Showing 51001 words to 54000 words out of 72709 words

Chapter 18 - AUREN HADI COMPLETE DOCUMENT WRITING Samira Haruna.txt

da alkairinsa, Allah ya baki juriya da hak'urin zama dani, ni kuma Allah ya bani ikon kyautata maki, Allah ya bani ikon saka ki farin ciki har k'arshen rayuwata, hakane kawai zaisa na saka maki da alkairin da kika min."




Ya kasa tashi daga wurin dan gani yake kamar wani abu zai sameta idan ya gusa, a hankali Ummi ta fara motsawa tana san tashi, b'angaren da take ya dawo tare da k'ura mata ido yana jiran ta bud'e nata idon, ido ta bud'e ta sauke su akan Salman hakan yasa taji kunya taja zanin rufar ta rufe fuskarta.


Zaune yayi tare da fad'in " ki bud'a fuskar mana, na jima ina jiran naga tashinki, dan naga yanda jikin naki yake fa."


Hannu yasa ya janye bargon yana sakar mata murmushi, tana ganin haka ta yunk'ura danta tashi, wani irin bala'i ne taji da gaba d'aya jikinta k'asanta kam kamar ta kama ruwa da yaji haka take ji.


Cike da rad'ad'i ta rik'e hannunshi sosai tare da matse fuska take wasu k'walla suka zubo mata, hannayenshi ya kai da nufin ya gyara mata zama zafi yaji a jikinta mai matuk'ar zafi sosai, gyara mata zaman yayi ya koma ya zauna yana kallon fuskarta, k'asa tayi da kanta yayin da take addu'a ya tashi ya fita dan ta koma ta kwanta dan zaman ba dad'i, hannayenta ya kamo duka biyu yace,


" *ZEINAB* kiyi hak'uri ki yafe..."da sauri Ummi ta rufe masa baki da hannunta, kai kawai ta girgiza dan ba zata iya magana ba ko tayi ma ba zai ji ba, kallon idonta yayi ya d'oke hannunta yace,


"A'a Ummi, ki barni na saka maki albarka tare da nuna maki tsantsan farin cikina idan ba zaki bari na nemi yafiyarki ba."


Ci gaba yayi da fad'in "ZEINAB, INA SONKI SO MAI TSANANI, SON DA BA ZAN IYA RAYUWA BABU KE BA."


"Ummi kin zama silar sauyawar rayuwata, kin sabinta min ita ta hanyar da banyi tunani ba, ko kad'an ban tab'a tunanin kece wacce zata kawo wannan sauyin a rayuwata ba, Ummi na san ni mugu ne a idonki kuma azzalumi, amma duk da haka baki hanani kanki ba a gaskiya na gode maki sosai."


Ganin hawaye na zarya a fuskarta yasa Salman rud'ewa ya fara goge mata da hannunshi yana fad'in "kiyi hak'uri idan na fad'i wani abu da bai maki dad'i ba, Ummi bana san ganin hawayenki ko kad'an saboda suna tab'amin zuciya sosai."


Tashi yayi tare da fad'in "bari na kawo maki tea kisha kafin na samo maki abinda zaki ci kisha magani, dan naji jikinki da zafi."


Yana fad'a ya fita ya barta, yana fita Ummi ta fara k'ok'arin saukowa daga gadon dan tayi fitsari ta dawo ta kwanta, ansha daga kafin ta iya sauko da k'afafunta tana sauke numfashin wahala, Salman ne ya sake shigowa d'akin dan ya tambayeta ko zata iya cin indomie ya dafa mata.


Tsaye yayi yana kallonta ganin ta kasa tashi yasa ya k'araso yana fad'in "bari na taimaka maki tunda naga kin kasa."


Hannu ta d'aga masa alamar ya barshi, kallonta yayi yace "bari na taimaka maki mana, ko zaki iya ne?"


Kai ta d'aga masa alamar Eh, d'aga kafad'a yayi yace "ok, zaki ci indomie na d'ora maki."


Dariya ce ta sub'uce mata har tana nunashi da hannu, cikin dakusashiyar muryarta tace "wai kaine zaka dafa indomie naci?"


Kallon mamaki ya bita dashi kafin yace "me kike nufi to, ban iya ba? to ni tun kafin a haifeki nake dafa abinci."


Kai kawai ta girgiza masa dan ita kad'ai ta san me take ji, juyawa yayi zai fita tace "yaya dan Allah ka kawo min madara."


Tsaye yayi yana kallonta kafin yace "kenan ba zaki daina shan madarar nan ba ko?"


Bud'a baki tayi tace "rayuwata ce fa, me yasa zan daina lokaci d'aya haka?"


"Saboda kin zama babbar mace."yana fad'a ya bar d'akin, binshi tayi da kallo kafin ta tab'e baki dan bata gane komai ba.


Cije leb'en k'asa tayi ta rufe ido haka ta dogara ta tashi da k'arfi har takai kanta toilet d'in, saida ta k'ara saka wasu ruwan zafin sannan ta kama ruwa dasu tare da yin wanka tayo alwala sannan ta fito, sallaya ta shinfid'a ta d'auko doguwar rigar Salman ruwan k'asa ta saka.


Zaune tayi bakin gado tana sauke numfashi dan kwance kawai take so tayi, Salman ne ya shigo da plate d'in indomie da robar madara da ruwa a hannunshi, ajewa yayi gefe ya kalleta yace " da alama kin fara cin gadona tun yanzu, ina fatan dai kinyi sallah?"


Cike da shagwab'a ta turo baki tace "kai nake jira ka d'auko min hijab, tunda kai ma ka ci gadon k'afafuna."


Dariya ya tin tsire da ita har ya fita daga d'akin yana dariya, yana kawo mata ta saka ta kabbara sallah a daddafe, tana sallamewa tabi lafiyar sallaya ta kwanta dan ko kad'an zaman babu dad'i, Salman daya fito daga wanka ne ya kalleta yace "malama tashi kici abincin mana, idan kin ida kya fad'amin me kika ji."


Da sauri ta d'ago kai ta kalleshi tana fad'in "na fad'a maka me?"


Juyowa yayi ya kalleta yace "karki damu, ina nufin ki fad'amin ya kika ji abincin."


Ajiyar zuciya ta sauke tare da sake komawa ta kwanta, har saida ya shirya cikin wata dalleliyar shadda (couleur préféré) d'inshi bleue sai walk'iya take kai dagani ka san ansha kud'i wajen, ga hula da takalma da agogo ta fata duka kalar d'inkin rigar bak'ak'e, wani irin shek'i ne fuskarshi keyi kamar sabon wata dan sha hud'u, bayan k'yali da fuskarshi keyi ga tsantsar kyanshi daya k'ara fitowa fili, k'amshi kawai yake zubawa na had'add'en turarenshi DOLBY, sak ya fito angonshi.


Da kanshi ya zo ya bata abincin sannan taci tasha madara ya bata magani tasha, saida yasha rarrashi kafin ta yarda tasha maganin.


Kwance ta sake komawa yana kallonta yace "anya kuwa Ummi zaki kai yamma, ko dai na d'auko wuka na k'arasa ki kafin ki min musai."


Sai dai ba tayi magana sai ko amai ya sub'uce mata, sosai tayi amai dan saida ta maido duk abinda taci, hankalin Salman ya tashi sosai duk ya rud'e ya rasa ya zaiyi, yana gyara mata jikinta d'auke sallaya ya wanke ya shanya ya dawo wajenta ya zauna yana kallonta.


"Ummi bari na d'auko maki kaya ki canja sai muje asibiti a duba min ke, dan watak'ila har na samu k'aruwar yaro ko yarinya."


Kunya ce ta rufeta ta fad'a jikinshi tana dukan k'irjinshi, zameta yayi daga jikinshi yace "ina zuwa."


Riga da zane ya d'auko mata simple d'inki ba kwalliya sosai, saida ya canja mata kaya kawai ta dage ita babu in da zata je kawai taje a mata tonon asiri sai kowa ya san me ya faru.


Dole ya sake bata paracétamol tasha bayan tasha madara dan cikinta babu komai, komawa tayi ta kwanta ya rufeta da bargo ba jimawa bacci ya sake d'aukarta, ya jima yana kallon fuskarta gaba d'aya sai yaga yau tafi masa kyau akan kullum, wani shek'in amarci take ita kanta, falo ya dawo ya zauna dan dama ita yama kwalliyar kallo ya fara cike da farin ciki murmushi ya kasa barin fuskarshi dan har yanzu yana taro daren jiya, daren daya fi kowane dare a wurinshi daren da ba zai tab'a mantawa dashi ba, ajiyar zuciya ya sauke fuskarshi d'auke da k'asaitaccen murshi yace,


"Ummi ba dai zafi ba."


_Hum wai zafi._😏😏😏
25/03/2019 à 16:14 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑


_Samira Harouna_




~ALLAH YA BARMU DA MASU SON MU~




🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛


*Page*


8⃣7⃣-8⃣8⃣






Har sallah azahar Ummi na bacci saida Salman ya dawo daga masallaci ya tasheta tayi sallah, tana kammalawa ta fito falo da tafiya kamar mai koyo tana zuwa ta zauna k'asa kusan k'afafun Salman, saukowa yayi ya zauna kusa da ita yana fad'in "aljannata ya jikin naki?"


Kallonshi tayi da mamaki tace "aljannarka kuma, yanzu kenan na tashi daga aljana na koma aljannarka?"


Gira ya d'aga mata yace "in dai har Ubangiji yana bamu aljanna a duniyar nan, to ni kece aljannata."


Had'a kanta tayi da gwiwa tana murmushi, yana ganin haka ya fara mata cakulkuli yana fad'in "tunda ba zaki fad'a ba sai mu sake komawa ciki."


Ummi kam dariya take tana bille bille duk ta hayeshi, saida yaga hawaye sun fara fitowa a idonta tsabar dariya sannan ya daina, ba tare data tashi daga jikinshi ba ta gyara kwanciyarta ta yanda suke kallon juna tace "nifa yunwa nake ji."


Wani kallon so ya mata yace "na sani dama dole zaki ji yunwa, amma kiyi hak'uri na kira Mama na fad'a mata kuma yanzu zata aiko maki da abinci."


Cikin yaushi ta kalleshi tace "yanzu fad'awa Mama kayi?"


"A'a, na dai fad'a mata ba kiyi d'ori ba tasa dake a nasu."


Kallonshi tayi tace "yaya Salman na d'auka fita kayi duk kasa hankalina ya kasa kwanciya."


Cike da mamaki yace "me yasa?"


"To ai naga kayi kwalliya ne dayawa, kuma naga ko a aurenmu ba kayi irinta ba."


Dariya yayi yana kallon fuskarta yace "kwalliya fa,to kenan kwalliyarce ta d'aga maki hankali?"


"Yaya Salman ina jin baka duba madubi ba bane shi yasa, kai kyakyawane kuma yau naga kafi kullum kyau, kaga dole hankalina ya tashi dan ban san da suwa zaka had'u ba."


"Wai mata kike nufi?"


Turo baki tayi tace "Eh mana."


Gashinta ya fara shafawa yana fad'in "da a jiya kika fad'i haka kafin dare, to da saina yarda, amma yanzu ni Salman na Ummi ne ita kad'ai babu k'ari."


Murmushi tayi sosai hakan yasa ya saka d'an yatsarshi a kurmin kumatunta yana kallonta cewa tayi "amma fa yaya Salman kai kace zaka k'ara aure."


"Eh, a dah kenan, amma banda yanzu da Ummi ta zama ta Salman suka had'u suka zama manyan yara."


Dariya tayi tace "ni dama babbar yarinya ce."


"Da gaske, to shikenan zamu gani."


Cikin shagwab'a tace "yaya Salman da gaske ba zaka k'ara aure ba?"


Murmushi yayi yace "ba zan k"ara in dai kina tare dani."


Tashi tayi zaune ta tara mashi tafin hannunta tace "ka rantse ba zaka k'ara ba."


Fashewa yayi da dariya ya janyota jikinshi ya had'e kanta da k'irjinshi yace "Allah ya shirya min ke."


Tashi tayi daga jikinshi tace "yaya Salman wallahi da gaske nake, in san samuna ne na zauna da kai ni kad'ai, wallahi ba zan juri ganinka da wata mace ba."


Tsaida dariyar sa yayi ya sauke ajiyar zuciya, tabbas ya fahimci da gaske take kuma ga dukkan alama Ummi zata iya yin komai dan taga ta sameshi ita kad'ai.


Ganin baiyi magana yasa Ummi tace "yaya Salman dan Allah kamin alk'awarin zama dani ni kad'ai, idan kamin haka ni kuma zan zama kamar baiwa a gareka, ba zan tab'a gajiyawa da hidimarka ba insha Allah."


Fashewa tayi da kuka, dan yanzu kam yanda take jin Salman a cikin zuciyarta ba kamar kullum ba, zuciyarta ta gama tunbatsa da soyayyarshi, sake kwantar da ita yayi a k'irjinshi yana fad'in,


"Kiyi hak'uri Ummi, ki daina kuka bana san ganin hawayenki, kuma in dai akan maganar k'arin aurena ne yasa kike kuka, to ki kwantar da hankalinki dama wasa nake maki babu wani auren da zanyi yanzu, ke kad'ai kin isheni rayuwa."


Cikin kuka tace "da gaske?"


"Da gaske nake Ummi, kece kika sabinta min rayuwata, burina yanzu shine na samar da farin ciki a rayuwarki kamar yanda kika sani farin ciki nima."


"In ko hakane yaya Salman, to kasa a ranka cewa daga yanzu farin ciki shine abokin rayuwarka, bak'in ciki kuma sai dai kaji a wani wuri, in dai ina raye babu kai babu shiga kunci da yardar Allah."


D'agata yayi daga jikinshi ya d'ora hannayenshi a kumatunta suna kallon juna, murmushi ya sakar mata yace "zanyi iya bakin k'ok'arina wajen ganin na samar da farin ciki a tare dake, Ummi ki zauna tare dani, nima zan zauna tare dake tare da killaceki anan har k'arshen rayuwata." ya fad'a tare da d'ora hannunshi a k'irjinshi b'angaren da zuciyarshi take.


K'ayataccen murmushi ta sakar masa tare da had'e hannayensu waje d'aya tace "insha Allah, zan zauna da kai har abada, zamu rayu tare cikin so da k'aunar juna, tunda har kamin alk'awarin zama dani ni kad'ai."


Kallon mamaki ya mata kafin yace "aljannata, nifa ban maki alk'awarin zama dake ke kad'ai ba, amma fatana da burina shine na zauna dake ke kad'ai, alk'awari wani muhimmin abune wanda idan kayishi yana buk'atar ka cikashi ko dan kiyaye imaninka, Ummi ban san rayuwar da Allah ya tsaramin ba anan gaba."


"Ummi mun tashi a babban family, wanda ya had'a mutane iri iri muna ganin masu mata sama da d'aya, mafi wayancinsu basa cikin farin ciki sai tashin hankali, amma ana b'oyewa saboda gudun b'acin ran Alhaji."


"Ummi bana fata nayi rayuwa irin ta iyayena, ban san ko kin tab'a fahimtar zamansu ba?amma basa farin ciki da junansu, tunda na fara mallakar hankalin kaina na fahimci haka duk da suna b'oyewa kar a fahimta, Ummi duk tsawon lokacin nan da suka d'auka wallahi har yanzu basa k'aunar junansu musamman ma Mama, na tabbata rabone ya kawomu duniya amma kamar yanda Mama bata son mahaifinmu haka ma bata k'aunarmu kamar yanda kowace uwa ke k'aunar nata 'ya'yan, na san dole akwai soyayya ta tsakanin uwa da 'ya'ya amma dai nuna mana ita ko kad'an ba tayi, wannan ne yasa na fahimci matsalar dake cikin *AUREN HA'DI*.


"Zan godewa Allah da yasa abinda nake tunanin ba zai yiwuba ya yiwu, ko a mafarki ban tab'a tunanin zamu so junanmu ba, amma gashi iko na ubangiji yasa mun zama d'aya kuma masu k'aunar junansu, Ummi a kullum ina ji ina ma ace La Mama ita ce mahaifiya saboda uwace da kowane d'a zaiyi burin mallakarta a matsayin uwa saboda jajircewarta akan tarbiyar yaranta."


"Soyayyar da take nuna min tana sani farin ciki, kamar yanda kema kinfi jin dad'in zama da mahaifiyata da haka nake mana fatan farin ciki mai d'orewa tare da iyayenmu, Allah kuma ya bamu jikan da zasu soshi fiye damu, akan k'ara aurena kuma ki kwantar da hankalinki bani ba wata."


Rumgume juna sukayi sosai kamar zasu had'e waje d'aya, Ummi ce tace "hakane yaya Salman, ina jin dadin zaman gidanku saboda a waccen lokacin tunanina shine mahaifiyata bata sona, a gidanku kad'ai nake samun hutu amma a gidanmu, kamar baiwa La Mama take mai dani bana baccin safe saboda dafa abincin kari, bana baccin rana saboda sarrafa na rana idan kuma na gama ba zan kwanta ba tace yana saka ragwanci, saina tabbatar na aje komai a in da ya dace kafin na kwanta baccin dare, bayan kankanin lokaci zata tashemu sallah dare duk wannan lokacin gani nake tana takura mana ne, kullum hirar mu da ita bai wuce yanda za muyi ba idan munyi aure kullum maganarta dai miji miji, gani nake kawai tana so mu zama kamar bayin mazane ashe ba haka bane gatane take nuna mana wadda uwace kad'ai take nunawa yaranta shi."


Kallonta yayi yana shafar fuskarta yace "La Mama akwai tsanani, amma kuma tana yinshi ne dan saboda taga kun zama mutane na gari, ni kaina baki ga yanda take min fad'a ba idan nayi ba daidai ba?"


K'ara matseshi tayi tace "gaskiya ne, nima yanzu na gane komai soyayyace tasa take mana haka."


K'aran bubbuga k'ofa suka ji, dan haka Salman ya kalleta yace "gimbiyata, ko zaki iya yimin izini naje naga ko waye?"


Cikin shagwab'a tace "to waye yazo da yake neman rage min jin dad'i?"


"Umm, ina jin mai kawo abincin ne yazo, amma kiyi hak'uri ai yanzu zan dawo ba dad'ewa zanyi ba, idan na dawo kinga ko goyaki sai nayi."


Cikin kasala ta tashi shi kuma ya fita, har ta zauna ta koma ta kwanta dan har yanzu tana jin zafi a k'asanta sosai, bai jima ba ya dawo d'auke da kulolin abinci guda biyu, yana zuwa ya aje ya nufi cuisine ya d'auko plate da cuillère tare da ruwa da jus da kuma madara domin Ummi.


Zuba masu yayi shinkafa da miyar naman rago, sosai Ummi taji dad'in abincin haka suka ci suka k'oshi, haka suka ci gaba da hira abinsu kai kace Ummi da Salman sun jima suna soyayya, shagwab'a kawai take zubawa san ranta yayin da Salman keta biye mata yana rarrashi koma kamar k'aramin yaro, haka ya wuni gida masallaci kad'ai ke fitar dashi waje yana idawa zai dawo gida su ci gaba daga in da suka tsaya.




Haka suka kwana mak'ale da juna kamar za'a rabasu duk da Ummi tana jin kunyarshi har yanzu bata iya had'a ido dashi, Ummi ta yarda su kwanta tare ne saboda yace mata babu abinda zai faru, dan har yanzu tana jin ciwo zata so ya barta har taji sauk'i sosai in yaso aci gaba, shi kam yayi ta mazane ya daure amma ko yanzu aka ce dashi ya k'ara k'arawa zaiyi da gudu, dan har yanzu yana tuna daren jiya.


*DAREN JIYA* manya sunan wani film ne.🤣
25/03/2019 à 16:14 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑


_Samira Harouna_




🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛


*Page*


8⃣9⃣-9⃣0⃣




A hankali Salman ya bud'a idonshi ya sauke a b'angaren da Ummi ke kwance, ganin bata nan yasa ya tashi zaune saida ya wartsake kafin ya sauko daga kan gadon yana jinshi kamar wani sarki, toilet ya fad'a dan yin wanka dan yasan Ummi watak'ila tana aiki ne.


Tsaf ya shirya cikin wata had'ad'iyar shadda maroon, sosai kayan suka masa kyau sai dai bai d'ora hula ba wannan karin, fitowa yayi daga d'akin sai dai babu Ummi a falo amma kuma yasha gyara sai k'amshin turaren wuta yake had'e da airfreshner, saida ya k'are kallon falon kafin ya shiga d'akin Ummi nan ma bata nan sai gyaran d'akin da tayi, fitowa yayi da nufin ya shiga cuisine, turus ya tsaya yana kallon Ummi dake aje wasu manya plate a dinning.


Ba wannan ne ya tafi dashi ba illa kayan dake jikinta, kayan da akafi sanin buzaye ne dasu colour ja daya k'ona sosai kamar jinin kare masu kwalliya sosai rigar iya gwiwa da zaninta bak'i, duk da kayan manya ne bai hana su fito mata da surarta ba, d'aurin d'an kwali simple tayi ta maida jelarshi saman wuyanta b'angaren dama, sakin gashinta tayi ya bazu a bayanta sai mak-eup da tasha sosai dan dama gwana ce wajen iya kwalliya kawai dai bata son yine, sai dogayan takalmin data saka bak'ak'e.


Haka ya k'araso in da take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login