Showing 30001 words to 33000 words out of 72709 words

Chapter 11 - AUREN HADI COMPLETE DOCUMENT WRITING Samira Haruna.txt

ina ruwanshi kuma."


Kamar daga sama taji yace "ba jaraba bace, kawai dai inaso in sani ne dan nasan kwana nawa kike bakya sallah"


Kallonshi tayi k'asa k'asa yanda ba zaiji ba tace "ashe yaji"


Nan ma ji tayi yace "a'a banji ba, nasan dai abinda zaki fad'a kenan"


Hanyar k'ofa ya nufa zai fita tace "to yallabai" juyowa yayi cike da jin haushi yace "miye kuma yanzu? bacci fa nake so nayi"


Cike da shagwab'a tace "kayi hak'uri naga baka d'aukomin pants bane kuma zaka fita"


Rik'e k'ugu yayi "ke wai d'an aikinki kina mayar dani ko me?" jin tayi shiru yasa ya nufi wadrob d'in ya bud'e, da hannu ta masa ishara inda take aje k'ananan kayan, haushi yaji ya kama shi dan ganinsu gasunan masu yawan kuma duk sabbi, gashi ya riga ya siyo mata masu yawo shima.


Wasu jajaye ya d'auko mata a had'e da bras d'in yake, jefo mata yayi tare da fad'in "size nawa kike sakawa?"


Ta gefen ido ta harareshi tace "to waini wannan wace irin tambayar k'wak'wafi ce haka?"


Bata rai yayi yace " ke in zaki fad'amin ki fad'a, dan naga kamar kina saka wanda suka fi k'arfin ki"


Kallon raini ta masa cike da masifa tace "wacece, ni d'in, wallahi sai tayi, kaji in fad'a maka number 40 nake sakawa na bras haka ma pants,ashe ma kallon tsoro kake min bakasan babbar macece ni d'in ba."


Saida ya k'are mata kallo ya juya zai fita, cikin kunkuni tace "haba bakasan niba ne, kai kullum tunaninka bai wuce an haifeni a gabanka ba, amma muna nan da kai akwai lokacin da ni d'innan zan d'aukeka tsaf wallahi."


Cak Salman ya tsaya tare da juyowa saida yazo gabanta ya rusuna kamar zai sumbace ta sannan yace "karki saké tunanin haka ko a mafarki, nafi k'arfinki ko kad'an ba zaki iya dani ba, kafin abinda kike tunani ya faru sai an had'a kamar ki guda goma, dan ke kad'ai kinmin kad'an, tamilon wofi."ya fad'a tare da dan gware mata kai.


Yana fita tayi wata doguwar k'wafa tare da cewa " aiko zaka san ka fad'amin haka, dan wallahi sai nasa ka gane kurenka, kuma wallahi saika d'and'ani kud'arka dani kake zancen, kai har yanzu bakasan Annabi ya faku ba, ba komai ne shekaru keyi ba amma zaka fahimci haka ranar da ka zubar da hawayenka a kaina."


Daga zaune ta gyara ta saké pants d'in tasa coton, sannan ta gyara kwanciyarta sai bacci.


_To Allah yaba mai Rabo sa'a_







```Muje zuwa```😍
05/03/2019 à 17:31 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑


_Samira Harouna_


🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛


*Page*


6⃣5⃣-6⃣6⃣




Cikin dare Ummi ta farka bayan tayi fitsari tayi brush ta dawo ta kwanta taci gaba da baccinta.


Haka ma Salman koda yayi alwala masallaci ya nufa tunda yasan Ummi bata sallah, yana dawowa kuma shima kwance yayi yaci gaba da bacci.




*Safiya*nayi Salman ya shigo d'akin Ummi dake bacci har yanzu, pillonta ya girgiza dan haka ta bud'a ido tare da tashi zaune tana addu'a, kallonshi tayi lokaci d'aya kuma ta kawar da kanta gefe saboda fad'uwar da gabanta yayi, bak'ar singlet ce a jikinshi ta kamashi sosai duk surarshi ta k'akk'arfa ta fito, sai dogon wando shima bak'i murya k'asa k'asa tace "wannan ba k'aramin k'ato bane gaskiya a daren farko zai kasheni, dan haka na hak'ura da d'aukar fansa ta"


Wani shu'umin murmushi yayi yace "aiba ma zan fara ba, dan kuwa kin min kad'an sai an har had'a irinki guda goma sannan zaki isheni kallo."


Kalllonshi tayi tace "ni d'in, wallahi nasan na isa harna wuce, waya fad'a maka mace nawa namiji kad'an , hasalima kune kukewa yaran mutane fyaa..." saurin kame bakinta tayi, kallonta yayi yace,


"Ki fada mana, nasan za kice maza kewa yara fyade, amma ki sani ba irina bane su dan ni bake ba wacce tafi kima tamin k'arama bare kuma ke, sannan ki sani mace nawa namiji kad'an amma namiji bayawa mace kad'an."


"Ki fito falo ni zanje gida." ya fara ya dak'ile


Juyawa yayi zai fita ummi tace "to wa zai fidda ni?"


Tsaye yayi yana kallonta kafin ya matso yace "d'an aiki kika mayar dani ko me?"


Shirun da tayi yasa ya matso yana shirin d'aukarta, da k'arfi ta d'aga murya tace "a'a ni bana san d'auka goyo nake so"


Cikin b'acin rai yayi k'wafa sannan ya juya ya sunkuya, Ummi kam tintsirewa tayi da dariya kafin tace "to yaya Salman taya zan hau nan?ai sai an aza min tsani ko kai bakasan dogo bane?"


Juyowa yayi yana nunata da yatsa yace "wallahi karki b'atamin rai da safiyar nan kinji na fad'a maki."


Turo baki tayi tare da d'aga hannu cikin shagwab'a tace "pardon"


Tsaye tayi akan gadon tare da d'anewa bayanshi, amma ko kad'an tak'i yarda jikinsu ya had'u ta mashi wani zok'ok'o kamar ya d'auko buhun k'aya, cikin masifa Salman yace,


"Ke wannan wane irin iskanci ne, kinsan bakya son had'a jiki dani miyasa kika ce saidai na goyaki, munafuka kawai."


Tunda ya fara magana take ta murgudar baki kamar ta cireshi, a hankali tace "to haka kawai saina had'a jiki da kai"


Haushi ne yasa Salman finciko hannunta ya manna ta a bayanshi da k'arfi, wani numfashi ta sauke jinta a bayanshi kwance, Salman kam mutuwar tsaye yayi jin gaba d'aya albarkatun k'irjkinta sun sauka akan bayanshi da k'arfi.


_🤣🤣🤣🤣🤣 waya aike ka dama?_




Kunya ce tasa Ummi ida narkewa a jikinshi ta kasa d'agawa, da 'kyar Salman yayi k'arfin d'aga k'afarshi ya doshi hanyar fita idonshi lumshe, tunda yake bai tab'a jin abinda yake jiba a yanzu a haka suka kai falo ya direta kwance kamar yarinya, juyawa yayi ya mata runfa da faffad'an kirjinshi kamshin turarenta ne ya fara tafiya da imaninshi, duk da ba sosai ake jinshi ba sai kana gaf da ita.


Kallon fuskarta kawai yake wani abu na fizgarshi da k'arfi, ganin Ummi tak'i had'a ido dashi yasa ya cusa kanshi tsakanin kafad'arta da fuskarta ma'ana a wuyanta yana shak'ar kamshinta yana sauke shed'a sannu sannu.


Ummi duk bata jin dad'i saboda ganinta yau kwananta biyu ba tayi wanka ba saboda ciwo, duk da dai tasan akwai turare a jikinta wanda ko zatayi sati tofa zai zauna a jikinta.


D'ago ido yayi harsun canja kala cikin wata irin murya k'asa k'asa yace "sunan turarenki ma? gaskiya yana da dad'i."


Murmushi Ummi tayi jin wata irin tambaya a jirkice kafin tace " *ARABIAN OUD*"


D'agowa ya sake ya kalleta saidai, baisan lokacin da ya had'a bakinshi dana taba ya fara tsutsa kamar mai shan sweet, tun yana abun a hankali harya fara mata cikin sauri da son aika sak'on cikin gaggawa.


Ummi najin hannun Salman na shirin shiga cikin rigarta tayi saurin rik'e hannun tare da tureshi daga kanta, zaune ya fad'a akan kujerar har yana shirin danne mata k'afa, kanshi kasa idonshi rufe yake sauke numfashi da sauri sauri ya kasa tuna komai, haka ya tashi ya shiga d'akinshi ya saka rigarshi yayi tsaye yana k'are ma kanshi kallo.


Yana fitowa ko kallonta baiyi ba ya wuce, yana shiga mota ya kifa kansa a stiyari ya jima kafin d'ago kanshi yana fad'in "pourquoi, pourquoi je fais ça, pourquoi je fais ça de cette idiot fille? "


"Pourquoi je envis de cette pagaille fille? oh mon Dieu aide moi."


Ya jima kafin ya tayar da motar ya nufi gida, tunda yaje gida babu walwala a tare dashi haka ya karb'i abincin ya fito, saida ya aje abincin a mota sannan ya shiga gidansu Ummi dan su gaisa dasu La Mama.


Yana shiga dole ya saki ransa saboda ganin su Inna Hajara (kakar Ummi) da Tanti Fateema (k'anwar La Mama), gaisawa sukayi sosai kafin Inna ta shaida masa sunzo ganin Ummi ne, cike da jimami yace "haba Inna aida ba kuyi wahalar zuwa bama wallahi tunda da sauk'i"


Dariya Inna tayi tace "ai dama nasan da kunsan zanzo da ba zaku bari ba"


La Mama ma haka tace "nima saida na fada masu da sunyi zamansu tunda da sauk'i."


Koda Salman zai wuce yace su tashi ya tafi dasu, haka suka tafi tare saidai tun a hanya Inna ta fahimci damuwa a tare da Salman, dan haka tace "d'ana shin da matsala ne zaman naku kai da k'anwar taka?"


Cike da san basarwa yace "a'a Inna babu wata matsala ko kad'an"


Bata yarda dan haka ma taci alwashin gano matsalar idan taje gidan, dan tasan kuruciyar Ummi dama Salman d'in, ta kuma san yanda aurensu ya kasance dan haka ita a nata ganin babu wani dalilin da zaisa Ummi tabar mijinta cikin damuwa koda kuwa ba itace silar shigarsa damuwar ba.


Suna zuwa kuwa Ummi ta taresu da murna tana masu sannu da zuwa, Salman ne ya aje mata abincin a gabanta ya juya zai fita, cikin b'acin rai Inna tace "kaga d'ana zo zauna nan"


Tun kafin ya zauna Inna tace "kace babu matsala amma gashi daga zuwana na hango babbar matsala a tsakaninku"


Maida kallonta tayi ga Ummi dake kallon Salman, saiko saukar mari a fuskar Ummi a kid'ime ta dafe kunci tana hawaye, Inna kuwa d'orawa tayi da fad'in " 'yar iska marar mutunci, ashe baki canja halinki ba?"


"Ummi sai yaushe zakiyi hankali? mijinki na sunna kina kallo ya shigo daga fitar da nasan kece sanadi amma ko kallon fuskarsa baki yiba bare yasa ran samun sannu da zuwa daga wajenki, kuma abin haushi kina kallonshi da kaya amma kinfi k'arfin ki amsa koda daga zaune."


"Sannan kuma kina kallo ya juya zai fita ba tare daya ci abincin ba,amma ke ko a jikinki kuma kinsan baici komai ba, haka kika bishi da ido ba tare da addu'a wa mijinki ba zai fita."


"Wannan wane irin zamane kuke mai kama dana dadiro ko kuma rik'akk'u 'yan bariki, zaman da babu girmamawa a cikin shi bare mutunta juna?"tayi maganar tare da kallonsu su dukansu.


Salman ne ya bud'e baki zaiyi magana Inna ta dakatar dashi da cewa "a'a laifin kane daka kasa dorata a turban da kake so, kaine namiji kuma babba kaine zaka tsawatar mata amma gashi ka kasa, ka zama wani lusari a gaban k'aramar yarinyar da aka haifa a gabanka."


Ummi ta kalla tace "ke kuma kici gaba, amma ki sani akwai ranar da zakiyi kuka ranar da nadamarki ba zata anfaneki da komai ba, maza irin mijinki ba'a masu haka, duk wacce ta samu irinshi k'ok'arinta shine ta mallakeshi ta hanyar yi masa biyayya ko kuma bin bokaye da malami, nasan kinsan yanda zaki kula da miji a wajen mahaifiyarki amma kike so ki zubar mata da daraja, ba komai kici gaba."


Hannu Islam Inna ta fizga suka wuce cike da b'acin rai Fateema ko damar magana bata samu ba, suna fita Salman yabi bayansu amma fafur suka k'i shiga mota ya kaisu sai adaidaita suka hau.


Salman kam baima dawo gidan ba ya shiga gari, Inna kuma suna zuwa suka fara shiri tace kawai da safe komawa zasuyi, La Mama tayi tambayar koda matsala amma dayake Fateema tace karsu fad'a mata yasa sukayi shiru, Islam kuma ko gidan bata shiga ba ta fad'a gidansu Salman d'in wajen k'awarta Zeinab (autar su Salman).


Duk da ana zuwa duba jikinta amma haka tayi wunin ranar babu walwala duk abin duniya ya zund'umeta ta kasa farin ciki, haka har dare kowa ya watse amma Salman bai shigo ba da kanta taje ta kwanta kafin ya dawo gidan shima ya kwanta.


_Miji fa yana da daraja sosai 'yan uwa mu kula_.
05/03/2019 à 17:31 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑


_Samira Harouna_


``` Kai kai kai, gaskiya babu abinda yafi dad'i kamar kayi abu a yaba, labarin Salman da Ummi kowa magana yake akai, wasu na dariya wasu na nishad'i, abin farin ciki yanda na samu abokanan fad'a wato 'yan team d'in Ummi.```




🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛


*Page*


6⃣7⃣-6⃣8⃣




*Da safe*koda Ummi ta tashi wanka tayi cikin dabara saboda kar ciwonta ya jik'e sosai, haka ta fito ta shirya powder kawai ta shafa a fuskarta sai turarenta data shafa a jiki, gajeran siket ta saka ko gwiwa bai kai mata ba, saboda ciwonta gaba d'ayanshi a baje yake sai bak'ar riga data dace da zanen siket d'in mai siraran hannaye.


A hankali ta fito falo harta zauna saman kujera ta mik'e k'afafunta, bata lura da Salman ba dake zaune akan d'aya daga cikin kujerun dinning d'in da kayan sport a jikinshi yana shan ruwa tare da sauke gajiya.


Saidai tun fitowar Ummi ya saki baki yana k'are mata kallo, in har yace bata birgeshi ba to tabbas k'arya ya fad'a, dan haka ya ci gaba da kallonta har saida takai kallonta in da yake, cikin sauri tace,


"Ina kwana"


Bud'a baki yayi amma kuma sai ya nemi kowace kalma ya rasa, in'ina ya fara da k'yar ya samu yace mata "bonjour"


Ita kam ko kallonshi bata saké ba, tashi yayi ya shiga d'akinshi dan yayi wanka, Ummi kam sunna tv ta kama tana kallon d'aya daga cikin malaman dake birgeta wato (malam Lawan Shu'aib Aboubakar).


Salman na fitowa d'akin Ummi ya shiga ya d'auko magungunanta, ya juyo zai fita ya koma kan madubi yana duba turarukanta, duk wanda ya shinshina baya jin mai wannan k'amshin, gashi kuma ya manta sunan data fad'a masa saboda lokacin baya cikin hankalinshi, harya juya zai fita ya kuma dawowa 'yar k'aramar kwalbar daya gani ya d'auka tare da karanta sunanshi, cike da farin ciki yace,


"Yes shine, arabian oud"


Abin mamaki sai yasa cikin aljihu.


_Ni kam nace toh_🤔
_Wannan aro ne ko gani zaiyi, ko kuma dai dogon aro ne_


Yana fitowa ya bata maganin yace ta aje kafin ya dawo, fita yayi daga gidan yana shiga mota ya ciro turaren ya bud'e tare da shinshinar shi, lumshe ido yayi a hankali ya bud'e ido ya ya saké maida shi cikin aljihu sannan yaja mota.


Ummi kam tana ganin ya fita tace "to komi ya kaishi d'akin nawa, kodai ajiya yayi dani bansani ba?"


Yana zuwa gida yaga canji daga wajen Mama, dan kuwa ko gaisuwarshi bata amsa ba fad'a kawai ta balbaleshi dashi, wai jiya yasa an yiwa Ummi fad'a harda mari, bayan kuma laifinshi ne tunda baya sakar mata jiki da itama ta saba dashi.


Yayi mamakin jin abinda ya faru a bakin Mama saboda shi bai fad'a ba, tashin hankalin kuma shine tunda Mama ta sani, to La Mama ta sani kenan kuma abinda ita za tayi tofa ko kad'an bazai masa dad'i ba, dan ko baya san abinda zai tab'a lafiyar Ummi yanzu.


Cikin ladabi ya kalli Mama yace "Mama wai dan Allah waya fad'a maku wannan maganar?"


Cikin b'acin rai Mama tace "dama ai kai bâ fad'a za kayi ba, to Islam ta fad'a min tunda gabanta a kayi."


Cike da mamaki ya saké maimaita sunan "Islam" gira ya had'e kafin ya mik'e tsaye zai fita, cikin fad'a Mama tace "ni tsaya na d'auko maka abincinta ka kai mata"


Cak ya tsaya ba tare daya juyo ba, Mama kuma wucewa tayi tana fad'in "aikin banza kawai, kai d'in wani k'aramin yaro ne da za ace saita baka abinci, idan kana jin yunwa aika sani ka kuma san inda zaka je ka nemi abinci, amma haka kawai a dinga takura yarinya harda bata lafiyar ma."


Bin Mama yayi da kallo, ganin ta dage tana ta fad'a akan abinda ba laifinshi bane, ajiyar zuciya ya sauke yana tunanin abinda zai yiwa Islam d'in, saidai kuma ba zaya iya mata komai ba saboda mutuniyarshi ce sosai, wata dabara ce ta fad'o masa in har baya so La Mama ta b'ata ma Ummi rai, to dole ya nemi alfarma wajen Maman.


Mama na zuwa ta mik'a mashi kwanan harda dan gwara masa, karb'a yayi yace "Mama dan Allah wata alfarma nake so kimin , in ba damuwa?"


Jin tayi shiru ya bashi damar cewa "dan Allah Mama kuje kuba La Mama hak'uri, kunsan halinta wallahi zata iya zuwa gida kawai dan taci mutuncinta, dan Allah kuce tayi hak'uri, sannan ku nuna mata nine mai laifi kamar yanda kuke ganin nine da laifin abinda ya faru."


Zaune tayi a kujerar dake bayanshi hakan yasa ya juya yana kallonta tare da sunkuyawa yana sauraran abinda zata fad'a, ba tare data kalleshi ba tace,


"Bana jin ta sani, dan kuwa da dare na shiga gidan mu kayi ban kwana dasu Innar, kuma nidai banga wani alamu ba, haka ma Islam nan gidan ta wuni har dare, saida tayi bacci Abbanka ya kaita gidan, ni kad'ai ta fad'ama saidai ko safiyar yau ta fad'a mata."


Tsaye ya mik'e yace "ok bari naje gidan na gani, Allah yasa bata fad'a ba."


Dogon tsaki Mama tayi tace "in ma ta fad'a saime? ai hankalinka ya kwanta kenan saika zuba ruwa k'asa kasha, dama burinka bai wuce a jibgeta ba, kuma uwarta ta mata fad'a shikenan sai kaji dad'i."


Ko kad'an baiji dad'in abinda ya fito daga bakin Mama ba, amma haka ya dake yabar gidan, kuma dama hakane famillynsu, kana k'in naka ne sai 'yan uwa su soshi, yafi matuk'ar jin dad'in zama a gidansu Ummi saboda soyayyar dasu La Mama suke nuna masa, haka kuma Ummi wani lokacin ma saita kwana ta wuni gidansu Salman ba tare data lek'a gidansu ba.


Yana shiga kamar yanda ta saba haka ta tarbeshi cike da fara'a, zaune yayi k'asa kusa da Abba inda yake break ya mik'a masa hannu su kayi musabaha, da kanshi ya zuba kunun gyad'ar da Maman tayi wanda yasha madara sosai ya fara sha suna hira.


Yanayin La Mama bai nuna masa tasan da abinda ya faru ba, dan haka suka dinga hira har Islam ta fito daga d'aki cikin shirin riga da wando masu kyau, yana kallonta sai yaga sak ta masa kama da Ummi saidai ita tafi ummi dogon hanci, Ummi kuma ta fita jar fata da manyan ido, amma har girman jikin da yatsun k'afarsu masu kyau duka d'ayane.


Da gudu ta k'araso wajenshi ta fad'a jikinshi tare da fad'in "yaya Salman bonjour?" (ina kwana Yaya Salman)


Cike da sakin fuska yace "bonjour Islam, bien réveillé ." ( lafia lau Islam, kin tashi lafia )


Hannu ta zura ta d'auki cup d'in da yake shan kunu ta kai bakinta, tana fad'in "bien , où est-Elle ?" ( yayi, ina take?)


Kallon idonta yayi yace " qui?" ( wa?)


Hararan wasa ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login