Showing 48001 words to 51000 words out of 72709 words
Chapter 17 - AUREN HADI COMPLETE DOCUMENT WRITING Samira Haruna.txt
tunanin zai damu haka ba, amma data ga ya nuna damuwa a fili saita k'ara narkewa tana zuba shagwab'arta.
Zaune suke a falo duk Ummi ta dunk'ule a cikin k'aton bargon da Salman ya d'auko mata a d'akinshi wai ita zazzab'i, Salman ne ya fito daga cuisine hannunshi rik'e da cup na tea, yana zuwa ya zauna kusa da ita yana fad'in " yawwa Abun Alhaji to karb'i kisha wannan, Insha Allah zaki ji sauk'i kinji."
Ganin bata amsa ba yasa ya kalleta, idonsu ne suka had'e dana juna ganin idonta suna neman kawo ruwa yasa hannunshi ya shafe mata idon yana fad'in "miye kuma?"
Leb'en k'asa ta turo gaba kamar mai shirin fashewa da kuka tana fad'in "tsoro nake ji yaya Salman."
Kallon mamaki ya mata yace "tsoron me kuma? keda kina tare da ni miye zai baki tsoro a duniyar nan."
Wani shu'umin kallo ta masa tace "da gaske yaya Salman? to amma ai bana da tabbacin zaka zauna tare dani har k'arshen rayuwata."
Wani kallo ya mata da yasa tayi k'asa da kanta kafin yace "Ummi, me yasa kike tunanin haka?"
Kai ta girgiza tana fad'in "ba komai."
"To in dai hakane karki sake wannan tunanin, ni ina tare dake kuma zan zauna dake har abada, sannan babu abinda zan bari ya cutar dake matuk'ar ina raye, saboda ni yayanki ne mai alhakin kula dake."
Dad'i ne ya kama Ummi yasa ta fad'a a k'irjinshi tana murmushi tare da fad'in "oh, mon ice cream."
Lek'a fuskarta yayi yana fad'in "aw, da ice cream zaki had'a yayanki?"
Dariya tayi tare da tusa kanta cikin k'irjinshi tace "to ai saboda irin son da nake masa ne yasa."
"Kenan son da kike min ma baya dayawa?"
Da sauri ta d'ago daga k'irjinshi za tayi magana, suna had'a ido ya mata kwarjini dan haka tayi shiru ta koma k'irjinshi tana fad'in "kawai ka ban tea nasha."
Daga kan k'irjinshi ya dinga bata tana shan tea d'in dashi ya had'a mata yaji cinta sosai da lemon tsami, tana sha Salman yace "yanzu kenan ke kika koma mai tea d'in dare?"
Ba tare data d'ago ba tace "to ai nice kesha da dalili, dama kai kana shane saboda ra'ayi da kuma karka barni na huta."
Tana fad'a ta rufe bakinta dan ta gane tayi sub'ul da baka, cewa tayi "kayi hak'uri yaya Salman sub'utar baki ce."
Cike da nuna rashin damuwa yace "ba komai, ai kin riga da kin fad'a, amma zan tuna maki kin fad'i haka ranar da amaryata ta shigo gidan, tunda ke iya fahimtarki kenan."
Tashi tayi daga jikinshi tana kuka tana fad'in "wallahi tallahi ni bada kai nake ba, kuma ai sub'utar baki ce kuma na baka hak'uri, wallahi idan yarinyar nan tazo gidan nan ko kwana d'aya ba zatayi ba."
Rik'e dariyarshi yayi ya kalleta yace "ni kuma naga idan kece kika kawota gidan, aure kuma ba fashi." yana fad'a ya mik'e ya shiga d'akinshi.
Tashi tayi da bargon a jikinta ta bishi, toilet ya shiga amma tayi tsaye tana masifa har ya fito d'aure da towel alamar yayi wanka, tsaye yayi yana shafa mai haka tayi ta bali'i wai ita wallahi ba zaiyi aure ba dan yaci mutuncinta.
Wadrob ya bud'a ya d'auki kayan baccinshi saida ya saka wando sannan ya cire towel d'in zai saka riga, muryar Ummi yaji tana fad'in "gashi ma wannan ciwon naka har tambayarka nayi me yaji maka amma kak'i fad'amin, wallahi saina fad'a ma Mama watak'ila ita ta fad'amin."
Tsayawa yayi daga saka rigar ya jawota har kan gado ya kwantar da ita shima ya kwanta ya rumgumeta a jikinshi yace "in har kika fad'awa Mama to tabbas ranar zan nuna maki ciji."
Cikin sigar rarrashi tace "dan Allah kayi hak'uri wallahi ba zan fad'a mata ba."
"Ah to, da yafi maki."
"To amma yaya Salman me yasa ba zaka fad'amin ba? nifa matarka ce."
Ajiyar zuciya ya sauke akan fuskarta tare da k'ara matseta yace "hakane, zan fad'a maki amma sai ranar da kika zama cikakkiyar macen aure na."
Ido ta d'aga ta kalleshi tace "dama ni ban cika matarka ba har yanzu?"
Kuka ta fara shi kuma ya fara rarrashin yana fad'in "ba haka nake nufi ba Ummi, shifa aure da kika gani ana gina shine a bisa wasu sharadd'ai, idan har babu d'aya a ciki tofa ana iya raba aure akan wannan d'ayan a cewar wasu malamai."
"Ummi hakk'in saduwa ba k'aramin hakk'i bane akan ma'aurata, ni ba yaro bane haka kema kuma mu 'yan adam ne masu matuk'ar sha'awa dole muna buk'atar junanmu kafin mu rayu musammam ma ni, to amma ya zanyi ke kina nuna tsoro ni kuma ba zan iya maki ta k'arfi ba Ummi."
"Yaya Salman dan Allah kar kayi fushi dani, wallahi ina jin tsoro sosai ban san taya zan fuskanci wannan k'alubalen ba, amma dan Allah ka yafe min in har baka so Ubangijina yayi fushi dani."
Haushin maganarta Salman yaji, dan ya d'auka zata bada kaine kawai amma ta kasa, sassauta rik'on da yayi mata yayi yana fad'in "shikenan kiyi bacci."
K'ara lafewa tayi a jikinshi tace "mu zauna haka yayana, zamu iya rayuwa ko babu wannan abun haka ma ai muna cikin farin ciki."
Gaban Salman ne ya fad'i wata zufa yaji ta tsatsafo masa, a sanyaye yace "ba zai yiwuba Ummi na fad'a maki mu 'yan adam ne, muna buk'atar wannan d'in domin mu rayu, a k'alla na fara cinye k'uruciyata ba tare da anfanar ni'imar da Allah yayi min ba."
Yana fad'a ya juya mata baya yana sak'e sak'e, yanzu kam in dai har ba zata canja ba to dole yayi aure, dan shi kam ba zai iya mata ta k'arfi ba dan yafi kowa sanin wanene shi, in har ya mata ta k'arfi to ko bata mutu ba za tayi k'anwar mutuwa in kuma ba haka ba to za tasha jinya ba kad'an ba.
```My Lovely Heenat ya kika ce ne akan wannan lamarin?```
11/03/2019 Γ 17:51 - Mamar Latifπ: πAUREN HA'DI π
_Samira Harouna_
*Wallahi fans ina matuk'ar jin dad'in comment d'inku, bayan _KAUSSAR_, _AUREN HA'DI_ shine na biyu da nafi so*
_Komai wayon amarya sai ansha manta._
```ALLAH KASA MU CIKA DA DUNIYA LAFIYA```
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
*Page*
8β£3β£-8β£4β£
Kwana uku kenan Ummi na fama da matsananciyar mura ga zazzab'i da ciwon kai, sosai Ummi ta fita hayyacinta duk ta susuce kamar ba ita ba, sosai Salman ya tausaya mata halin da take ciki dan yanda yaga duk ta koma ko abinci baya mata dad'i sai abu mai yaji ko tsami.
Yau ta tashi kuma jiki da sauk'i sosai, haka ta wuni har dare ba tare data ji zazzab'i ba, kamar yanda Salman ke kula da ita kullum haka yau ma saida ya bata tea ta tasha mai cinta da lemon tsami sannan ya bata magungunanta tasha yace taje ta kwanta.
Tana shiga d'aki ta kwanta tare da dunk'ulewa cikin bargo tana san tayi bacci, daga k'asan gado ta fara jin motsin abu hakan yasa ta tashi zaune tana zare ido taga daga abun ina zai fito, shiru shiru babu komai amma kuma har yanzu tana jin motsin, a hankali ta sauka daga kan gadon da gudu ta fita daga d'akin ta nufi d'akin Salman.
Salman dake zaune bakin gado da waya a hannu da kuma towel a jikinshi ya nuna wanka zai shiga, kallonta yayi cike da mamaki kafin yace "miye kuma haka zaki shigo wuri babu sallama? yanzu da babu komai a jikina fa kuma sai kice kinga ciji."
Kamar zatayi dariya kuma dai tayi shiru tare da turo baki tana fad'in "to miye a ciki? ai kai mijina ne duk abinda na gani halak d'ina ne."
Wani kallo ya mata tare da jinjina kai yace "uhumm, aiko zan gani."
Mik'ewa yayi zai shiga toilet da sauri ta tareshi tana fad'in "yaya Salman dan Allah bari na fara wanka, idan na fito saika shiga." Ummi ta fad'i hakane saboda a d'akinshi take so ta kwana, bata so yaji wani abu a jikinta da ba kamshi ba koda komai ba zai faru ba.
Zaune Salman yayi yana fad'in "to shiga, amma kiyi sauri."
Tana shiga ta cire kayan jikinta ta fara sakarma kanta ruwa cike da farin ciki, Salman dake zaune k'ofar ya k'urawa ido yayin da zuciyarshi keta sak'a mashi tana kwance mashi, zuciyarshi ce tace "SALMAN kaga wata kyakyawar dama?"
"Hakane, amma ba yanzu ba."
"To sai yaushe kenan?"
"Sai lokacin daya dace."
"Wane lokaci kenan?"
"Akwai abubuwan da nake so na fara gabatarwa kafin wannan."
"Amma ai wannan ba zai hana wannan ba, zaka iya gabatar da wannan kafin waccen."
Salman bai gushe ba har saida zuciyarshi ta gamsu da wannan shawara, tsam ya mik'e ya nufi k'ofa key naga yasa ya rufe tare da kashe fitilar d'akin.
Ido rufe Ummi ke wanka ruwa na sauka har kanta tana jin dad'in ruwan, kamar tafiyar maciji taji a bayanta dan haka ta juyo da iya k'arfinta, Salman ta gani shima dai kamar ita babu komai a jikinshi, da k'arfi taja da baya tare rangad'a k'ara mai k'arfi.
A sukwane Salman ya k'arasa wajenta har saida ya dan ganata da bango sannan ya matse mata baki da hannu yana fad'in "karki sake kimin ihu."
Yanda sukayi kusa sosai ne yasa Ummi jin numfashinta ya fara rauni, kallo d'aya zaka mata kasan a tsorace take jikinta b'ari kawai yake duk idonta sun fito waje, ta k'ame waje d'aya ta kasa motsi numfashinta ne ya fara tafiya da sauri dan haka Salman yace,
"Idan kuwa kika saki kika suma wallahi sai dai na k'arasa ki."
Da sauri tasa hannu ta rufe bakinta hawaye na zarya a kumatunta kallonshi kawai take da ido, jawota yayi tsakiyar panpo ruwa suka fara sauka a jikinsu a haka kuma ya dinga wasa da ita kamar 'yar tsana, ita kam ta daskare waje d'aya.
Saida suka jima a haka kafin ya fito da ita daga toilet d'in ya shimfid'eta akan gado, yanzu kam Ummi ta fahimci da gaske Salman yake dan haka ta yunk'ura danta tashi, da k'arfi Salman yasa hannunshi a k'irjinta ya maida ita kwance tare da mata runfa ya kai bakinshi a kunnenta yace "ki nutsu kefa ba yarinya bace."
Lokacin kam abu d'aya ne ya rage da Ummi zatayi, iya k'arfinta tasa ta fara tureshi daga jikinta tana k'ara had'e da kuka, cizo yakushi duka aika mashi take amma Salman ko motsi.
Ganin abin yayi yawa yasa Salman rad'a mata a kunne "dan Allah Ummi kiyi shiru, karki saka naji maki ciwo wallahi ba zan iya dakatar da kaina ba, idan na tsaya zan iya rasa rayuwata nasan kuma ba zaki bari haka ta faru ba, Ummi ina cikin wani hali mai wuyar fassarawa idan kika barni nayi ni kuma na maki alk'awarin zan fad'a maki komai a game da ciwona da kike san kiji."
Kamar hanjinta zasu fad'o k'asa haka k'irjinta kamar zai fito waje, cikin kuka tace "a'a nidai ka k'yaleni wallahi bana so, tsoro nake ji dan Allah ka rabu dani."
Salman da baya hayyacinshi ko kulata bai sake yi ba har ya fara k'ok'arin shiga hq.
_To daga nan nima nayi waje dan kam yau na deb'o ruwan dafa kaina, falo na dawo na zauna ina jin kukan Ummi amma ba yanda zanyi, karo na farko da naji tausayinta to amma ya za'ayi hakk'ine dole a sauke shi._
Rabin tsawon daren nan Salman akan Ummi yayi shi, ba tare da sarara mata ba ko d'aga mata k'afa, dan Salman yunwarshi ta tsawon shekara hud'u yau saida ya kusan darjeta akan baiwar Allah Ummi.
Tsaye yake a toilet ruwa na sauka tun daga kwanyar kanshi har kan k'afafunshi, Salman yau ji yake kamar ya bud'a k'irjinshi ya fito da zuciyarshi ya rage tsabar farin cikin dake cikinta ko yaji sauk'in farin cikin da yake ciki.
A sannu sannu ya dinga magana da zuciyarshi,
"Ashe wannan itace ni'imar da Khamis yake fad'amin a tattare da mata?"
"Lallai Khamis yayi gaskiya da yace su keda kayan marmari, amma ai nihin gaskiyar maganar shine, mata sune mafi kayan dad'i kuma ni'imar da Allah ya bamu a duniya. "
"Dolenmu mu girmama mata, dole ne garemu mu rarrashe su ko dan samun nutsuwarmu, yanzu na fahimci Khamis da yace ana rarrashinsu."
"Hak'ik'a na zama mafi girman sakarai a duniya, da nake tunanin Ummi ba zata iya dani ba kuma tamin k'aramta, ashe abun ba daga nan take ba, yau gashi Ummi ta canja salon labarin rayuwata."
Lumshe idonshi yayi lokaci d'aya kuma ya bud'e yana tunanin ta yanda zai fuskanci Ummi, haka ya tsarkake kanshi kafin ya fito ya bud'a drower ya d'auko doguwar riga fara tas wacce ta dace da daren ya saka kafin ya kunna fitilar d'akin dan ya taimakawa Ummi.
Da sauri ya rufe bakinshi da hannu lokaci d'aya gabanshi ya fad'i, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un." saida ya maimaita haka har sau uku, da azama ya k'araso wajen Ummi inda fuskarta ke kallo, zubewa yayi akan gwiwoyinshi yana kallon Ummi da idonta ke rufe kai kace gawace in banda numfashin da take a hankali ba zaka tab'a cewa tana raye ba.
A kid'ime ya fara tattab'ata yana fad'in "Ummi na, Ummi dan Allah ki tashi karki min haka, ki tashi dan Allah Ummi karki mutu akan wannan shashashan mahaukacin kuskuren nawa."
Ummi kam azabar da take ji har zaifi ace mutuwa tayi, a hankali ta bud'a idonta da suka kumbura sukayi jawur saboda kuka ta kalli Salman, hannunta ta fara k'ok'arin d'agawa tana so ta mik'awa Salman, Salman na ganin haka yayi saurin rik'o hannunta yana fad'in "Ummi ki tashi ki min magana dan Allah."
Magana ta fara amma ko d'aya babu wanda Salman keji saboda shak'ewar da muryarta tayi, k'ara matsawa yayi ya kara kunnenshi a bakinta yace "kiyi magana Ummi ina jinki."
A shak'e duminta ya fita tace
"ina, ina, ina sonka yaya Salman, ba bana so na mutu ban fad'a maka ba."
Wasu hawaye ne suka fito a idonshi bai san lokacin daya fashe da kuka ba ya k'ara matse hannunta ya had'a da goshinshi yana fad'in "a'a Ummi ba zaki mutu ba insha Allah, zamu rayu tare kuma mu mutu tare, Ummi nima ina sonki so mai tsanani so marar misaltuwa, Ummi ba zan iya rayuwa babu ke ba dan Allah ki taimaka min ki tashi kinji."
Wani tattausan numfashi Ummi ta sauke lokaci d'aya farin ciki ya rufeta, ko a mafarki ba tayi tunanin Salman zai fad'a mata haka ba, amma gashi a zahiri Salman na fad'a mata yana sonta kuma ba zai iya rayuwa babu ita ba.
Murmushi tayi mai kama da kuka har saida hawaye suka zubo a fuskarta, tashi yayi ya had'a mata ruwa ya dawo ya d'auketa yakai cikin bahon wanka ya nasa, da sauri ta rik'e hannunshi tare da fad'in "washsh,zafi"
Zaune yayi bakin bahon yana rike da hannayenta lokacin idonshi suka sauka akan rigarshi data b'ace saboda d'aukar daya mata, dubara yayi ya rufe wajen da hannunshi yana fad'in "kiyi hak'uri kinji Ummi na, insha Allah zaki ji sauk'i, ki yafe min a bisa waoutata."
Sun jima a cikin toilet kafin ya barota ya fito, bakin gadon ya dawo ya sake zubewa akan gwiwoyinshi yana kallon jinin dake kwance akan zanin gadon, ba lallai kaga haka ba a daren farko amma ya dangata da yanda kajewa macen, kai ya girgiza yace "kiyi hak'uri, ba haka na so ba banyi haka da gangan ba."
Wani zanen ya shinfid'a shi ma ya sake wata farar rigar sannan ya koma toilet d'in, ya samu ta gama dan haka ya d'aukota sai kan gado ya direta, rigar bacci ya d'auko mata da kanshi yasa mata sannan ya gyara mata kwanciyarta durk'ushe yayi a gabanta yana shafar fuskarta had'i da kanta har baccin wahala da gajiya ya d'auketa, addu'a ya mata kafin ya mik'e.
Alwala yayi ya dawo raka'a biyu yayi dan ba zai iya yin nisa da Ummi ba, yana sallamewa ya d'auko Alqur'ani ya zauna gefen Ummi saman gadon ya mik'e k'afafu ya fara karanta suratul AN'AM.
dan danan ya kalli Ummi dake saurin sauke ajiyar zuciya saboda kukan da tasha, duk lokacin daya kalleta wani basaraken murmushi ne ke bayyana kan fuskarshi, haka har aka kira sallar asuba, sallah yayi yana kan sallaya ya kalli Ummi yace,
"Na yau kad'ai za kiyi jinkirin sallah, ba zan iya tashinki ba a wannan halin da kike ciki, ki gafarce ni."
Daga nan zaune ya d'ora kanshi akan gadon har bacci ya d'aukeshi, basu farka ba har saida kiran Khamis ya tayar da Salman....
12/03/2019 Γ 13:53 - Mamar Latifπ: πAUREN HA'DI π
_Samira Harouna_
```FARIN CIKIN MARAR MISALTUWA, INA JIN DAD'I MUTANE NA SAI DAI FATAN ALLAH YA BARMU TARE DA MASOYANMU.```πππ
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
*Page*
8β£5β£-8β£6β£
Yana d'aukar wayar Khamis ya fara masifa "yanzu kai dan Allah miye haka? ka wani shige gida ka zauna bayan kasan akwai masu jiranka a waje."
Muryar da yayi magana da ita ne yasa Khamis yasan akwai wani abu, cikin tattausan murya yace "kaga dan Allah karka takura min, kaji da harkokin na yau ba zan samu damar fitowa ba."
"Iye, ba zaka fito ba fa kace, to me yasa?"
"Wannan ba matsalarka bane, kayi abinda nace kawai."
"To naji zanyi, dan naga alama kamar Ummi ta fara juyaka yanda take so."
Maida kallonshi yayi ga Ummi data gyara kwanciyar ta a hankali tare da yamutsa fuska duk da a cikin bacci take, ajiyar zuciya ya sauke kafin yace "zata iya yin duk yanda take so dani, ni Salman nata ne halak d'inta ne ni."
"Ahan, ni kam me Ummi ta baka ne kasha?"
"Kaga kayi abinda ke gabanka, sai an jima."
Yana fad'a ya kashe wayar ya aje gefen gado ya zauna yana ci gaba da kallon Ummi, a hankali ya fara magana da kanshi "ban sani ba ko haka duka mata suke, ko kuma kece kad'ai haka."
"In har haka kuke, to tabbas dole mu godewa Allah daya halitta mana ku, in kuma Ummi nace haka, to hak'ik'a nafi kowane namiji sa'ar mata a duniya, Ummi kin had'u tako ina sai dai na biki da addu'a kawai."
_Hey Salman , stop this nonsence, what do you mean Ummi, π(kaga har kasa na fara sambad'o turanci), mu ma haka jariranmu ke fad'a mana._
Ci gaba yayi da maganarshi bayan hararar daya watsa min,
"Ummi na Allah ya albarkace ki, Allah ya saka maki