Showing 3001 words to 6000 words out of 72709 words

Chapter 2 - AUREN HADI COMPLETE DOCUMENT WRITING Samira Haruna.txt

ganin ta daka da gudu ya ciro wayar shi ya kira AUWAL Babban d'a ne ga baba Yahaya, yana d'auka yace" kai kana ina?" cike da ladabi yace" yanzu na shigo gida zan gaida su Mamma" to mu had'u da kai gidan baban ka Hamidu" bai ko amsa ba ya kashe wayar, tunda Ummi ta shiga d'aki ta kasa zaune ta kasa tsaye dan tasan yaou kam sai ta Allah babu abinda zai hana a dake ta a gidan nan, Addu'a ta ke koda za'a dake ta to kowama ya dake ta amma banda yaya Auwal.


kai tsaye falo ya shiga ya zauna yana 'kare ma su La mamma kallo babu wanda ya iya tambayar shi lafiya saïda Auwal ya shigo sannan ya kalli La mamma yace" Hawatan kin bani kunya banyi tsammanin haka daga gare ki ba,na d'auka amanar da na baki zaki kula da ita ashe ba haka bane" cikin rashin fahimta jiki na rawa La mamma tace" mi kuma ya faru wallahi bansan Komai ba Alhaji" maida kallan shi yayi ga Salman yace" kira min ita"wucewa yayi yana tinanin komi ta aikata hatsabibiyar oho.


yanda yaga tana ta safa da marwa yasa yace" wace tsiyar ki kayi?" hararan shi kawai tayi taci gaba da kai da kawo warta," to wuce muje Alhaji na kiran ki kuma Allah yasa ya bani bulalar da kai na na zane ki" yan cikinta ne suka kad'a da sauri tace" bulala kuma?" gira ya daga yace" ai ke da kinga Auwal kinsan yana tare da bulalar shi sabida ire irenku" Inna Lillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un na shiga uku, Dan Allah yaya Salman ka taimaka min wallahi babu abinda nayi, kace karya dake ni" ke wuce mu tafi ni babu ruwa na nasan mi kika aikata, ina mijinki amma bansan fitar kiba saidai naga kin dawo" wucewa yayi ya bar tanan kamar zatayi fitsari daga tsaye, jin muryar Alhaji ne yana fad'in" kaga kace in ba zata fito ba ni sai naga shiga na fiddo ta" a hankali ta bud'e K'ofar d'akin tana raba idanu ganin Auwal ya k'ara kad'a mata yan hanjinta, kusa da La mamma ta durk'usa kamar zata shige jikinta, cikin b'acin rai Alhaji yace" Ummi ni zaki zubarwa da mutunci, ni zaki tozarta a unguwar nan da aurenki ki fita kije wajen wani dan Iska har yana rik'e hannunki" to bari kiji wallahi baki isa ba ko ubanki bai isa in shinfid'a doka ba ya 'ketare bare ke yar da ya Haïfa" carbin dake hannunshi ya tilla ma Auwal yace" zanemin ita ta yanda bazata saké tinanin saba Umarni na ba nan gaba" tsabar rashin imani da tausayi yasa Auwal jayo Hijabin Ummi ya fara tsula mata carbi kamar Allah ya aikoshi, Ihu take tana ba Alhaji hakuri amma ina ga Abba zaune amma babu yanda zaiyi koda Ummi taji duka yana ratsa har cikin ruhinta sai ta fara kiran sunan" wayoo La mamma kice yayi hakuri wallahi bazan sake ba, Abba ka bashi hakuri wallahi babu abinda nayi, wayoo yaya Salman dan Allah kace yayi hakuri" har saida hijabinta ya fita ta zama daga ita sai doguwar riga, ganin yanda take ta k'o'karin shigewa jikin Auwal tana so ta rike carbi yasa Salman jin ba dad'i, mikewa yayi ya rik'e carbin ya kamo Oummi da hannu daya ya kalli Alhaji yace" Dan Allah ayi hakuri ba zata saké ba Insha Allahu" mikewa Alhaji yayi tsaye yace" k'warai ba zata saké ba kamar yanda ba zata k'ara koda Awa daya ba a gidan nan ba" kallan ta yayi ya daka mata tsawa" wuce mu tafi" raba ido tayi dan bata san inda zata wuce ba duk ta rud'e" zaki wuce ko sai'' na sa ya d'auko min ke?" da sauri ta d'auki hijabinta jiki na rawa duk zugi ta keji a jikinta saïda ta kai bakin k'ofar d'akin ta juya ta kalli su Abba cikin kuka tace" Abba ku yafemin dan Allah, La mamma kiyi hakuri" da sauri ta bar wajen suna fita K'ofar gida Alhaji yace ma Salman " d'auko motar ka na kai ta gidan ta" mamaki yasa Salman yin tsaye amma daya mashi tsawa saiya wuce babu shiri ya d'auko mota, basu tsaya ko ina ba sai sabon gidan Salman da duka jiya ne aka kammala gyaran shi.
Yana iza k'eyar ta yace Salman ya maida shi gida suna tafiya Ummi ta fad'i a tsakar falon ta fashe da kuka tare da k'ara kamar ta kashe kanta take ji.
27/02/2019 à 17:30 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑


_Samira Harouna_


🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_ 🤜🤛


*page*




2⃣1⃣-2⃣2⃣






Koda Salman ya shigo ya sameta nan bai tankata ba ya wuce d'akin shi, Oummi kam bata farka ba sai da aka gama sallah asuba tana tashi zaune tayi akan kujera tana tinanin inda zatayi alwala tayi sallah, zazzab'i ne ruf ya rufe ta da k'yar ta fito farfajiyar gidan ta samu panpo tayi alwala ta dawo falo tayi sallah ta koma ta zauna.


Har saida gari ya waye sannan Salman ya shigo gidan daga massalaci lokacin har bacci ya saké d'aukar ta saman kujera, kallanta yayi ya kalli agogon dake mak'ale a bango dab da ita yazo ya kama kafar ta ya fizgo har saida ta fad'o k'asa, a tsora ta bud'e ido ta sauke a kanshi, gyara zamanta tayi cikin muryar da tasha kuka tace" miye haka dan Allah?" cikin fad'a yace" Dallah malama tashi kiyi sallah kin wani saki baki kina bacci har safiya tayi" hararan shi ta murgud'a baki tace" amma ai nayi sallah" tsayuwar sa ya gyara yace" to naji abin karyawa fa, ko shima harkin gama?" tashi tayi tsaye tace" haba dan Allah wane irin abin karyawa kuma, ni ban dafa ba kuma gaskiya ba zan'iya ba" tana rufe baki ya kama kunnenta ya murd'e yace" karki saké bari saina maki magana akan abin karyawa, ki tashi kiyi abinda nasa ki idan kin gama zan fada komai a kaina dan bana san shirme" ganin batada niyar tashi yasa ya d'aga carbin shi zai tsula mata da gudu ta shiga cuisine kin ta fara had'a abin kari.


Dak'yar ta kammala sabida zazzab'i gashi duk jikin ta ciwo yake sabida dukan da tasha, falo ta same shi zaune cikin shiri a jiyewa tayi ta juya zata koma cuisine tunda har yanzu bai bata d'aki ba," ke zo nan" a hankali ta dawo zaune tayi hankalin ta a tv, cikin b'acin ray yace" miye wannan kika dafa?" wani banzan kallo ta masa tace" aw kai bakasan ko miye wannan ba?" tassss ya kwashe ta da mari yana fad'in" ke dan kin raina ni na zauna ina jiran abinci tsawon minti ashiri, amma a k'arshe ki kawomin wannan abar a matsayin abinda zanci na fita, to bari kiji ni ba haka nake kayana ba komai ina yinshi da tsari ki buda kunnuwanki kiji abinda zan fad'a maki" ganin gaba d'aya hankalin ta na kan tv yasa ranshi ya k'ara b'acewa da k'arfi ya fizgota ta fad'o k'asa kusa da shi yana kallan idanta yace" ki nutsu idan bâ haka ba wallahi jikin ki zai dinga fad'a maki kinji na fad'a maki sakarya kawai."


Kuka ta fara haka shi kuma ya fara zana mata sharad'an shi da k'a'idojin shi kamar dai....,


" ki tabbatar kowace safiya ina samun abun Kari na da missalin k'arfe 08:00, 08:01 tofa bazan d'aga maki k'afa ba, sannan k'arfe 14:00 na rana ki tabbatar abinci ya kammala kafin na shigo, haka zalika da k'arfe 20:30 na dare kiyi k'ok'arin gamawa kafin minti d'aya ya hau sama"


"Sannan ya zama wajibi gareki da kin idar da sallah asuba kije har d'aki na ki gaishe ni, sannan kowane dare kafin ki kwanta bacci sai kin tabbatar kin kaimin Tea mai kayan kamshi a ciki sannan ki kwanta."


"Sannan ba komai nake ci ba, da safe inasan karyawa da abu mai nauhi,da rana kuma inasan abu mai romo,da daddare kuma zaki iya kawomin komai naci amma banda kifi,Kwaï,tuwo,wake, bana cin su da dare."


"Sannan kowane sati ina azumin litinin da alhamis, dan haka kowane bud'a baki ina bukatar salade, lemon zob'o,kayan marmari, haka kuma duk juma'a zaki dinga dama min fura da rana ina sha, sannan kowace juma'a ina yanka dabba sabida sadaka dan haka zaki dinga sarrafashi ta hanyar data dace sai ayi sadakar, sannan kowace asabar ina gayyatar abokaina suna zuwa muci abinci dan haka zaki dinga dafa abinci mai yawa."


"Sannan kowace juma'a zaki dinga wanke min kaya na kanana sannan ki gogemin su,sannan kowace safiya idan nafita dole zaki gyaramin d'aki na kafin na dawo, wannan shine tsari na kibi ki zauna lafiya, ki k'i bi kisha wahala dan nidai ba zan gaji da dukan ki ba, sannan ki d'auke wannan abar dan bata daga cikin tsari na wannan saike jaka."


Wani kallo ta watsa mashi tace" jaka kuma, ni d'in?" e ke d'in koba jakar bace?" kauda da kai tayi gefe ba tare da yanda zai jita ba tace" jakuna dai" mikika ce?" girgiza kai tayi ta mike tsaye tace" to Malam naji dokokin ka amma kasani ba zan'iya ko d'aya ba, kaji mutum sai kace wani shiya haifeni ko ya hallice ni da zaka zauna ka zana min dokoki" sa'ar cabko hijabinta yayi ya zaunar da ita ya rik'o hannayenta duka biyu, saidai zafin da yaji a jikinta na zazzab'i yasa yace" kar Allah yasa kiyi ko daya d'aya daga cikin abubuwan da na zayyana maki kigani saina lahira yafiki jindadi shashasha kawai mai k'wak'walwar kifi." tsallaka ta yayi ya wuce da sauri tace" to ina zan zauna ni kuma, ko d'akin naka zan dinga kwana?" juyowa yayi yasa hannu aljihu ya ciro makullin ya jefa mata, tayi saurin cab'ewa kamar masu jira a tare suka aikama juna harara Oummi harda tukwicin murgud'a baki, wucewa yayi ya barta nan, d'akin ta ta shiga dak'yar tayi wanka sabida ciwon dake jikinta ta shirya cikin riga da wando ta kwanta kuka ta dinga rerawa sabida takaicin abinda aka mata gashi shi kuma ba imani ne da shi ba.


_Tofa wannan zama_
27/02/2019 à 17:30 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑


Samira Harouna


```Dedecated to My Meelat``` 😘


🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
( _Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛




*Page*


2⃣3⃣-2⃣4⃣






Komawa tayi ta kwanta dan ko zai kasheta ba zata yi abinda yace ba, yana fita gidan su ya nufa ya fad'awa Mahaifiyar shi duk abinda ya faru a daren jiya, ta tausaya ma Ummi, ta kuma k'ara jaddada mashi ya rik'eta amana, d'akin shi ya shiga ya ida harhad'a sauran kayan shi yace zai aiko azo a d'aukar masa.




Haka ma daya shiga gidan su Ummi ya gaishe da su La mamma ta had'a mata sauran kayan ta yace zai aiko a d'auka anjima.




Tana bacci a d'aki taji bugun k'ofa, cikin magagin bacci ta taso ta bud'e, matashin saurayi ne ya kawo kayan su, karb'a tayi ta koma d'akin nata tai masu wajen zama, nashi kuma ta bar su nan kafin ya dawo, kwance tayi tana tunani shikenan ta rabu da gida kenan har abada sai in taje da ziyara, tunda take bata taba jin labarin wacce aka kai gidan miji kamar ita ba, kuka ne ya kwace mata ta nayi tana ajiyar zuciya har bacci ya saké d'aukar ta.




Ummi na gama sallah azahar ta shiga cuisine ta dafa indomie, badan ita take so ta ci ba saidan k'iwa, tana ci ta koma ta kwanta nan saman kujerar bacci ya saké d'aukar ta, ruwa da taji an watsa mata yasa ta tashi a tsora ce tana piki piki da ido, ganin Salman yasa ta fashe da kuka tana fad'in" ni dama nasani wallahi dan ka dinga min mugunta ne yasa ka aure ni, haka kawai ina zaman zama na an wani had'a ni da kai, gashi kana neman kashe ni" tsaki yayi kafin ya zauna idonshi a tv yace "kawo min abinci na," wata harara ta galla masa tare da juya baki tace "ban dafa ba, ai dama na fad'a maka ba bauta nazo yi ba."
Mik'ewar da tayi tsaye tana ta kakkabar riga, hakan yasa ya tashi tsaye cikin had'e rai yace "durk'usa" wani kallo ta mashi, hakan yasa ya d'auke ta da mari yana k'ara maimaitawa "ki durk'usa nace" zubewa tayi tana kuka ci gaba yayi da fad'in "ki saurare ni da kyau kiji, karki saké bari na dawo gidan nan ban samu abinci shirye ba, sannan daga yanzu karki sake tashi tsaye in har ina zaune, ko ina zaune ke ma kina zaune, dole ki girmama ni a matsayi na na mijin ki kuma wanda yake gaba da ke, kina jina.?"




Cikin turo baki ta d'aga kai, zaune yayi yana kallonta yace "ki tabbata Kin kawo min ordevre nan da minti talatin, idan kuma ba haka ba to rai zai b'ace," ganin babu alamar wasa a al'amarin yasa ta tashi dan gabatar da abinda yace d'in, awa d'aya ya d'auke ta kafin ta kammala ta kawo masa ta koma ta d'auko ruwa ta aje masa, tana turo baki ta koma d'akin ta tana gunaguni.


Yana ida wa ya mik'e tsaye yana k'walla mata kira "ke! ke!! ke!! ko ba kiji ne.?"


Cikin gadara ta fito tayi tsaye tana kallon k'ofa, bugu ya kai mata a kai yana fad'in "me na gaya maki yanzu?" kamar zata fashe haka tana ji tana gani ta durk'usa gaban shi yana fad'in "saura ki kwanta bacci tsiya ki k'iyin abinda na saki, wallahi da kinga k'ask'anci a gidan nan dan sai na k'arya ki" kallan shi tayi tace "wai yaya Salman me kake nufi dani ne, wannan fa ba daidai kake yi ba, haka kawai kayi ta wani samin doka kamar kai ka halicce ni ko kuma siyo ni kayi. ?"
Waige waige da ya shiga yi ne na neman abun bugu yasa ta arta a guje ta shige d'aki ta Kulle tana fad'in "wallahi saidai ka kashe ni amma ba zanyi ba, haka kawai daga zuwa na zaka wani ce wai abokanan ka zasu zo dan bak'ar jaraba."
Jin abinda take fad'a ya santa farin sani ba zata yi bâ, dan haka ya fita ana idar da sallah la'asar ya dawo gidan ya sata aikin dole hannun shi rik'e da tsumagiya, harta gama aikin tana kuka shiko ko a jikin shi tunda ta mashi abinda ya ke so wannan ba matsalar shi ba ce ko kukan jini zata yi.
Tana idar da sallah isha'i tayi wanka ta shirya cikin riga da wando na bacci tunda babu wani abun daya rage mata daya wuce ta kwanta tayi kuka bacci ya d'auke ta, Salman ne ya k'wank'wasa k'ofar d'akin a hankali ta bud'e tana kallan shi tace" ya dai Malam?" tun daga sama har k'asa ya kalleta kafin yace "ki fito ku gaisa, amma ki sanyo hijjab." Wuce wa yayi ya barta ita ma ta koma ciki ta d'auko hijjab tasa sannan ta fito.


Oummi ta d'auka wasu bak'i ne ashe ma su Khamis ne da sauran y'an uwan nasu, cikin farin ciki suka gaisa Oummi ta zuba masu abinci ta aje a gaban kowan ne, Salman ta zuba ma tana dariyar mugunta da gangan ta zuba masa abincin a jiki, da sauri ya mik'e yana fad'in "ke! ke!! wai ke wacce irin sakarya ce baki gani ne?" juya baki tayi ta wuce tana rera waka ta barshi nan, hakuri Khamis ya bashi suka ci gaba da cin abinci suna hira cikin nishad'i.








_Yan Uwa ance tuna baya shine rok'o, amma ance waiwaye Adon tafiya_
27/02/2019 à 17:30 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑


_Samira Harouna_


🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S* _
( _Gidan zaman lafiya da_ _amana_ insha Allah)_ 🤜🤛


*Page*


2⃣5⃣-2⃣6⃣


*Alhaji Usman mai Dala* Tshoho mai ran k'arfe haka jikokin shi suke kiran shi wani lokacin, ya nada mata hud'u, *_Hajia Salamatou_ _Hajia_ Zeinab* *Hajia Hawa'ou Hajia* *Mariya* , ya nada yaya ashirin da takwas jikoki da dama, mutum ne mai kakkausan ra'ayi mai tilasta iyalen shi akan duk wani abu da yake so koda basu san shi, ya d'auki turbar had'a tsakanin yayan shi da yayan yan uwa aure dan k'arfafa zumunci, duka yaran sa babu wanda ko wacce ta kawo zabinta duka *AUREN HA'DI* ya masu.


Zaman da matan shi suke sai san barka zama ne da kowace take girmama abokiyar zamanta, sabida tsari da tarbiyar gidan yasa kowane yaro bai san ainahin wacece ta haife shi ba, kowa mama ce kuma kowace tana d'aukar d'an yar uwar ta amatsayin d'anta, da haka ne Alhaji Hamidu ya saka ma yar shi sunan Zeinab duk da bâ ita ta haife shi ba.


Ba iya nan abin ya tsaya ba har jikoki haka yake tsitar su da dai daya yana had'a su aure, sannan auren kaka manu kamar auren zobe ne babu saki saidai ya yarda duk wanda aka ma ba daidai ba ya kawo kara, amma ko yaji kayi to take za'a d'ora maka kayan ka aka ka koma inda ka fito.


Sabida rik'o da addini yasa babu d'à ko jika da ya kai shekara goma sha takwas ba tare da ya aura da shi ba, sai Oummi tayi wannan sa'ar sabida k'wak'walwa da Allah ya mata harta sauke Alkur'ani ta nada shekara goma sha hud'u sannan ta samu( BEPC) ta nada shekara goma sha shida, hakan yasa ya barta ta ci gaba da karatun Alkur'ani harta samu harda lokacin ta nada shekara goma sha takwas, Oummi dai ba wata kyakyawar yarinya bace face abu biyu da Allah ya bata, jar fata da manyan ido masu kyan gani sai dinple wanda ko d'umi take yake k'ara mata Kyaou.


Salman shi ne na farko a duka iyalen da kaka manu ya fi so, dan haka yake daga mashi k'afa harya haura shekarun da ya ke ma mazan aure, amma ba dan yana so ba, dama yana cewa idan lokaci yayi zai bashi mamaki to gashi ya mashi aure babu shiri.



_Kwana hud'u kafin d'aurin_
_auren___ *Salman da Oummi*




~Ku ja muje👌~
27/02/2019 à 17:31 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login