deeyana suka fara fita suna shiga mota Dameer ya kama hannun Deeyana ya had'a da nashi ya matse har Sai da Deeyana tayi K'ara sannan ya saki kallon shi tayi cikin shagwa'ba tace, "wannan wani irin mugunta ne? ".
Tab'e Baki yayi sannan yace, "hukunci na Miki" "hukunci kuma mai nayi? " ta fad'a cike da mamaki.
"Waye ce Miki ana fita ba'a sanar ma miji ba to shine laifin da kikai kuma na miki hukunci shikenan ya huce" ya fad'a yana basarwa, turo baki Deeyana tayi tana Shirin mayar mai sai ta hango su Amma.
Fitowa su Amma sukai da sauri Dameer ya fita ya bud'e masu mota murmushi Abba yayi sannan ya dafa kafad'ar shi yace, "Allah ya maka Albarka" murmushi Amma tayi tana cewa Ameen.
Suna shiga ya tada motar sai gidan su baba Basu wani dade a hanya ba suka Isa duka suka fito suka shiga gidan, baba ya dawo daga kasuwa kenan mama tana kitchen tana girki suka ji sallaman su Abba mama ce ta fito tana musu sannu da zuwa sannan ta shinfid'a musu tabarma.
Bata ma ga su Dameer ba sai daga baya tayi murna sosai Baba ma da ya gansu yaji Dadi nan mama ta kawo musu ruwa suka sha sai da suka dan jima suna Hira sannan Abba ya gyara zama ya fara ma baba bayanin komai tun daga ranar da mai-martaba ya Kore shi har zuwa ranar da baba ya ganshi a wannan runfa ya taimaka mai.
Ba Wanda be zubar da hawaye ba dan tausayi baba yace, "Allah mai Ido Ashe kai dan gidan sarauta ne shiyasa duk mutumin da ka gani karka wulak'anta shi sabida baka San baiwar da Allah ya Mai ba ita kuma wannan Mata abunda ta muku Allah ya Mata dan ta cutar da ku yanzu shi wannan yaron ita gimbiya khaujut d'in ne? ".
D'aga Kai Dameer yayi sannan yace, "Ammi ma tana k'asar Nan Dan tare muka zo da ita" baba yace, "lallai ba wanda ya Isa yayi wannan Abu sai Allah yanzu garin muguntar da take so tayi gashi ta had'a zumunci kuma insha Allah wannan Abu da tayi shine sanadin tonan asirin ta".
Haka sukai ta tattaunawa har na dan wani lokaci sannan Abba yace, su Deeyana su tashi su tafi gida dan dare yayi Deeyana ji tayi kaman tace baza ta ba dan ba k'aramin dadi take ji ba in tana tare da mahaifan ta ba hakan nan suka tashi suka musu sallama suka tafi.
A mota Deeyana tayi shuru can kasan zuciyar ta kuwa farin cikin ne wanda bata san dalilin shi ba, murmushi Dameer yayi dan shima cikin farin cikin yake yanzu Deeyana k'anwar shi ce kuma matar shi amma ya gode ma Allah driving yake cikin nishadi dan ji yayi farar daya son Deeyana ya shiga zuciyar shi addu'ar shi kawai Allah yasa itama ta so shi.
Suna Isa masarauta ya fito yazo inda Deeyana take ya bud'e mata zata zura kafa ta fito kawai taji ya sungumai ta k'ank'ame shi tayi tana gudun karya yarda ita murmushi yayi ganin yanda take rik'e mai riga sai kace yace zai yarda ita, da kafa ya bud'e k'ofan parlour su yana shiga ya fara juye-juye da ita.
Kara Deeyana ta fara yi tana k'ara k'ank'ame shi a haka har suka shiga bedroom d'in ta Kan Bed ya aje ta yana dariyan mugunta, turo baki Deeyana tayi sannan tace, "Allah nima sai na rama haka kurin ka jinjigani" shima kokayan muryan ta yayi sannan yace, "sai dai ki ramai yariya dan ni baza ki iya dani ba".
Kwafa tayi sannan tace, "to shikenan mu zuba zaka ga na rama kuwa" tab'e Baki yayi sannan yace "okayyyyy" yana fita daga D'akin, murmushi tabi bayan shi da shi tana jin wani annashuwa a tare da ita.
D'akin shi yaje yayi wanka sannan yayi alwala yazo ya fara nafila yana gode ma Allah da ya fara warware ma matsalolin shi daga karshe kuma ya fara rokan Allah yasa Deeyana ta so shi dan ya daukarwa kan shi alk'awarin bazai tab'a kusantarta ba har sai ranar da ya tabbatar tana son shi ita ma ta tabbatar yana sonta.
Washe gari da wuri ya tashi sabida zai fita Ball Park tunda ya leka Deeyana ya tabbatar tana lafiya ya fita, wajan karfe bakwai ya gama Ball d'in shi gidan da Ammi take ya nufa dan ya kosa ya sanar mata da yaga uncle Aliyu, yana Isa ya fito daga motar shi ya shiga gidan babban gida ne dan har swimming pool akwai dan in yazo Nigeria wata ran nan yake sauka kaman gidan shan-iskan shi ne.
Bedroom ya shiga dan yasan tana can a kan sallaya ya tatda ta zaunawa yayi kusa da ita, sai da ta kammala azkar d'in ta sannan ta kalle shi da mamaki tace, "Kaine yanzu da safan nan Ina ka bar Deeyana nan?".
Gaisheta yayi sannan yace, "Deeyana na gida na fito Ball ne shine nace Bari na zo na ganki na miki wani albishir kuma" ya k'arasa maganar yana murmushi.
"To Allah yasa alkhairi" Ammi ta fad'a tana mai da hankali ta kan shi, "Ammi jiya na hadu da uncle d'ina Ashe Ammi shine mahaifin Deeyana Ammi amma mai yasa baki gane Deeyana ba kuma suna kama da uncle Aliyu sosai".
Murmushi Ammi tayi sannan tace, "na gane Deeyana tun ranar da na fara ganin ta gaya maka ne kawai banyi ba sabida Ina so zuwan nan da nayi ya kasance mun hadu da Aliyu mahaifin Deeyana kenan na san zakayi mamaki sosai" gyara zaman shi yayi sannan yace, "Wallahi kuwa Ammi nayi mamaki jiya duk ya gaya mana komai da komai har wa'inda suka taimake shi kakan Deeyana kenan".
Ammi tace, "insha Allah yau zaka kaini gidan su Deeyana dan Ina so na hadu da Aliyu dan wannan karon Insha Allah sai mun kawo karshen gimbiya Haleematun-Sa'adiya" "nisawa Dameer yayi sannan yace, "to shikenan Ammi duk yanda kika ce hakan za'a yi Allah ya bamu nasara dai".
"Ameen " Ammi tace, tashi yayi sannan ya kalle Ammi yace, "Ammi Bari na tafi sai zuwa anjima jiya Deeyana sai mitar in kawo ta gurin ki take amma ammi bazan kawo ta ba" murmushi Ammi tayi sannan tace, "Deeyana kenan".
Sallama Dameer ya mata sannan ya fita, driving yake yana tunanin Deeyana murmushi yayi yana jin wani nishadi a tare da shi har ya isa gida direct bedroom d'in shi ya huce dan yafi so yayi wanka tukun zama yayi a bak'in Bed d'in shi sannan ya fara cire takalmin shi yana gamawa ya dauka towel ya shige toilet.
Daure take da towel ta fito daga toilet dan yau bata tashi da wuri ba sabida tana fashin sallah zaunawa tayi gaban miroo ta fara shifa mai, tana gamawa ta huce gun wardrobe d'in ta ta fito da kayan da zata saka sauri-sauri ta saka kayan dan ji tayi ana noking fitowa parlour tayi tana kallon kofar parlour su kaman daga nan ne ake noking ita a zaton tama Dameer ne dan ta duba bedroom d'in shi d'azu baya nan.
Isa tayi gun kofar ta bud'e gimbiya Haleematun-Sa'adiya ce tsaye ita da jakadiya sai kuma kuyangu uku, sai da gaban Deeyana ya fad'i amma hakan nan ta k'ak'alo murmushi ta fara gaisher da gimbiya Haleematun-Sa'adiya, kallon ta gimbiya Haleematun-sa'adiya tayi sannan ta sakin mata murmushi wanda daga ganin shi kasan na makirci ne.
"Deeyana ya kike Ina Dameer d'in Kuna lafiya ko?" Gimbiya Haleematun-Sa'adiya tayi maganar tana kallon Deeyana, jinjina Kai Deeyana tayi sannan tace, "lafiya lau" jakadiya tace, "to a ba mai girma gimbiya Haleematun-sa'adiya guri zata huce" murmushi Deeyana tayi sannan tace, "daman yanzu zance mata ta shigo" tana fad'an haka ta dan matsa a kofar shigowa gimbiya Haleematun-Sa'adiya tayi jakadiya da kuyangu suna take mata baya.
Duguwar kujera ta zauna Deeyana ta shiga kitchen kawo mata abin motsa baki jakadiya ta matso ta sannan ta fara mata magana a kunne, daga kai kawai gimbiya Haleematun-sa'adiya tayi tana murmushi Deeyana na fitowa rik'e da babban tare cike da kayan motsa baki kuyangun suka tashi da sauri suka amsa suka aje gaban gimbiya Haleematun-sa'adiya.
Zaunawa Deeyana tayi a kujeran kusa da gimbiya Haleematun-Sa'adia tayi k'asa da kanta dan gaba daya jikin ta rawa yake, miko mata leda jakadiya tayi sannan tace, "wannan kyauta ce gimbiya Haleematun-Sa'adiya ta baki yau ya kamata ki ziyarci mahaifin ki dan haka ake wa duk wacce aka kawo masarautar nan to bayan biki zata je gidan su dan tama iyayan ta ban gajiya to ku Dan kunyi tafiya ne amma yanzu tunda kin dawo sai ki Kai mai".
Amsa Deeyana tayi tana kallon ledan murmushi Gimbiya Haleematun-Sa'adiya tayi sannan tace, "y'ata da fatan Baki raina ba in dai baki raina ba sai anjima