Showing 63001 words to 66000 words out of 72709 words
Chapter 22 - AUREN HADI COMPLETE DOCUMENT WRITING Samira Haruna.txt
mijin Khairat yaya Noura da mijin Jawahir yaya Khamis suka k'ara aure na biyu, mijin Hafsat ma haka wato yaya Shamsu yana nan yana shirin k'ara aure.
A lokacin auren ansha badak'ala sosai, amma dama duk abinda Allah ya hukunta babu wani mahaluki daya isa ya dakatar face Ubangiji, duk da dai Khamis ba zab'inshi bace domin kuwa Mamarshi ce ta zab'a mashi yarinyar d'iyar k'anwarta ce, hak'uri kawai Jawahir tayi tare da kau da kanta daga duk wani abu da zai sata bak'in ciki, lokacin kuma Khairat ta kasa hak'uri da b'oye kishinta har saida ta baro gidan mijinta tayi yaji, amma tana zuwa ta samu Salman a gidan hakan yasa ya fafarota da kanshi ya mayar da ita gidan mijinta tare da mata kashedi akan kar ta sake maimaita wannan kuskuren.
Lokacin hankalin Ummi ya tashi sosai saboda a tunaninta ai Salman da Khamis kullum suna tare, dan haka in dai har Khamis zai k'ara aure to Salman ma dole zai k'ara wataran, musamman ma ita da bata haihuwa, hakan da Salman ya fahimta ne yasa ya fara kwantar mata da hankali ta hanyar sake kusanci da ita, kuma hakan yayi amfani saboda ta shiga farin ciki sosai.
Daf da bikin Khamis Ummi da La Mama da Sa'ada da Islam suka tafi AGADEZ wajen bikin d'iyar aunty Fateema k'anwar La Mama, sun tafi da niyyar yin sati biyu dan suga 'yan uwa saboda jimawa da sukayi basu je ba, a ranar da suka je Inna ta kalli Ummi tace,
"Ummi kenan, gashi yanzu an girma hankali kuma yazo maki?"
Dariya tayi tace "Inna dama ai ina da hankali, girman daine ya k'ara zuwa yanzu."
Murmushi Inna tayi tace "humm, haka kika ce dai, ya mai gidan naki babu wata matsala dai ko?"
"A'a Inna babu matsalar komai, lafiya k'alau muke."
"Ai koda matsalar ma ba fad'a zakuyi ba daga ke har shi d'in, dan shima abinda yake fad'a kenan duk lokacin da mukayi waya."
Cikin mamaki Ummi tace "Inna dama suna kuranku?"
Hararanta tayi tace "kin d'auka shima mara kula ne kamar ke, ai duk safiya ta Allah saiya kirani ya gaishe ni."
Dariya Ummi tayi tace "to amma ai nima ina kiranki ko?"
"Eh, kina kira sati ko kwana biyar ba."
Dariya sukayi gaba d'ayansu, Inna kuma ta d'ora da "gaskiya yaron nan yana da kirki sosai, wallahi ko 'ya'yan dana haifa basa min abinda yake min, kinga duk wata saiya aiko min da kayan abinci da kuma kud'i, kuma abinda yake min dad'i kullum godiya yake min da nuna jin dad'in zama da jikanyata."
Murmushi Ummi tayi tace "to yanzu kin tabbatar muna zaune lafiya ko?"
"Eh mana, dama tsokanarki nake."
Haka akayi biki aka gama cikin farin ciki, yayin da a gida kuma ake bikin Khamis cikin rikici da tashin hankali, domin kuwa amaryar akwai rawar kai dan ko fad'a da akayi amaryar ce gaba, Ummi data samu labari ta waya ji tayi kamar tayi hira tazo wajen bikin.
Kwana d'aya da gama bikin nan Inna tace su tattara su koma in da suka fito, nan suka fara mata magiya da ban hak'uri akan ta barsu su kara koda kwana uku, amma ina tace sai dai su kuma su kula da mazajensu, jin haka yasa La Mama tace to su sutafi su barta ta k'ara kwanaki, bud'ar bakin Inna cewa tayi,
"Au, kenan ke zaki zauna su sutafi ko?"
"Eh, tunda su yara ne su tafi kawai, ni saina zauna daga baya naje."
"Ke hin ki kiyaye ni wallahi, ki tashi ku tattara kayanku gobe ku koma kinji na fad'a maki, in banda hauka waya fad'a maki ana tsufa da kula da miji da za kice wai su yarane."
Haka suka shirya suka dawo badan ransu ya so ba, a daren ranar kam Salman yayi farin ciki sosai, dan kwana hud'u da Ummi tayi bata nan ya jikkata sosai.
Tunda Salman ya d'aukosu daga gidan bus ya kawosu gida, yana aje Ummi kayanta kad'ai ya shigo mata dasu ya fita, ita kuma tana ganin haka ta shiga 'yan gyare gyare tana idawa ta fad'a toilet tayi wanka tana fitowa ta shirya cikin k'ananan kaya, riga mai sirara hannu sai wando jeans bak'i iya cinyoyinta, sakin kitsonta tayi k'anana ya bazu a bayanta mai kawai ta shafa da turare sannan ta fito falo, mamaki had'e da murmushi ne ya bayyana kan fuskarta har ta k'araso in da Salman ke zaune yana kallo.
Duk da ta jima a d'aki amma tayi mamakin ganinshi cikin wata sabuwar shiga, babban rigace da yar ciki da wandonsu sak dai ango, ga hula da agogo da takalmi komai fari sosai yayi kyau sai k'amshi da yake bugawa, tana zaunawa ya mik'e ya nufi cuisine yana fitowa ya fito hannunshi d'auke da plate mai fad'i, gabanta ya aje tare da kamo hannayenta ya zaunar da ita k'asa sannan ya zauna.
Mamaki yak'i barin fuskarta har yanzu, plate d'in kawai take kallo wanda ke d'auke da gasassar kaza wacce akayi mechuix d'inta sai kuma tsire a gefe ga kuma kayan marmari an yankasu, sai jus da ruwa da madarar Ummi, cike da mamaki tace "wai wannan duk na miye haka?"
Wani tattausan murmushi ya sakar mata kafin yace "na amarcinki mana, ko kin manta baki ci kazar amarci ba."
Wata irin dariya Ummi ta fara shek'awa har saida cikinta ya fara k'ullewa kafin ta tsagaita tana nuna kayan da hannunta tace "wannan duk na amarcina ne, to wane irin amarci kenan?"
"Amarci dai da kika sani, shi nake nufi."
Dariya tayi tace "gyaran amarya bayan d'aurin, kawo amarya ba shiri ba tare da rakkiyar 'yan uwa ba, lefe kuma bayan tariya, yau kuma ga kazar amarya bayan an riga da an kashe arna, kai gaskiya ni 'yar baiwace komai nawa daban dana saura, haka k'addara rayuwata take watak'ila zanyi nak'uda ne bayan na haihu." ta k'arasa fad'a tana dariya.
Dariya yayi shima yace "hakane kam, amma dan Allah kar kice ba zaki ci ba."
"Ni na isa nace ba zan ci ba, amma fa karku manta da Allah yasa rabonmu na kusa, to da yanzu nima ina da 'ya'ya biyu watak'ila ma dana uku a jikina, dan haka ni banga amfanin wannan kazar ba yau tunda kusan kullum ina cinta."
Langab'ar da kai yayi yace "ai shi yasa nace maki wannan ta amarci ce kinga kenan ta dabance."
Murmushi tayi tare da fad'in "to Allah ya k'ara mana kwanciyar hankali, ya kuma bamu hak'urin zama da juna sannan ya barmu tare har k'arshen rayuwarmu."
Da "ameen ameen my chocolat." ya amsa mata, da haka suka fara ciyar da junansu cikin nishad'i da annashuwa, haka kuma suka raya daren kamar daren farkonsu kamar sababin amaren da suka tare a ranar.
*Washe gari* da yamma Ummi ce tsaye Salman na zaune akan kujera wai a dole aski zata masa ta kuwa d'auko tondeuse d'in ta jona da waya ta rik'e taja daga, shi ma kuma ya dage akan ba zata b'ata masa kai ba, da k'yar ya nuna mata yanda yake so haka ta fara deb'e masa gashin sama sama kamar yanda yace saboda lokuta da dama tana ganin yanda yake yi, hannunshi rik'e da madubi yana dubawa yana nuna mata har Khamis ya shigo ya samesu a haka.
Ko gaisawa basuyi ba Khamis yace "kai kuma miye haka, yanzu askin ma sai a gida za kayi saboda karka je in da zaka biya a maka?"
Dariya sukayi dukansu Salman ya d'ora da cewa "kaji mun mutum dan Allah wa yak'i banza, kowa ai yana san sauk'i a rayuwa, ko kuwa ya ki kace madam?"
Hannu ya d'ago mata ta baya suka bige biyar tana fad'in "ah to, nima dai shi na gani."
Tsaki Khamis yayi yace "ku dai kuka sani, kullum iskancinku k'ara gaba yake."
Wata dariyar suka sake sakawa tare da sake kashewa da hannu, Salman ne yace "kaga kayi abinda ya kawoka dan Allah ka barni da jaririyata, yau amarci muke shi yasa ko fita banyi ba."
Tab'e baki yayi tare da fad'in "kaga karbi nan sak'on da kace na karb'o maka ne."ya fad'a yana mik'a masa enveloppe d'in dake hannunsa.
Karb'a yayi tare da cewa "yawwa d'an k'anena ka kyauta."
"Ba wani na kyauta, ni dai dan Allah karka sake takura min ina tsaka da wata hark'alla dazu ma ka kira ni, wallahi dan kana yayana ne yasa naje aiken nan."
Ummi dai rik'e dariyarta tayi Salman kuma yace "lallai ango kana shak'atawa fa, mata biyu sun saka tsaka sai kwantar ma da hankali suke, gaskiya naso naji yanda ake jin dad'in nan na mata biyu, ni gashi k'waya d'aya ma duk ta baibaiyeni da farin ciki har na fara jin tsoron kar sai an kaini asibiti ace jin dad'i yamin yawa sai an rage min."
Khamis kam cewa yayi "kai, wallahi na rabaka ai zaifi maka dad'i ka ci gaba da zama da k'waya d'ayanka yafi kwanciyar hankali, dan ni yarinyar nan wallahi in tayi wasa ta kusa komawa gidansu, kaini gaba d'aya wallahi tsantsaninta ma nake tayar min da zuciya kawai take idan na ganta."
Jin irin dariyar da suka saka masa ne yasa ranshi ya b'ace ya fice ya bar masu gidan yana fad'in "ai ku dama shed'anu ne in dai kun had'u waje d'aya, saiku kashe mai rai."
*BAYAN KWANA UKU*
Ummi ce ta fito daga d'aki da gudu ta taka d'aya daga cikin kujera dinning ta d'are kan dinning d'in tana dariya daga ita sai d'armin k'irji da key motonta a hannu, Salman ne ya fito cikin k'ananan kaya yana tara mata hannu yana fad'in "haba jaririyata ki bani mana yanzu zan dawo fa."
Cikin dariya tace "um um , gaskiya ba zan baku ba, nasan yanzu da kun tafi saina koma ina kiranku, ni kuma gashi nayi wanka kaya kawai zan saka ba sai muje na kaiku ba."
Dafe k'ugu yayi yace "kin yarda zaki kaini da kanki?"
Cike da tabbatar masa tace "Allah kuwa da gaske nake."
"To kije kiyi sauri kisa kayan dan Allah karki jima."
"To" ta fad'a tare da d'aga masa hannuwa tace "to sauko dani na kasa."
Kallonta yayi yace "da nine na d'oraki?"
Turo baki tayi tace "dan Allah ku saukeni, koso kuke wajen saukowa da kaina na bud'e k'afafuna iska ya shiga?"ta k'arashe maganar tana fashewa da dariya.
Ido ya zaro tare da zura hannayenshi ya sauko da ita yana fad'in "kai, ai ba zanso haka ba, bana so ko shi iskan ya shiga."
Haka ya zauna yana jiranta, bata jima ba ta fito cikin doguwar rigar atamfa sai hijab da nik'ab data saka, fita sukayi ta kulle ko ina kafin ta goyashi akan babur d'inta suka wuce izuwa in da yake zama, ya yarda da tuk'inta shi yasa ya dinga mata hira suna dariya wani lokacin har tsakulkuli yake mata, haka har suka kai in da yake zama kaf abokananshi idansu ne ya dawo kansu, yayin da mafi yawansu suka k'ara ji har zuciyarsu sun birgesu tare da fatan ina ma sune, 'yan bad'anul aswad kuma suka ji ransu ya b'aci tare da takaici.
Gaishe dasu tayi cikin girmamawa kowa ya amsa da fara'arsa,Khamis ne ya taso suka gaisa da Salman sannan yace ma Ummi "yau kuma ke kika kawoshi da kanki?"
"Eh, yaya Khamis yau rigima suke ji wai dole da motona zasu fito, ni kuma kaga zan fita shi yasa na biyo dasu."
"To ina zaki yanzu?"
Saida ta tayar da moton tace "gida zanje, amma saina biya naga Jawahir da kuma amaryarka."
"To Allah ya kiyaye hanya, ki gaishemin da Jawata nima."
Dariya tayi tace "to amaryar fa?"
"Kiyi abinda na saki kawai."ya fad'a yana jan Salman izuwa wajen zamansu.
Hannu Salman ya d'aga mata yace "ki kular min da kanki, sannan ki kula da hanya sosai kinji ko."
Itama hannu ta d'aga masa tace "ku kular min da kanku, saina dawo."
Saida ta b'ace ma ganinshi sannan ya zauna suka fara gaisawa da abokan nasu, anan kuma hira ta b'arke irin tasu ta maza.
Bata jima gidansu Jawahir ta wuce gida zuciyarta d'auke da tunanin yanda taga matar Khamis kamar ba amarya ba, dan kayan dake jikinta ma daban daban ne, haka har takai gida, gidan su Salman ta fara zuwa taga tarba wajen Mama dan da k'yar ta samu ta fito ta lek'a gidan Alhaji da kuma nasu gidan, ko kad'an Mama bata nuna mata damuwa ko wani abu dangane da rashin haihuwarta, wannan kuma na k'ara kwantar mata da hankali tana kuma jin dad'i sosai.
Sai bayan sallah isha ta kama hanya, saida ta biya ta d'auki Salman sannan suka wuce gida cikin farin ciki da nishad'i abinsu.
```Fans```😍
26/03/2019 à 11:20 - Mamar Latif💃: 💑AUREN HA'DI 💑
_Samira Harouna_
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
*Page*
9⃣7⃣-9⃣8⃣
*SHEKARA BIYU BAYA*
Ummi ce zaune a tsakiyar gado tana ta ruzgar kuka iya k'arfinta, Salman ne gefenta ya k'ura mata ido yana kallo dan ya gaji da rarrashinta, ganin kukan bana k'arewa bane yasa sake gyara zama yace "Ummi na baki hak'uri yafi cikin carbi amma kink'i hak'ura, ban san ya kike so dani ba."
K'ara fashewa tayi da wani kuka yayin da ya d'ora da cewa "dan Allah kiyi hak'uri ki daina kukan nan, kinfi kowa sanin bana k'aunar ganin kukanki, amma shine ki keyi dan ki d'aga min hankali."
Bata kulashi ba hakan yasa ranshi ya b'ace ya daka mata tsawa "ke, wai ba dake nake magana ba kina jina kinyi banza dani, miye haka raina nine ki kayi ko me? wallahi idan baki daina kukan nan ba to ranki zai b'ace fiye da tunaninki."
Tunda ya mata tsawa ko shed'a ba tayi ba saboda tsorota da tayi, cikin shashek'ar kuka tace "dan Allah kuyi hak'uri, wallahi ba laifina bane zuciyata ce ta kasa hak'uri, ban san yanda zanyi ba."
Cikin fad'a yace "to me yasa ba zaki taushi zauciyar taki ba, haka zamu zauna kullum in dai kinji anyi haihuwa sai kin tayar da hankalinki kisa kanki damuwa, haka kawai ki dinga kuka kina d'aga min hankali saboda baki haihuwa, shekara shida ce fa, kinsan wasu lokacin da suka d'auka basu haihu ba."
"To wai in tambayeki, shin haihuwar nan waye ke bayar da ita?"
Cikin kuka tace "Allah."
Ajiyar zuciya ya sauke tare da janyota jikinshi yace "to kuma kinsan da haka amma shine kike bawa kanki wahala, kuka ba naki bane addu'a ce taki, mu dage da addu'a insha Allah muma wata rana za muga jininmu a duniyar nan, har yanzu ban cire rai da samun haihuwa ba kuma koda Allah bai ban ba, toni zan zauna dake ba tare da tsangwama ba ko na had'aki da wata saboda rashin haihuwa, ki daina damun kanki hakan babu kyau dan kamar kin kasa hak'uri da k'addarar Ubangiji ne, koda Allah bai bamu haihuwa ba idan mukayi duba da rayuwar mu za kiga akwai abinda Allah ya bamu wanda bai bawa kowa ba, shin ko zaki iya fad'a min miye wannan abun?"
Saida ta k'ara lafewa a k'irjinshi cikin muryar kuka tace "farin ciki da kwanciyar hankali had'e k'aunar junanmu."
"Ahan, to in dai har hakane meye zaisa mu tada hankalinmu saboda wani abu da Allah bai bamu ba, wanda ko dashi in har babu wad'ancen abubuwan na baya to akwai matsala, da wannan nake cewa ki k'ara hak'uri, kuma tunda naga abin hakane to gaskiya ba zaki bikin Nadiya ba gobe idan Allah ya kaimu."
D'aga kanta tayi ta kalleshi tace "a'a dan Allah kuyi hak'uri karku hanani, wallahi ba zan sake ba daga yau nayi alk'awari."
Tunda tace tayi alk'awari yasan zata daina, ko bata daina ba to zata kiyaye dan haka yace "shikenan to tunda kinyi alk'awari, Allah ya kaimu gobe."
A haka bacci ya d'aukesu, cikin dare Ummi ta farka jikinta lullub'e da zazzab'i da ciwon kai, gudun karta tayar da Salman daga bacci yasa ta lallab'a ta tashi drower ta bud'a ta d'auki magani tasha, tana komawa ta kwanta sai ko taji abu ya taho mata da sauri ta tashi zaune tana shirin tashi da nufin ta shiga toilet, tuni aman ya taho mata bata ankara ba, a firgice Salman ya tashi cikin bacci ya fara tambayar ta lafiya, maganin da tasha gaba d'aya ta maidoshi hakan yasa tayi tunanin maganin da tashane kawai ta maido.
Dafe kanta tayi a lokacin da aman ya tsagaita mata tana sauke numfashi, saida taga Salman a gabanta yana gyara wurin data b'ata, kallonshi tayi tare da mik'ewa tsaye tana fad'in "na tasheku ko? wallahi zazz..."bata k'arasa ba ta shiga toilet da gudu wani aman.
Toilet d'in ya shiga ya sameta tsaye tana kurkure bakinta, saida ta juyo da nufin fitowa yace "me yake damunki ne haka, ko wani abu kika ci?"
"Wallahi zazzab'i ne kawai naji ya rufe ni, shine nasha magani kuma gashi ina amayarwa."
Abu kamar wasa sai Ummi ta dinga tsula amai ba k'akk'autawa, kafin gari ya waye ta galabaita sosai Salman kuma ya jikkata saboda tausayinta, ga amai ga ciwon kai ga zazzab'i mai zafi safiya nayi Salman yace su tafi asibiti, amma Ummi tace kawai ba zata je ba haka ya dinga lallab'ata amma tak'i yarda sutafi dan allura kawai ta tsana.
Ganin ta dage akan ba zata je asibitin ba yasa ya kira Kareema (yayar Nadiya) dan tazo gida ta dubata, yana fad'a mata tace masa tana kasuwa siyan kayan cefanai na abincin biki, amma sai tace masa idan zai yiyu ya kawo Ummi gidan bikin saita duba nan, Ummi najin haka tace Eh ta yarda ya kaita dan dama zuwan take so, ba dan yaso ba haka suka shirya suka tafi gidan bikin da sunan ya kaita biki ne.
K'ofar gida ya zauna tare dasu Khamis ita kuma ta shiga ciki, Mama da La Mama da Mama Hawa ta fara karo dasu suna hira zaune, durk'ushe tayi akan tabarmar da suke suka gaisa kafin La Mama tace "Ummi sai yanzu kika taho har an fara kiran sallah azahar?"
Saida ta had'iye wani d'aci da take ji a bakinta cikin sanyin murya tace "wallahi La Mama da bama zanzo ba, bana jin dad'i yanzu ma aunty Kareema nake jira tazo ta duba ni."
Cikin tashin hankali Mama tayi karaf tace "subhanallah, Ummi ba kida lafiya amma kuma kika zo nan!"
La Mama cewa tayi "to meya sameki?naga jiya lafiyarki k'alau da kika biya can kuma ki kace nan zaki zo."
Fuskar nan a