Showing 36001 words to 39000 words out of 72709 words
Chapter 13 - AUREN HADI COMPLETE DOCUMENT WRITING Samira Haruna.txt
hankali Ummi ta bud'a idonta kamar mai jin bacci, tana had'a ido da Salman ta zabura ta mik'e zaune tana fad'in "wayyo Allah dan Allah ka rabu dani wallahi ni ba 'yar iska bace."
Rumgumeta yayi a jikinshi sosai tare da d'ora bakinshi a kunnenta ya fara fad'in "ya isa haka Ummi ki nutsu babu abinda zan maki, na kawo ki nan ne saboda Islam bana so taje ta fad'a cewa ni da ke kowa a d'akin shi yake kwana, kin santa da surutu shiyasa na kawo ki nan."
Gaskiya kam ta gamsu da abinda ya fad'a dan haka tayi shiru tana shak'ar k'amshin jikinshi tana sauke numfashi a hankali, bata sake motsawa ba har bacci ya d'auketa a k'irjinshi.
Gyara mata kwanciya yayi ya mata addu'a yana kallonta na d'an wani lokaci, kafin ya mik'e dan ya gabatar da nafilfili dan kusancin da suka samu da ita yanzu yasa service d'in shi ya fara sauka, kuma idan ya ci gaba da zama haka to wani abu zai iya faruwa amma duk da haka saida naga ya b'alli maganin nan yasha kafin ya fara sallah.
```ALLAH SARKIN DAD'I IN JI B'ARAWON TAKAND'A```.
Har asuba Salman bai idar da sallah ba, saida yayi sallah asuba sannan ya kwanta akan dardumar bacci ya d'auke shi.
K'wank'wasa k'ofa ne ya farkar dasu a tare suka tashi zaune suna kallon juna, Salman ne ya mik'e cikin sauri dan jin muryar Islam na kiran sunan aunty Ummi, yana bud'ewa ya kalli Islam yace "Islam kin tashi?"
Cikin shagwab'a tace "na tashi ina aunty Ummi take?"
Gefe ya matsa tare da nuna mata ita yace "wuce ciki"
Tana shigowa ta haye saman gadon tare da jan zanin da Ummi ke rufe a ciki ta kwanta, Ummi ce tace "ke tashi kiyi sallah"
Bud'a idonta tayi tace "aunty nayi sallah fa"
Kallon tuhuma Ummi ta mata tace "kai Islam yaushe kika tashi?"
"Allah ko aunty nayi lokacin dana tashi fitsari sai naji ana sallah, kawai nima sai nayi."
"To naji kwanta muyi bacci" Ummi ta fad'a tana sake kwantawa, Salman na tsaye yana kallonsu ganin sun sake kwantawa yasa shi kuma ya fita daga d'akin ya koma falo ya kwanta kan doguwar kujera tare da rufe ido.
A hankali yake jin abin kamar daga sama ya kuma rasa ta ina yake fitowa, zaune yayi yana k'are ma d'akin kallo saidai baiga komai ba, sake kwantawa yayi amma har yanzu yana jin abun ruf da ciki yayi yana k'ara tusa kanshi cikin kujerar yana shak'ar k'amshin, sai lokaci ya tuna da kujerar da take zama ce tunda ta ji ciwo.
Idonshi a rufe yace "wannan wane irin turare ne mai rikita mutum idan yaji k'amshin sa?"
Haka ya dinga birgima akan kujerar tsikar jikinshi na tashi yana dad'a k'ank'amewa har bacci ya d'aukeshi marar dad'i.
_AH TO FANS DAI SUKA CE WAI ANAYI SUNA JIN DAD'I_
Bai jima ba ya tashi saboda shi kad'ai ya san me yake ji, daki ya shiga har yanzu bacci suke abinsu, toilet ya shiga yayi wanka ya fito ya shirya cikin k'ananan kaya bleue riga da bak'in wando da takalma sau ciki colour rigar, tsaf ya fito had'add'en guy shi ya d'auki tabarau irin na 'yan zamani bak'i ya kifa, turaren Ummi ya dauka yasa aljihu sannan ya k'araso wajenta ya sunkuya cikin kunne ya rad'a mata,
"Hajia Abu tashi rana fa tayi sosai"
Ummi na tashi taga kamar a mafarki ne take yanda taga Salman ya had'e, shirun da tayi tana kallonsa ne yasa yace "ki shiga toilet d'ina kiyi wanka zan d'auko maki kaya d'akinki."
Fita yayi ta bishi da ido, haka ta shiga toilet d'in tana mai k'ara jin haushin Nuseiba dan tana kallonshi taji ta tuna da ita, ji take yanzu ace duk wannan gayun da kyawu na yaya Salman ba zata mallakeshi ita kad'ai ba.
```A YAU GA BANZA SUNAN WANI UNGUWAR MU```🤣
05/03/2019 à 17:33 - Mamar Latif💃: 💑AUREN HA'DI 💑
_Samira Harouna_
*SADAUKARWA*
*Ga*
_Aunty Hawa_
_Aunty Hawa Jamil_
_Huseina_
_Fiddausi_
_Hussylurv_
_Hakeema ta_
_Fateema mom dady_
_Sister Ruky_
_Choukra_
_Salma Abdrur-rahman_
_Maman Samha_
_Kakata Haleema_
_My Lissa_
_My Heenat_
```ALLAH YA BAR MIN KU MASOYA NA INA K'AUNAR KU```😍😍 *JE VOUS AIME*
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
*Page*
7⃣3⃣-7⃣4⃣
Haka Ummi ta fito daga wanka sanye da rigar wankan Salman, amma babu kaya babu Salman d'an k'aramin tsaki tayi tace "kaji wai har yanzu d'auko kaya gashi ko brush banyi ba."
D'akinta ta nufa rik'e da kayan data cire tana fad'in "yanzu haka ma ya manta da alamarina ya shiga sabgar gabanshi."
Tana shiga ta watsa kayanta saman gado ta bud'a wadrob ta d'auko wata doguwar riga fara mai siraran hannaye tare da bras da pants black, drower ta bud'a ta d'auki coton sannan ta saka tana sawa ta cire rigar wankan ta jefa saman gado tana shirin d'aukar bras taji motsi a bayanta, da k'arfi ta juyo take tsoro ya bayyana a fuskarta ganin Salman ya fito daga toilet rik'e da brush da maclean da kayan jikinta a hannu.
Kasa magana tayi sai hannu da tasa ta rufe k'irjinta wanda Salman ke kan kallo, bud'a baki yayi yana so yayi magana amma ya kasa "aaaaaaaaa" kawai yake fad'a haka ya fara takawa yazo ya aje kayan akan gado hanyar fita ya nufa amma sai ya juyo yana kallon ma zaunan Ummi, da sauri ta juya tana kallonshi cikin tsiwa tace,
"Wai dan Allah miye haka? ka fita mana"
Gaf da ita ya matso yana kallon idonta duk da ta sauke nata k'asa, cikin taussasan murya yace "Ummi zaki iya...?" kuma sai yayi shiru a hankali ta d'ago kanta ta kalleshi.
Rintse ido Salman yayi dan ba zai iya hakura ba yana bud'a ido yasa hannayenshi ya tallabo fuskarta sannu sannu yakai bakinshi a nata bakin ya sumbata, ya d'auka zai iya tsayawa daga nan amma ina saiya k'ara had'a bakinshi da nata ya fara tsutsa cikin salo, daga a hankali sai ya fara gaggawa da sauri, k'afafunshi ne yaji sunyi nauyi jikinshi b'ari kawai yake idonshi rufe a yanda yake ji babu wanda ya isa ya dakatar dashi yau d'in nan.
A hankali ya lula da ita akan gado hannayenshi kam akan k'irjinta kamar zai cirasu, Ummi ta fara jin zafi dan haka tayi shirin k'watar kanta, abu fa ya ta'azzara ni dai jiri ma ya fara d'ibata sai My Lissa na mik'ewa biro danta ci gaba da rubutun, ma chérie Hakeema kuma ta b'allo paracétamol ta ban na had'iya.
Ummi kam kamar gunki dan har yanzu bata yarda da gaske ne hakan ke faruwa ba, dan ta san yaya Salman ba zai aikata haka ba, jin abun ya fara girma yana shirin kai hannunshi ga mararta yasa Ummi ture Salman daga jikinta tare da tashi cikin sauri.
Durk'ushewa yayi gabanta amma kanshi k'asa ya kasa d'agowa, saida tayi nesa da shi ta tsaya tare da rufe jikinta da rigar wankan nan ta fara magana cikin shed'a sama sama,
"Dama haka kake ban sani ba, ashe duk cika bakin nan na banza ne, tirr" ta fad'a tare da kau da kanta, ci gaba tayi da cewa,
"In dai haka kake to baka dace da girman kai ba, banyi tunanin haka daga gareka ba, kuma ka sani wallahi koda ina cikin tsarki ba zan tab'a baka kaina ba, domin kuwa kana min kallon k'ask'anci, na san zaman mu ba zai d'ore ba dan haka zan ci gaba da ajiyar budurci na dan na kaishi in da ya dace."
Tana fad'a ta shiga toilet ta barshi nan, yanda kanshi ke sarawa ga jikinshi rawa kawai yake a daddafe ya kai d'akinshi ya d'auki maganinshi saida ya had'iyi maganin sannan ya shiga toilet ya kifa kanshi a pampo ya sha ruwa.
Fitowa yayi daga d'akin saboda har yanzu Islam bacci take, kai tsaye motar shi ya shiga ya kifa kansa a stiyari ido rufe, kalaman Ummi ne kawai ke dawo masa wai " wallahi koda ina cikin tsarki ba zan tab'a baka kaina ba."
Kuma wai "zan kai budurci na a in da ya dace"
"Waye ya dace kenan daya wuce ni mijinta?" babu amsar tambaya.
Ya jima sosai a haka kafin ya bud'a idonshi cikin muryar tausayi yace "Allah ka kare ni daga aikata ba daidai ba"
Wasu zafafan hawaye ne suka zubo a kumatunshi, gogewa yayi tare da tayar da mota ya fita.
Yana saman hanya ya kira Khamis ya tambaye shi yana ina, cewa yayi "ina gida amma yanzu zan fita, zanje gida wajen su Mama"
Cikin dakusashiyar muryarshi yace "ok jira ni ina zuwa yanzu."
"To sai ka zo" ya fad'a a takaice.
Yana zuwa Khamis ya fito suka wuce, a hanya ne Salman ne ya kalli Khamis yace "Khamis dan Allah ka taimaka min, ka sanar dasu Abba ina neman auren Nuseiba wallahi bada wasa nake ba."
Cike da kosawa Khamis yace "Salman na fad'a maka ka daina sani cikin maganar nan, idan fa ka fad'a babu wanda zai hana ka auren Nuseiba amma ka tsaya ni kana takura min."
Cikin damuwa Salman yace "me yasa ba zaka gane ba Khamis? ina cikin wani hali kuma ina buk'atar taimako wallahi bana so na ci gaba da zama da yarinyar nan a gidan nan mu kad'ai, in ba haka ba ban san mi zai biyo baya ba."
"Khamis yau saura kad'an na aikata abun kunya, saura kad'an na jawa kaina raini, saura kad'an na aikata abinda zai dameni a gaba, saura k'iris na kusance ta."
Cikin raini Khamis yace "wai raini, kai a ganinka wannan ne raini?"
"To bari kaji, wallahi ko yanzu in kayi wasa to ina baka tabbacin cewa abinda ya faru a baya shine zai sake faruwa a yanzu, dan tabbas sai kaga likita."
"Cousin, kayi abinda ya dace da kai kafin ka jefa rayuwarka cikin matsala, kana da mata dan haka banga dalilin da zaisa ka bari ciwo ya illata ka ba."
"Malam ka sauke girman kai da izza ka kwashi albarkatun dake tattare da mace, Ummi yarinya ce sosai idan aka had'ata da kai, zaka iya tafiyar da ita yanda ranka yake so domin kuwa k'wace goriba a hannun kuturu abune mai sauk'i."
Girgiza kai yayi yana kallon gabanshi yace "baka san wacece wannan yarinyar ba shiyasa, ka san ma mi tace min?"
"A'a" kallonshi yayi yace "tace ba zata bani kanta ba saboda ban dace ba"
"Hahahaha, to ai gaskiya ta fad'a saboda yanda kake cin magani haka wacece zata yarda ta baka kanta? ai su mata saida rarrashi da lallami sannan idan kayi sa'a su baka ka lasa."
Cike da mamaki yace "bayan rarrashin ma sai kayi sa'a?"
Dariya Khamis yayi yace "sosai kuwa, tunda kayan marmarin suna gurin su."
Kai ya girgiza yace "wannan k'ask'anci ai yayi yawa, bayan ma jikina da zata gani saina tsaya ina lallab'ata bayan matata ce sadaki na biya, kuma a haka ace wai sai nayi sa'a haba."
Kallonshi Khamis yayi yace "kai ma ai jikinta zaka gani, ko kuwa?"
Tabe baki yayi bai sake magana ba har suka kai gidan, da sallama suka shiga sun samu su Mama duka a tsakar gida suna 'yan aikace aikace, gaisawa su kayi kafin suka zauna.
Mama ce ta fara kiran "Rumana, Rumana" daga cikin d'aki ta amsa da "iye"
"Ke ki kawo ruwa"
"To" ta fad'a a takaice, Salman kam takaici kawai yake wai ace mahaifiyar ki ta kira ki kice mata iye babu ladabi babu girmamawa, wannan shine dalilin da yasa baya san shiga harkarta ma.
Haka ta fito gantsar gantsar ta aje masu ruwa da wata doguwar rigarta ko d'an kwali babu a kanta, ko kallon ruwan Salman baiyi ba dan yanda yaga kanta a cunkushe yaji zuciyarshi ma na tashi, "ina kwana".
Ta fad'a tare da juyawa zata koma d'aki, cikin fad'a Salman yace "ke ina d'an kwalinki kike yawo haka?"
Cikin jin kunya tace "yana d'aki"
"Oho shine kike yawo haka? to in kika sake bari mu kayi ido biyu dake haka wallahi saina k'ona gashin nan"
Rumana kam dad'i ne ya kasheta dan wannan tsananin na yaya Salman shine yasa take sonshi, dan a tunaninta idan ta aureshi zata rik'eshi gam tsananin shi kuma zaisa ya d'auke kanshi daga wasu matan.
Tana shiga d'aki ya kalli Maman Nuseiba yace "Mama ina Nuseiba ne ko bata nan?"
Cewar Mama "tana d'aki kam kuma na san tana jinka, shiru dai tayi"
Shiru yayi har Khamis ya gama abinda ya kawoshi suka tashi zasu wuce, saida suka kai k'ofar gida Nuseiba ta fito tana fad'in "ina kwana yaya Salman?"
Juyowa yayi yana kallonta yace "ashe kina ciki kika yi banza dani?"
Wani fari tayi da ido mai kashe zuciya tace "lah yaya Salman ba haka bane, kawai dai ina so mu gaisa ne ba'a cikin mutane ba"
Shagala yayi da kallon bakinta daya sha pink d'in ja leb'e (in ji uncle d'i na), hira suka fara tab'awa suna dariya Khamis kam ya gama k'ulewa ganin yanda take wani fari da ido na kissa, haushi ne ya kamashi yace "kaga malam dan Allah wuce mu tafi, ke kuma wuce gida"
Saida ta harare shi ta k'asan ido tare da ji a ranta cewa yana mata bak'in ciki ne, ciki ta shiga su kuma suka wuce.
Tunawa da Salman yayi yaune ranar komawar Ummi asibiti yasa ya dawo gida suka shirya tare da Islam suka kama hanyar asibiti, suna zuwa suka nufi d'akin da zai sada su da wajen likitar data duba Ummi ranar.
Layin da suka gani yasa su tsayawa suna k'ara kallon mutanen dake wurin, Salman mota ya koma kafin layin ya rage, mutane na shiga kuma suna fitowa dan danan haka yasa layin ya ragu sosai, mutane uku suka rage su Ummi su shiga Salman na ganin an kusa kawowa garesu ya fito daga mota ya zo.
Suna haka wani kyakyawa kuma matashin likita ya fito daga wani d'aki kusa dasu, yana ganin Ummi ya washe baki tare da fad'in "lah mutuniyar kece kika dawo? a to bari na kai sak'on nan na dawo na rik'e ki dan na san yauma ba zaki tsaya ba."
Murmushi kawai ta masa shi kuma ya wuce d'aya d'akin, Salman kam kamar a tab'a shi ya fashe saboda cika, an d'an d'auki lokaci kafin Ummi ta mik'e zata shiga, cikin fushi Salman ya fizgo hijabinta yana fad'in "waye waccen?"
Saida ta kalleshi sama da k'asa tace "ban gane waye waccen ba?kai baga ko waye ba ko baka iya fahimtar kayan aikin mutane?"
"Kamar zai bigeta kuma dai ya tsaya tare da fad'in "ina tambayar ki kina tambayata, ki fad'a min miye tsakanin ki dashi?"
Ummi kam tuna Nuseiba tayi da irin haushi da k'uncin data shiga saboda su, dan haka tace masa "ayya ai ya taimaka min ne ranar da muka zo nan shi ya rik'e ni aka min d'inki da allura."
"Ya rik'e ki" wucewa tayi ta barshi nan, bin bayanta yayi Islam kam na zaune daga waje da k'yar Ummi ta mik'a k'afarta dan a cire mata zaren da aka mata d'inki, saida Salman ya matse ta ya tutsa kanta a cikin k'irjinshi sannan aka fara d'ebe mata.
Ana gamawa Ummi ta d'ago kanta fuskarta duk ta jik'e da hawaye da majina, Salman kam duk rigarshi ta jik'e sai kuma ta bashi tausayi haka aka gama masu suka kama hanyar gida.
Daidai *Maradi Store* yayi parking, Islam ya kalla dake baya yace "Islam muje ko."
Fita tayi shi kuma ya kalli Ummi yace "ki jira anan muna zuwa yanzu" har zai fita Ummi tace "ni kad'ai zan zauna, me yasa ba zamu je tare ba?"
A dak'ile yace "banga anfanin zuwanki ba, idan kuma kina da sak'o ki kawo na siyo maki?"
Ba tare data kalleshi ba tace "ina da amma dole sai in ni naje da kaina."
Bud'a murfin motar yayi yace "sai kiyi ta zama anan to"
Ta jima zaune kafin suka fito daga ciki, ledar hannunshi ya mik'a mata tana karb'a ta bud'e farin ciki ne ya bayyana a fuskarta ganinta kayan k'walam da mak'ulashe, bata tsaya b'ata lokaci ba ta d'auki wata chocolat ta fara sha, jefi jefi Salman ya kan kalleta yana mamakin yanda ta kasa masa godiya, amma Islam ma dake k'arama ta masa tun kafin su fito, ya san ba daga tarbiya bace kawai dai tsarinta ne haka, haka har suka isa gida.
Ko abincin rana Ummi bata ci ba saboda ciye ciye da tayi, da yamma ma kam suna zaune farfajiyar gida ita da Islam Jawahir ta shigo a hargitse, Ummi ce tace "ke kuma lafiya haka, daga ina kike kamar an koro ki?"
Saida ta zauna ta cire nik'ab da hijab tace "kedai bari wallahi, hadari ne a gari shiyasa nayi saurin k'arasowa karya riske ni a hanya"
Sai lokacin Ummi ta kalli sama tace "hadari fa, kinga muna nan sai a tashi duniya bamu sani ba."
Dariya Jawahir tayi tace "idan aka kawo gareku ai zaku sani" kafin Ummi tayi magana iska ya taso da k'arfi, dan haka suka koma ciki nan fa aka fara ruwa kamar da bakin k'warya dan dama an kwana biyu ba ayi ba.
21:00 aka d'auke ruwa ba jimawa kuma Salman da Khamis suka shigo gidan, Ummi ko kallon Salman ba tayi amma ta gaishe da Khamis, haka ta shirya Islam suka tafi tare da Jawahir, tunda Salman ya fita ya matsu ya dawo gidan dan sosai yaji haushin banzan da tayi da shi gaban mutane.
Yana dawo har cikin d'akinta ya shiga amma abun mamaki kwance take tana hawaye, tunani yayi ko dan Islam ta tafi ne, matsowa yayi cikin muryar fad'a yace "Ummi naga har yanzu ba kya neman zaman lafiya da ni, ke kinfi k'arfin ki gaishe ni ko?"
Zuciyarta a wuya take dama dan haka ta harareshi sama da k'asa tare da tsaki ta kau da kanta gefe, mamaki ne ya bayyana a fuskarshi cikin b'acin rai da zafin nama ya cabko hannunta yana fad'in,
"Wa kike harara, ni kike wa tsaki?"
Cikin muryar kuka da fitar hayyaci Ummi tace "ka sake ni mugu kawai azzalumi, wallahi sai Allah ya saka min kuma wallahi ka auri Nuseiba sai zaman gidan nan ya gagareta dan babu abinda zai hana ni ci mata uwa, mugu kawai kana fad'a wai ni nama k'aramta amma kuma shine zaka auri yarinyar dana bata shekara hud'u, dama ita kake so shi yasa zaka aure ta."
Sakinta Salman yayi