Showing 72001 words to 72709 words out of 72709 words

Chapter 25 - AUREN HADI COMPLETE DOCUMENT WRITING Samira Haruna.txt

kafirci."


Da gudu na bar d'akin, har na fita kuma na tuna da sak'on MY HEENAT hakan yasa dole na kuma bud'e k'ofar d'akin a hankali na lek'o kaina ina fad'in "dan Allah yaya Salman minti biyu?"


Cike da k'osawa Salman ya kalleni yace "oh my gosh, na rasa yanda zanyi da yarinyar nan, to miye kuma yanzun?"


Saida na tattare siket d'ina sannan na fara masa bayani cikin sauri "dama my heenat ce tace wai na fad'a maka akwai k'annenta, idan kana son d'aya daga ciki zaka iya yin magana saita had'aka da d'aya daga cikinsu."


Remonte d'in dake aje gefe naga ya d'auka tun kafin ya jefo min na bar d'akin @360, gudu nayi sosai har saida na bar unguwar na tsaya ina sauke numfashi cikin zuciyata kuma ina fad'in "my heenat da nasan haka sak'onki zai zama, da ban fad'i ba."


Sai lokacin na lura ban d'auko takalmana ba, amma dai nace ma chΓ©rie da Maman dady suzo su d"auko min, danni da gidan Salman sai kuma haihuwa ta biyu idan Ummi tayi.


Ashe ina fitowa Ummi ta kalli Salman tace "haba babban mutum, aunty Sam d'in kama haka, kasan itama fa tana da masoya wallahi zamu ji ba dad'i fa idan ta fad'a masu."


Cikin wani yanayi yace "gobe zanje na bata hak'uri, shikenan hakan ya maki?"


"Idan ma baku jeba ni zanje na bata hak'uri."


Hancinta ya kama yace "amma bada izini na zaki jeba."


Hararanshi tayi sama da k'asa cikin dariya tace "to waya fad'a maku dama ina neman izininku idan ina san fita."


Dariya yayi dan ya fahimci ta tuna dah ne, a lokacin da ta nemi izinin fita ya hanata har tayi hatsari, cewa yayi "in ko ki kaje to zaki rasa ido ko k'afa."


Cikin dariya tace "idan ma na rasa ai kune za kuyi jinyata."


Kafad'a ya d'aga yace "um um, ba zanyi ba wannan karin, za kiji da kanki ne"


Dariya tayi tace "dole zakuyi kodan gudun kar na maku fitsari akan kago."


Fashewa yayi da dariya yace "ai a gadonki zakiyi jinyar ba a nawa ba."


Cikin kunne ta rad'a masa "amma ai kunfi jin dad'in bacci akan gadona."


Kallonta yayi yace "kuma fa hakane yarinyata."


Hararan wasa ta masa tace "wacece yarinyar?"


Hannu ya d'aga mata yace "afuwan, to 'yan matana."


Duka ta kai mashi a k'irji lokaci d'aya kuma ta rumgumeshi tare da fad'in "shashasha na kenan, ina sonku sosai."


Shima rumgumeta yayi yace "nima ina sonki sosai rabin raina."


Haka suka lula duniyarsu mai wuyar fassarawa da kuma dad'i da annashuwa a wajensu.


*ALHAMDULILLAH, ALHAMDULILLAH, ALHAMDULILLAH KASIRAN.*




_ALLAH NA GODE MAKA DAKA BANI IKON KAMMALA WANNAN NOVEL LAFIYA KAMAR YANDA NA FARASHI LAFIYA, 'YAN UWA KUMA MASOYANA INA SONKU INA ALFAHARI DAKU._


*BANDA NOVEL D'IN DAYA FI _KAUSSAR_ AMMA KUMA _AUREN HA'DI_ MA YA ZAMA ZAKARAN GWAJIN DAFI, DAN DAGA IRIN MASOYAN DAYA SAMU NASAN CEWA SAK'ON DA NAKE SAN ISARWA YAJE IN DA NAKE SO YAJE.*


```AUREN HA'DI BAWAI NAYI SHI BANE KAWAI DAN NISHAD'I KO SAK'ON SOYAYYA, DUK IN DA AKACE AUREN HA'DI, TO CIKIN BIYU DOLE D'AYA ZAI FARU,```


_1-IN MA ZUMUNCI YA D'ORE KO KUMA YA WARGAJE,_


_2-TSAYAWA TSAYIN DAKA AKAN KOWACE UWA AKAN 'YA"YANTA, MUSAMMAN MATA DOMIN GIDAN AURE ZASU JE, KAMAR DAI YANDA LA MAMA TAYI._


_3-SANIN GIRMAN MIJI DOLE AKAN KOWACE MACE MAI NEMAN ALJANNA._


_4-SOYAYYA KAN IYA SA MACE TA MANCE DA KOMAI, KAMAR DAI YANDA UMMI TAYI DUK DA BATA SAMU HAIHUWA DA WURI BA, DAMA MU MATA 'YAN SOYAYYA NE HAKA ALLAH YA HALLINCE MU._


_5-GIRMAMA MIJI TA HANYAR YI MASA BIYAYYA DA LADABI DA KUMA JIN MAGANARSA._


_WANNAN SUNE GINSHIK'IN DA YASA NA SAKE RUBUTA WANNAN NOVEL, SANNAN 'YAN UWA BANCE MAKU HAR ABADA BA, AMMA DAI BANA TUNANIN SAKE RUBUTU MUSAMMAM MA NAN KUSA, AMMA WATAK'ILA KU JIMU A CI GABAN *AURENMU A YAU* WANDA MUKE NI DA 'YAN HANUNA._


*ALLAH KA YAFE MIN KURA KURAINA DAKE CIKIN WANNAN RUBUTU, A IN DA NAYI DAIDAI KUMA KA BANI LADAR TARE DA LADAR FAD'AKARWA, DUK WANDA YA KARANTA KUMA YA K'ARU ALLAH KAYI MASA ALBARKA, ALLAH KA SHIRYA MIN YARANA KA K'ARA MAMU DANK'ON SOYAYYA DA MIJINA D'AYA TAMKAR DA DUBU, INA ALFAHARI DAKU, DOMIN KUNA BANI 'YANCINA A MATSAYINA NA MACE, KUNATAUSAYA MIN A MATSAYINA NA MAI RAUNI, KUNA WASA DANI DA HIRA DANI A MATSAYINA NA ABOKIYAR ZAMANKU. LUV YOU MON ANGEπŸ’‹*πŸ‘πŸ‘πŸ’ƒ






*SEE YOU GUY'S*πŸ™‹β€β™€πŸ˜






_SAMEERA CE_πŸ€œπŸ€›

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login