Showing 18001 words to 21000 words out of 72709 words

Chapter 7 - AUREN HADI COMPLETE DOCUMENT WRITING Samira Haruna.txt

da su Jawahir da Khairat Kwance akan gado tana tsakiyar su tayi dariya sosai hak'oranta sun bayyana ga kumatunta sun lotsa kamar ka saka k'wandala kuma ta zauna daram, babu ko d'igon Kwalli a fuskarta amma tayi kyau, shi ya aika mata yace" wacce tafi zama bak'a a ciki to ke ce ita, kuma banga mijin naki ba?" dariya ta aika masa tace" ka canka dai-dai, dan haka ka zo da kumatunka ka karb'i cadeaux d'inka, banda photon mijina" _tambayarta yayi" ban gane kumatuna ba? miyasa baki da photon mijinki?" maida mashi tayi" kaga nifa ina da abinyi , dole ne saina samu photonshi?nida nake ganinshi kullum a cikin zuciyata, dan haka sai anjima_ " _tana aika masa ta sauka ta kwanta sai bacci_ .




Tunda Ummi tayi sallah ta koma ta kwanta sabon bacci, dan rabon da tayi baccin safe harta manta, lokacin da Khamis zai fita yana break ya tambayi Jawahir Ummi, data fad'a masa tana bacci dariya yayi yace" to wannan baccin haka take yin shi ko gidan malam manu?inko hakane akwai dangwarma dan shi nasan ba yada da'bi'ar siyan abincin waje, kuma yana fita da wuri to kenan ya yake oho"Jawahir ce tace" ai in fad'a maka yaya Salman yanzu ya fara gyara mata zama, dan jiya zuwanta nasha labari , nidai har cikina ma ya fara ciwo tsabar dariya" da gaske kike?" ya tambayeta, " e mana, amma gaskiya yaya Salman baya kyautawa dan inda kaga jikinta duk duka ne,wallahi sai taban tausayi kuma da naga jikinta a farfashe" wani iska ya hurar yace" ni nasan dama sai haka ta faru, dan Ummi ba taji, Salman kuma ba yada hak'uri ga zuciya" to mijina me zai hana ka masa magana akan dukanta, kaga fa hakan babu kyau tunda yanzu tana yin abinda ya sata" ajiyar zuciya ya sauke yace" zan masa, amma sai ya dawo daga tafiya, dan kinsan halin shi murd'add'an mutum ne" haka su kaci gaba da tattaunawa harya gama break ya fita.




Jawahir ce zaune a falo tana charting, Salman ta gani en ligne dan haka ta gaishe shi ya amsa, tambayar ta yayi ina Ummi tace tana bacci, cewa yayi taje ta tasheta, haka taje tasa Ummi gaba tana tadi amma tak'i tashi, dole ta fad'a masa tak'i tashi, kiranta yayi appel vidéo yace ta bata wayar, da k'yar Ummi ta bud'a idonta ta kalli wayar sai magagin bacci take da hamma,


"ke dallah tashi malama, wato an samu dama ko?" juya baki tayi tace" dole kam na dama, tunda nazo gidan yanci, ba kamar wancen kurkukunba" tsaki yayi yace" yanzu ai kin fad'i komai, tunda kinga bana kusa dake" d'an karamin tsani tayi tace" wai ni malam miye na sawa a tasheni ina bacci na dan Allah? kuma kai bâ wani abu mai anfani zaka fad'amin ba, ko dai harka fara kewata ne tun yanzu?"cike da takaici yace" waye zaiyi kewar ki? ni? Allah ya kiyaye" a cikin muryar baccinta tace" in dai hakane to kashe wayar" tana gama fad'a yako kashe wayar, tsaki tayi ta koma ta kwanta.




k'arfe 10:15 tana ta baccinta saiko Ihu da kwaramniya anata jinjigarta ana fadin" ki tashi ki tashi ke" cikin Farin ciki ta bud'a ido dan ta d'auki muryar yan uwan nata, Kallonsu tayi tace" Khairat daga ina kuke yanzu?" kinga kedai taso muje falo" hannunata taja suka wuce da kayan bacci a jikinta riga da wando k'anana,falo suka fito, tana fad'in" wai ku kuma miya kawoku nan ne ku dukan ku?" Nadia ce da duk yayi wani yaushi tace" dama mun san yaya Salman zaiyi tafiya, shine yaya Khamis yace kina nan , shiyasa muka zo dan munyi kewarki" gyara zamanta yayi tace" amma kuma su yaya suka kawo ku?" cikin zumud'i Khairat tace" e mana, kuma sunce ma zasu dunga kawo mu har lokacin da zaki koma" aifa nan hira ta b'arke Ummi ko wanka ta kasa yi saboda dad'in hirar da suke, haka lokacin ya tafi har azahar kafin Ummi ta kalli Jawahir tace"uwar gidan Khamis ba kishan furarki saida nono" dariya tayi tace" kai yar uwa duk wannan kirari haka, ai saiki fasamin kaina" ita ma dariya tayi tace" to ai girman ki ne, kinga nifa yunwa nake ji, me kika dafa mana ne?" hararan ta tayi tace" saidai kije ki dafa, dan wanda na dafa munci ni da Mijina" baki bud'e Ummi tace" lallai ma yarinya, kina nufin ina bak'uwarki amma zanje na dafa abinci da kaina, kamar a gidan wancen mugun, ai kam ba zata sab'u ba"dariya Jawahir tayi ta mik'e tsaye tace" to uwar gidan yaya manu mi kike so in dafa maki?" k'ara shigewa tayi cikin Kujera tace" ki kawo min Tea da bred,sai ki soya kwai yaji albassa sosai,amma karki samun arom ( d'and'ano),gishiri kawai ya isa." wucewa tayi tana murmushi ta shiga cuisine, Khairat kuma cewa tayi" yayi dai hajia Abu, kenan haka kike bawa Yayana umarni ko a gidan?" tab'e baki tayi tace" ke wannan yayan naki? wanda ko murmushi ba yayi bare dariya ai shi kibar shi inda kika ganshi kawai"


Tana gamawa ta kawo mata, k'asa ta zauna tana ci suna hira harta kammala, haka suka wuni a gidan cikin farin ciki, tare sukayi girkin rana dana dare, suna idawa Jawahir ta shiga wanka ta cab'a kwalliya wa mijinta, tana fitowa ta d'auko blander tasa jik'akk'en dabino data jik'a da ranke da kanunfari a ciki ta markad'a, ta koma tasa kankana ta markad'a ta tace ruwan, sannan tasa maltina a ciki da madara peak da k'ank'ara (glasse).


Ummi data saki baki tana Kallonta tace" Jawahir kema harkin fara wannan tsirfa tsirfen na bawa kai wahala ko?"dariya tayi tace" wannan aiba na bawa kai wahala bane, wannan har lafiya zai k'ara maki, ko ba kiga da kanana a ciki ba? ga madara sannan ga dabino da kanunfari"mik'a mata tayi tace" sha kiji kema" waro ido tayi waje tace" ni, rufamin asiri kinji, wannan ai saiku masu maza" hararanta Khairat tayi tace" bana san iskanci, ke kuma fa ina kika kai mijin naki, nasan Yayana fa wallahi namiji ne na gaske, kisha dan Allah kiji akwai dad'i fa" ke wannan mutumin babu abinda zai shiga tsakaninmu, dan na tsaneshi babu ta yanda zan bashi kaina wallahi" Hafsat ce ta tab'e baki tayi tace" kinga karb'i in kinsha, in kuma ba zaki sha ba ta bamu musha" Kallon mamaki ta bita dashi tace" oo Hafsat kema wai har kinsan anfanin wannan, keda mijin naki nawa kuke?" dariya suka saka mata kafin Nadia tace" ke namiji fa namiji wallahi baya kad'an" kau da kai Ummi tayi tace" ni dai kam na rainashi gaskiya" Hafsat ce tace" lallai baki san shi bane shiyasa, amma wallahi ina jin abinda yake ko mijinki baya yinshi" Jawahir ce tace" ku baku san dalilinta na fad'ar haka ba, yaya Salman dai duk ya girme ma mazajen mû, a shekaru dama girman jiki, kinga kenan ita kad'ai tasan azabar da take ji, amma in za'a fad'i gaskiya Hafsat kinsan babu ta yanda za'a had'a yaya manu da yaya Deen" ido ta fiddo tace" ke rufamin asiri, ina ni ina wannan ai sai ya kasheni" dariya suka saka mata, Jawahir kuma ta saké mik'o mata, sannan ta karb'a ta kifa kai, bata sauke ba saida Jawahir tace" ke bani nan malama, sai kin shanye?" dago kai tayi tace"kai gaskiya da dad'i" dariya su kayi Jawahir tace" dad'i a baka, dad'i a k'asa ba" tab'e baki Ummi tayi tace "humm, kina nufin wannan dad'in a baki haka yake ko a wajan mai gida?" shigowar Khamis ne yasa su shiru, da sauri Jawahir ta mik'e ta tare shi,nan ya fad'a masu su tashi mazajen su na jiransu, haka kowace ta kama gabanta su naji kamar kar su rabu.


Ummi na ganin hankalin Jawahir ya koma wajen mijinta ta d'aga kai ta shanye sauran, cikin sand'a ta mik'e ta shige d'akinta dan tasan akwai tashin hankali inta fahimci ta shanye.






~Kuja muje~
05/03/2019 à 17:28 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑


_Samira Harouna_


🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛


*Page*




4⃣9⃣-5⃣0⃣






Da safe Ummi da Jawahir suna zaune tana since mata kai suna hira, Abba ta kira bayan sun gaisa take fad'awa Abba tana neman gafara akan abinda ya faru, budar bakin Abba yace,


"Haba Mamana babu komai fa ni nasan ba laifinki bane, dan haka ki kwantar da hankalinki kinji."


"Abba na gode amma ku nema min gafarar La Mama itama tana fushi dani?"


Cewar Abba "a'a ko kad'an mahaifiyarki ma bata fushi dake"


"To Abba na gode sosai ku gaishe min da kowa da kowa"


"Zasu ji insha Allah, nasan mijinki ya tafi yanzu to ke kad'ai ke zama a gidan?"


Dariya tayi tace "a'a Abba ina gidan yaya Khamis, amma fa Abba karku bari Alhaji yaji."


Dariya Abba ma yayi yace "karki damu ba zai ji ba"


Haka su kayi sallama, Ummi da Jawahir haka suka wuni suna shan hirarsu suna aiki har dare Khamis ya shigo yace masu Nadia bata da lafiya.


Bud'ar bakin Ummi cewa tayi "haba ni nasan sai anyi haka dama, dan tunda naga Nadia jiya nasan akwai wani abu a cikin cikin nan nata data aje."


Jawahir ce tace "ke kuma ina ruwanki da cikinta to?"


"Haba wane ina ruwana dan Allah kina ganin yarinya ta d'auki ciki duka ko sati uku ba ayi da aurenta ba."


"To sai me in ta d'auka ai albarkar auren kenan "


"Gaskiya tayi sauri kawai daga ta b'ata sai ciki kamar dama jira take, ai wannan tayi saurin bada kai nasan ma yaron kama zaiyi da ita idan ta haiho shi."


Khamis daya saki baki tunda ta fara magana yana kallonta ne yace "lallai Ummi ashe kin wuce in da nake tunaninki."


Tashi tayi cikin jin kunya tace "kayi hak'uri yaya Khamis na manta kana nan"


Jawahir kam dariya tayi ta haye k'afafun Khamis tare da shafar cikinta tace "nima fa ina ganin kamar na d'auka"


Shafa cikin nata yayi yace "ashe dai ni bana wasa bane"


"To ba zan iya ganewa ba"


"Oho haka kika ce? to bari yau d'in nan saina saka mashi dan haka ki shirya da kyau kuma babu raki babu wannan kukan."


Haka su kaci gaba da hirarsu irin ta ma'aurata cike da nishad'i.




*Da safe*Ummi na kallo bayan sun kammala cin abinci Jawahir ta shirya suna shirin fita ita da Khamis, cike da mamaki Ummi tace "Jawa yau kuma tare zaku fita kenan?"


"E tare zamu fita amma ni gidan Nadia zai aje ni."


Zama Ummi ta gyara tace "kinji 'yar banza, yanzu zaku fita tare amma shine kika k'yaleni?to tare zamu tafi yarinya."


Khamis ne yace "a'a kar ma ki fara dan babu in da zaki je sai kin fad'awa mijinki sannan ki fita."


Cikin shagwab'a tace "haba yaya Khamis dan Allah ka bari naje idan na dawo saina fad'a masa."


Cikin tsawa Khamis yace "ke ashe ba kida hankali, to wallahi babu in da zaki a gidan nan, in kuma kina so kije ki kira ki fad'a masa"


"Haba wallahi dana kira na fad'a masa k'wara na zauna banje ba, wannan d'an rainin hankalin idan na kirashi zai cikani da surutun banza kuma k'arshe ba zai bari naje ba."


Cikin jin haushi Khamis yace "ke Ummi ashe ba kida hankali ina kallonki kamar mai hankali, mijin naki kike fad'a ma haka, to bari kiji in dai kina so mu shirya dake to dole ki girmama mijinki in dai muna tare dake dan ba zan d'auki wannan rainin ba, kuma wallahi na sake ji saina nuna maki d'anyan kai fiye dana Salman."


"Shashasha kawai kina nan kina shirme kin kasa tsayawa ki kula da mijinki har kinsa shi tunanin k'ara aure ko wata d'aya baki cika ba a gidanshi, za kiyi kuka in kika bari ya auro Nuseiba k'anwarki a matsayin abokiyar zamanki." yana fad'a ya fice daga gidan.


Ummi kam tv ta k'ura ma ido ta kasa d'aukewa har saida taji hawaye nabin fuskarta.
05/03/2019 à 17:28 - Mamar Latif💃: 💑 AUEEN HA'DI 💑


_Samira Harouna_




*Choukoura (maman deeja)*


_Ina jin dad'in comment d'inki sosai, nima ina yinki💯_




_yan uwanmu, kuma ma'kotanmu *NIGERIA* muna muku fatan alkairi, muna tayaku addu'a Allah ya zab'a maku shugaba na gari mai adalci da taussayinku, Allah yasa baba *BUHARI* yaci gaba da mulki dama ire irensu masu adalci da 'kaunar talakawansu._




_My Heenat ( *RAHEENAT)* ina tayaki murnar kammala wannan daddad'an littafin naki mai suna *RAYUWAR SAUDAT* tabbas ya fad'akar kuma ya ilimantar tare da wa'azantarwa, ina maki fatan alkairi tare da kaifin bassira da zak'in hannu, Allah kuma ya yafe maki kura-kuran da kikayi a ciki, dai-dai kuma Ubangiji ya baki lada ya kuma sa sanadiyar shigarki aljanna kenan_


```Daga Samirar ki 😍ina sonki 'yar hannun dama na.```








🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛








*Page*


5⃣1⃣-5⃣2⃣




Abu kamar wasa sai Ummi ta d'aga murya sosai tana kuka, kusan minti biyar tayi a haka, daga bisani wata zuciyar ce ta tambayeta" wai mi kike ma kuka ne, auren da akace zai 'kara, ko kuwa dan an hanaki fitar?"


Da sauri ta goge hawayenta tana fad'in" haba ni d'ince zan tsaya ina kuka saboda zaya aure, to ina ruwana da aurenshi, idan yana so yayi mata hud'u lokaci guda ma, ni ina ruwana."


Maida kallonta tayi ga tv, amma sai taji wasu hawayen sun zubo mata, kawai saita saduda, danta fahimci ciwon daga k'ark'ashin zuciyarta ne yake tasowa, dan haka ta fad'a saman kujera ta 'kara fashewa da kuka, d'aci kawai ta keji a cikin zuciyarta to amma meyasa.




Tunda Salman ya dawo daga dubo kayan da suka kawoshi garin, ya kwanta akan dan madaidaicin gadonshi a k'aramin gidan daya kama haya.


Sosai ya shagalta da kallon pic d'in da tun jiya yake kallonshi, wanda jawahir ta tura masa, ya burgeshi sosai jeans ne a jikinta bleue dark iya gwiwarta, sai bak'ar riga mai kama da singlet d'in maza, tasha kitso k'anana sosai wanda ya zubo har kafad'unta, pink colour d'in jan-baki ne a bakinta sosai pic d'in ya burgeshi.


Ya rasa me yake damunshi amma tun jiya yake jin babu dad'i, har yanzu bai saké ganin Ummi en ligne ba amma har k'asan zuciyarshi yana ji yana so ya saké hira da ita, watak'ila kodan bai tab'a hira da mace bane irin haka, amma yana so ya saké hira da ita ko zata deb'e mashi kewar dake damunshi.


Wayarshi ya d'auka ya danna, pic d'in Ummi na gani a écran d'in tasha abaya bak'a ta yane
kanta da k'aramin dan kwali, sai jan-baki ja da tasa, yana bud'e code d'in wayar nan ma pic d'in tane ya fito inda take sanye da wandon nan, saida ya kalli pic d'in da kyau sannan ya shiga WhatsApp saidai Ummi bata en ligne, ba yada zab'i daya wuce kiran numberta.


Ummi na ganin kiran Salman taji ranta ya b'ace gaba d'aya haushinshi ya kamata, d'aukar wayar tayi ta kashe gaba d'aya dan karya sake damunta.




Takaici ne ya rufe Salman ganin ya kirata amma ta kashe masa waya, k'arshe tama kashe wayar gaba d'aya, tana tunanin ko ya fara damuwa da al'amuranta ne shiyasa zata masa wannan wulakanci, k'wafa yayi yace" ba laifinki bane, laifina ne dana damu sai nayi magana dake, dama wannan nake gudu shiyasa nake nesanta kaina dake, amma ba komai, wallahi ba zan saké kiranki ba harna dawo." jefar da wayar yayi ya saké mirginawa akan gadon.




Baifi minti talatin ba jawahir ta dawo gidan, ta samu Ummi kwance akan kujera tana ta kuka, kusa da ita ta zauna ta cire hijab d'inta ta d'ago da ita k'yar ta fara tambayarta" sister lafiya, miya faru ne haka kike kuka?"


Share hawayenta tayi tace" babu komai, ba kuka nake ba" hararanta tayi tace" karki rainamin wayo mana, ko yaro ya ganki a haka ai yasan kuka kike, ki fad'amin abinda ke damunki kawai"


Kai ta girgiza tace" nace maki babu komai, karki damu kanki" tashi tayi ta shige d'akinta, binta tayi da kallo tana tunanin abinda ke damunta, dan a iya saninta bata tab'a ganin Ummi na kuka ba tunda take.




Sallah kad'ai ke fiddo Ummi waje, amma ko abinci ta kasa ci duk bata jin dad'in komai, madararta kad'ai take kurb'awa kad'an kad'an, jawahir duk ta shiga damuwa da hakan, shiyasa ma ta kira khamis ta tambayeshi ko akwai abinda yama Ummi ne, amma yace babu komai sannan yace ta rabu da ita.




Har khamis ya dawo gidan baiga Ummi ba, jawahir ta rok'eshi yaje yaji abinda ke damunta har yasa ta kuka amma yak'i, saima fad'a mata da yayi auren da Salman ke son k'arawa da zaran ya dawo tare da nuseiba.


Cikin rashin Fahimtar jawahir tace" aure kuma, da nuseiba, nuseiba dai k'anwarka, amma yaushe yaya Salman yayi aure har yake tunanin saké wani auren, kuma yaushe suka fara ma soyayyar bâ tare da kowa ya sani ba.?" kallonta yayi yace" e ita, ni bama wannan ne a gaba na ba, kinsan mamarmu tana so ta had'a rumana da Salman, shi kuma nuseiba ce tafi kwanta masa a rai, dukansu 'yan uwana ne amma fa rumana ciki d'aya muka fito, duk inda na goyi baya sai na shiga matsala, shiyasa nake so ya nemi k'uri'arshi da kanshi bana so na shiga cikin maganar."


Bata sake cewa komai ba, dan a ganinta hakan bai dace ba kuma yaya Salman zaiyi hakane dan ya nuna ma duniya baya son Ummi.




*Bayan kwana uku*




Salman ne a d'akinshi keta birgima a k'asa, duk yayi kaca-kaca da d'akin da kaya ya barbaza komai, hatta zanin gadon ya jayoshi izuwa k'asa ya rufe jikinshi dashi.


Abu guda kawai yake fad'i a bakinshi" Allah Allah Allah na wayyo Allah" kamar mazari haka jikinshi ke rawa, duk jijiyoyinshi sun tashi idonshi jawur kamar garwashin wuta, hak'oranshi had'e sai hard'ewa suke.


Cikin wannan yanayin ya d'auki wayarshi ya dannan, pic d'in Ummi ne ya bayyana, kallo yake kamar zai had'iyeta, sai gani nayi ya buga wayar da bango yana wani irin gunji kamar kuka kamar kuwa, saidai ya kasa furta ko kalma d'aya.


Da k'yar ya iya rairafawa ya kai ga jakarshi ya d'auki magani har kala biyu ya b'alli guda bibbiyu ya had'a.


A hankali ya fara dawowa normal kamar yanda yake, nunfashinshi ya daidaita saidai har yanzu akwai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login