Showing 27001 words to 30000 words out of 72709 words
Chapter 10 - AUREN HADI COMPLETE DOCUMENT WRITING Samira Haruna.txt
yana mata yawo a k'wak'walwa, a hankali take rera kukan hannayenta biyu a kanta.
Salman dake tsaye yana nafilfili yaji tashinta dan haka ya shigo cikin azama dan yaga mike faruwa.
Zaune yayi kusanta yana fad'in "Ummi lafiya miya faru?"
Tana d'aga kai ta kalleshi kawai saita fad'a jikinshi ta k'ara fashewa da kuka, rigar shi kawai take ta cukuikuyewa tana k'ara tusa kanta cikin k'irjinshi tana fad'in "yaya Salman shi nake gani wallahi tsoro nake ji, zamu k'ara fad'uwa, dan Allah karka tafi duk jini ne a jikinshi ga kanshi ma ya fashe"
Shiru yayi yana tunani (dole ne abun ya tsaya mata a rai, dan yanda aka fad'a masa gawar mutumin dole ko namiji yaji abu bare kuma mace mai rauni), hannayenshi ya dora a bayanta yana cewa "shikenan to ya isa haka kinji, insha Allah bazai saké dawowa ba, calme toi"
Haka yaci gaba da shafa bayanta har bacci ya d'auketa, a hankali ya maida kanta saman pillow yayi mata addu'a ya shafa mata, idonshi akan fuskarta, mik'ewa yayi ya shinfid'a sallayarta yaci gaba da sallarshi.
Har aka kira sallah asuba Ummi na bacci, Salman ne ya taso ya tayar da ita dan tayi sallah, saida ta tashi zaune tayi addu'ar tashi daga bacci sannan ta kalleshi.
"Malama ki tashi kiyi sallah" yana fad'a ya juya zai fita, yunk'urawa tayi ta tashi amma ina k'afafu sunyi tsami.
_Wayyo Ummi wallahi irin ciwon da naji nima kenan lokacin da na fad'i da moto, saida na zama gurguwa ta kwana uku_
Da sauri tace "yaya Salman dan Allah kaini toilet"
Dawowa yayi ya tsaya yana kallonta kafin yace "haka ake neman taimako cike da bada umarni?"
Turo baki tayi tare da zabga uwar harara ta kau da kai gefe tana wani jijjiga, k'ura mata ido yayi yana jiran yaji ko zata rarrasheshi amma shiru kake ji.
Ummi tunaninta shine ya zatayi ta rarrashi mutum, batasan yanda zatayi ba dan tunda take bata tab'a rarrashi ba idan tana son abu, ita dai idan taga abu tana so koba nata bane to kawai za tace ne abata, idan ba'a bata ba ta fashe da kuka su Hajia Alhaji maman Salman mahaifinta suna kewaye da ita su zasu goyi bayan abata ko sun san ita ce marar gskiyar wannan shine.
Jin fitsari na shirin kubce mata yasa ta saké kallonshi tace "dan Allah haba ka kaini fitsari nake ji fa"
Kallonta kawai yake kamar gunki, kwab'e fuska tayi tace "ni dai inba zaka kaini ba wallahi zanyi shi a nan"
Baisan sanda dariya ta sub'uce masa ba, amma saiya dake yace "to kiyi mana gadonki ne fa ba nawa ba"
Hawaye ne suka fara taho mata tusa hannayenta tayi tsakankanin cinyoyinta tana ta matsewa wai karya fito, saiko taji fitsarin ya fara zubowa, fashewa tayi da kuka tana fad'in "dan Allah ka kaini wallahi zai taho"
Cak ya d'auketa yayi toilet da ita ya aje tsaye, ina yana ajeta fitsarin ya ida tahowa, Salman kam mutuwar tsaye yayi yana kallonta kafin ya fara shek'a dariya har yana rik'e ciki.
Ummi kam ko a jikinta dan inta nuna masa taji kunya to ta shiga uku kenan zai dinga tsokanarta kullum, cikin shagwab'a tace "ni dan Allah ka fita to na gyara jikina"
Da k'yar ya dakata daga dariyar ya nunata da hannu yace "ke yanzu ko kunya bakya ji kamar wata k'aramar yarinya fitsari daga tsaye"
Turo baki tayi tace "to miye a ciki ai laifinka ne, kuma ma da kake cewa bana jin kunya, kunyarka zanji? kaifa yayana ne kuma mijina to miye a ciki dan nayi fitsari gabanka."
Kallon rigarshi yayi yace "dubi kinsa na d'auka ke kin b'atamin riga, yanzu dole saina canja wata." juyawa yayi ya fita yana dariya.
Yana sauyawa ya nufi masallaci zuciyarshi cike da farin ciki, haka kawai yake jin nishad'i, tabbas Ummi ta birgeshi yau data nuna ba wani abu bane dan tayi fitsari daga tsaye kuma a gabanshi, dariya ya saké b'allewa da ita harya isa masallacin.
Ta kasa tsaye da kyau dole ta zauna k'asa tunda dai dama kayanta sun riga sun b'ace, gashi hannu na ciwo ta kasa cire su dole ta zauna zaman jiran Salman, tare da tunanin cire kunya ta rok'eshi ya cire mata kayan, sannan ya mata wanka.
```Irkwai beri```
Yana dawowa ya shigo d'akin ya sameta zaune a toilet, tambayarta yayi "miye haka ke kuma, kina zaune har naje na dawo ba kiyi komai ba?"
Turo baki tayi tace "to ni dan Allah ka ciremin bazan iya ba" ido ya fiddo waje yace "ke d'an aikinki kika mayar dani ko me?"
Langab'e kai tayi tana shirin kuka tace "dan Allah ka ciremin" hararanta yayi yace "ke in zaki tashi kiyi abinda ya dace ki tashi, in kuma ba zaki yiba to ki zauna nan har sarkin zama ya sameki."
Juyawa yayi zai fita Ummi tace "dan Allah yaya Salman, *AGU TIZEDAT*(kayi hak'uri) *WURTU ZILISA*(ba zan saké ba)."
Juyowa yayi yace "iyee, d'iyar Mama kenan wato harda buzanci yau, kin tuna yaren mahaifiya kenan, amma karki manta ni ban iya buzanci ba dama fulatanci ne to da sauk'i ina ji kad'an kad'an"
Yanda tayi kalar tausayi yasa ya shigo toilet d'in ya kama hannunta ya mik'ar da ita tsaye, kallon juna sukayi Ummi kam kawar da kai tayi gefe , zuciyar ta na k'ara tsananta bugawa.
Bayanta ya koma a hankali ya fara zuge zif d'in rigarta, da k'yar ya had'iye wasu yawu da suka tarar masa k'irjinsa kamar zai fito, take hannayensa suka fara kakkarwa kamar mazari, Ummi najin ya sab'ile mata rigar ta zube k'asa ya rage daga ita sai bras da pants, da sauri ta juya tana fuskantarshi amma kanta na kallon k'asa rufe jikinta tayi tace.
"Ya isa haka nagode" kamar jira yake dama saiko fit ya fice daga d'akin gaba d'aya, yana shiga d'akin shi ya fad'a saman gado ruf da ciki idonshi rufe yana sauke numfashi a hankali, tashi yayi ya bud'e drower ya d'auki maganinshi guda d'aya yasha sannan ya shiga wanka.
Ummi kam da k'yar ta samu ta wanke jikinta duk inda ya b'ace, sannan ta fito ta d'auki wata doguwar riga tasa ta zauna tayi sallah, tana idawa bata tashi ba saima tunani data shiga yi.
"Na d'auka kamar yanda nayi fitsari gabanshi ba tare da na ji nauyi ba, na zata haka zan iya jarumtar fiskantarshi ya ciremin kayana sannan yamin wanka ya saké min kaya, ashe ba haka abin yake ba, yana da wuya ka iya jarumtar tsayawa wani ya kalli tsiraicinka ba tare da baka ji wani abu ba."
Ganin safiya tayi yasa ta tashi da k'yar ta dinga d'ogala k'afafu haka ta kai kanta falo amma fa anci wuya.
_ALLAH YA BADA LAFIYA_
05/03/2019 à 17:31 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑
_Samira Harouna_
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
*Page*
6⃣3⃣-6⃣4⃣
Salman ne ya fito cikin k'ananan kaya farar riga mai dogayen hannu sai bak'in wando, yayi kyau sosai tsaf Ummi ta k'are masa kallo cike da birgewa.
Ganin yanda yake kallonta shima yasa tace " *WAYIWAN NEDIS*(ina kwana)"
Kallonta yayi sosai kafin yace "amma ai na fad'a maki bana jin buzanci ko, gwara kimin fulatanci ko indianci sunfi sauk'i"
Kallon rainin hankali ta masa kafin ta girgiza kai tace "Ok *EN VETII JAMNA*(antashi lafiya)?"
Kallonta yayi saidai baiyi mamakin jin fulatanci daga bakinta ba, domin kuwa yasha samun su ita da Mama tana koya mata, murmushi ya mata yace " *NOI CHOMRII*(ya gajiya)?"
Shiru tayi dan kuwa ta manta sauran darusan da Mama ta koya mata, maida hankalinta tayi ga tv tana kallo, ganin ba zata amsa ba yasa ya kalli tv ya kalleta yace " sai son kallon india amma baki jin mai suke fad'a"
Harya wuce yaji tace " *KAISE HO TUM*(ya kake)?"
Dawowa yayi kusa da ita yace" *HUM THEEK HOON*(lafiya lau nake), *AUR TUM*(ke fa)?"
" *HUM BILKUL THEEK HOON*"
Dariya yayi yace "lallai ba laifi, inaga zanje dake india idan na tashi tafiya" da sauri ta dafe mararta tare da cije leb'e tace "wayyo mara ta ciwo take"
Matsowa yayi kusa da ita yace "ya dai miyake damunki?" wani kallo ta masa tace "ba komai" tab'e baki yayi ya ficewarsa daga gidan, haka ciwon ya fara takura ta amma ta daure.
Salman na fita gida ya nufa dan Mama tace yaje ya karb'o masu abinci, yana shiga Mama ce kad'ai zaune a falo, da sallama ya shigo ya zauna yana fad'in "Mama ku kad'ai zaune?"
Saida tayi hamma sannan tace "wallahi ni kad'ai duk sun tafi makaranta"
"Ok ina kwana?"
"Lafiya lau, antashi lafiya?"
"Lafiya lau Mama, ya gida ya gajiya?"
"Ba gajiya, ya d'iyata da jikin kuma, ina fata dai da sauk'i?"
"Um da sauk'i Mama tana nan lafiya"
Kallonshi tayi da kyau tace "ina fatan dai kana kula da ita baka mata cutar nan daka saba ko?" dariya yayi yace "Mama kenan aini bana dukanta idan bâ laifi tamin ba, ku kuma baku ganin laifinta, shiyasa kullum kuke ganin nine mai laifi ba ita ba."
"Hmm, kaidai ka saba da narkarta kawai ko babu laifin fari bana bak'i kana jin dad'in dukanta."
Jingina yayi a kujeran kamar zai kwanta yace "to Mama yanzu ai na bari tunda ita ma ta rage tunda babu k'afafu da hannu d'aya"
Waro ido Mama tayi tace "aw kenan ciwon data ji kad'ai yasa ka daina dukanta? shiyasa taji dad'in zamanta gidan Khamis."
"A'a Mama ba haka nake nufi ba, nasan dai yanzu zata rage tsokana tunda ta samu rauni, ba zata iya jan fad'a ta ruga a guje ba."
Tab'e baki Maman tayi lokacin data mik'e tsaye tana fad'in "kaidai kasani kaci gaba da dukanta tana matarka, akwai ranar horo ko kuma idan ka mata bugun da zai b'aran mata da ciki, ai kaga saika huta."
Da k'arfi ya d'ago daga zaman da yayi cikin d'aga murya yace "ciki Mama, tace maki tana dashi?"
Juyowa Mama tayi tace "saita fad'amin tana da, bayan rashin lafiyar da Jawahir tace tayi ta kwana biyu harda su amai."
Shigewa tayi danta d'auko mashi abinci, shi kam shiru yayi gaba d'aya tunaninshi ya tafi akan abinda Mamar ta fad'a, harta fito ta aje masa kwanukan guda biyu bai masan ta aje ba.
Zaune Mama tayi tana kallonshi, gyara zamansa yayi yana kallon Mama yace "Mama wai da gaske yarinyar nan ciki ne da ita?"
Tsaki Mama tayi tace "kaji wani rainin wayo, tana matarka amma bakasan tana da ciki ba duk da rashin lafiyar da tayi, kodan baka nan?"
Cikin mamaki yace "amma Mama aini na d'auka wannan rashin lafiyar saboda wata matsala ce dake damunta, amai kuma saboda taci abincin da yafi k'arfinta ne shiyasa ta aman.?"
Hararanshi tayi dan ita a ganinta yana so ya b'oyene saboda baya so a sani ko kuma kunya, cewa tayi "wace irin damuwa ce zata ja mata rashin lafiya, kuma dan anci abinci mai yawa sai ayi amai.?"
To ganin Mama tak'i yarda ta fahimceshi yasa yace "Mama wai kun duba kayan nan kuwa?"
"E na duba naga sunyi sosai, saura kud'in d'inkin kayan ko?"
"To Mama nawa ya dace a saka kenan?"
"To ai basai na fad'a maka ba, babu wanda ya kaika samun mata a b'agas, tunda gashi za'a kai mata Lefe tana d'auke da juna biyu, aiko kaga kai dan baiwa ne, dan haka tuwon girma miyarsa nama kayi bajinta kawai."
Cike da damuwa ya kalli Mama yace "Mamaa, bana so kina cewa tana da cikin nan, ba tada komai fa"
Tab'e baki tayi tace "kaidai kasa ni, ni dai ka hanzarta kawo kud'in dan a samu akai kayan da wuri"
Mik'ewa yayi yasa hannu a cikin aljihu ya ciro kud'i masu yawa ya bawa Mama, karb'a tayi tana kallon kud'in kafin tace "wannan kud'in haka har nawa ne?"
Dariya yayi yace "Mama kuda gasunan a hannunku, ku irga mana"
"Kai bazan iya ba, idan ma na fara ba'cewa zanyi ka fad'amin kawai"
" Mama kenan, to d'ari biyar ne (500.000F CFA)"
Baki Mama ta washe tace "kai amma naji dad'i, yanzu ka tabbatarmin da kai mai yaba kyauta ne, gaskiya naji dad'i Allah ya maku albarka, Allah ya albarkaci aurenku, Allah ya bata lafiya ya rabata da abinda yake cikinta lafiya."
Ganin Mama tak'i fahimtarshi yasa sukayi sallama a haka, ya d'auki abinci ya kama hanyar gida zuciyarshi cike da wasi-wasi.
Yana zuwa da kanshi ya zuba mata abinci a plate ya mik'a mata tare da zaunawa kusa ita yana k'are mata kallo, wai mai ciki "to cikin wa?" ya tambayi kanshi.
Ummi kam dan danan ta cije leb'e saboda ciwon da mararta keyi, saida ta malmalo lomar fankasu daya sha jar miya zata kai bakinta, cak ta tsaya tare da kallon Salman.
Tunawa tayi jiya yace yana jin yunwa da Hajia tace ya d'auketa, kuma a iya saninta bata ga sanda yaci wani abu ba da idonta, dan haka ta mik'a masa plate d'in tace "ci"
Cike da mamakin abinda tayi ya girgiza mata kai yace "kici kawai"
Shagwab'ewa tayi tace "dan Allah kaci nasan kana jin yunwa, tun jiya baka ci komai ba."
Kallonta kawai yake kafin yace "ki fara ci, idan kin ida zanci"
Kai ta girgiza masa tace "bazan iya ciba yaya Salman"
Idonshi akan tv yace "parce que (saboda)?"
A ranta kam cewa tayi "saboda kana jin yunwa" amma a fili sai tace "saboda bazan iya ci ba alhalin kai baka ci ba."
K'yar idon Salman a kanta kamar zai had'iyeta, mamakin furcinta yake sosai da k'yar yace "Ummi miyasa kika damu da sai naci, bayan kema nasan kina buk'atarsa.?"
Shiru tayi tana tunani, ba zata iya fad'a masa haka kawai taji tana so ya fara cika cikinsa kafin ita ba, a hankali ta d'ora hannunta akan mararta tana matse fuska, karb'a yayi ya yanko loma mai kyau, a hankali ya nufi bakin Ummi da ita tare da cewa "haa."
Bud'a baki tayi ya saka mata, kallon junansu kawai suke, Salman ya had'a ido da ita ne saboda yana so ya gano wani abu a tare da ita, kallon ne yayi yawa yasa Ummi k'asa da idonta, amma duk da haka bai bar bata abincin ba shima kuma yana sawa nashi bakin, haka har suka gama.
Suna idawa ya maida kwanukan ya aje ya d'auko mata madara daga nan zaune tana kurb'a, shi kuma ya fita ya bar gidan zuciyar shi nata tunanin juna biyun da Mama ta fad'a masa wai Ummi tana da.
Gidan Ummi ko kad'an bai tsagaita ba saboda tururuwar da 'yan uwa suka dinga yi a gidan kamar ana biki, Ummi tsabar farin ciki kamar ta k'urma ihu, bayan hana 'yan uwanta da Alhaji yayi zuwa gidanta, yau gashi dangi sun cika gidanta saboda zuwa ganinta.
Sai misalin 22:30 kad'ai gidan yayi shiru ya rage Ummi kad'ai a gidan, sai lokacin ta fara jin ciwon mararta yana dad'a taso mata, haka tayi ta murk'ususu har bacci ya d'auketa daga nan kan kujera.
23:40 Salman ya shigo gidan, saida ya k'are mata kallo daga sama har k'asa, durk'usawa yayi yana kallon cikinta daya lafe a mararta, tsintar kansa yayi yana murmushi kafin ya mik'e tsaye yana fad'in "ta yaya za ace akwai ajiyar yaro anan wurin, bayan a shafe yake."
Tsaf ya d'auketa ya direta akan gado tare da ja mata zanin rufa, sannan ya tofeta da addu'a ya shafa kanta yace "saida safe".kamar tana jinshi.
Ciwon mara ne ya tayar da Ummi daga bacci, yarfa hannu kawai take gashi ba lafiya bare ta samu damar murk'usawa da kyau, haka ta dinga cizar leb'e har taji Salman na k'ok'arin shigowa d'akin, da sauri ta kwanta ta rufe ido kamar mai bacci.
Kallo d'aya Salman ya mata ya gane idonta biyu, dan daga yanda take sauke numfashinta da sauri sauri,tsaye yayi a kanta yace " tashi ko malama"
Da k'yar ta tashi ba tare data kalleshi ba, zaune yayi kusa da k'afafunta yace "miyake damunki wai"
Ko kad'an ba zata iya fad'a masa tana ciwon marar jinin al'ada bane, dan haka tace "ciwona ne kemin ciwo"
Kallonta yayi kamar mai son gano wani abu a tare da ita, ajiyar zuciya ya sauké yace "kinsha maganinki?"
"Bansha na dare ba gaskiya"
Harara ya dalla mata yace "zan d'auko maki yanzu kisha, amma wallahi idan kika k'isha to ranki zai mugun b'aci a daren nan." fita yayi falo ya d'auko ledar magungunan tare da ruwa.
B'allowa yayi ya mik'a mata, karb'a tayi ta rik'e a hannu tana shirin kuka, zaro ido yayi yace "wallahi zanci gidanku kinji na fad'a maki"
Turo baki tayi tana kunkuni haka ta jefa maganin a cikin baki ta kora da ruwa, ganin tasha yasa ya mik'e zai fita daga d'akin, motsa k'afafunta tayi amma taji su gam kamar ba'a jikinta suke ba, da sauri tace,
"Yallab'ai" cak ya tsaya ya juyo yana fad'i a ransa "wato akwai abinda kike so shiyasa na samu wannan sunan."
Kar kace kai tayi tace "dan Allah taimako nake nema?"
Ba murmushi a fuskar nan yace "ina jinki"
Da hannu ta masa alama da drower tace "dan Allah ka mik'o min coton a ciki"
Saida ya gama hararanta sannan ya nufi drower ya bud'e, coton Vania ya gani dan haka ya d'auko ya nuna mata tare da fad'in "wannan kike nufi?"
D'aga masa kai tayi alamar eh, k'arasowa yayi yace "yanzu kema kinfi so kiyi anfani da wannan, a maimakon kiyi anfani da abinda zaki wanke da hannayenki bayan kin kammala saboda k'iwa ko?"
"Shin ko kinsan darajar wannan jinin, Allah ne fa ya halinceku dashi saboda dacewarku dashi d'in, yafi daraja da mutunci mace tasa hannayenta tâ wanke da kanta, duk da yana k'azanta amma kuma ta wani b'angare cuta kuke fitarwa, sannan shed'anun aljanu suna samun damar sauk'in shiga jikinki a lokacin da kuka jefar dashi cikin shara dama duk wani mai son cutar daku ta hanyar samun jinin hailarku."
Girgiza kai tayi tace "a'a yaya Salman wallahi bana aiki dashi haka kawai, sai inhar zan fita unguwa saboda gudun kar jikina ya b'ace ban sani ba da kuma canzawa idan buk'atar hakan ta tashi,dan shi d'in yafi k'yale wani lokacin, amma tun lokacin dana fara Mama ta fad'amin komai akanshi,harma da mahimmancin wankewa da hannuna."
Ya gamsu da maganarta sosai dan haka ya bud'e ya ciro d'aya ya mik'a mata, tana karb'a yace "yaushe bak'on naki yazo?"
Baki bud'e ta kalleshi kafin ta kawar da kanta gefe, jin tayi shiru yasa yace "dake fa nake magana?"
Ba tare data kalleshi ba tace "yanzu"
Juyawa yayi danya mayar da coton d'in yace "yaushe zai tafi?"
Dam!taji gabanta ya fad'i, a ranta kuma cewa tayi "wannan jaraba har yaushe da irin ta, ko