Showing 9001 words to 12000 words out of 72709 words
Chapter 4 - AUREN HADI COMPLETE DOCUMENT WRITING Samira Haruna.txt
dan Allah miye haka, haka ake tada mutum daga bacci kamar a gidan mahaukata, kai idan aka maka haka sa kaji dad'i?" ke rufe min baki ina abinda na saki?" kallaonshi tayi ido bud'e tace" wane abu kuma?" dan 'kuwa ya mata yace" ban sani ba, Tea k'in fa, ko ni kike so naje na dafa?" kau da kai tayi tace" nifa ba zan'iya ba, ace Tea ba za'a shashi da safe ko da rana ba sai dare yayi kuma sai na kai har cikin d'aki haba gaskiya da saké" ganin ya fara waige waige yana neman abun bugu yasa ta tashi da gudu ta bar d'akin ta shiga cuisine ta fara had'awa.
Tana kammalawa ta kawo mashi har d'akinshi, kallo d'aya ya mata yaga bacci pal a idonta dan haka ya mata tsaki yace" ba kida aiki sai bacci kamar kasa" lumshe ido tayi ta saké mik'ama mashi faranti tace" ni ka karb'a dan Allah in tafiya ta" wata harara ya watsa mata yace" ki aza a kaina mana tunda ba babu wurin ajewa" gefen gadon ta d'ora harta juya zata fita yace" waye zai zuba kenan?" dawowa tayi ta zuba mashi kallonshi tayi cikin muryar bacci tace" sugar nawa zan saka a ciki?" d'aya" ya bata amsa idonshi na kallon hannayenta da suka sha jan lalle da bak'i abin sha'awa,tana gamawa ta mik'a mashi wani kallo ya mata yace" ki aje ko dole sai na karb'a" ajewa tayi ta juya cikin magagin bacci ta fita, har saida ta bace ma ganinshi sannan ya kalli faranti yanda ta k'awatashi ma kad'ai da abin birgewa ne ga kamshin da ke tashi mai dad'i, d'auka yayi ya kurb'a har saida ya lumshe ido dan Khairat bata taba dafa mashi mai dad'in wannan ba kuma gashi duk abinda ake sakawa a waccen nan ma an saka "to miye banbanci?" ya tanbayi kanshi.
Yau ma da zazzab'i ta tashi tana yin sallah asuba ta nufi cuisine dan ta tuna abinda ya fad'a mata akan girkin, gashi kuma ta d'ora mai wuya abincin da Abbanta yafi sone ya karya dashi ta d'ora tuwon shinkafa da miyar agushi, duk da ta d'ora da wuri saida tayi late akan lokacin da ya bata sakamakon zazzab'in daya addabeta ga kuka da tasha abunta ta k'oshi.
Tana fitowa zata aje kwanukan ta ganshi zaune ya hakimce rai a b'ace saida ta gama jera duka kayan ta zuba mashi zata wuce d'aki yace" zonan" dawowa tayi ta tsaya sannan yace" k'arfe nawa yanzu?" da k'yar ta gane lokacin dan jiri kawai take gani, a hankali tace" 08:22" bien" ya fad'a yana kallonta yace" nawa mu kayi da ke na dinga samun abinci a nan" kamar za tayi kuka tace" dan Allah kayi hakuri banji dad'i ne shiyasa, kuma kaga tuwo ne nayi" cikin tsawa yace" to sai me, ina ruwana da abinda kika dafa, kina nufin haka zan dinga zaunawa jiranki kullum kenan?" dafe kanta tayi saboda sarawar da yake mata gashi shi kanshi Salman k'in guda uku uku take ganinshi dan haka tace" kayi hakuri dan Allah ka taimaka ka siyo min madara wallahi mutuwa zanyi" wani kallo ya mata yana magana akan wani abu ita kuma tana magana akan wani abu daban, kafin ya ankara ya jita a k'asa ta dad'i hannunta kam har yanzu a kanta ya ke cikin bacin rai yace" ke dan Allah tashi miye haka kamar wacce tasha k'waya" ya jima yana mata magana amma kamar bada ita yake ba, dan haka ya ka mata ta mike tsaye ya zaunar da ita akan kujera, da k'yar take bud'a baki tana fad'in" madara yaya Salman dan Allah ka Siyo min in sha" hararanta yayi yace" ke tafi can sai naci na k'oshi in yaso na siyo maki jarababba kawai kin d'ora ma kanki shan madara kamar wacce saniya ta haifa" kanta a duk'e tace" kaima miyasa ba zaka siyo min ba in yaso sai kaci tuwon, kenan duk jarabar gare mu, kuma wallahi saina fad'ama la mamma nace ka ce mata saniya tunda ai kasan ita ta haifeni in ba kana san cin zarafinta ba miye na had'a yar da ta haifa da saniya" maida hankalinshi yayi ga cin abincin shi har saida ya koshi sannan ya fita ya barta a wannan halin.
Tunda ya fita bai saké tuna wata Ummi ba harkokin gabanshi kawai yake hankali kwance har saida lokacin dawowar shi yayi da rana, kai tsaye yazo gidan yana shigowa baiga alamun girki ba dan haka ya d'auko belt a d'akinshi ya nufi d'akin Ummi da ke kwance tun safe ga ciwon kai ga zazzab'i ga amai da take na duk wani abinda ta ci.
Yanda ya ganta cikin bargo ya k'ara k'ona mashi rai matuk'a, bai ko tsaya Haye bargon ba ya fara tsuga mata belt kin nan, ba tayi wata Kara ba sai kuka daya saké kubce mata mai tsanani yana cikin dukanta amai ya taho mata haka ta fara kelayashi dole ya tsaya yana kallon ikon Allah, duk ta b'ata gadon dan haka ta rairafa ta dawo k'asa ta rakub'e tana kuka, tsaki ya mata ya fita daga d'akin dole ya fita nemo madara da magani da abinda zai ci.
27/02/2019 à 17:34 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑
_Samira Harouna_
```dedecated```
```To```
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da_ _amana insha Allah)🤜_ 🤛
*Page*
3⃣7⃣-3⃣8⃣
Yana dawo ya sameta in da ya barta, da kanshi ya zubo mata madara a cup da abincin ya kawo mata mik'a mata yayi kawai sai tak'i amsar ta cup d'in sai ta cikin gorar, tana karb'a ta kafa kai saida ta sha fiye da rabi sannan ta aje tana maida nunfashi a hankali, Salman zaune yayi yana kallonta baki bud'e ganin zata kwanta yace" ke tashi dan Allah kici abinci" da k'yar ta koma ta zauna ta d'auki abinci saidai ba taci sosai ba ta aje ya bata magani nan fa aka sha fama, yana mik'a mata ta ya tsina fuska tace" a'a ban sha" kwance tayi ya fizgota yana fad'in" tashi Dallah malama, wato magani ne ba zaki sha ba, amma abun dad'i kinci kinsha ko maza karb'i kisha nan" ganin ba zata sha ba yasa ya d'auki cokalin da taci abinci da shi ya k'wandara mata akai dole ta karb'a tasha tana kunkuni.
Baifi minti biyar ba bacci ya d'auketa, kujerar da ke fuskantar ta ya zauna ya fara cin abinci yana tunani iri iri, inda wata zuciyar ke saka mashi ya horata ta hanyar yi mata wasa da madara, wata zuciyar kuma na fada mashi kar yayi hakan tunda tana shiga matsala in bata sha ba.
Ana sallah la'asar ta farka, wanka tayi sannan tayi alwala tayi sallah ta shiga cuisine dan gabatar da abincin dare, tana d'orawa ta shiga d'akin shi ta fara gyara masa duk da bâ wani datti yayi ba haka ta gyara shi tayi turare sannan ta rufe d'akin taci gaba da sauran ayyukanta, sai bayan Magriba ta kammala komai tana shiga d'akinta wanka tayi ta saka riga da wando na bacci ana kiran sallah isha'i ta saka doguwar riga tayi sallah sannan ta kwanta saboda gajiyar da tayi, dan tunda take bata taba aiki mai yawa kamar na yau ba.
Bacci mai dad'i ya d'auketa, amma shigowar Salman ya mata wani hargitsantsan tadi da ruwan sanhi saboda ta fito ta zuba masa abinci, haka ta fito tana kuka tana zuba abinci, tana idawa ta ajiye masa ta koma d'aki ta kwanta ta dinga shek'a kuka tana fad'in" shikenan haka rayuwata zata k'are, an rabani da iyayena da yan uwana da kowa nawa ba'a barni nayi ban kwana da su ba, gashi wannan mugun yana neman kashe ni, wallahi ba zan zauna gidan nan ba dole na barshi in ba haka ba to zai kashe ni ko ni na kashe shi" tunda ta fara kukan Salman ya tsaya k'ofar d'akin yana sauraranta yana jin tace ko ta kashe shi ya bud'o k'ofar da k'arfi ya shigo dab da ita ya tsaya ya kama kunnanta yace
"Wallahi karki bari zuciyar ki ta fara raya maki ki kashe ni, dan kafin ki kashe ni ni zan kashe ki, kuma zama daram a gidan nan babu inda zaki je kuma dolenki kiyi abinda na saki in kuma ba haka ba" k'wafa yayi alamar tasan mi zai biyo baya.
Iya k'arfinta ta sa ta tureshi da sauri ta mik'e daga kan gadon tana k'ok'arin guduwa, yaji zafin turar data masa dan haka yayi saurin rik'ota duk da yayi nasarar rik'o k'ugunta a tare suka fad'a saman gadon inda Salman ya fad'a samanta da gaba d'aya nauyinshi, k'ara ta saki lokaci guda kuma ta soma kici kicin k'waceya, d'agata yayi yana kallonta kafin ya juya ya fita daga d'akin.
Haka ta takure taci gaba da kukanta tsawon lokaci, duk da bata manta da Tea d'in shi ba amma tayi niyar ba zata kai bâ saidai ya kasheta.
Tunda yaga 00:30 tayi ya tabbatar ba zata zo ba shi kuma yana so ya canzata dan haka ya shigo d'akin hannunshi rik'e da belt, yana ganinta kwance duk da baccin bai jima da d'aukarta ba haka ya ware iya k'arfinshi ya zabga mata belt d'in nan, a gigice ta mike zaune tana dube dube tana ganinshi ta fashe da kuka lokaci guda kuma ya soma tsula mata belt d'in, duk in da ta nufi saiya tarota ta shige cikin bargo ya yaye shi da k'yar ta samu ta rik'e belt d'in tana fad'in" dan Allah kayi hakuri, kayi hakuri wallahi ba zan saké ba na daina daga yau, zanyi duk abinda kace wallahi ko, dan Allah kayi hakuri."
Wata harara ya wurga mata yace" nan da minti goma ki kawo min Tea d'akina" yana fad'a ya wuce d'akinshi ya barta nan, ita ma tashi tayi jiki na rawa ta shiga cuisine dan had'a mashi, hak'ik'a yau ta matuk'ar tsorata da al'amarin Salman, yana dukanta ko a gida amma bai taba mata irin dukan daya mata yau ba, dan-danan ta gama ta kai mashi d'aki, harta juyo zata fito yace" ke saurara kiji" cak ta tsaya tare da juyawa tana kallonshi" daga gobe k'arfe 23:00 zaki dinga kawo min Tea, idan kika wuce lokacin dana baki to jikinki zai fad'a maki" saida ta murgud'a baki sannan ta juya da sauri yace" ke wa kike juyama baki?zo nan" tana zuwa yace" gwiwanki k'asa" ba gardama tayi abinda yasata, ta d'auka zai fad'a mata wata magana ne amma wasa wasa sai ga Ummi durkushe sama da awa d'aya, da tayi yin k'urin tashi zai dalla mata harara dole ta koma, shi kuma yana ta latse latse a wayar shi yana dariya, shi kam bai san Ummi raguwa bace daga nan ta d'ora kanta saman gadon sai bacci.
Tunda Salman yaga haka ya gyara kwanciyar shi yana fad'in" saidai ki kwana a haka mahaukaciya kawai" Allah sarki kamar na daddab'ata ta tashi.
02:40 Ummi ta farka ta kalleshi tayi tsaki tace" mugu azzalumi wallahi kai ma sai kaji abinda naji" cup d'in da yasha Tea ta d'auka ta zuba Tea d'in a ciki ta d'ora saman gadon ta ja k'afafunta da sukayi nauyi ga ciwo ta fita ta bar d'akin.
Bata koma bacci ba har akayi sallah, tana idar da sallah ta fito ta shiga d'akin Salman dan ta gaishe shi kamar yanda yace, tana shiga ta same shi akan sallaya kau da kanta tayi daga tsaye tace" ina kwana" kallon banza ya bita da shi yace" bari na tashi sai mu gwada tsawon" ta gane mi yake nufi dan haka ta durkusa ta saké fad'in" ina kwana" a wahalce ya amsa mata da" lafiya" tashi tayi dan ta shiga cuisine yace" zauna" zaunawa tayi yayin da ya mik'o mata Al-Qur'ani yace" fara daga Hizib biyar har zuwa Al-Nass" karb'a tayi ta fara rera 'kira'a, masha Allah kamar ruwan sama ga tattausan murya Salman sai yaji kamar ya samu kullum ta dinga karanta masa, musamman Suratul Munafiqun kai kace gabanta akayi wahayinta ko wace kalma ko wane harafi yana fita daki daki, tana karantawa yana jin tsantsar abinda surar take magana akai, bai san lokacin da hawaye suka fara zubo masa ba har saida ta kai Suratul K'alam ya d'aga mata hannu yana share hawaye tana d'ago ido su ka sarke dana juna, ashe ita ma kuka ne take haka suka share hawayensu ta tashi ta fara aikin gabanta.
27/02/2019 à 21:27 - Vous avez ajouté My Meelat
28/02/2019 à 17:02 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑
_Samira Harouna_
```dedecated to```
```Fans```
( __Luv you my mom tu est très chers pour moi, ce toi qui m'adonner une bonne éducation pour devenir comme ca, je te remercie beaucoup bizou😘)_
*RABBIR HAM HUMA KAMA RABBAYANI SAGIRAN.*👏👏👏
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_ 🤜🤛
*Page*
3⃣9⃣-4⃣0⃣
Tana cikin aiki taji yana k'walla mata kira, da k'asaita ta shigo d'akin tayi tsaye tana kallonshi, dama ranshi a matuk'ar b'ace yake dan haka ya falleta da mari yace" wani rainin wayo ne wannan? ina tsaye kina tsaye kina kallona da idon kinnan kamar na aljanu" k'wallan da suka cika idonta ne ta matso su hannunta a kumatunta a hankali ta zube k'asa, shi kuma ya d'ora da tambayar ta" ya akayi wannan Tea d'in ya zuba akan gadon nan? dan ni dai nasan ban aje ba." kallon gadon tayi ta kalleshi tace" ni kuma ta yaya zan san lokacin da kayi fitsarin kwancen ka" tana rufe baki ya sake d'auketa da wani wawan marin da yafi na d'azu, zafi daya kai mata kawai sai ta mik'e tsaye cikin zafin rai ta d'auki cup d'in da ta zuba Tea d'in ta jefa masa a k'irji tana fad'in" karka saké dukana mugu kawai azzalumi macuci" dafe k'irji yayi yace" Ummi ni kika jefa?lallai wuyanki yayi kauri, kuma idan banyi da gaske ba to wata rana dukana za kiyi kema, amma bari yanzu nayi maganin wannan tantirancin naki" wayar chargeur d'inshi ya d'auka a gefen gado sai ko ya fara zabga ma Ummi ba 'kakk'autawa, haka Ummi ta dinga ihu tana neman taimako da agaji, amma ina babu haka Salman ya daketa san ranshi ya gaji ya bari, jefar da chargeur yayi ya shiga douche ya barta nan rakub'e da gado tana ruzgar kuka jikinta sai rad'ad'i yake mata kamar zai cire duk jikinta ya farfashe.
Haka ya fito ya shirya saida ya harareta ya nuna ta da yatsa yace" wallahi idan har kika ce ba za ki girmani ba, to wallahi ranki idan yayi dubu zai dinga b'aci, ya zama dole kisan abinda zai dinga fita daga bakin ki sakarya kawai" ficewa yayi ya barta nan tana kuka.
Awa biyu ta d'auka kafin ta tashi ta fito daga d'akin, cuisine ta nufa dan tunawa da tayi tana cikin d'ori ne ya kirata, tayi mamakin ganin gas a kashe tasan shi ya kashe dan haka ta koma d'akinta ba tare da ta bud'a tukunyar taga abinda ke ciki ba, ko wanka ba tayi ba ta kwanta saman gado taci gaba da kuka da k'unar zuci.
12:20 taga zaman ba zai gyarata ba ta fito ta shiga cuisine ta fara girkin rana, tsananin yunwa da zafin jiki ga ciwon kai duk ya taru ya mata yawa, haka ta kammala girkin da k'yar kamar zata mutu.
Tana idawa ta koma d'aki tayi sallah ko wanka ba tayi ba saboda raunikan dake jikinta, tana kwance Salman ya shigo d'akin yace" wa kika aje da zai zuba maki abincin" fita yayi bai jira amsarta ba tashi tayi tabi bayanshi, tsaf ta zuba masa shinkafa da miyar kayan cikin ragon da tayi, bud'a ciki yayi ya ci abincin sosai, yana kammalawa yayi wanka ya fita bâ tare da ya bi ta kan Ummi ba.
Abun ya k'ara tsananta ma Ummi kamar za tayi hauka ta keji, ga zafin ciwo da rad'ad'i ga ciwon kai saboda kukan da take sha ga bakin ciki da kad'aici, tuna dukan da Salman ya mata yasa ta shiga cuisine dan sarrafa abincin dare, macaronie da miyar naman rago ta dafa d'an kad'an wanda zai ishe su.
Da k'yar ta watsa ruwa dan ciwon da ke jikinta ba zai bari ta cud'a ba, d'aure take da towel tana ta kai da kawowa saboda wani sabon rad'ad'i da take ji, mai ta shafa tasa turare gajeran wando tasa iya cinyoyinta sai bras da ta saka wanda taji kamar ma karta saka, maganin da Salman ya siyo mata tasha sannan ta kwanta ba jimawa bacci ya d'auketa.
Kusan awa biyu kenan da Salman ya shigo gidan amma babu ko motsin Ummi, abinci kawai ya ke so yaci amma ya k'i zubawa yana jiran Ummi, a hankali ya bud'a k'ofar d'akinta ya shigo, k'ura mata ido yayi yana k'are mata kallo tas, duk da shatin bulalar da ya gani ya fito sosai a jikinta duk jini ya kwanta ga manyan birridda duk a bayanta ya kwanta, tausayinta ya ji ya kama shi sai yaji baiji dad'i ba lokaci d'aya kuma ya ji wani abu yana tsargar masa tun daga kwanyar kanshi har babban dan yatsan k'afarshi, yana jin abun yana k'ara girmama yana fizgar shi kamar zai aikata wani abu yasa ya daddab'a k'afarta, a hankali ta juyo da kanta sannan ta tashi zaune tana murza fuskarta cikin tattausan murya yace,
"Wa kika aje da zai zuba min abincin?ko ni kike so in zuba da kaina?juyawa yayi har ya kai k'ofar d'akin ya tsaya ya juyo yana kallanta, ganin bata taso ba yasa yace" wai ba kiji ne ina maki magana?" a hankali tace" ina zuwa riga zan saka" kenan sai na zaune ina jiranki harki gama, kinsan awata nawa a gidan nan ina jiranki,ko so kike yinwa ta kashe ni?" yin k'urawa tayi ta tashi ta nufi drower, tsawa ya mata da k'arfi" ke wai ba da ke nake