Showing 39001 words to 42000 words out of 59965 words
Chapter 14 - JARUMAN DUNIYA Book Complete Littafin yaki Writing by Sarkin Marubutan Yaki .txt
lokaci sai daga bisani ayarin arnan dajin suka ɗaga makaman su suna ihu da kururuwa mai firgita DANDAZON MAYAƘA a filin daga.
Ko da ganin hakan sai su sarki Himras suka zare kaman su suna masu gyara tsayuwa, shi ma aljani Narguz sai ya zare wani zabgegen gatari a damtsenshi cinyar shi domin yin gumurzu.
Da ya ke arnar dajin sun yi masu ƙawanya ne sun rugo ta ko ina sai jaruma sharilat ta fuskanci na ɓangaren yamma,Muzaifar ya tari na gabas,Himras na arewa, Kuhairu na kudu,
Aljani Narguz kuwa sai ya fuskanci wadanda ke tasowa daga ƙarƙashin ƙasa.
A lokacin da aka haɗu sai aka yamutse da masifaffan yaƙi mai matuƙar muni daban tsoro.
Wohoho! tabbas masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce " idan ka ji ana ga ƙi guda to da gudu ne bai zo ba", kuma haƙiƙa tashin ba'a sa ma shi rana.
Idan gwarzontaka ta haɗu da ƙarfin damtse juriya da naci suka game waje guda dole ne artabu ya zamo abin tsoro da tashin hankali.
Ana fara wannan yaƙi ne dukkan ɓangarorin biyu suka fara gane cewa shayi ruwa ne ba abinci mai nauyi ba, domin kowannen su ya wanzu yana kaiwa abokin gwamin shi sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta.
Duk sa'adda makaman su suka haɗu da juna sai dai kaji an kwantsama wata tsawa tamkar hadari zai gangamo a kece da ruwan sama.
Sai da aka shafe tsawon rabin sa'a ana wannan artabu babu sassauci, al'amarin da ya yi matukar bawa kowane ɓangare mamaki kenan bisa ganin babu wanda ke da rinjaye.
Su dai arnar dajin suna mamaki ne bisa ganin cewa iya tsawon wanzuwar su fiye da shekaru dubu ɗari basu taɓa yin artabu da halittar da ta gagare su ba sai a wanann rana .
Su sarkin Himras kuwa suna mamaki ne bisa ganin cewa dukkanin su suna artabun da dukkan ƙarfin damtsen su da zafin nama amma sun gaza koda yiwa dakarun ƙwarza ne.
Lokacin da ɓangarorin biyu suka zo nan a tunanin su sai zukatansu suka harzuƙa ainun suka sake tsanantawa juna da yaƙi suna kai hare-hare cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta.
Idan sarki Himra,yarima Muzaifar, tsoho kuhairu da jaruma sharilat suka kaiwa arnar dajin sara da makamansu sai kaga ƙura ta tashi ko gezau basu yi ba tamkar dutse suka sara.
Sai da sa'a ɗaya ta sake shuɗewa ana wannan artabu, Ana cikin wannan hali ne wani daga cikin arnar dajin ya shammaci sarki Himras, da kuhairu ya gabza masu naushi a fuska.
A lokaci guda su duka ukun suka rikito daga kan alajni Narguz suna masu kurma ihu, kafin wani daga cikin ya yi wani yunƙuri arnar dajin sun turmushe su sun ɗaure hannaye da ƙafafuwan su da wasu sarƙoƙi, sannan wasu daga cikin arnar dajin suka gabato da wani katon keji da akayi da zallar mulmulallan bakin ƙarfe, suka ɗauki su sarki Himras suka saka su a ciki suka mayar da kejin suka rufe.
Sannan wani narkeken ƙato ya ɗauko wata hodar sihiri a aljihun shi ya busawa jaruma sharilat da aljani Narguz take suka ɓingire ƙasa suka fara minshari.
Cikin matuƙar farin ciki narkeken ƙaton ya ɗauki sharilat ya saɓata a kafaɗarshi tamkar ya ɗauki sillan kara, zaratan samari uku suka ɗaure Narguz da waɗansu sarƙoƙi suka shiga jan shi a ƙasa tamkar wani shirgegen dutse, dakarun uku suka ɗauki kejin da su sarki Himras ke ciki suka aka ɗunguma izuwa cikin daji cikin matuƙar farin ciki.
Sa'adda sarki Himras ya ga halin da suke ciki sai ya shiga yin amfani da ƙarfin shirin shi domin ya ceto rayuwar su amma shiru babu labari.
Al'amarin da ya yi matuƙar dugunzuma hankulan su kenan suka shiga damuwa ainun.
Tafiyar daƙiƙa ɗari biyu kacal aka yi aka fara hango dogayen gine-ginen birnin da aka yi su da zallar duwatsun wuta masu kwarin gaske gami da itace manya-manya.
Lokacin da jama'ar birnin suka hango jaruman su sun dawo daga farauta ɗauke da ganima sai suka cika da matuƙar farin ciki suka fito suka tare su suna masu yi masu kiɗa da kirari.
Sa'adda da su Himras suka tsinci kansu a birnin sai suka cika matuƙar mamakin yadda birnin yakasance, gaba ɗaya gine-ginen birnin an yi su bisa tsari mai ƙayatarwa tamkar alkannar duniya, Gaba ɗaya jama'ar birnin maza da mata yara da manya basa sanye da tufafi sai dai bante na fatun dabbobi da suka rufe tsiraicin su alamun ƙarfin damtse ya bayyana ga maza da matan su, kuma matuƙar yawan su ya huce hankali.
Haka dai arnar dajin suka ci-gaba da tafiya suka ratsa saƙo da lungu na birnin har suka iso ƙofar suka ja suka tsaya can.
Ko da tsayuwar ta su sai wani basamuden kato ya zira hannun shi a damtsenshi ya ciro wani zungureran ƙaho ya kafa a baki ya busa da dukkan ƙarfin shi.
Faruwar hakan keda wuya sai ga jama'ar birnin na tuttuɗowa daga kowace kusurwa a birnin suna taruwa a wajen kafin wani lokaci fadar ta cika maƙil babu masaka tsinke.
Jim kaɗan sai aka hango sarki da tawagar fadawanshi sun shigo fadar.
Shi dai sarkin arnar dajin yakasance basamuden kato mai ƙirar sadaukai, sanye ya ke da tufafi riga da wando na fatar damuwa da suka sha ado da ƙyale-ƙyale na sarauta, a kanshi yana sanye da kambun sarauta,hannun shi riƙe da wani kwagiri na sarauta, a ƙafarshi yana sanye da takalmi da aka yi mashi ado da gashin ɗawisu,
A gefen hannun shi na dama wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa ce tagaban kwatance sanye da doguwar aljanna shuɗiya mai ratsin fatsi-fatsi, gashin kanta baƙi ne siɗik mai ƙyalli ya zuba har izuwa kan gadon bayanta.
Haƙiƙa wannan budurwa ta cika kyakkyawa tagaban kwatance da babu wani ɗa namiji da zai ganta face ya kwaɗaitu da soyayyar ta, Waɗansu irin samudawan dakaru na take masu baya shirye cikin gagarumar shigar yaƙi tamkar za su ci babu sai muzurai su ke yi.
Lokacin da sarki da ayarin shi suka iso wani gayayyen tudu a fadar sai gaba ɗaya jama'ar da ke fadar suka sunkuyar da kawunansu domin girmama a gare su, kuma fadar tayi tsit tamkar mutuwa ta kawo ziyara.
Tsawon daƙiƙa ashirin ana cikin wannan hali sai daga bisani ne sarki ya yi buɗi baki cikin wata irin kakkausar murya mai kama da kukan hali ya ce "ya ku jama'ar wannan fada tawa mai albarka kuyi sani cewa wannan farauta da jaruman mu suka yi a yau cike take da ɗumbin tarihi, sanin kanku ne cewa fiye da shekaru ɗari biyu ba'a taɓa farauto aljani ba sai a yau.
Sa'adda sarki yazo nan azancen shi sai jama'a suka ruɗe da shewa da tafi.
Sarki ya ɗaga hannun shi sama fadar tayi shiru sannan ya cigaba da cewa
"Sanin ku ne cewa mai girma abin bauta kungi zabbuba yana fushi da mu saboda rashin yanka ma shi bil'adama a shayar da jinin shi, Dalilin hakan mun faɗa yunwa da ƙishi da cututtuka,
Ina mai farin cikin sanar da ku cewa kayan mu ya tsinke a gindin gaba, domin a gobe da safe zamu yankawa abin bauta waɗannan fursunoni da aka farauto mana". Ya ƙare Maganar ta shi yana mai yana mai nuna su sarki Himras dake cikin keji da kwagirin dake hannun shi.
Sannan bincike ya tabbatar mini da cewa wannan kyakkyawar budurwa da ke cikin fursunonin ita ce mace ta ƙarshe da zan aura na samu gagarumin ƙarfin sihirin tsafi da jarumta fiye da kowa a wannan nahiya ta mu.
A lokacinne zan ɗaukaka wannan birni namu da ƙabilarmu fiye da kowacce a wannan nahiya.
Ko da jin wannan ƙarin daga bakin sarki sai jama'a suka sa ke ruɗewa da shewa da murna.
Sarki ya juya ya shige gaba yana riƙe da hannun 'yarshi, take tawagar shi suka mara masa baya tare da wannan badakare da ke ɗauke da sharilat a hannun shi, koda suka zo giftwa ta gaban kejin da su sarki Himras ke ciki sai yarima Muzaifar ya lura da kallon da 'yar sarkin arnan dajin ke yi ma shi har suka shige izuwa cikin gidan sarauta.
Sa'adda yarima Muzaifar ya ga an shige da jaruma sharilat izuwa cikin gidan sarauta sai Idanuwanshi suka ciko da ƙwalla ya shiga rusa kuka, Tsoho kuhairu kuwa duk da cewar ya makance amma da ya ji kukan yarima sai da ƙwalla ta cika ma shi idanu.
Ko da shigewar sarki izuwa gidan sarauta sai waɗannan samudawan dakaru suka ɗauki kejin da su sarki Himras ke ciki suka durfafi wata hanya a birnin.
Waɗansu dakarun na daban kuwa suka ɗaure Narguz a jikin waɗansu diraku, suka zare makaman su suka shiga yin rangadi a ƙofar gidan sarautar domin tabbatar da cikekken tsaro.
Sai da dare ya raba su sarki Himras suna zaune a cikin kejin har dakarun dake gadin su suka ta fi wasu sabbi suka zo, batare da an ba su ko da ƙwayar hatsi ba, nan fa ya zamana cewa tsananin yunwa ya addabe su da ƙishi suka fara galabaita ainun a lokaci guda su duka ukun suka fashe da kukan baƙin ciki.
Ana cikin wannan hali ne kwatsam sai su sarki Himras suka ga waɗansu kibbau na sauka a kan dakarun dake tsaron, kafin shuɗewar daƙiƙa ashirin gaba ɗayansu sun sheƙa barzahu,
Shine wane ne ya hallaka waɗannan dakaru ?, Shin yana so n ya ceto rayuwar mu ko kuwa Sharilat ta tsira daga sharrin sarkin arnan dajin?.
Amsar tambayoyin da su Tsoho kuhairu suka kasa bawa kansu kenan kawai suka zuba idanu domin su ga wane ne.
Kwatsam sai suka hango wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa shirye cikin gagarumar shigar yaƙi rataye da kwari da baka a gadon bayanta a gwiɓin cinyarta kusa tana ɗauke da wata sharbebiyar takobi a cikin kuben ta.
Budurwa ta kasance mai matsakaicin kaurin jiki baza a kira ta da doguwa ko gajera ba, gashin kanta baƙi ne dogo siɗik mai ƙyalli ya zuba har zuwa kan Kwankwasonta, cikinta kuwa a shafe ya ke tamkar bata taɓa cin komai ba, tana da kyawun diri, batun hanci,baki,wuya tamkar ita ce ta tsara kanta yadda ta ke buƙata.
Sa'adda Sarki Himras,tsoho kuhairu da yarima Muzaifar suka yi arba da kyakkyawar budurwar sai suka cika da matuƙar mamaki ba wani abu ne ya ba su mamakin ba face sai bisa ganin cewa budurwar ita ce 'ya ga Sarkin arnan dajin.
Tun daga nesa yarima Muzaifar ya lura da irin ƙayataccen kallon da budurwar ke yi ma shi nan take ya ji ya ɗimauce saboda kyawun surar ta.
Lokacin da budurwar ta iso daf da su yazamana tazarar da ke tsakanin su bata huce taku biyu ba sai ta ja ta tsaya cak!, a kayi kallon-kallo, Sannan daga bisani budurwar ta buɗi baki cikin zazzafar murya tamkar sarewa ta ce "ya ku waɗannan fursunoni kuyi sani cewa ba na zo nan ba ne domin wani abu sai domin na ceto rayuwar ku daga sharrin jama'ar birnin mu nasan cewa za ku yi tsammanin cewa ni ma na kasance azzalauma kamar yadda mahaifina ya ke, a rayuwa ta babu abin da na tsana fiye da zalunci gami da ɓakin zaluncin Abbana, babba buri na shine na rabu da jama'ar birnin mu har da mahaifina na tafi can wata nahiya ko da zan rayu a matsayin baiwa.
Na ji a jikina cewa ku ne mutanen da zasu taimaka mini cimma wannan buri nawa na ƙauracewa abbana,
Yanzu idan kun amince za ku cika mini alƙawarin bisa gaskiya ku faɗa mini ni kuma nan take zan buɗe ku dags cikin wannan keji.
Ko da jin wannan jawabi daga bakin budurwar sai kowa ya shiga juya al'amarin a ran shi.
Sai daga bisani ne sarki Himras ya dubi budurwar ya ce " ya ke wannan gimbiya kiyi sani cewa ni da abokan tafiyata mun amince da wannan sharaɗi na ki amma bisa sharaɗin cewa za ki taimaka ki ceto abokiyar tafiyar mu wacce mahaifin ki ya ke shirin aura a gobe.
Ko da jin wannan batu sai budurwar ta yi tattauna murmushi ta ce " in dai don wannanne ba ku da matsala matsawar kun bani goyon baya akan aniyata.
Gama faɗin hakan ke da wuya sai ta nuna kejin da su sarki himras ke ciki da hannunta na hagu tana mai karanta dalasiman tsafi nan take ƙarafan suka fara narkewa suna ɗigewa a ƙasa tamkar ruwa zuwa can sai sarki Himras, kuhairu, da yarima Muzaifar suka faɗo daga cikin kejin tim ! a matuƙar galabaice.
Sannan suka mike tsaye da kyar suna masu ƙarƙaɗe ƙurar da ke jikin tufafin su, a sannanne suka lura cewa har yanzu aljani Narguz na ɗaure a jikin wannan dirka da sarƙoƙi yana sharar barci,
Har sarki Himras ya yunƙura da nufin ya yi wata tsatsuba ya tashi aljani Narguz daga barci sai budurwar ta daga mashi hannu ta na mai nuni da cewa ya dakata ta ce "ya ke wannan jarumi kayi sani cewa bisa dokar wannan birni na mu babu wani tsafi da ya ke tasiri face na mutanen mu, matsawar kayi yunkurin wani sihiri ta ke asirin mu zai tonu, kuma ina so kuyi sani cewa haidar sihirin da aka shaƙawa abokan tafiyar na ku zata ɗauki tsawon sa'o'i kafin ta sake su.
Ko da kammala wannan jawabi sai budurwar ta tsugunna ƙasa ta zare kibbau ɗin da ke jikin dakarun da ta hallaka gami da mayar da su cikin kwanson da ke gadon bayanta,
Sannan ya shige gaba tana mai yafito su sarki Himras da hannunta da ke nuni da su biyo bayan ta, batare da gardamar komai ba kuhairu, Himras,da Muzaifar suka mara mata baya su ka durfafi wata hanya ta musamman a birnin suka bar aljani Narguz kwance yana ta minshari tamkar an yanka raguna arba'in suna kakarin mutuwa.
Sai da aka shafe tsawon daƙiƙa hamsin ana ratsa saƙo da lungu na unguwannin birnin yazamana duk inda budurwar ta ɗauke sawunta nan su sarki himras ke ajiye ƙafafuwan su,
Har aka fara shiga daji ana bishiyu da duwatsu nan fa su sarki Himras suka cika da matuƙar mamaki,
"Wannan fa shi ne masu iya magana ke cewa da ɗan gari akan ci gari yanzu gashi wannan budurwa ya fitar da mu daga birnin su batare da mun fita ta kofa ba".
Sarki Himras ya yi wannan furici a cikin ran shi batare da ya bayyana ba,
Sai da aka samu wani waje mai tattare da ni'ima da ƙoramu sannan aka yada zango bayan an tsaya ne sai budurwar ta cire wata jaka a gadon bayanta ta ɗauko abin guzuri ta miƙawa su sarki Himras, da ya ke suna cikin matuƙar buƙatar abincin nan take suka shiga kimtsa cikin su bayan sun kammala sun sha ruwan ƙorama sun ƙoshi.
A bun ka da waɗanda suka kwaso gajiya nan take suka ɓingire ƙasa suka fara sharar barci a sannanne budurwar ta ƙurawa yarima Muzaifar idanu tana duba irin kyawun halittar shi nan take tsananin ƙaunar shi ya mamaye zuciyar shi.
*****
A can birnin Rum kuwa kamar yadda gimbiya Hulaifa ta ɗaukarwa mahaifinta sarki Usulu-haibar alkawari haka al'amarin yakasance.
A daren ranar da sarki ya kamu da cutar shanyewar ɓarin jiki ne gimbiya Hulaifa ta fara shirye-shiryen tafiya nemo maganin lalurar shi.
A iya tsawon lokaci ne fiye da rabin jama'ar birnin su ka kamu da cutuka daban-daban gami da Annobar fari da yunwa,
Nan fa jama'a suka shiga cikin ƙunci da matsin rayuwa,
A daren kwana na uku ne gimbiya Hulaifa ta sanya aka yi shela a birni da ƙauye cewa ana buƙatar ganin kowa a fada a gobe.
Aikuwa kashe gari tunda duku-dukun