Showing 54001 words to 57000 words out of 72709 words

Chapter 19 - AUREN HADI COMPLETE DOCUMENT WRITING Samira Haruna.txt

baki bud'e yana kallonta, rumgumeta yayi ta baya tare da tusa kanshi tsakiyar wuyanta yana sumbatar ta, murmushi ta saki ta langab'ar da kanta ta d'ora a nashi kan suka had'e waje d'aya tana fad'in "ina kwana *MON ANGE*."


Cikin murya k'asa k'asa ya amsa da "lafiya lau aljannata, kin tashi lafiya?"


"Lafiya lau na tashi nima."


Juyowa yayi da ita saida ya k'are mata kallo ya rik'o hannayenta biyu yana murmushi yace " *MA REINE* kinga kuwa yanda kika had'u? ashe dama b'oye mana kyawun kike kar mu gani.?


Wani shu'umin murmushi tayi ta fara shafar k'irjinshi cikin salo tana kallon idonshi tana fad'in "lokaci ne yayi na in bayyana, dama ina b'oyewa ne saboda banga wanda ya dace daya gani ba, amma yanzu dana samu sahibin raina shi yasa zan fara nunawa."


Cikin sigar zolaya yace "ashe dai kin jima kina sona shi yasa ma kika guji tayar da kishi na, dan kinsan ina da kishi sosai."


Fari tayi da ido kamar wata 'yar duniya tace "kusan hakane, dan tunda na lura kana da kishi na daina kwalliya gaba d'aya."


Murmushin da tayi tare da ci gaba da gyara dinning d'in yasa Salman fahimtar magana ce ta fad'a masa, cabko k'ugunta yayi yana fad'in "me kike nufi kenan, kina so kice nima ina sonki tun waccen lokacin?"


Cikin dariya tace "ban sani ba, amma dai nasan gabanka na fad'uwa idan ka ganni saboda tsoro."


Hancinta ya kama yaja tare da fad'in "ke ko, wallahi baki da dama, to waya fad'a maki haka?"


Cike da dariyar mugunta tace "da kaina na gane hakan."


Hararanta yayi yace "ta yaya kenan?"


Tana kallon idonshi tace "daga yanda kake had'a gumi idan muka had'u, sannan baka cika san kallona ba."


Wata irin dariya yayi tare da janyota jikinshi suka rumgume juna suna dariya, Ummi ce tace "kaga zauna ka ci abinci."


Sakinta yayi yaja d'aya daga cikin kujerun yana fad'in "me kika dafa min?"


Bud'a plate d'in tayi wanda tayi had'add'en ordevre d'ayan kuma salade, sai bred da aka yanka aka tsomashi cikin ruwan kwai da kuma lemon orange da aka matse ruwanshi (natural).


Saida ta had'a komai sannan ta zauna suka fara cin abincin cikin nishad'i, Salman ne ya kalli Ummi yace "amma fa kinyi k'ok'ari, duk wannan aiki ace da safe kika yishi."


Murmushi tayi tace "to miye a ciki, bauta ce kuma ko ba komai wa mijina nayi."


Cike da gamsuwa yace "hakane, Allah ya miki albarka."


Cike da jin dad'i tace "ameen *MON ROI*."


" *ZEINAB*." ya kira sunanta cikin wata murya mai nuna tsantsar abinda yake so ya fad'a daga zuciyarshi yake.


D'ago manyan idonta tayi ta sauke a kanshi, tana jin wani abu a cikin ranta duk lokacin daya kira sunanta, cikin sanyin murya ta amsa mashi da "na'am."


"Ina sonki, ina sonki son da ba zan iya misalta shi ba, Dan Allah Zeinab karki barni ki zauna tare dani har abada, idan kika barni ban san wane irin garari zan fad'a ba, amma nasan zan shiga bala'in daya fi na baya, dan kece kika sabinta rayuwata ta hanyar jiyar dani abinda ban tab'a ji ba tunda nake a duniyar nan."


Aje cokalinta tayi ta kalleshi tana fad'in "haba yaya man, me yasa kake tunanin zan iya rabuwa da kai? karfa ka manta a baya ma mun zauna tare lokacin da bama jituwa, to sai yanzu ne zamu rabu bayan ni da kai duka muna da tabbacin rayukanmu zasu shiga had'ari idan har muka nisanta da juna, ai kaga wannan ba abu bane mai sauk'i, ni Ummi ina tare da kai har izuwa numfashina na k'arshe da yardar Allah."


Kamo hannunta yayi ya janyota zuwa kujerarshi ya zaunar da ita akan cinyoyinshi yana shafar fuskarta yace "nagode sosai Ummi, in haka ta kasance ni kuma Insha Allah zan kula da ke ta yanda kowace mace zatayi fatan ina ma ita ce ke."


Cokali ya d'auka ya soma bata abincin a baki ita ma tana bashi har suka kammala, Salman ne yace zai fita Ummi har da kuka wai ba zai tafi ya barta ita kad'ai ba, da k'yar ya lallab'ata tare da mata alk'awarin ba zai dad'e ba zai dawo.




Bayan fitarshi Jawahir ta kira Ummi bayan sun gaisa Jawahir ta fara tsokanarta wai "Hajia Abu naji ance yanzu kin fara mulki a gidan yaya Salman, dan ance jiya ko fita baki bari yayi ba."


Dariya Ummi tayi sosai kafin ta tsaya tace "oh Allah, yanzu wai ace gulma ta bar kan mata ta koma kan maza, wannan ai shine sa ido kana rayuwarka amma mutane idonsu yana kanka, bamu damu da kowa ba amma kinji har an fara barbard'amu, ai na d'auka sai mara aikin yi ke sa ido ashe kice har yaya Khamis ma ya fara tab'awa."


Gimtse fuska Jawahir tayi kamar suna gaban juna tace "ke bana san iskanci, mijin nawa ne d'an sa ido?"


Tsaida dariyarta tayi tace "Eh mana, shi d'in, nasan shine ya fad'a maki dan shi kad'ai ya san da haka."


Dariya Jawahir tayi tace "ashe dai gaskiya ya fad'a kin fara mulkin, kin san wani abu? nifa ina so naga yaya Salman yana maki k'aramar murya."


"Eh, na fara d'in sai me? kinga fad'a min abinda yasa kika kirani, dan bana da lokacin ki tashi zanyi na sake sabon shiri kafin mijina ya dawo."


Cikin d'aga murya Jawahir tace "Iye, yarinyar nan fa ba kida dama, da alama wannan hutun na makaranta ya maku dad'i ko?"


"Sosai kam, nifa watak'ila ma ba zaku sake ganina ba koda an koma makaranta, dan na riga dana gano abinda yafi min karatun wato kula da mai gidana."


Dariya sosai Jawahir tayi har saida Ummi ta fara k'ulewa sannan tace "haka ya maki kyau, ba kuma zan hanaki ba dan ban san zumar da yaya Salman yake d'ubga maki ba kina sha."


D'orawa tayi da "dama cewa nayi bari in kira in fad'a maki gobe réunion na famille na k'arshen wata, dan Allah Ummi wannan karan ki takura yaya Salman ya barki ki zo kema cikin 'yan uwa kiga mutane mutane su ganki."


Cikin sanyin jiki tace "zan k'ok'arta amma fa banda takura masa, dan abune da ba zanso wani ya masa ba bare kuma ni, idan ya barni zaki ganmu tare, idan kuma bai bari ba, to zaki ganshi shi kad'ai."


"Amma dai ya kamata kiyi k'ok'ari ko dan ki had'u da 'yan uwanki, karfa ki manta tunda ki kayi aure ko sau d'aya baki ziyarci gida ba sai kace wata matar kulle."


Ajiyar zuciya ta sauke tace "to ya zanyi, kullum cewa yake wai saina zama cikakkiyar mace, ban sani ba ko yanzu zai fara barina tunda na zama yanda yake so."


Cike da zolaya Jawahir tace "ke dan Allah 'yer uwa, kenan dai kice an kashe boss mai film na likita."


Tsaki Ummi tayi tace "kinga matar Khamis sai an jima, idan zanje na kiraki."


Tana fad'a ta kashe wayar ta fad'a kogin tunanin yanda rayuwarsu ta canja cikin k'ank'anin lokaci, dan bata tab'a tunanin ko nan da shekara d'aya ba zasu fara fahimtar junansu bare kuma maganar soyayya.




***************


Kamar yanda ya mata alk'awari, bai jima ba ya dawo gidan dan tare sukayi girkin rana dama na dare, sosai suka shiga nishad'i su kansu take suka fahimci tsantsar farin cikin da suke ciki, suna jimawa kafin su kammala girkin saboda duk rabin aikin soyayyarsu suke bugawa tare da wasanni.




Saida sukayi shirin kwanciya sannan Ummi ta fad'ama Salman tana so taje réunion gobe ita ma, ak'alla saida yayi minti d'aya kafin ya kalleta yace "Ummi kiyi hak'uri, ba zan barki ki fita gobe ba tunda har yanzu jikinki babu kyau."


Shiru tayi na 'yan dak'ik'u tare da tuna abinda mahaifiyarta ta fad'a mata a irin wannan gab'ar, ajiyar zuciya ta sauke cikin tattausan murya tace "shikenan *GORKO*, ba komai Allah yasa haka shi yafi alkairi."


Wani hamshak'in murmushi yayi ya shafi fuskarta yace "da kyau haka ake so, amma waya fad'a maki sunan miji da fulatanci."


Kafin tayi magana yace "au, na manta fa, ashe ke d'in 'yar Mama ce dole ki iya yarenta."


Cike da shagwab'a tace " Eh mana, kuma nasan ko kai dake ba fulatanin baka kaini jin yaren ba."


Dariya yayi yace "a'a nanfa d'aya, karki ma had'a kanki dani, dan ni kullum cikin yaren nake dan wani lokacin Mama bata min hausa sai fulatanci."




Tab'e baki tayi ta fara magana tare da nunashi da yatsa tana kalkad'ashi tace "amma ka sani tunda ba zani ba, to kaima ba zaka da wuri ba, dan haka sai kayi sallah azahar a gidan sannan ka tafi."


Dariya yayi yace "na yarda ma reine."


Daga haka suka lula duniyar ma'aurata, duk da dai Ummi sabon shiga ce babu abinda ta iya yi daya wuce sauraren Salman na juyata son ranshi.


Ko kad'an abin ba sauk'i, dan kuwa yau tafi shan wahala fiye da shekaran jiya sai dai kawai waccen shine farko, dan haka rad'ad'in ya banbanta, Salman kam a ganinshi kuma a tunaninshi ai Ummi yanzu ba sabuwar shiga bace dan haka ya zage damtse ya d'irki abarshi son ranshi, ganin abin bana k'arau bane yasa Ummi ta fara kuka tana rok'on ya barta, da k'yar ya barta ko motsi ba tayi ba bacci ya d'auketa tana numfashin wahala, Salman kam tsayuwar dare yayi yana saka ma Ummi albarka har sallah asuba sannan ya tasheta ya had'a mata ruwa tayi wanka sannan ya nufi masallaci.
25/03/2019 à 16:14 - Mamar Latif💃: 💑 AUREN HA'DI 💑


_Samira Harouna_


``` 'YAN UWA GASKIYA INA GODIYA DA IRIN K'AUNAR DA KUKE NUNA MIN```😍


*AUREN HA'DI, DUK DA CEWA NAYI LABARIN SHEKARA BIYU DATA WUCE, AMMA YANZU SAI NAKE JINSHI KAMAR YANZU NE FARKO SABODA IRIN MASOYAN DAYA SAMU, DUK DA NA SAKE WASU ABUBUWA A CIKI DAN WANDA SUKA SAN LABARIN A BAYA ZASU FAHIMCI HAKAN, AMMA KUMA SUNCE WANNAN D'IN YAFI MASU DAD'I SOSAI.*👏🤝🤜🤛




🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛


*Page*


9⃣1⃣-9⃣2⃣




Tunda Salman ya lura da Ummi duk tayi sukuku da ita jikinta babu k'wari, hakan yasa yace mata "nifa tea nake buk'atar nasha mai kauri da kuma bred, dan duk jikina babu k'wari duk na k'arar da kazar kazar d'ina jiya."


Hararanshi Ummi tayi tare da fad'awa jikinshi tace "bana so fa ka daina."


Dariya yayi yace "to shikenan na daina, yanzu zaki iya had'amin abin karin, ko na had'a da kaina kema saina had'a maki?"


Kwance tayi akan doguwar kujera tare da fad'in "ka had'a kawai nima saika kawo min, tunda ka gama gajiyar dani."


Cuisine ya nufa yana fad'in "an gama ranki shi dad'e, yanzu zan wadata gabanki da abin kari."




Haka ya had'a abin karin har da soyayyen k'wai, haka suka ci suka gama kafin suka shiga wanka tare suka fito, sun d'auki kusan awa d'aya kafin su gama shiryawa su fito falo saboda soyayya da wasa cikin raha.




Misalin k'arfe 09:40 Salman ya kalli Ummi yace "kinga tashi ki canja kayanki kizo mu wuce ko."


Da mamaki ta kalleshi tace "zuwa ina kenan?"


Kallonta yayi yace "Ummi burin kowane namiji shine ya samu macen da zai bata umarni kuma tabi kai tsaye ba tare da jinjina al'amarin ko tambayar dalili ba, kin faranta raina jiya a lokacin da nace ba zaki ba kuma kika amince ba tare da kin b'ata ranki ba, to in dai har kinyi hakane dan ki faranta min ko dan biyayya a gareni, to ni me zai hana nayi haka dan na kyautata maki, dan haka jeki ki shirya nasan baki manta colour d'in kayan da ake sakawa ba."


Cike da farin ciki Ummi ta mik'e tsaye tace "kai mijina gaskiya naji dad'i sosai wallahi, Allah ya saka da alkairi, to tashi muje mu sake kayan tunda kaima ba sune a jikinka ba."


Tashi yayi tsaye tare da rumgumota yace "to amma sai in ke zaki saka min kayan, kin yarda?"


Cike da tabbatarwa tace "oui j'accepte."


Tare suka shirya suka fito, masha Allah sunyi kyau sosai kasancewar shadda bata cika birge Ummi ba hakan yasa ta shirya cikin wani rantsantsan boyel fari tas mai duwatsu farare, riga da siket ne sosai kayan suka kama jikinta cif suka fito da surarta, farin hijab da sac da takalmi ta saka sai dai ba tayi kwalliya ba sai jan jan-baki data saka.


Haka ma Salman farar shadda yasa dogon d'inki ne aka mashi kalar zaren da aka mashi kwalliyar dashi, kalar takalma da hular da agogon da yasa bak'ak'e, saida suka d'auki kansu photuna kafin suka fita suka bar gidan.


Ummi bakinta yak'i rufuwa saboda farin ciki, haka har suka kai gidan Alhaji gaba d'aya Ummi gani tayi unguwar ta sauya mata kamar ba in da ta tashi ba, Ummi na fitowa daga mota yara dake wasa k'ofar gidan kowa da fararen kayanshi suka tarbeta da murnarsu tsalle kawai suke wasu na fad'in "aunty Ummi, wasu na fad'in aunty, wasu na fad'in Ummi sak, wasu na fad'in tanti."




Masha Allah gidan ya cika tamk'am da 'yan uwa 'ya'ya jikoki da 'yayan jikokin, nan Ummi ta dinga kwasar gaisuwa ga manyanta dama na k'asa da ita, kowa dake wajen yayi mamaki da kuma farin cikin ganin Ummi da Salman a tare, ko ba'a tambaya ba kasan suna farin ciki dan dukansu jikinsu ya nuna hakan, fatarsu tayi fresh kamar k'wai ga k'iba da Ummi ta k'ara, hakan ba k'aramin dad'i yama mutanen dake wajen ba.




Mamar Nuseiba da Mama Hawa basu ji dad'in hakan ba, dan kuwa a tunaninsu shirin Ummi da Salman kamar barazana ne ga 'ya'yansu wajen hanasu shiga gidan Salman a matsayin mata, Ummi ma haka ta gaishe dasu sama sama ba kamar yanda tama kowa ba, dan a ganinta suna so su rabata da farin cikinta ne, su Jawahir murna har tayi masu yawa saboda ganin Ummi, saida ta gama gaisawa da kowa ta shiga babban falo nan ma ta jima sosai suna gaisawa da kakanin nasu suna tsakonarta ita da Salman wai sai yau ya barta ta fita har yasa ta kod'e fatarta ta fice tayi haske.




Alhaji kamar ya d'aukesu ya goya ganin yanda suka zama abin sha'awa, gashi alamu ya nuna suna zaune lafiya da junansu, Mamar Salman kam tunda ta zauna kusa da Ummi ta d'ora kanta a saman cinyarta tana ta shafar kanta fira kawai suke gashi ta hanata ta tashi suyi hira dasu Jawahir da suke fama da 'yan cikunnansu da basu wuce wata hud'u ba, duk da basu girma ba amma kallo d'aya zaka masu ka gane dan ya d'an turo rigunansu gaba.


Mama duk tunaninta shine Ummi ma ciki gareta shi yasa take ta nan-nan da ita kamar jaririya, haka Ummi ta kwanta saman k'afafun sarakuwar tata hira kawai ake sha cike da farin ciki wanda kuma dama wannan ne musababbin yin taron a kowane k'arshen wata.


Salman kam kallon mahaifiyar tashi kawai yake tare da matar tashi da suke hira abinsu kamar ba surukai ba, farin ciki da soyayyar Ummi na k'ara nunkuwa a cikin zuciyarshi tare da girmanta, ya kuma yarda Mama zata iya yi masa komai akan Ummi d'in.


La Mama ma kallonsu kawai take ita har kunya ma take ji, yayin da Mamar Nuseiba ranta ke k'ara b'acewa tana ganin Mama ma zata iya basu matsala akan burin nasu, haka aka dinga hira ana raha har sallah azahar sannan maza suka nufi masallaci mata kuma suka fara aika tasu sallah a cikin gida.


Ummi na kammala sallah a d'akin Hajia Zeinabou ta mik'e ta cire hijabinta zata fito falo, Hajiar ce ta kalleta cike da mamaki tace "takwara halan wasa kike da cin abinci?"


Cikin rashin fahimta Ummi tace "me kika gani Hajia?"


Ci gaba tayi da d'aura d'an kwalinta tace "naga 'yan uwanki kowace cikinta ya fito, amma banda ke, na sanki fa da tsinannen tamne tamne, kinga damar ki maida kayan mak'ulashe abincinki."


Gyara tsayuwarta tayi tace "to Hajia su ba ciki garesu dole cikinsu zai taso mana, ni kuma me na aje a cikin?"


Hajia tasan Ummi da barkwanci, dan haka tace "shikenan to."


Tab'e baki tayi ta bud'a labulen d'akin dan ta fito, tsaye tayi ganin Nuseiba da Rumana zaune cikin 'yan uwa ana hira, kallonsu take sosai dan kamar ta shak'e wuyan ko wacce a cikinsu take ji.


Salman ma idonshi na kan Ummi data fito babu hijab, ranshi ya b'ace duk da dai kusan kowa dake nan haka suke, amma ai ya kamata ace ita ta rufe jikinta ko dan yanda kayan suka ma jikinta d'araf, cikin sanyin jiki ta k'arasa fitowa ta zauna wajen da La Mama ke zaune tare da Mama suna hira yayin da Mama ke gyaran zogale saboda Ummi.




Nuseiba sarkin tsoro tuni cikinta ya d'uri ruwa dan tasan Ummi farin sani, tsaf zata cinyeta ko ruwa ba zata sha ba, tunda tayi k'asa da kanta bata sake d'agowa ba sai gabanta dake fad'uwa, har yanzu kuma tana nan akan bakanta akan son auren yaya Salman duk da dai tana ganin canji yanzu daga wajenshi, kusan wata biyu kenan baya kiranta babu text, idan ita ta masa baya maido mata to amma kuma duk da haka bata sare ba, gashi yanzu ma da suka zo gaisuwarsu kawai ya amsa bai sake ko kallonta ba bare kuma Rumana da dama ba ra'ayinta yake ba.


Ummi kam har yanzu bata daina kallonsu ba, juyawa tayi in da Salman d'in yake, karaf idonsu suka had'e dana juna dan dama kallonta yake, kunya ce ta rufeta dan ta d'auka za taga yana kallon d'aya daga cikinsu ne, k'asan da tayi da kanta tare da d'an murmushi yasa Mama ta kalleta tace,


"Ya dai Ummi na?"


Cike da shagwab'a ta girgiza kai tana fad'in "ba komai Mama."


D'ora kanta tayi a kafad'ar Mama, La Mama kam take ta jefeta da wata harara wanda tasa Ummi d'aga kanta daga kafad'ar Mama, duk a idon Mama hakan ta faru shi yasa Mama ta sake maida kan Ummi a cinyarta tace "kwanta ke rabu da ita kinji."


Kallon La Mama tayi tace "dan Allah Hawatan ki rabu da yarinyar nan, haba kamar ta tsare maki wani abu."


Hararan Ummi ta sake yi tana fad'in "kenan baki fahimci abinda nake nufi ba ko,ke marar kunyar ina ce, wannan ba sarakuwarki bace da zaki maida ita kamar abokiyar ki?"


Ummi na shirin d'aga kanta Mama ta sake kwantar da ita tace "bana san haka fa Hawatan, akan me zaki takura mata, ke ko tausayinta ma ba kya yi? kuma mu babu ruwanmu da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login