Showing 24001 words to 27000 words out of 59965 words

Chapter 9 - JARUMAN DUNIYA Book Complete Littafin yaki Writing by Sarkin Marubutan Yaki .txt

09 Dec 2024

9386

Cikin Ladabi Yace "Ya Shugabana Na ji Dukkan Bayanin ka Sai Da Wani Hanzari Ba Gudu ba, Kasan Cewa Wannan Shine Aiki Na Ƙarshe A Gareka Ma'ana Wanda Da Zarar Na Kammala Zan Samu 'yanci.
Ko da Jin Wannan Batu Sai Dariya Ta Suɓucewa Baddadul-Arus Har da Ƙyaƙyatawa Sai Bisani Ya Shi Fuskarshi Cike Da Annuri Yace " Haba SARKIN SADAUKAI MUTUWAR SARAKAI Mai Ka ke Ci Na Baka Na Zuba Ai Alƙawarin mu Yana Nan Daram, Kamu Wani Abu Da Baka Sani ba Shine Matuƙar Mu Kayi Nasara A Wannan Tafiya Bayan Na 'Yan Taka Zan yi Maka Wata Gagarumar Kyauta Wacce Ni Kaɗai Nasan ta.
Da Jin Wannan Batu Sai Aljani Zamzaru Ya Shimfiɗe Gadon Bayanshi Sarki Baddadul-Arus Ya Hau Ya Zauna 'Yar Shi Uzaima Tayi Koyi Dashi, Sarki Baddadul-Arus Ya Ƙwallawa Hadimin Shi kira Mai Suna Hulaifa Take Ya Tawo Izuwa Gareshi Tare Da Waɗansu Dakaru Ɗauke Da Abin Guzuri Suka Ɗora Bisa Kan Aljani Zamzaru Jikin Na Ƙyarma Tamkar A ce Ƙyat Su Falfala Da Gudu Saboda Matuƙar Tsoro, Sannan Zamzaru Ya Buɗe Manyan FukaFukanshi Ya Ta Shi Izuwa Sararin Samaniya Yana Mai Keta Gajimare Cikin Matuƙar Gudu Tamkar Giftawar Tauraruwa Mai Wutsiya.
Tafiyar Rabin Sa'a A kayi Aka Iso birnin Jarul-Iman Domin Haka Sai Zamzaru Ya Sauka A Turba, Ko da Tsayuwar Sai Baddadul-Arus Ya Buɗe Bakin shi Ya Karanto waɗansu Ɗalasiman Tsafi Yana Gama Rufe Bakinshi Sai Wani Kyakkyawan Tsuntsaye Ma'abocin Kyawun Launi Ya Bayyana A Gareshi, Kawai Sai Tsuntsun Ya Kaɗa fuka-fukanshi Ya Durfafi Hanyar Birnin Jarul-Iman.


A Birnin Jarul-Iman kuwa Sarki Huraisu Na Zaune A bisa karagar mulkinshi, Sanye Da Ƙayatattun Tufafi Na Hamshaƙan Sarakai, Fadawanshi Na Kewaye Da Shi, A Gefe Guda Kuwa Sauran Jama'ar Gari ne Zaune Ana Tafiyar Da Sha'anin Mulki Cikin Annashiwa Da Jin Daɗi.
Ana Cikin Wannan Hali ne Ƙwatsam Sai Aka Hango Wata Ƙyakƙyawar Tsuntsuwa Ta Shigo Fadar, Har Dakarun Dake Tsaro Sun Zare Makamansu Domin Su Afka Ma ta Sai Sarki Huraisu Ya Ɗaga Musu Hannu Yana Mai Nuni Da su Dakata.
Sannu A Hankali Tsuntsuwar Ta iso in da karagar Mulki Take Sai Kawai Aka ga Ta Sauka ƙasa ta Sunkuyar Da Kanta Alamun Tana Miƙa Gaisuwa, Sannan Ta Buɗe Baki Tace" Yakai Wannan Sarki Mai Daraja Kayi Sani Cewa Bakomai Ba ne Ke Tafe Da ni Izuwa Gareka ba Sai Domin Na Gabatar Ma ka Da Aiken Shugabana Sarki Baddadul-arus, Sakon Da Ya Aiko ni Da shi Shi ne, A halin Yanzu Shi Da Tawagar Suna Bakik ƙofar Gari Suna jiran ka Domin Gudanar Da Tafiyar ku Izuwa Birnin Rum, Domin Ɗauko TAKOBIN SIHIRI.
Ko da jin Wannan Batu Sai Fuskar Sarki Huraisu Ta Faɗa ɗa Da Murmushi, Al'amarinDa Yayi Matuƙar Ba wa Jama'a Mamaki Kenan Domin Basu Taɓa Ganin Dabba Mai Hankalin Wannan Tsuntsuwa ba Tabbas Akwai Aiki Na Sihiri A Tattare Da Wannan Tsuntsuwa.
Koda Tsuntsuwar Ta Kammala Wannan Jawabi Sai Kawai Ta Kaɗa Fuka-fukanta Ta Yashi Sama Ta Fice Daga Fadar jama'a Su ka Bi ta Da Kallo.
Kawai Sai Sarki Huraisu Ya Miƙe Tsaye Tsam Daga Kan Karagar Shi Ya Fuskanci Jama'a Sannan Yayi Gyaran Murya Yace "Ya ku Jama'a ta Kuyi Sani Cewa A Yau ne Nake Farin Cikin Sanar Da ku Cewa Zan Shiga Izuwa Duniya Domin Samun Abokiyar Rayuwar Da Nake Da Muradin Aure, Na sani Cewa Kun So ni Tamkar Ɗan Da Ku ka Haifa, Kuma Za ku So Ashe Banyi Ne sa Da ku ba.
Duk Da Cewa Nasan Waɗansu Za Su Ƙalubalance Akan Cewa Duk 'yan Matan Da ke Cikin Birnin Nan Na rasa Wacce Zan Kaunata, Sai Dai Idan Mu kayi Lakari Da Wani Batu Na Masu Iya Magana Da Suke Cewa Garin Masoyi Baya Nisa, Kuma Shi So Ba'ayin Ma shi Dole, Don Haka Za'a Yi Mini Uzuri.
Da wannan Nake Yi Maku Fatan Alkairi Sai Mun Sake Damuwa, I na Mai Bar Muku Waziri Rufyan A Matsayin Halifana Da Zai Cigaba Da Tafiyar Da Sha'anin Mulki.
Ko da Gama faɗin Hakan sai Sarki Huraisu ya taka da Ƙafafunshi Ya Sauko Daga Matattakalar Fadar Ya durfafi Wata Ƙofa, Take Waɗansu ZARATAN MAYAƘA masu Jajayen Tufafi Hannayensu Ɗauke Da Miyagun Makamai Su ka Mara Ma shi Baya, Nan fa Fadar Ta Ruɗe Da Ce-ce ku ce Kowa Na Faɗin Albarkacin bakinshi, In da Waɗansu Ke Nuna Alhininsu Kan Tafiyar Sarki, Wasu Har Suna Zubar Da Hawaye.
Sai Da Sarki Da Dakarun Shi Su ka Ƙule A cikin Wannan Ƙofa Sannan Fadar Watse Kowa Ya Kama Gaban shi.




*****
A can in da Sarkin Baddadul-Arus Da Gimbiya Uzaima Suka Yada Zango Bisa Kan Aljani Zamzaru Suna Jiran Dawowar Wannan Tsuntsuwar Tsafi, Sai Suka Shafe Tsawon Daƙiƙa Talatin A Cikin Wannan Hali, Sannan Tsuntsuwar Ta iso Kuma Ta Bayyana Mashi Dukkan Abinda Ya Wakana Tsakaninta Da Sarki Huraisu, Koda Kammala Bayar Da Saƙon Sai Baddadul-arus Ya Sake Nuna ta Da Hannun shi Ta Ɓat Tamkar Bata Taɓa Wanzu ba.
Daga Can Sai Aka Hango Sarki Huraisu Tare Da Wani Hadimin Shi Sun Durfafo Wajen A bisa Dawakai, Shirye Cikin Gagarumar Shigar Yaƙi Mai Matuƙar Kwarjini Da Ban Tsoro.
Tun Daga Ne sa Uzaima Ta Ƙura Mashi Idanu Ko Ƙiftawa Bata yi, Matuƙar Kyawun Surar Shi Suna Sake Fuzgar Zuciyarta.
Lokacin Da Ya Zamana Tazarar Dake Tsakanin Su Bata Huce Taku Ashirin ba Sai Dawakansu Da Suke A Kai Su ka Yi Turjiya Gami Da Haniniya Suna Ɗaga Ƙafafuwansu Sama Suna Neman Jefo Da su, Bakomai Ne Ya Haddasa Hakan ba Sai Bisa Arba Da Aljani Zamzaru Da Dawakan Su kayi.
Ba Shiri Sarki Huraisu Da Hadimin Suka Kama Linzamin Dawakan Su ka Sauko Ƙasa Haɗe Da Takawa Da Ƙafafuwansu Su ka Durfafi In da Su Baddadul-Arus Su ke Tsaye.
Baddadul-Arus Ya Dube Su Fuskarshi Cike Da Annuri Yace "Lale Marhaban Da Sarki Huraisu Na Birnin Jarul-Iman Kuma GWARZON DUNIYA.
Ko da jin Wannan Batu Sai Dariya Ta Suɓucewa Huraisu Har Fararen Haƙoranshi Suka Bayyana Masu Haske, Ya Ƙurwa Uzaima Idanu Na Ɗan Wani Lokaci Daga Bisani Ya Buɗe Bakinshi Yayi Gyaran Murya Yace "Umh Barkan ku Da Zuwa Ya Abokan Tafiyata, Wannan Da Ku ka Ganni Tare Da shi Hadimi ne Shaibat Da Nake Matuƙar Ƙauna Kuma Ina So ne Ayi Wannan Tafiya Tare Da shi, Shaibat Ya Risina Ga Sarki Ya Miƙa Gaisuwa Sarki Ya karɓa Sannan Yace " Ai Sai Ku Zo Mu Tafi.
Ko da jin Wannan Batu Sai Huraisu Da Shaibat Suka Haye Bisa Kan Aljani Zamzaru Suka Zauna Ne Sa Kaɗan Da In Da Baddadul-Arus da Uzaima Su ke, Sannan Zamzaru Ya Yunƙura Ya Tashi Zuwa Sararin Samaniya Yana Mai Keta Gajimare Cikin Matuƙar Gudu Tamkar Giftawar Tauraruwa Mai Wutsiya.




*****
Fadar ta Ƙawatu ainun Da kayan Ƙawa da alatun jin daɗin rayuwar duniya har da ma abin da Idanu Basu Taɓa Gani ba, Duk ƙasaitar BASARAKE ko Attajiri Idan Ya Tsinci Kanshi A Cikin Wannan Fada Dole Ya Zamo Cikekken Ɗan Ƙauye Kuma Ya Tabbatar Dacewa Gaba Da Gabanta.
Duk inda Mutum Ya Kalla A Fadar Kawunan Bil'adama ne Babu Masaka Tsinke Tamkar DANDAZON kiyashi, 'yan Majalissar Sarki Na Zaune A Bisa Waɗansu Ƙayatattun Kujeru Na Alfarma, Dakarun Duk yiwa Fadar Ƙawanya Ɗauke Da Miyagun Makamai Suna Kai Komo Domin Tabbatar Da Cikekken Tsaro.
Nesa Kaɗan Da in da 'Yan Majalissa ke Zaune Bisa In da aka yi Matattakala Hudu bisa Wani Gayayyen Tudu A Nanne Aka Ajiye Wata Ƙasaitacciyar Karagar Mulki Da Akayi ta Da Zallar Dutsen Zubar Daju Aka Yi Mata Feshi Da koren sinare Ta na Sheƙi Da Ɗaukar Idanun Duk Mai Kallo.
Bisa Karagar Wani Shirgegen Mutum ne Ma'abocin Kasumba Da Gemu Baƙaƙe Siɗik, Sanye Cikin Tufafin Alfarma Irin Na Hamshaƙan Sarakai, Sanye A kanshi Akwai Kambi Na Sarauta Da Aka Sana'anta shi Da Zallar Zinare Da Lu'ulu'u, A Gadon Bayanshi Yana Rataye Da Wata Sharɓeɓiyar Takobi, Kuma Ya Ɗora Ƙafarshi Ɗaya Kan Ɗaya, Takalmin Dake Ƙafar Tashi An yi Ma shi Ado Da Gashin Ɗawisu Yana Canza Launi Lokaci zuwa lokaci, Fuskarshi cike Da Annuri Ana tafiyar Da Sha'anin Mulki.
Ana Cikin Wannan Hali ne Kwatsam Sai Aka Hango Boka Hushaib Ya Bayyana A Fadar Fuskarshi A Murtuke Babu Annuri Tamkar An Aiko Mashi Da Wasiƙar MUTUWA, Ya Zube Ƙasa Ya Kwashi Gaisuwa Cikin Ladabi, Sarki Ya Dube shi Yace "Ya Abin Dogaro Shin Ina Dalilin Zuwan ka A wannan Lokaci ?.
Ko da jin Wannan Tambaya Sai Boka Hushaib Ya Sake Murtuke Fuska Saboda Fushi Har Hatsine Take yi, Sannan Ya Gyara Zaman shi Yayi Gyaran Murya Cikin Kakkausar Murya Mara Daɗin Saurare Yace " Ya Shugabana Kayi Sani Cewa Ba Wani Abu ne Ya Kawo ni A wannan Fada ba Sai Domin Na Sanar Da kai Wata Guguwar Musiba Dake Tunkaro Wannan Birni Namu,
Ta Bayyanar Waɗansu ZARATAN SARAKAI biyu Sarki Baddadul-arus Da Sarki Himras Na Kasar Darul-kushur Domin Su Ɗauke Sarƙar Tsafi Dake Ajiye A Cikin KUSHEWAR Margayi Boka Aulad.
Sanin ka Ne Cewa Fiye Da Shekaru Dubu Uku Baya Ba'a Samu Mahaluƙin Da Ya Taɓa Shiga inda KUSHEWAR Take Ba Har Ya Ɗauke Sarƙar.
Binciken Dana Gudanar Bisa Halarar Tsafina Ya Tabbatar Dacewa Matsawar Mu ka Rasa Wannan Sarƙar Burinmu Zai Faɗa Cikin Musibar Fari, Yunwa, Cututtuka Guda Casa'in Da Tara Waɗanda Basu Da Magani.
Ko da Jin Wannan Batu Daga Bakin Boka Hushaib Sai Hankulan Jama'ar Dake Fadar Ya Ɗugunzuma Ainun, Sarki Kuwa Sai Fuskarshi Ta Canza Daga Annuri zuwa Tashin Hankali Ya Dubi Boka Hushaib Cikin Kaɗuwa Yace " Ya Abin Dogaro na Shin Mene ne Mafita Game Da Wannan Musiba Dake Tunkaro mu ? Kuma Tsawon Kwanaki Nawa ne Su ka Rage Sarakunan Su Iso Nan?.
Da jin Waɗannan Tambayoyi Sai Boka Hushaib Ya Buɗi Baki A karo Na Uku Yace "Ya Shugabana Sarakunan Za Su Iso Wannan Birni Namu ne Nan Da Kwanaki Huɗu,
Mafita Kawai Ita ce Mu yi Shirin Yaƙi Domin Jiran Zuwan su.
Da jin Amsar Wannan Tambayoyi Sai Sarki Usulul-Haibar Ya Miƙe Tsaye Tsam Daga Kan Karagarshi Cikin Matuƙar Fushi Ya Fuskanci Jama'a Cikin Kakkausar Murya Yace "Ya ku Jama'ar wannan Fada Tawa Mai Albarka Kun ji Dai Dukkannin Bayanin Da Boka Hushaib Yayi Sanda Da Haka Kowannen ku Ya Fara Shirin Yaƙi Kuma Ban Ɗaukewa Kowa ba, Domin Kare 'Ya'yanmu Da Dukiyoyinmu Har Ma Birninmu.
Ko da Gama Wannan Jawabi Sai Sarki Usulul-Haibar Ya Tako Matattalar Fadar Ya Sauko Ƙasa, Ya Nufi Wata Ƙofa Ta Musamman A Fadar Dakarunshi Na Take Mashi Baya.
Nan Take Fadar Ta Watse Kowa Ya Kama gabanshi cikin tashin Hankali.




****
Sarki Usulul-Haibar Ibn Zumar Yakasance Ƙasaitaccen Sarki Kuma GWARZON MAYAKI Mai Tarwatsa DANDAZON JARUMAI a filin fama.
Mutum ne Shi ma'abocin tarin dukiya dangin Lu'ulu'u Da Zinare, Yana Matuƙar Ƙaunar Jama'arshi Da Son Ganin Ya kyautata masu, A Jerin Sarakunan Da Su ka Yi Mulki A Birnin Rum Shine Sarki Na Ɗari Uku, Kuma Ba'a Taɓa Yin Sarkin Da Arzikin Birnin Rum Ya Bunƙasa A Zamanin Shi ba Kamar Shi.
A Gaba Ɗaya Nahiyar Babu Birnin Da Yakai Na Rum Saboda Yadda Suka Tara ZARATAN MAYAƘA Masu Juriya A Filin Fama.
Sarki Usulul-Haibar Yana Da Wata kyakkyawar Yara Guda Ɗaya Jal Mai Suna Hulaifa, Gimbiya Hulaifa Yakasance Tsaleliyar Budurwa Mai Kyan Diri Da Sura Tamkar Ita Ce Ta Ƙera Kanta Yadda Take Buƙata, Ta Gaji Mahaifinta A Ƙarfin Damtse Gami Da Son Talakawa, Kuma Ita Ce Kaɗai Ta Rage Ga Usulul-Haibar A Cikin Zuri'arshi.
Bisa Wannan Dalili Ne Ya Sanya Sarki Usulul-Haibar Ke Matuƙar Ƙaunarta Fiye Da Komai A Rayuwar Shi, Baya Son Abinda Zai Ɓata Mata Rai Ko Sa Ta A Damuwa, Domin Akwai Wata Rana Da Wani Hatsabibin Boka Ya Zo Birnin Domin Ya Aure Gimbiya, Sarki Usulul-Haibar Ne Kaɗai Ya Yaƙi Bokan Da Tawagar Shi Bai Bar Ɗayansu A Raye Ba, Tun Daga Wannan Rana Sarakunan Dake Nahiyar Suke Shakkar Sarki Usulul-Haibar Da Girmama Shi, Domin Dai Masu Iya Magana Na Cewa Idan Gemun Ɗan Uwanka Ya Kama Da Wuta Sai Ka Shafawa Naka Ruwa Domin Tsira Da Daraja Da Mutumcin ka .
Wannan Shi Ne Abin Da Ya Wakana A Birnin Rum Dake Yamma Maso Gudancin Duniya.




*****
Lokacin da Aljani Narguz Ya Cigaba Da Keta Sararin Samaniya Yana Ratsa Gajimare Cikin Matuƙar Gudu Tamkar Giftawar Tauraruwa Mai Wutsiya Ɗauke Da Sarki Himras, Yarima Muzaifar, Tsoho kuhairu Da Jaruma Sharilat.
Sai Sarki Himras Ya Dubi Yarima Muzaifar Fuskarshi Cike Da Annuri Ya yi Ajiyar Zuciya Yace "Ya Ɗana Abin Alfahari Naga Kana Cikin Alamun Damuwa, Duk Da Cewar Bansan Mene ne Ya Haddasa Maka Damuwar ba, Bari Na Baka Wani Labari Da Zai Ɗebe Maka Kewa.
Ko da Jin Wannan Batu Sai Yarima Ya ce Ina Sauraren Ka Ya Abbana.
Sarki Himras Ya yi Gyaran Murya Ya Gyara Zama Sannan Ya Fara Dacewa".




****
Kimanin Shekaru dubu ɗaya da ɗoriya bayan zamanin Sarki Nu'umanu na birnin Zainul-Ansar, An yi wata Gawurtacciyar Basadaukiya Mai Suna Nashmira Bintu Abu-Hizam.
Nashmira Takasance Ƙyaƙƙyawa Ta Gaban Kwatance Mai Ƙyan Diri Da Sura Kuma Mace Mai Kamar Maza, Bokayen Duniya Da Masu Hasashe Sun Tabbatar Da cewa, A kaf Nahiyar Larabawa Baƙaƙen Fata Babu Jaruma Mai ƙarfin Damtsenta, Domin An Ce Tana Iya Yaƙar Gari Guda Ta Cinye Su Da Yaƙi, Tana Iya Gudun Sa'a Goma A ƙafa Batare Da ta Gaji ba, Kuma Tana Iya Shafe Tsawon Sa'a Uku Tana Yaƙi Batare Da Ta ci ko Ta Sha ba Ballantana Ta Gaji Har Ayi Mata Ƙwarzane.
A Rayuwar Jaruma Nashmira Babu Abin Da Ta Tsana Fiye Da 'ya'ya Maza, Bakomai Ne Ya Janyo Hakan ba, Sai Domin Tun Da Ta Taso A Rayuwarta A Hannun Mahaifiyarta Ta Girma Ita Ce Ke Kula Da Komai Na Rayuwarta, Duk Sa'adda Nashmira Ta Tambayi Mahaifiyar ta Shin Ina Abbana Yake? Kuma Wane ne Shi Ya Tafi Ya Bar mu A Cikin Wannan Hali Na Ƙuncin Rayuwa?
Sai Mahaifiyarta Ta Ta Kasa Bata Amsar Wannan Tambaya Ta Shiga Zubar Da Hawaye, Nan Take Nashmira Zata Rungume Ta Ta Fashe Da Kukan Baƙin Ciki, Har Mahaifiyarta Ta Rasu Bata Sanar Da ita Wane ne Mahaifinta ba.
Abin Da Nashmira Ta Fahimta Shi ne Tabbas Akwai Wani Rashin Adalci Da Mahaifinta Ya yiwa Ummanta.
Bisa Wannan Dalili Ne Yasanya Nashmira Ta Sha Alwashin Cewa Matuƙar Tana Numfashi A Doran Ƙasa Sai Ta Mayar Da Dukkanin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login