Showing 6001 words to 9000 words out of 72709 words

Chapter 3 - AUREN HADI COMPLETE DOCUMENT WRITING Samira Haruna.txt

HA'DI 💑


_Samira Harouna_


_Cette page ce pour toi mon macho *Meelat AHK,* tu auras la bénédiction da Dieu insha, que Dieu te bénisse. Bizou_ 😘


```dedecated to```


🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛


*Page*


2⃣7⃣-2⃣8⃣




Kamar yanda ya zama al'adar gidan yake idan ya rage saura sati d'aya a d'aura aure to amare su kan dawo da zama gidan Alhaji har a d'aura auren.


Ummi ma ta dawo tare da amaren dan bâ zata iya zama babu su ba sune k'awayenta ita ce k'awarsu kuma yan uwan juna, yaou tunda safe suke takura Ummi akan taje ta karb'o sauran dinkin su daya rage amma sabida san jiki irin nata taki tafiya har saida marece yayi ta fara shirin tafiya amma kuma hajia Babba tace ba zata ba tunda babu wanda zai kaita kuma Alhaji ya hana su shiga adaidaita dan haka ta zauna jiran Allah ya kawo wanda zai kaita.


Zaune take tana jiran taga wanda zai shigo, kwatsam Khamis da Salman suka shigo cikin farin ciki suna hira,saida suka gaishe da su hajia suka fito zasu tafi hajia Babba tace" yaran albarka ina zaku haka?" Khamis ne yace" hajia yadai ko ba kisan mu fita ne?" tsaki tayi tace" kai tafi can ina ruwana da ku dan kun fita, wace uwar zaku bani idan kuna gidan ma, ina so inji inda zaku ne dan ku biyamin da wannan yarinyar" to ina zataje ita?" wajen tailleur kin su karb'o sauran dinkin su" to ai ba damuwa dama wajen aski zamuje yanzu, taso muje Ummi" Salman ne yace" kaga karfa ka d'auko mana yarinyar nan kasan yanzu raina zai b'ace" kafad'ar shi ya dafa yace" haba karka damu wannan fa k'anwarka ce" maida kallanshi yayi ga Ummi yace" taso muje".


Haka suka d'auki hanya Khamis da Ummi nata hirar su, Salman kuma ko tanke bai kula su ba har suka isa wajen, ta samu ana cikin dinke na k'arshe dan haka ta zauna ta jira Khamis kuma yace Salman ya kaishi wajen askin saiya dawo ya d'auketa, haka kuwa akayi ya dawo d'aukar Ummi amma na second d'aya bai jira ba haka ya fara zuk'a mata oder dole ta fito a hargitse tana saka kayan a leda ta shiga mota suka wuce, suna bisa hanya hadari ya taso aka fara iska gari yayi jawur harda baki ga k'ura da k'yar kake ganin gaban ka.


Salman ne yayi tsaki yana fad'in" wannan jaraba har yaoushe da irinta, gashi kinja min na rasa aski sabida bakin halinki kod'an saurayi ma ba kida shi wanda zai maki anfani idan irin haka ta taso, murgud'a baki tayi tace" e d'in banada ai kai naga kanada budurwar, kuma duk bakin halin mutum ai baya rasa massoyi saidai in hali baizo d'aya ba" da k'arfi yasa hannu ya bige bakin Yayana fad'in" yimun shiru kona taka ki yanzun nan marar kunyar banza" rufe baki tayi tace" wallahi saidai mu taka juna, haka kawai zaka takuramin" cikin d'aga murya yace" ke ni kike fad'awa haka, Allah saina sauke ki a nan naga abinda zai faru" cike da tsiwa Ummi tace" yo ka sauke ni mana saime inada wanda zai maida ni idan ma ka sauke ni" OK haka kika ce, to sauka ya fad'a lokacin da yayi parking kamar wasa ya sauke Ummi a nan ba tare da wani tinani ba, ganin yanda gari yake yasa har saida tayi kuka sannan ta matse kayanta ta d'auki hanya a k'afa.


Tafe take tana share hawaye tana tinanin abinda zata ma Salman idan taje gida, oder taji Daga bayanta wata tsaleliyar mota ce ke biyar ta amma bata tsaya ba har saida ya tare gabanta sannan ta tsaya, wani santalelen saurayi ne ya fito daga ciki yana fad'in" haba hajia inata oder amma kinki tsayawa" hararanshi tayi tace" to lafiya?" kinga yanzu dai ba wannan ba ki shigo dan Allah na rage maki hanya inba damuwa" sabida bacin rai yasa tace" da damuwa malam, dan Allah ka wuce ka barni" zata wuce taji anyi tsawa mai k'arfi alamar ana ruwa a wani wajen, abar da tafi tsoro kenan dan haka ta bud'e motar da sauri ta shiga tana k'ilu k'ilu da ido, dariya yayi ya shiga saida sukayi nisa yace" yan mata ni suna na JAMAL, ke kuma fa?" bata fad'a mashi ba sai kwatancen gidan su ta mashi dan ya sauke ta.


Dak'yar ya samu ta bashi number wayarta, tana fitowa yayi dai-dai da kawowar Salman dan haka tabi bayanshi dan ta sauke ruwan bala'i, Jamal kam bin bayanta yayi da kallo yana lasar leb'e yace" ina san faran mace amma fa badan na aureta ba, kema zan latsaki kad'an duk da naga akwai tsiwa da jan aji a tare da ita, amma ba komai naga wanda suka ninka ta so dubu dan haka zan fara shawo kanta kafin nan sai in abka mata" kara lashe leb'en yayi yaja motar ya wuce.


K'ofar gidan ta tsayar da shi tace" to dan ciki bakin nazo gida lafiya babu abinda ya sameni sai ka mutu tsabar takaici" tana fad'i ta wuce gidan su Alhaji a tinanin su kuma Salman ne ya dawo da ita, tana shiga su Khairat suka karb'i kayan suka fara dubawa, ba bata lokaci saiko aka keto da ruwa mai k'arfin gaske.


_To bari muji wai wannan Yar tsama yaoushe ta fara tsakanin Ummi da Salman ne?🤔_
27/02/2019 à 17:32 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑


_Samira Harouna_


```Mommyn Khadija``` ( ma Belle)
```Mommyn Sultan```
```Mommyn Labyb``` (Mamien mu)
```My Heenat``` (Raheenat)
```Choukoura``` (Chouk Beby)
```Halima```
```Maman samha```


( *Cette page ce pour vous)*


~Luv u😘~


🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
( _Gidan zaman lafiya da_ _amana insha Allah)🤜_ 🤛


*Page*


2⃣9⃣-3⃣0⃣


__A fahimtar Salman shine k'arshen rainin da mace zata ma namiji to ta harareshi ko tsaki had'e da murgud'a baki, dan ko a film yaga haka to ya tsani wannan matar kenan dan ko miji da matar shine ta_ _ma shi haka to ta gama raina shi dan haka ya tsani abin sosai._


__Tunda Ummi ta tashi tana k'arama ya zama in dai Salman zai mata magana to sai tayi abinda ya tsana harta girma, bayan ta mallaki_ _hankalin kanta sai ta gane Salman baya so ita kuma sai ya zama d'abi'arta hakan, duk lokacin da yake mata fad'a ko ya dake ta akan ta raina shi sai Mahaifiyar shi tace, kawai dai dan ya sama ransa ne shiyasa ko d'umi tayi sai yaga kamar tayi abinda baya so, Mahaifiyar Ummi kuma tana cewa, da gangan ta keyi dan tasan baya so, to haka_ _dai ya zama kowa da bayan wanda ya ke bi, kasancewar su mak'otan juna dan Ummi bata wanka ta bushe sai a gidan wajen k'awarta Khairat, haka ma Salman ya fi wuni gidan akan gidan su sabida k'annan Ummi da Mahaifiyar su yana jin dad'in zama da su._
_
_Rayuwar Iyalin tana da ban sha'awa dan Ummi da su Jawahir duk lokacin da babu école ko makaranta to suka_ _zab'i gidan da zasu je su kwana biyu a can, haka zasu dinga farin ciki suna d'aukar photunan junan su sabida_ _tarihi shiyasa suka shak'u sosai ba su tab'a samun sab'ani ba._


_In dai Ummi zata ma Salman_ _abinda baya so to ya kan dage ya tumurmushe ta san ransa kuma hakan ya samu asali ne sabida la mamma tace duk sanda ta mashi to ya daketa har sai ranar da ta daina dan kanta, burin Iyayen nasu bai wuce suga an had'a auren su ba to amma yaran ma sunki jituwa tsakanin su duk da dama ana had'a_ __auren ne ba sai wanda ka ke so ba ko ku ke fahimtar juna._
_
```Wannan kenan``` 👈


_
Washe gari amare suka shirya zuwa wajen kitso,Salman da Khamis ne su ka kai su a mota ma saida aka samu matsala tsakanin Ummi da Salman sakamakon..., sorry dear wayar ta gaji😞.
27/02/2019 à 17:33 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑


_Samira Harouna_


*(Yan uwa ku gafarceni a bisa kuskuren da nayi wajen saka num page, kamata yayi wannan ta zama 27-28)* 👏


🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛


*Page*


3⃣1⃣-3⃣2⃣




Salman da Khamis ne a gaba, yayin da su Jawahir ke su biyar ke baya Ummi kuma tana bisa k'afafun Jawahir a bayan kujerar da Salman ke tuk'i, saboda rububin da yayi yawa da ramuka dake wurin yasa Salman shiga wani rame da baisan da shi ba hakan yasa kowa saida ya girgiza Ummi da ke k'afafun Jawahir saida tayi kamar zata fad'i da sauri ta rik'e kafad'un Salman duka biyun tare da fad'in" Inna Lillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un, malam kashe mu kake so kayi ne?"da k'arfi Salman ya fizge hannayenshi yana fad'in" ke wannan wani irin abu ne? muguwa kawai" mugu dai, kaji mutum kamar makaho da ba zaka kalli inda zaka saka mu ba" ke rufa min wannan banzan bakin naki kinji ko" idan kuma naki fa saime ya faru?" sai kisha dan banzan duka kuwa mahaukaciya kawai" turo baki tayi ta harare shi kallanta yayi ta madubi dan haka ya zuro hannu ya mazge kanta, haka suka kai suna fad'a.


Amare kitso aka masu Ummi kuma kunshi, bayan sun koma gida duk da dare yayi amma la mamma ta mata nata kitson kanana mai kyawun gaske irin na buzaye.


Yau ta kama ranar Juma'a washe gari kuma d'aurin aure, Ummi da amare ne zaune a d'aki suna hira hajia Babba ta kira Ummi tana fitowa tace" d'oki abincin nan ki kaima su Khamis a d'akin baki" Kallan hajiar tayi tace" su yaya Khamis kuma,miya kawo su nan da har za suci abinci?" to ina ruwanki?kiyi abinda na saki kawai" gwalo ta mata tace" naji tsohuwa mai ran k'arfe"duka ta kai mata bata sameta ba tace" ke tafi can in banda shegantaka babu abinda kika aje" d'auka tayi ta wuce tana dariya.


Saida tayi sallama suka bata izinin shiga sannan ta shiga, tana ganin Salman ta murtuke fuska irin babu wasa dinnan, gaishe da Khamis tayi ta duk'a ta aje ta tashi zata tafi Khamis yace" k'anwata ina kika baro min amarya ta?" murmuchi tayi tace" yaya Khamis ko dai zance kazo? in kira maka ita" dariya yayi yace" a'a rufan asiri karki sa tsohon nan ya balbaleni da masifa" dariya tayi ta juya zata tafi idonta suka sauka akan Salman dake kallan kumatunta, harga Allah suna birgeshi idan sunan lotsawar nan amma ba yarinyar ba, kamar daga sama Ummi tace" malam lafiyar kallo na?" cikin d'aure fuska yace" ke ni sa'anki ne? wallahi ki kiyaye ni" juyawa tayi ta fita saida ta kai kofar d'akin tasa takalminta sannan tace" kana kallan mutum kamar maye" da gudu ta ida fita shi kuma ya bita da kallo ya, girgiza kai yayi yace" Allah ya shirya ki" Khamis ne yace" da wannan Addu'ar ka ke mata ma tun tini da yanzu ta shiryu" tsaki yayi yace"wannan din?ai ka barta inda ka ganta kawai" abincin suka ci bayan sun kammala suka fito Khamis ya shiga wajen su hajia, Salman kuma ya nufi b'angaren Alhaji.


Bayan sun gaisa Alhaji yace" Salman kaga dai yanzu gobe za'a d'aura auren yan uwanka, na so ace da kai a ciki amma Allah bai nufa ba, nayi nayi da kai ka fiddo da mata a cikin yan uwa, amma kayi wasa da damar da na baka wacce ban taba bawa kowa ita ba, amma ba komai akwai lokacin da zan baka mamaki" kanshi k'asa yace" kayi hakuri Alhaji, insha Allah zan samo nima nan ba dadewa ba" kafadu Alhaji ya daga yace" kai ka sani, ni nasan da ka duba da ka samu, tunda ga sunan birjik muna da su iri iri, in kuma wannan ka kake so abokiyar fad'anka sai ka fad'a babu yar da zaka nema ka rasa a cikin dangin nan" wani kallo Salman ya masa kafin yace" ba komai Alhaji zan nemo, amma ba wannan ba" haka su kayi sallama Alhaji yana mamakin irin wannan rashin jituwa.
27/02/2019 à 17:33 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑


_Samira Harouna_


🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_ 🤜🤛


*Page*


3⃣3⃣-3⃣4⃣




Washe gari da safe, Ummi ce keta bilinbituwar neman chargeur ta saboda wayar ta ta kusan d'aukewa, cikin masifa tace"Khairat ke wai ina kika d'ora min chargeur ta ne?" Khairat da ke dunkule cikin hijabi tace" to ni ina zan sani tunda ban d'auka ba" ke wallahi ba zan yarda ba, duk in da kuka kaita sai kun fiddo ta" Nadia ce ta lek'o da kanta daga cikin hijabi tace" ke jiya fa yaya Mubarak ya aiko yaro aka karb'ar masa shi ma wai bai ga ta shi ba" hararanta tayi tace" oho kenan ke kika bada dan yana mijinki? kuma kina ji ina tambaya kika min shiru, ta tashi ki karb'o min kaya ta" ido Nadiya ta fiddo tace" wacece zata karb'o makin?ina ga ko da ba kiyi abinda za kiyi da ita ba, kafin wannan ranar ma aka hana mu zuwa b'angarensu bare kuma yau" tsaki tayi tace" to kenan nice zan karb'o da kaina, wai ku dan kunga zaku aure ne shiyasa kuka raina ni?" a'a su Ummi manya ba haka bane, kije dai da Kanki zaifi" amma kinsan yanzu suna tare da wannan dan rainin hankalin,ba zan juri kallon banza ba ma daga gare shi bare bak'ar magana" dariya sukayi dan sun san wa take nufi, juyawa tayi ta fita Jawahir kuma cewa tayi" kai Allah yasa a had'a yaya Salman da Ummi aure muga cakwakiya" Hafsat ce tace" ke ai ko in Ummi bata kashe shi da bakin ciki ba, to shi ya kashe ta da duka, ai had'a su bana jin zai haifar da d'a mai ido".


Sallama tayi suka amsa Mubarak ne ya bata izinin shiga, saida ta shiga tayi da na sanin shiga saboda yawan su su da abokansu ne sunfi su goma sai shiri ake, Mubarak kawai ta kalla tace" yaya Mubarak chargeur kina nazo karb'a" cikin sakin fuska yace" OK na kine dama? bari in d'auko maki" tsaye tayi tana jira Khamis ne yace" k'anwata gaskiya kinyi kyau sosai, ina ma hada ke zamu angwance, gashi sai k'yalli kike kema kamar amarya" murmuchi tayi in da Salman ya bita da wani kallo dan yasan dama saita murmusa shi kuma yana so yaga dinple kinta, wani daga cikin abokanne yace" abokina da in dai baku mata miji ba to ni kam ina so" kai na rabaka, kai bâ kasan auren dangin mu ba?" to miye a ciki in haka ne ai sai na komo cikin dangin naku" dariya suka saka, Salman kam cewa yayi" lalle kam da kayi asara ka dawo danginmu saboda wannan abar" kallon mamaki suka mashi d'aya yace" to saboda me, wannan zuk'ek'iyar budurwar, ko ni in har za'a bani ita ai da gudu zan dawo" hararanshi Salman yayi yace" ka koji haushi wallahi ba kayi zab'en k'warai ba" Khamis ne yace" ku fa baku fahimce shi ba yana so ya nuna maku ita d'in matar da zai aura ce, amma kunk'i ganewa" da dariya ya k'arashe maganar, Salman kam kamar ya kai mashi duka, kafin yayi magana Ummi ta murgud'a baki tace" haba yaya Khamis kamar dai maza sun k'are a garin da zan auri wannan halintar" wani bakin ciki ne ya taso ma Salman da yaji an kwashe da dariya, kallanta yayi yace" ke bar nan wajen" tana karb'ar chargeur kin ta wuce saida ta kai k'ofar d'aki ta juyo tace" to kama bakin ni ka daina kallona" wannan maganar ba k'aramin b'ata masa ray tayi ba,( *to fa shine yan uwa ku kaga Salman ya biyo ta a guje har kuma suka zama miji da mata* ).


```CiGaban Labari```




Su Khamis na tafiya Salman ya shiga d'akin Ummi dan ya san da gangan ta zuba masa abinci a jiki, tsaye ya same ta tana gyaran shinfid'a ko riga babu a jikinta sai bras da ta kamata sosai abunka ga mai yar k'iba hakan yasa duk bayanta ya kakkarya gata jawur sai shatin bulaliyar da ta sha sai dogon wando a jikinta shi ma bak'i kamar bras kin, shiru yayi ya ma rasa abinda ya zo fad'a Ummi kam ba tayi wani k'ok'arin rufe jikinta ba duk da ta ganshi.


Hannunta rik'e da pillow ta kalleshi tace" malam ya dai lafiya ka shigo min wannan lokacin haka?" da sauri ya d'auke kanshi daga kallanta bai ce k'ala ba dan haka tace" ka shigo d'aki babu sallama, ba tapé ba excuse kawai ka shigo, yanzu idan nayi ihu nace za kamin fyade kana ganin zaka fita?" ci gaba tayi da abinda take, ganin ba yada abin fad'a yasa ya juya ya fita, d'akinshi ya shiga ya kwanta saman gado yana kallon sama a hankali yake rufe idonshi yana bud'ewa wani sabon abu yake ji a tare da shi, surarta ce take dawo mashi a k'wak'walwar shi a haka bacci yayi gaba da shi duk da yaso ya fita.
27/02/2019 à 17:34 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑


_Samira Harouna_


🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)🤜🤛


*Page*


3⃣5⃣-3⃣6⃣




Misalin 23:30 ya farka, wanka ya farayi ya fito ya kalli agogo tsaki yayi yana fad'in" mi yarinyar nan take nufi da ni ne da har yanzu bata kawo min Tea na ba?"wani tsakin ya k'ara saki ya fito ya nufo k'ofarta, zai bud'e wata zuciyar ta gargad'eshi karya saké ganinta a yanda ya ganta d'azun, ya dan jima a tsaye kafin ya zira kai cikin d'akin, ga dukkan alama tayi nisa a cikin baccin ta har yanzu babu riga a jikinta tayi rub da ciki, sai lokacin ya kalli shatikan carbin da ke bayanta duk ya farfashe, ga kananan kitsonta daya kwanta a bayanta kamar ya taba wata zuciyar ta gargad'e shi, k'afarta ya kama ya fizgo a tsorace ta mik'e zaune tana murza ido tare da kallonshi kafin tace" wai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login