Showing 33001 words to 36000 words out of 72709 words
Chapter 12 - AUREN HADI COMPLETE DOCUMENT WRITING Samira Haruna.txt
masa tace "aunty Ummi"
"Oho, elle est a la maison, elle va parfaitement bien ( tana gida, tana nan lafia k'alau)
Abba ne yace "Salman kana so ka mayar min da yarinya banasariya fa, ka dinga mata hausa mana tunda shine yaren mu."
Dariya yayi yace "Abba 'yar école ce fa, dole sai ana sirka mata danta dinga fahimtar abinda ake koya mata da wuri."
La Mama ce tace "ai kuma gashi nan tana iya yin frensh da kai, amma yanzu ko zan kasheta ba zata fad'amin ina kwana da yarena ba"
Gyara ma Islam zama yayi a cinyarshi yana kallon fuskar ta yace "lah bakya jin buzanci ashe?"
Turo baki tayi inda shi kuma yabi bakin da kallo, La mama ce tace "ai dama duk cikin su Ummi ce mai k'ok'arin son yare na da kuma yinshi amma fa idan tayi niyya, kuma abin mamaki idan taso zata iya yin hira mai tsawo da harshen, kuma kaga ko Inna babu abinda zata fad'a Ummi bata fahimce ta bâ."
Shiru yayi idonshi na kallon k'asa, sai ya ji ta k'ara birgeshi, dan haka ya mik'e tare da Islam yace "to La Mama ni zan wuce, Abba sai anjima"
Islam ce ta k'ara rik'e hannunshi kamar mai shirin kuka ta kalli La mama tace "La mama zan bishi ya kaini wajen aunty Ummi ?"
Salman ta kalla tace "yaya Salman je vien avec toi, s'il te plais?"(zan tafi tare da kai),ta fad'a tare da zubo hawaye, durk'usawa yayi akan gwiwoyinshi ya share mata k'walla yace " kema saurin kuka kamar auntynki ko?"
La Mama ce tace "ina Islam aiko rabin kukan Ummi ba tayi ba, Ummi fa tana k'arama ko hararanta kayi sai hawaye, yanzu haka kuma da za tayi hamma sai ruwa sun zubo a idonta, ai ita saurin kukanta ma babu kamarta duk gidan nan, sai kuma d'an banzan rashin ji."
Murmushi kawai Salman yayi, dan kuwa saidai Ummi ba tayi niyyar kuka ba, yanzu ne hawaye zasu cika kuncinta.
Haka Salman suka lallab'i La Mama ta barshi ya tafi da Islam d'in, amma da alk'awarin zai dawo da ita gobe.
Ummi na zaune tana kallo Islam ta shigo da gudu tana kiran "aunty Ummi naaa"
Ummi na ganin Islam ta bud'e mata hannayenta ta rumgume ta suna murna, zaune tayi kusanta tace "Islam waya kawo ki?"
Kafin tayi magana Salman ya shigo, nan fa suka fara zuba ba k'akk'autawa, Islam na bawa Ummi labarin abokanan wasar data sake tunda tayi aure suka daina wasa tare.
Kular abinci dake hannunshi ya aje gaban Ummi sannan ya wuce ya d'auko plate da cuillère da madara, tunda tafi sonta akan ruwa da jus, yana zuwa ya zuba abincin mai yawa ya aje.
Hannayen Ummi ya kama ya sauko da ita k'asa sannan yace ma Islam "to sauko muci abinci"
Haka suka keyawa suna cin abincin Islam na hira suna dariya tare da kallon juna jefi jefi, Islam ce tace "aunty wai yanzu kina jin dad'in zama anan keda yaya Salman?"
Ummi kallon Salman tayi shima ita yake kallo, murmushi tayi tace "sosai kam ina ji, amma miyasa kika tambaya?"
Kallon Salman tayi tace "to ai naga yaya Salman bai iya irin wasar da muke ba nida ke a gida"
Salman kam da yayi mamakin amsar data bawa Islam yace "wace irin wasa kuke a gidan?"
Nan fa ta fara zayyana masa suna dariya, harda cewa "kuma yaya Salman muna wasan goyo goyo, muna da d'iyan wasa muna masu kwalliya mu masu d'aki, kuma muna wasan ruwan amma La Mama fad'a take mana bata barin mu."
Salman kam Mamaki ne ya cika shi dan haka yace "to amma tun yaushe kuke wannan wasar haka?"
Cikin nuna rashin damuwa Islam tace "ai da Alhaji ya mata aure ne shikenan sai muka daina, yanzu gashi bana da abokin wasa, kuma fa yaya Salman har rawa mukeyi"
Salman kam sauraran ikon Allah kawai yake, haka har suka gama cin abinci ya shiga d'akinshi, turaren ya fiddo daga aljihunshi ya aje akan madubinshi yana k'are masa kallo, a hankali ya tambayi kanshi "wai miyasa na d'auko wannan turaren, me zanyi dashi?"
Tab'e baki yayi yace "ko ma dai miye ina son k'amshin, kuma zanci gaba da ajiyarshi anan."
Yana fitowa Sa'adat ya samu zaune suna gaisawa da Ummi cikin farin ciki, k'arasowa yayi suka gaisa da ita, Islam yaga nata faman hararan Sa'adat dan haka yace,
"Islam miye haka wannan ba yayarki bace?" turo baki tayi tace "to ni ina ruwana da ita, ai bata sona."
Cikin tsawatarwa yace "ke Islam bana san haka fa, ki kiyaye ni" Sa'adat ce tayi dariya tace "ai yaya Salman daka daina b'ata yawun bakinka, in dai nida Islam ce mun saba, dan ita dama duk wanda baya wasa da ita to mak'iyinta ne, bana saké mata kuma idan suna shirme ita da abokiyar shirmen ina magana, shiyasa take cewa bana sonta."
Kallon Islam d'in yayi saiya ganta mak'ale a k'irjin Ummi kamar d'iyarta, ko kuma zata bata nono harda daddab'ata take tana fad'in "ke rabu da ita dama tazo ne dan ta b'ata mana rai"
Murmushi kawai Salman yayi ya fita,yana shiga mota tuk'i kawai yake kamar baya so, ga favorite music d'inshi na tashi a hankali tana ratsa sassan jikinshi yana kuma biyar wak'ar kamar shi yayi ta .
Ko kad'an Ummi bata da matsala, kawai dai tana da taurin kaine da raini ga wanda ta raina.
Wani abu yaji yana k'ara narkuwa a cikin zuciyarshi, farin ciki yake ji har k'asan ranshi.
Sa'adat ce ta kalli Ummi tace ".
05/03/2019 à 17:32 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑
_Samira Harouna_
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
*Page*
6⃣9⃣-7⃣0⃣
"Ummi nifa wani abu ya ban mamaki, mijinki naga ya fita amma ko kalllonshi ba kiyi ba, bare ki masa addu'ar Allah ya tsare ko sai ka dawo.?"
Turo baki tayi ba tare data kula taba, cikin b'acin rai Sa'adat tace "Ummi anya kuwa kinyi hankali? ga dukkan alama har yanzu baki gyara halinki ba, amma ba komai wallahi za kiyi nadama in har kika ci gaba a haka."
Kallonta Ummi tayi a shek'e tace "nadama, akan me fa?"
"Hmmm, lallai Ummi ba kisan ciwon kanki, shin ko kinsan irin tururuwar da 'yan uwa keyi akan mijinki?"
"Ko kinsan yanda iyayenmu suke 'ko'karin had'a 'yayansu da mijinki saboda dacewarshi da wuyar samun namiji kamarshi.?"
"Ummi ki nutsu kisan abinda ya dace dake tun kafin lokaci ya k'ure maki, namiji kamar yaya Salman ba irin mazan da ake samu bane arha, amma ke gashi kin samu duk da cewa kinsan yaya Salman yafi k'arfinki ta wani b'angaren, musamman idan ana maganar kyau."
"K'anwata ki nutsu ki kama mijinki da kyau ta hanyar kyautata masa dayi masa biyayya, zamanin nan abin tsoro ne 'yan mata suna nan bila adadi a gari, wasu ido bud'e suke neman mazan aure sannan idan sun samesu su kyautata masu kota wace irin hanya.
"Kama daga hanyar data dace dama wacce bata dace ba,Ummi kin tashi a gaban mahaifiyar mu kinfi kowa sanin yanda ya kamata mace tama mijinta, dan tun muna k'anana muke gani a wajen mahaifiyar mu, na tabbata kina da sani sosai akan yanda zaki kula da yaya Salman amma shashanci ya hanaki tsayawa ki kula dashi."
"Ummi ko kinsan cewa aunty Hawa (mamar Khamis) tana k'ok'arin cusa ma yaya Salman Rumana dan ya aure ta, haka ma aunty Rabi (kishiyar Hawa) tana so ta mak'ala masa Nuseiba tazo a matarshi ta biyu."
"Kuma fa duk suna hakane saboda tabbacin da suke dashi a kanki na sanin ba zaku tab'a zaman lafiya, saboda sanin yar tsamar dake tsakaninku dashi, to in hakane miyasa ba zaki bawa mutane kunya ba ki rik'e mijinki hannu bibbiyu ta yanda zaki bawa kowa mamaki."
"Ummi kisan fa duk abinda kika yi to zai iya shafar mutuncin Mamar mu, kuma Allah ma shaida ne akan cewar mahaifiyar mu tayi iya abinda zata iya yi akan mu, kuma kema kin sani irin maganganun da ake akan mahaifiyar mu cewa wai ta mallake mahaifinmu har yanzu ita kad'ai ce a gidan."
"Bafa komai bane yasa ake fada mata haka sai dan iya kula da miji dayi masa biyayya, dan haka 'yar uwata ki maida hankalinki kiyi abinda ya dace dake kafin ranar da zata zo kiyi nadama ko kuma kiyi kuka da hawayenki, dan ko kad'an su aunty ba suda nufin alkairi a kanki idan d'aya daga cikin 'yayan nan ta shigo gidan nan."
Tana fad'a ta gyara zamanta ta maida hankalinta ga tv tana kallo, Ummi kam duk jikinta yayi sanyi tunani take in har akace za'a rabata da yaya Salman a yanda take jinshi a yanzu, ba lallai bane ta iya daurewa.
Babu wanda ya k'ara magana a cikin su har su Mama da aunty Hawa suka shigo gidan cikin sallama, tarbansu su kayi saida suka zauna sannan samarin da suka zo da su suka fara shigowa da akwatinan lefen Ummi.
_😔😔😔 lefe kenen bayan tariyar amarya_
Akwati guda takwas haka aka shigo dasu kowace taf take da kaya na alfarma, Sa'adat ce tace "amma Mama ku kad'ai kuka zo? gashi nan ma babu kowa"
Dariya Mama tayi tace "a'a karki damu, Alhaji dama yace mu dake manya muzo kawai ba sai an tara jama'a."
Sai lokacin Ummi ta fahimci irin kallon da Mama Hawa take mata tare ma da kayan, sosai ta k'ara shiga hankalinta tare da cin burin kyautatawa yaya Salman sannan ya zama nata ita kad'ai.
Haka su Mama suka koma bayan tafiyar su Sa'adat ta duba kayan, matuk'a kayan sun birge sosai sunyi kyau, haka suka wuni gidan Ummi da Islam nata shirmen su sai yamma Sa'adat ta kammala girki da sauran gyaran gidan bayan takai akwatinan d'aki sannan ta shirya dan tafiya gida.
Tana saka hijab d'inta tace "to Ummi ni zan wuce sai kuma na sake dawo wa, dan Allah k'anwata kiyi tunani akan abinda na fad'a maki."
"Karki damu zanyi insha Allah" Ummi ta fad'a tana kallonta.
"Yawwa ko kefa, ni na wuce saida safe"
Kallon Islam tayi dake ta cakular kan Ummi wai tana mata kitso duk kitson dake kanta , cewa tayi "to autar La Mama sai anjima ko"
Saida ta turo baki gaba tace "ni dai ki gaishe min da d'iyana"
Dariya Ummi tayi tace "k'awar yau kenan kin yarda d'iyanki ne?"
Dariya su kayi gaba d'ayansu ita dai ta wuce abinta, su kuma suka ci gaba da harkokin su cikin nishad'i.
D'aki Ummi taje ta d'an gyara jikinta ta canja kaya hannu takai ta d'auki turarenta sai taga wayam, tayi mamaki amma saita bud'a jakarta ta d'auko wani irinshi ta shafa sannan ta fito falo ta zauna, Islam kam kallonta kawai take tana so tayi magana kuma ta kasa.
Wayar Ummi Islam ta d'auka ta sambad'a masu wak'a, nan fa suka fara casu ba kama hannun yaro, tun Ummi na rausaya daga zaune harta mik'e duk da k'afafunta amma haka ta dage suna rawa.
Salman kam daya shigo gidan tsaye yayi yana kallon ikon Allah, wai Ummi mai ciwo a k'afa amma gashi tana ta tik'ar rawa da k'afafun, ya shagala sosai wajen kallonta ganin yanda take biyar kid'in da kyau.
Yana lab'e yana kallonsu har aka kai k'arshen wak'ar *DACE* wajen wani baiti da ake fad'an,
_"Lokaci muke jira sai ka zo_"
_"In da rai rabon mu dole sai yazo_"
_"Babu kai kad'ai nake kira gwarzo_"
_"In da kake ba kira kawai nazo_"
_"Zuciya na saki, ba batun cire ki_"
_"Sa hannunka doki, banyi maka tsaki_"
_"Babu shi babu duka a tsarin soyayya_"
_"Na sani babu duka a tsarin soyayya_"
Take Salman yaji kamar dashi Ummi take, hannayenshi ya kalla duka biyu murmushi yayi tare da fad'in "wannan shine dalilin da yasa yanzu bana san dukanki"
Maida kallonshi yayi garesu har sun shiga wata wakar ita ma ta Umar m sharif mai taken *BABBAR RANA*
Kallonsu yake duk yanda tayi haka Islam keyi sai dariya suke suna farin ciki, kamar ba ita ke rawar ba saboda gwanancewa har aka kai wani baiti daya saka shi darawa,
_"Mu tuk'a mota mata tukunya_"
_"Mota ba taje ba in babu taya_"
_Gida babu gida in babu mata_"
_"Mutum babu mutum in baida mata_"
Dariya yayi tare da kutsa kai cikin d'akin, da sauri Ummi ta zube k'asa tana fad'in "wayo Mamana k'afata zata cire, wayo Allah na"
Murmushi kawai Salman keyi harya sunkuya wajenta ya rik'e k'afar yana kallon k'wayar idonta yace "to yaya da sauk'i yanzu?"
Kunya ce ta rufe Ummi dan haka tace "da sauk'i, sannu da zuwa"
Cike da mamaki yace "Ummi yau ni ake wa sannu da zuwa?"
Kallonshi tayi cike da jin kunya tace "kayi hak'uri, muje kaci abinci"
Tana fad'a ta mik'e ta nufi dinning ta fara zuba abinci, kamar wawa haka ya bita ya zauna yana kallonta cike da birgewa, Islam kam ba zata iya hak'ura ba dan haka ta kalli yaya Salman cikin rad'a tace,
"Yaya Salman wai aunty Ummi bata jin kunya ne?"
Kanshi ya sunkuyo wajenta tare da rufe baki yace "me yasa kika ce haka?"
Cikin rad'a tace "to ni naga duk ta zama wata 'yar iska, bata jin kunyar saka wannan kayan gabanka."
Bud'a baki yayi yana kallonta kafin yace "to ai ba komai bane, ni mijinta ne ke kuma k'anwar ta."
A tare suka kalli Ummi dake tahowa hannunta d'auke da ruwa da jus, d'an k'aramin siket d'inta sai wutsilniya yake, shi kam Salman yana jin dad'in ganinta a haka kamar su zauna haka har abada.
Salman na kai loma bakinshi yace "ashe haka kika iya rawa?"
Ko kai Ummi bata d'aga ba bare ta kalleshi, dan haka yace "waya dafa abincin nan?"
"Ni" ta bashi amsa tana kallonshi, shi kam cewa yayi "um um ba ke bace, saidai ko Sa'adat."
Jim Ummi tayi kafin tace "kasan ita tayi kuma kake tambaya?"
Ba tare daya kalleta ba yace "um um ba wai nasan ita tayi ba, saidai nasan d'and'anon abincin ki"
Kallonshi Ummi tayi tace "ashe kayi manquén (missing) abinci na?"
Kallonta yayi ita kuma tayi k'asa da kanta, suna kammalawa suka koma falo suna kallo, Islam da Salman na hira Ummi kam na jinsu har bacci ya d'auketa.
Islam ma bacci tayi saida Salman ya kallesu yace "dole kuyi bacci tun yanzu, tunda kun gaji."
Islam ya d'auka ya kaita d'akin Ummi ya dawo ya d'auki Ummi ya kaita d'akin shi, dan baya so ya bar wata k'ofa da zata falassa zaman da suke.
Yana direta akan gadon ta tashi a tsora ce tana fad'in "miye haka, ya zaka kawo ni nan bayan ga d'aki na can?"
Mik'ewa yayi ya nufi wadrob ya bud'a ya d'auko kayan bacci zai shiga toilet ya juyo yace "karki fita daga d'akin nan."
``` Salman kenan Ummin ce zaka bawa umarni haka```😏
05/03/2019 à 17:32 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑
_Samira Harouna_
*SADAUKARWA GA DUKKAN MASOYAN WANNAN LITTAFI, INA YINKU KUMA INA SONKU SOSAI*
_MY HEENAT TACE WAI MAI TAURIN KAI *SALMAN BA*NA UMMI* NI MA SUNA SANI DARIYA_😍
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
*Page*
7⃣1⃣_7⃣2⃣
Ummi na ganin ya shiga toilet ta bishi da harara tana fad'in "kaji min mutum dan Allah kawai sai na kwana a d'akinka, na san meka shirya min."
Fita tayi daga d'akin ko rufe k'ofar ba tayi ba dan kar yaji fitarta ma, kai tsaye fridge ta nufa ta bud'a ta d'auki madara tasha ta mayar ta d'auki ruwa ta kora dasu, zata rufe robar ruwan ta fad'i ruwan suka zuba, ajewa tayi ta nufi cuisine dan d'auko abinda zata goge a rashin tsammani ta taka ruwan da suka fallatsa in da ba tayi zato ba, sai ko sulb'i ya kwasheta tsaf ya ajeta k'asa ji kake timm.
K'ara tayi lokaci d'aya kuma ta kama bakinta tayi shiru, dafa fridge d'in tayi ta tashi tana kallon ruwan, Salman ne ya fito d'aure da towel a k'ugunshi gabanta ya fad'i saboda ganin ai niyin surarshi duk a mummurd'e, fizgota yayi da k'arfi bai tsaya da ita ko ina ba sai d'akinshi, wurgata yayi akan gado ya koma ya rufe d'akin da key ya kashe wutar d'akin.
_💃💃💃💃💃 FIRST NIGHT_
_MY HEENAT CE TA KWAB'E NI TACE "HABA MY MEERA ME YASA KIKA FIYA AZARB'AB'I NE WAI? KI BARI MU GANI MANA"_
Ummi na ganin haka ta tashi da guda ta mak'ale a jikin bango ta manta da raunin dake jikinta, Salman kam kallonta yayi yace "nace karki fita daga d'akin nan amma sai gashi kin fita, na d'auka kwanan baya kince zaki dinga jin magana ta"
"Ni na rasa miye Alhaji ya gani a jikinki da har yayi tunanin kin isa aure, bayan ke kuma har yanzu ba kida hankali."
Jin bata amsa masa ba yasa ya d'auko kayan baccin shi daga toilet, ganin yana shirin zare towel d'in daga jikinshi yasa Ummi juyawa tana kallon bango ta d'aga masa hannu ta baya tana fad'in,
"Miye haka malam? dan Allah ka rufa min asiri kar kasa naga ciji ina zaman lafiya na."
Kallonta Salman yayi cikin takon izza ya k'araso wajenta tare da juyota da k'arfi ya had'ata da bango yana kallon fuskarta yace "miye kuma ciji?"
Sai lokacin ta d'aga idonta ta kalleshi sai dai yayi kusa da ita sosai, dan haka ta fara in ina " a...amm....amm...e...bbb ba komai"
Gaf da ita ya matso ya had'a hancinta da nashi numfashin su na gauraya dana juna tare sark'a hannunshi ta bayanta ya rike kunkuminta ya had'a k'ugunsu waje d'aya, hannayenshi yasa a jikin bango ya dafe gaba d'aya ya rufeta ko ganinta ba ayi.
Cikin wani irin yanayi ya mata magana "zaki fad'a min miye ciji, ko sai na nuna maki ciji ganin idonki?"
Tana d'aga idonta k'wallan da suka taru suka zubo, gaba d'aya ta rasa iskan shak'awa ga takura da matsatsi ga bak'on abinda taji kusa da k'ugunta yana tab'a ta, ga kuma tambayar daya mata tare da cewa zai nuna mata ciji, da kyar ta fara fad'in,
"A..ddd....dan" kawai sai Ummi tayi luuu tana shirin zubewa k'asa, cikin sauri Salman ya tallabe ta yana kallon fuskarta cike da mamaki, kallona yayi yace "yarinyar nan fa suma tayi."
D'aukarta yayi ya shinfid'e akan gado sannan ya fara saka kayanshi yana ci gaba da kallon fuskarta yana matuk'ar mamakin suman da tayi, tab'e baki yayi yace "matsalar had'a hanya da k'ananan yara kenan, wacce ta suma saboda kusancin da muka samu ni da ita, to ina ga na kusanceta kenan sai mutuwa kamar yanda na fad'a."
Gefenta ya zauna tare da shafa mata ruwan daya d'auko a falo, a