Showing 57001 words to 60000 words out of 72709 words

Chapter 20 - AUREN HADI COMPLETE DOCUMENT WRITING Samira Haruna.txt

wata surukanta ka ni a matsayin 'ya na d'auketa kuma ita ma uwa ta d'auke ni, dan haka ki shafa mana lafiya muyi harkar mu."

Duk abinda suke Salman na kallonsu dan haka ya taso ya zauna k'asa ya lank'washe k'afafunshi, Ummi ya kalla yace "ina kika baro hijabinki?"


Kafin tayi magana Mama ta bishi da harara tace "bata sani ba, dama dan ka mata wannan tambayar ne ka zo nan?"


Sosa k'eya yayi yace "a'a, naga dai baya jikinta ne shi yasa."


"Mu da babu a jikinmu me yasa baka tambayemu ba?"


Baiyi magana ba La Mama ta kalli Ummi tace "wai ba dake ake magana kina ji kinyi shiru, ki tashi ki d'auko hijabinki."


Tashi tayi tana shirin yunk'urawa, take siket d'inta tayi hakan yasa ta koma ta fad'i zaune, da sauri ta rik'e k'ugunta ba dan taji wani abu dan gane da hakan ba, da sauri Mama ta janyota ta rumgumata a jikinta tana kallon Salman tace "kai tashi ka bani waje dan Allah, daga zuwanka kana nema kaja mana matsala."


La Mama cewa tayi "dan Allah ki barshi, ina kike so ya tafi daya wuce wajen iyalenshi, ko yana da wanda suka fi mashi mune a duniya."


Da hannu Mama ta nuna shi tace "to ki fad'a masa kar ya sake shiga harkar 'yata."


Haka suka dinga sama da k'asa yaran na jinsu dan dama wannan ba sabon abu bane a wajensu, Mama na gama gyaran zogalen ta tashi Ummi tare dasu Hafsat da Nadia da Khairat suka ci Jawahir kuma tace bata ci.


Suna cikin cin zogalen su Sa'ada da sukayi girki suka fara rarrabawa kamar dai a gidan biki, Ummi kam bata ci ba saboda zogalen data ci ta isheta, Mama kam saida ta kalli Salman tace "yarinyar nan nasan bata damu da cin abinci ba, kuma kai da yake sakarai ne baka damu da lallab'ata ba har ta samu ta ci, kanka kawai ka sani shi yasa kake mulluk'a uwar k'iba kana barinta."


Kusan kowa dake d'akin saida ya dara, Hajia Abu ce tace "to ai zaifi idan kika mata fad'a da kanki watak'ila taji maganarki, dan nima na lura da hakan kamar bata san cin abinci."


Shagwab'e fuska Ummi tayi dan har yanzu bata fahimci in da zancen yayi ba, haka kam kowa dinga sa baki yana fad'in ta dinga cin abinci kar tayi wasa da lafiyarta, Salman ta kalla dake nesa da ita suna cin abinci tare dasu Khamis, ido ta masa alama akan ita fa bata fahimta ba, shi ma da hannu ya mata alama ta hanyar d'ora hannunshi a cikinshi sannan ya nunata da yatsa alamar ita, da sauri ta bud'a baki ta dafe k'irji tana fad'in "ni d'in?"

Kallonta kowa yayi dan maganarta ta fito fili, haka aka kammala cin abincin daga nan kuma Alhaji ya nemi da kowa ya bashi hankalinshi akwai muhimmiyar magana, kusan yan mata biyar dake wajen babu wacce gabanta bai fad'i ba, dan sun san sun isa aure kuma in dai har maganar aure ce Alhaji zaiyi to zaiyi wuya su tsallake, daga ciki har da Nuseiba da Rumana.


Shiru kowa yayi yayin da Alhaji yayi gyaran murya ya fara da godiya ga Allah sannan d'ora da "to, kamar yanda kuka sani ne a kowane k'arshen wata akan had'u ba dan komai ba sai dan a sada zumunci tare da magance wata matsala data tun karomu ko take shirin tun karowa."


"A wannan karin ma babu wata matsala sai dai akwai ranar auren dana tsayar a k'arshen watan da zamu shiga, kenan nan da wata d'aya."


"Wannan karan AUREN HA'DI ne tsakanin, Nuseiba da ABDUL WAID, Rumana da KABIR, Zaliha da BASHIR, Rafi'a da ISHAQ, sai kuma Fatima da JUNAID."


Cikin fitar hayyaci Nuseiba ta dafe kanta da hannu tana fad'in "na shiga uku, Abdul waid kuma? ni dake burin ganin na zama matar rik'akk'en namiji kamar yaya Salman, kawai saina b'ige da auren Abdul waid."


Da sauri Mamarta ta dafe mata baki tana fad'in "ke rufa mana asiri."


Kowa dake wurin saida ya kallesu anan kowa ya san manufarsu, Ummi wayyo dad'i kasheta haba Ummi ai bata iya b'oye farin cikinta ba saida ta rangad'a bud'a irin tasu ta buzaye tace "kakana Allah ya k'ara maka lafiya da nisan kwana, gaskiya tunda nake ban tab'a jin dad'in AUREN HA'DIN da kayi ba kamar wannan."


Mama Hawa da bak'in cikin ya kawo mata wuya saboda bak'in cikin irin mijin da aka had'a 'yarta dashi, cike da takaici tace "ke Ummi, haka kika ji kowa yace? wa kika tab'a ganin yayi farin ciki da irin wannan ranar? ba kamata yayi ace kin taya 'yan uwanki jimami ba."


Kallonta Ummi tayi tace "tanti jimamin me kuma?aure fa za'a masu, kuma sun isa bare ace za'a masu aure shekarunsu basu kai ba, kuma naga ai sun iya soyayya."


Cikin b'acin rai Mama Hawa tace "ke uban wa ya maki haka lokacin aurenki?"


Cike da rashin tsoro Ummi tace "amma ai ni ban samu gatan da kowa ya samu ba, k'wara su ansa masu rana sun kuma san lokacin jiranshi kawai za suyi, ni kuma fa saida naji ance an shafa min fatiha."


"Amma dai Ummi ba kida mutunci, yaushe kika zama fitsararriya?"


"Ki gafarce ni tanti, banyi haka dan na b'ata maki rai ba, kawai na fad'a maki gaskiyar abinda yake cikin zuciyata ne, kuma har ga Allah ba zan b'oye ba kan cewa naji dad'in wannan had'in saboda an nesanta ni da k'udan dake bibiyar farin ciki."


Cike da tuk'uk'in bak'in ciki Mama Hawa tace "su wanene k'udan, ba dai 'ya'yanmu kike nufi ba ko?"


"Ni dai ban....." marin daya sauka a fuskarta har guda biyu yasa tayi shiru, kumci d'aya ta samu damar dafewa hawaye na zarya a kumatunta, Salman dake zaune wani gumi yaji ya fara tsatsafo masa, ta d'auki kusan sakan talatin kafin taga La Mama a gabanta ta kuma tabbatar ita ce kad'ai keda zarrar da zata iya dukanta, cikin tsantsan b'acin rai La Mama ke magana da rufewar ido da takaici dan abinda Ummi tayi ya k'ona mata rai fiye da kima.


"Ummi wannan ita ce tarbiyar dana baki, wannan ita ce tarbiyar dana koya maki raina na gaba dake, Ummi me yasa kike so ke kad'ai ki zamar min k'arfen kafa, me yasa kike so ki zamar min zakka a cikin 'ya'yana?"


"Ke kad'ai ce da ban a cikin yarana, masifarki ta fara hawan min kai, da farko kin raina Salman rainin da ko matarka ta maka shi, to ta gama raina ka, yanzu kuma shine kika zo mana da wani sabon iskanci rainin ya bar kan 'ya'yunku ya kuma kan iyaye."


"To bari kiji wallahi na gaji da wannan iskancin naki, daga yanzu ba zan sake yarda kina zubar min da mutunci a idon jama'a, Allah ya sani na baku tarbiyar data dace da kulawa a matsayina na uwa, amma ke kullum k'ok'arinki ki watsar da abinda na koya maku dan ki zubar min da mutunci."


Juyawa La Mama tayi cikin fushi ta bar gidan ta fad'a nasu gidan dan dama suna kallon juna ne, Alhaji ne ya kalli Ummi yace "Zeinabou tashi kiba tantinki hak'uri kinji."


Share hawayenta tayi ta mik'e har saida taje gaban Mama Hawa ta durk'usa tace "dan Allah tanti kiyi hak'uri ki yafe min, wallahi ba zan sake ba."


Dafa kafad'arta tayi dan kar a gane b'acin ranta tace "ba komai ya wuce, ki share hawayen kinji ko."


Kusan kowa dake wajen baiga laifin Ummi ba ,dan k'aramar magana ce tayi amma Mama Hawa ta mayar da ita ciwon kai, wasu kuma da suka san nufinsu akan mijin Ummi dad'i suka ji da abinda ya faru daga ciki har da jawahir da take sarakuwarta, Khamis ma dake d'anta baiji wani abu ba dan babu wata bak'ar magana da Ummi ta fad'a face gaskiya.


Gaba d'aya haka alhaji ya had'a kan iyalin nashi ya masu nasiha da gargad'i da rok'on su zauna lafiya tare da masu addu'ar samun farin ciki mai d'orewa, ana sallah la'asar kowa yayi sallah ya tattara nashi ya nashi ya tusa k'eyar yaranshi gaba suka koma in da suka fito, Ummi duk jikinta yayi sanyi hankalinta ya koma kan mahaifiyarta da ranta ke b'ace da ita, ta kama murfin mota zata bud'e Salman ya kalleta cike da kulawa yace,


"Kinga, kije gida wajen La Mama ki zauna, zuwa bayan sallah isha zan dawo na d'auke ki."


Duk da taji dad'i amma gabanta ya fad'i, kai kawai ta d'aga masa alamar to ta wuce cikin gidan, hirar da Salman ya tsaya da Khamis yasa suka d'an d'auki lokaci a tsaye, Ummi na shiga La Mama ta gani zaune tsakar gida tana yankan d'anyar kub'ewa.


Tana d'agowa taga Ummi ta tashi tsaye cikin b'acin rai ta d'auki muciyar da take d'ora miyar akai tana yankawa ta jefo mata, kare kanta tayi tare da sakin yar siririyar k'ara, cikin zafin nama La Mama tayo kanta tana fad'in...


😍😍😍 luv u guys.
25/03/2019 Γ  16:14 - Mamar LatifπŸ’ƒ: πŸ’‘AUREN HA'DI πŸ’‘


_Samira Harouna_




~Luv you guys~ πŸ’‹πŸ˜




πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›


*Page*


9⃣3⃣-9⃣4⃣






"Fita ki barmin gidan dan ubanki tun kafin na sabattaki."


Ummi kam fashewa tayi da kuku ta zube k'asa tana fad'in "dan Allah La Mama kiyi hak'uri wallahi na daina ba zan sake ba daga yau, kuma ma na nemi gafarar tanti gaban kowa, kuma ta yafe min."


Hararan sama da k'asa ta mata tace "ke d'in, ke dai dana sani ce zaki bada hak'uri cikin sauk'i haka?"


"Wallahi La Mama da gaske nake, ki tambaya ma kiji idan k'arya na maki ki hukuntani."


Zaune tayi akan kujerar data tashi ta ci gaba da yankan miyarta ba tare data kalleta ba tace "ban san me yasa kike haka ba Ummi, ita fa kamar mahaifiyarki ce amma ki rufe ido ki mata rashin kunya, alhalin duk ga yaranta a wajen, me kike so suji a ransu kenan?ai haka bai dace ba ki daure ki gyara halinki ko dan rayuwarki ta gaba, ki zama mai kau da kai ga abubuwan da ba zasu rageki da komai ba kinji ko."


Tashi tayi ta matso kusa da La Mama ta duk'a tace "insha Allah zan gyara, kuma na maku alk'awarin canjawa da yardar Allah."


Sai lokacin La Mama ta kalleta tace "Allah yasa zaki iya, yanzu ki tashi ki wuce gidanki yamma nayi."


Murmushi tayi tace "La Mama ai yaya Salman ne yace nazo nan...." bata k'arasa ba ta rufe bakinta saboda dukan da La Mama ta kai mata a bakin tana fad'in "mena fad'a maki akan kiran sunan mijinki?"

K'wallan da suka taho mata ne ta matsosu suka fito tace "kiyi hak'uri, dama su sukace nazo an jima zai zo ya d'auke ni."


Hararanta tayi tace "koda wasa kar na sake jin bakinki ya kira sunan mijinki haka kawai, ko naji kin kirashi da kai ko shi."




*GARGADI*


```'YAN UWANA MATA MU KULA WAJEN KIRAN MAZAJENMU DA SUNAN, (KAI KO SHI) WALLAHI BASU JIN DAD'IN HAKA, KOWANE NAMIJI YANA SO YAGA YA KUMA JI GIRMANSHI DAGA WAJEN IYALINSHI, BASU HAD'A MATAN DAKE KIRANSU DA KU DA WACCE ZA TACE KAI, ALLAH YA BAMU IKON KIYAYEWA.```


Turo baki tayi tace "naji ba zan sake ba."


Ba tare data kalleta ba tace "tashi ki wuce ciki to, kuma ina fata bake kika tilasta masa barinki ki zo ba?"


Tsaye ta mik'e tace "wallahi La Mama bani bace, shi..."tayi shiru sannan ta sake fad'in "su sukace nazo."


Juyawa tayi ta shiga d'akin da gudu, cikin d'aga murya La Mama tace "ke ke, zo nan."


Kamar zata fashe da kuka haka ta juyo ta dawo ta tsaya, kallonta tayi tace "wai yaushe za kiyi hankali? duk da abinda kike d'auke dashi sai kinyi wannan tsalle tsalle kamar ba matar aure ba."


Da farko Ummi taso ta harbo jirgin, amma da tace kamar ba matar aure ba sai tayi wani tunani na daban, dan haka tace "na daina."


Juyawa tayi ta shiga d'akin a hankali, babu kowa dan haka ta zauna ta kunna tv tana kallo, zaman ne ya isheta dan haka ta sanyo hijab d'inta ta fito, La Mama na ganinta tace "to azagwaigwai sai ina kuma?"


Saida ta had'iyi yawu tare da addu'ar Allah yasa kar ta hanata sannan tace "wajen Mama zanje."


A hankali La Mama ta kalleta tace "kin fad'awa mijinki?"


Rarraba ido ta shiga yi dan haka La Mama tace "to koma ki zauna kamar yanda mijinki ya umarceki har sai ya dawo."


Juyawa tayi tana kukan shagwab'a har ta shige ciki, dole ta hak'ura ta zauna har saida su Islam da Momy dasu Mubasheer suka shigo sannan ta fara deb'e kewa.


Ganin La Mama nata fama a cuisine yasa Ummi ta tashi ta gyara falo da tsakar gida dama wasu wajajen, tana kammalawa tayi alwala saboda kiran sallah da aka fara, sallah tayi a tsohon d'akinta tana idawa bata tashi daga wajen ba ta maida hankalinta ga Salman da kuma mu'amular data fara shiga tsakaninsu, gabanta ne ya fara fad'uwa take tsoro taji ya rufeta gaba d'aya zulumi ta shiga, dan a ganinta wahalar nan zata ci gaba da fama da ita kullum, gaba d'aya duk jikinta yayi sanyi ta rasa meke mata dad'i har La Mama ta aiko Islam ta kirata.


Tana fitowa ta samu La Mama zaune akan sallaya tana lazimi, sunkuyawa tayi da nufin ta zauna La Mama ta tsaida ita ta hanyar fad'in "zaman me za kiyi kuma? ki wuce kije ki deb'o abinci kici, kinsan yanzu mijinki zai zo d'aukarki."


Cikin sanyin jiki ta wuce in da La Mama ta bita sa ido tana zancen zuci "Allah yasa ba wannan dalanb'ayar kike masa a gidan ba."


Tana fitowa ta zauna gefen La Mama ta aje plate d'in dake hannunta, hannu tasa ta fara cin tuwon, kallonta La Mama tayi tace "Ummi wannan abincin ne kika deb'o ki ci?"


Kamar zatayi kuka tace " ya isheni haka La Mama."


Cike da tausasawa La Mama tace "kinga Ummi, kefa yanzu bake kad'ai bace dole kina buk'atar cin abinci ko dan lafiyar d'anki, koke baki so ki haifi yaro d'an dumul dumul?"


Cike da mamaki Ummi tace "La Mama, wai waya fad'a maku ina da ciki? nifa bana da komai har yanzu."


Haka ma La Mama cike da mamaki tace "ban gane ba, kina nufin ba kyada ciki, to kenan miye kike da da har yasa ki rashin lafiya har da amai?"


Ajiyar zuciya ta sauke tace "wancen lokacin ma fa kawai saboda naci abinci mai yawa ne, amma ni bana da komai."


Kallonta sosai La Mama tayi kafin tayi k'asa da muryarta tace "Ummi, kin tabbata kina bawa mijinki duk wani hakk'inshi?"


Shiru Ummi tayi na yan dak'ik'u kafin tace " La Mama ba zan iya tabbatar maku ba saboda ban san zuciyar yaya, amma ina tunanin ina k'ok'ari a kanshi yanda ya kamata."


"Kash Ummi, kinga ni kuma ba haka naso ba, Ummi naso ace kin yarda da kanki ta hanyar bawa kanki tabbacin cewa kina kula da mijinki yanda ya dace, bai zama lallai ace kin mashi yanda yake so ba d'ari bisa d'ari, amma koba komai ya dace ace ke kiji a ranki cewa kin kai duk in da wata mace maiji da kanta ta kai wurin."


"Ummi ina so ki k'ara k'ok'ari ta yanda ko wuk'a aka d'ora maki a wuya zaki iya cewa ke kinyi abinda ya dace, amma ba kice kina tunanin haka ba, gaskiya ki dad'a zage damtse kinji ko."


Cikin ladabi Ummi tace "nagode La Mama, kuma insha Allah zan k'ara k'ok'ari wajen ganin ban baki kunya ba, haka ma wajen ganin na kula da yaya yanda ya dace."


"Yawwa 'yar albarka nasan zaki iya in dai kinsa kanki, Allah ya maki albarka." tana fad'a ta mik'e ta shiga d'aki, Ummi kuma ta ci gaba da cin abincinta.


Duk tayi wani shiru da ita jikinta babu k'wari, haka su Islam suka shirya suka tafi wajen lessons yayi saura ita kad'ai zaune a falon, har saida tayi sallah isha sannan La Mama ta fito cikin kwalliya mai birgewa wanda ta dace da dattijuwa mai kamala, Ummi ba tayi mamaki dan ta san mahaifiyarta dama ko kad'an bata yarda Abbansu yaga wani abu marar kyau daga jikinta ba, kamar yanda bata gamsu mijinta ya shak'i wani abu da ba k'amshi ba daga jikinta ko gidanta.


Abba na shigowa Ummi da La Mama kusan a tare suka mike suna nufeshi da fara'ar su suna mashi sannu da zuwa, kan Ummi ya dafa yana fad'in "Mamana dama baki tafi gidanki ba?"


Kanta k'asa cike da kunya tace "Eh, Abba ban tafi ba amma yanzu zasu zo mu tafi."


Cike da jin dad'in yanda yaji Ummi ta girmama mijinta yace "ah to yayi kyau ma hakan."


Har suka zauna saman kujera Abba yana fad'in "Mamana banji dad'in abinda ki kayi ba dazu, amma kuma da kika bada hak'uri sai naji dad'i, kuma kinga Abbanki (Abban Salman) ma cewa yayi yaji dad'i dan baiga laifinki ba."


K'ara sunkuyar da kanta tayi tace "kuyi hak'uri Abba, ba zan sake ba daga yau."


"Yawwa yarinyar kirki, Allah ya maki albarka ya k'ara maki hak'urin zama da mutane a duk in da kika samu kanki."


Cike da jin dad'in addu'ar mahaifin nata tace "ameen ameen Abba nagode."


Sai lokacin ya kalli La Mama suna had'a ido ta galla masa wata harara ta kau da kanta gefe, murmushi Abba yayi dan yasa akwai rikici, cike da zolaya Abba yace "Mamana kinga ganinki yasa ban ko kula mamata ta ba ko, gashi yanzu kinsa ta fara hushi."


Dariya Ummi tayi ta kalli La Mama data rumgume hannayenta a k'irji wai ita a dole hushi take, kallon Abba tayi tace "Abba ai nasan yanzu zaku shirya in dai kune."


Tana fad'a ta tashi ta koma d'akinta, matsowa Abba yayi ya dafa kafad'ar La Mama yace "haba uwar gidana meya faru ne haka ake min wannan kumburin? kofa murmushin yau ban gani ba."


Ture hannunshi La Mama tayi ta kalleshi tace "au, ko murmushin kenan ma baku gani ba? duk wanda na maku tun shigowarku, dama ai na sani in dai kuna tare da Ummi to baku ganin kowa."


Murmushi yayi yace "haba wane ni na kasa ganinki dan tana tare dani, kawai dai shak'uwace ta d'a da uwa."


Ajiyar zuciya ta sauke tana kallonshi, jin ba tayi magana yasa yace "dan Allah to kimin murmushin nan na gani mai sanyaya min

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login