Showing 36001 words to 39000 words out of 59965 words

Chapter 13 - JARUMAN DUNIYA Book Complete Littafin yaki Writing by Sarkin Marubutan Yaki .txt

09 Dec 2024

9370

ya JARUMAR ASALI.
Sa’adda Jaruma Nashmira ta ji wannan jawabi daga bakin jarumi Hufairu ɗan maƙeri kahzib sai ta cika da matuƙar mamaki kuma ta yi shiru ta na mai zurfafa cikin Kogin tunani.


****
Lokacin da sarki Himras yazo dai-dai nan a labarin da ya ke bawa yarima muzaifar sai ya dube shi ya ce “Ana zan tsaya da baka wannan Hikaya ta jaruma Nashmira da Hufairu Ibn kahzib, Domin mu tattauna akan muhimmin abin da ke gaban mu, Sai ka biyo ni Izuwa masaukin su Sharilat amma idan kana son cigaban wannan hikaya sai ka nemi littafin FARAUTAR MAZAJE wanda fashin masanin hikayoyin nan ya wallafa wato SUFI.
Ko da gama faɗin hakan sai sarki ya miƙe tsaye ya fice daga tantin, cikin hanzari yarima ya yi koyi da shi fuskar shi cike da alamun damuwa bisa katse hikiyar jaruma Nashmira da sarki ya yi ma shi.
Da isowar su zuwa bakin tantin sai sarki ya yi gyaran murya sau biyu sannan ya kunna kai zuwa ciki yarima na biye da shi, Suna shiga ciki suka zauna a bisa kujeru dake fuskantar su sharilat.
Da ya ke a wannan lokaci tantin a haskake ya ke da fitilar ice, Suna ganin fuskokin junan su ƙuru-ƙuru sai yazamana Yarima Muzaifar da Jaruma Sharilat na satar kallon junansu cike da tsantsar so da ƙauna.
Sarki Himras Ya shirun da wanzu ta hanyar buɗe baki ya ja gwaron numfashi ya yi gyaran murya ya ce “Ya abokan tafiyarmu kuna da sani akan abin da yafaru tsakanin mu da su Sarki Baddadul-arus na kuɓucewar Sarkar Tsafi daga hannun mu shin yanzu me abin yi ?.
Ko da jin wannan batu daga bakin sarki Himras sai kowa ya yi shiru aka rasa wanda zai ce kala.
Sai daga can tsoho kuhairu ya yi gyaran murya ya ce “Yakai wanan sarki mai daraja kayi sani cewa ai koda su sai sarki Baddadul-Arus sun samu nasarar tashin boka Sharubu daga kushewar shi babu tabbacin zai amince da buƙatar su ta yi masu jagora Izuwa fadar Sarkin bokaye domin ɗauko SIHIRTACCEN KUNDI da takobin sihiri,
Domin masu iya magana na cewa ƙaɗe mage ba yankawa ba ne.
A iya nazarin da na yi game da wannan tafiya tamu, Tunda dukkanin mu Sadaukai ne majiya ƙarfi za mu iya jure duk wata musiba da bala’i, Zai yi kyau mu tafi kai tsaye zuwa fadar Sarkin bokaye domin ɗauko takobin sihiri, Tun da dama saboda ita ne zamu nemi buƙatar boka Sharubu.
Lokacin da tsoho kuhairu yazo nan a jawabin shi sai kowa ya cika da matuƙar farin ciki, Domin suna ganin cewa kuhairu ya kawo shawara mai kyau.
Shiru ne ya mamaye wajen a karo na biyu sai daga bisani sarki Himras Ya dubi kuhairu cikin alamun matuƙar damuwa ya ce “ Ya kuhairu haƙiƙa ka kawo shawara mai kyau sai dai ina so ka kiyi tunanin cewa ta ya zamu mallaki SIHIRTACCEN KUNDI bayan cewa boka Sharubu shine yasan dokokin tafiyarmu?
Ko da jin wannan tambaya sai kuhairu ya yi guntun murmushi mai kama da yaƙe sannan ya dube shi ya ce “A wasu lokutan ilimin tsafi yana bayyana mana abinda ba zai tabbata ba, Abin da za ka yi nazari akai shi ne shin kafin a mallaki SIHIRTACCEN KUNDI ne boka Sharubu zai yi amfani ko kuwa bayan an mallaka, Idan kana so ka tabbatar da hakan sai ka sa ke gudanar da bincike bisa halarar tsafin ka kafin wayewar gari.
Sa’adda sarki Himras ya ji wannan ƙarin bayani daga bakin tsoho kuhairu sai ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa, Batare da wani ɓata lokaci ba su ka yi bankwana da su Sharilat su ka koma Izuwa tantinsu.
Wannan shi ne abin da ya wakana a bangaren su Sarki Himras.


******
Al’amarin su Sarki Baddadul-arus kuwa, Tun sa’adda aljani Zamzaru ya ɗauke su daga filin yaƙi, Bayan sarki Baddadul-Arus ɗin ya samu nasarar kwace Sarƙar tsafi daga hannun Sarki Himras a cikin ɗakin kushewar boka Aulad.
Sai Zamzaru ya cigaba da tsala azababban gudu babu sassauc, Ana cikin wannan tafiya ne Gimbiya Uzaima ta sunkuyar da kanta ƙasa ta yi shiru tana mai zurfafa cikin Kogin tunani.
Abu na farko da ya faɗo mata a rai shi ne tabbas zuciyar ta ta kamu da matuƙar kaunar sarki Huraisu wacce baza ta iya jin kira ba, Shin yanzu ta wace hanya zan bayyana ma shi sirrin dake zuciya ta, Wani ɓangaren kuwa na cewa da ita idan ki ka yi haka kin zubar da darajar ki da ƙimar ki, Wai shin ma kin manta ne cewa sarki Huraisu ya yi wannan tafiya da ku ne domin ya samu irin macen da ya ke da burin ya aura, Kenan yanzu ke kina yin son maso wani ne ƙoshin wahala.
Sa’adda gimbiya Uzaima tazo nan a tunanin ta sai hankalin ta ya ɗugumzuma ainun.
Yanzu duk tsananin kyawuna da ‘ya’yan sarki ke mutuwa saboda da soyyayya ta amma ace yau ni ce wani namiji zai yi tarayya da ni fiye da Sa’a ashirin amma bai kamu da SO na ba.
Aɓangaren sarki Huraisu kuwa babu abinda ke yi ma shi yawo a zuciya face ya lura da irin kallon da gimbiya Uzaima ke ma shi a lokacin da suke fafata yaƙi tabbatar ya nuna ta kamu da matuƙar ƙaunar shi.
Amma kuma ai Uzaima ba ta cika sharuɗɗan da nake so wacce zan rayu da ita ta kasance ba, Wato ta ɗara ni a baiwa, Kuma ta yi tsawon sa’a goma tare da ni batare da kamu da so na ba duk da irin. Matuƙar kyawuna, Haka dai sarki Huraisu ya cigaba da wannan tunani.
Ana cikin wannan hali ne sarki Baddadul-Arus ya ji Jikin shi ya na yi ma shi tsami sakamakon raunukan da ya samu a filin yaƙi. Kuma ga shi duhun dare ya fara kawo kai don haka sai ya umarci aljani Zamzaru da ya sauka a turba.
Bayan sauka ne sa aka kafa tantuna kowa ya shiga yin kalaci, Shi kuwa Baddadul-Arus sai ya cire sulken yaƙin dake jikin shi ya sanya kanshi magani kawai sai ya kwanta bisa gadon shi ya fara sharar barci.
Wannan shi ne abin da ya wakana da tawagar sarkin Baddadul-arus.


******
Lokacin da likitocin birinin Rum su ka duƙufa akan sarki Usulul-Haibar domin ceto rayuwar shi.
Sai suka shafe tsawon sa'a ɗaya amma ba su ga ya yi wani motsi ba, Al'amarin da ya yi matuƙar dugunzuma hankalin su kenan.
Ana cikin wannan hali ne boka Hushaib da Gimbiya suka bayyana a gare su cikin tashin hankali.
Ya yin da suka iso daf da gadon da sarki ke kwance sai shugaban likitocin wani dattijo mai kakkaura mai cikar Kamala ya dubi boka Hushaib cikin ladabi ya ce "Ya shugabana dukkan ƙoƙarin mu ya gaza na ceto rayuwar sarki abu ya ci tura.
Ko da jin wannan batu daga bakin likita zayyan sai hankalin boka Hushaib da Gimbiya ya sake dugunzuma ainun.
Cikin matukar damuwa Gimbiya ta matsa daga da inda sarki ke kwance ta zauna a gefen gadon tana mai ƙura ma shi idanu.
A dai-dai wannan lokaci ne boka Hushaib ya ɗagawa likita zayyan hannu, Kamar zayyan yasan abin da ya ke nufi sai kawai ya ja tawagar shi su ka fice daga turakar yazmana cewa saura mutum uku kacal, wato Gimbiya Hulaifa, Hushaib da sarki Usulul-Haibar.
Ko da ficewar su likita Xayan sai boka Hushaib ya shiga yin wasu 'yan tsibbe-tsibben shi ya na mai zagaya izgar tsafin shi akan sarki usulu-haibar.
Sai da daƙiƙa ɗari biyu ta shuɗe a cikin wannan hali ne har Hushaib ya jiƙe sharkaf da gumi tamkar an tsoma shi a ƙaramar, Amma bai ga sarki usulu-haibar ya yi motsi ba.
Al'amarin da ya dugunzuma hankalin shi tare da gimbiya Hulaifa, Har gimbiya Hulaifa ta fara zubar hawaye domin ta na ganin cewa shi kenan sarki ya mutu.
Ana cikin wannan hali ne sai kawai aka ji sarki usulu-haibar ya saki ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ya ja gwauron numfashi sannan ya buɗe idanunsa shi a hankali.
Cikin matuƙar farin ciki gimbiya Hulaifa ta rungume mahaifinta su duka biyun suka fashe da kukan farin ciki.
Tsawon daƙiƙa ashirin a cikin wannan hali ne sai daga bisani ne gimbiya ta janye jikinta daga na shi, Usulu-haibar ya yunƙura domin ya miƙa zaune amma sai ya ji sashin jikinshi na hagu ya yi ma shi nauyi bazai iya tashi ba.
Ko da ganin hakan sai boka Hushaib ya karanto waɗansu dalasiman tsafi ya na mai nuni da yatsanshi na hagu ga ɓarin jikin sarki na hagu.
Kawai sai aka ga fuskarshi ta canza daga annuri izuwa ɓacin rai, Idanuwanshi suka kaɗa suka yi jajur tamkar garwashin wuta ya dubi gimbiya cikin alamun matuƙar damuwa ya ce "Ya shugabata ina mai baƙin sanar da ke cewa mahaifinki ya kamu da cutar shanyewar ɓarin jiki, Kuma shine mutum na farko da ya taɓa kamuwa da ɗaya daga cikin cututtukan da za su addabi al'ummar mu sakamakon suɓucewar sarƙar tsari mai daraja daga wajen mu.
Ko da jin wannan jawabi daga bakin boka Hushaib sai gimbiya Hulaifa da sarki Usulu-haibar suka sake rungume juna a karo na biyu suna masu fashewa da kukan baƙin ciki.
Al'amarin da je fa tausayi a zuciyar boka Hushaib kenan har ya ji kwalla ta cika ma shi idanu.
Daga bisani ne gimbiya ta janye jikinta daga na sarki ta dubi Hushaib fuskarta sharkaf da hawaye ta ce "Ya abin dogaro shin yanzu ta wace hanya mahaifina zai warke daga wannan lalura da ta same shi?.
Sa'adda boka Hushaib ya ji wannan tambaya daga bakin gimbiya Hulaifa sai ya yi shiru yana mai sunkuyar da kanshi ƙasa ya shiga dogon nazari.
Daga can sai ya dago da kanshi sama ya dubi gimbiya Hulaifa ya yi gyaran murya sannan ya buɗe baki ya ce "Ya tauraruwar birnin Rum ki sai cewa mai martaba da dukkan wanda ya kamu da wata cuta a wannan birni namu da ya kamu da da wata cuta ba zai taɓa warkewa ba face yasha ruwan sassaken wata itaciya wacce a halin irin gud ɗaya ce jal ta rage a duniya bishiyar ta na cikin wani kogon dutse da ke cikin dajin sarirul-maut da ke yammacin duniya.
Kafin mutum ya isa dajin inda bishiyar Shajarul-kair ta ke dole ne sai ya ƙetare waɗansu miyagun dazuka.
Daji na farko yakasance na waɗansu hatsabiban kuraye sara da suka ba sa tasiri a kan su, tsakanin ƙarfin damtsen su da yawan ya huce tunani.
Daji na biyu na wani hatsabibin maridi ne saboda shirin shi yana ina canza siffa duk yadda ya ke so, ƙarfin damtsen mutum bazai ƙwance shi ba face matuƙar sa'a da rabi.
Na ukun kuwa yakasance na waɗansu miyagun mayaƙan aljanu masu shan jinin bil'adama, A halin yanzu sun shekara goma ba su sha jinin ba don haka suna cikin matuƙar buƙata.
Daji na uku na waɗansu baƙaƙen macizai ne marasa adadi, ba sa da wani abin kalaci da ya huce shan kwanyar bil'adama.
Daji na biyar na wani zakin sihiri ne wanda ɓarin jikin shi na wuta ne ɗayan ɓarin kuwa na ƙanƙara ne, a halin yanzu babu wata dabba mai ƙarfin damtsen shi.
Daji na ƙarshe na wata aljana ne da ake yiwa laƙabi da zaitul-ukub, bincike ya tabbatar da cewa a halin yanzu babu matsafiya tamkar ta, wasu ma na na ganin cewa ita ce uwar bokayen duniya.
Bayan mutum ya samu nasarar ƙetare waɗannan miyagun dazuka bazai iya sassaƙar bishiyar Shajarul-kair ba face ya mallaki wata takobin sihiri.
Takobin sihiri takasance mallakin sarkin bokayen duniya boka Ayyamul-layal, takobin ce kaɗai za ta iya tasiri akan Shajarul-kair.
Sa'adda boka Hushaib yazo nan a jawabin shi sai hankalin gimbiya Hulaifa ya dugunzuma ainun ta dubi Hushaib a karo na biyu ta ce "Ya masanin ilimin tsafi shin a ina ne zamu samo takobin?.
Hushaib ya ce"A halin yanzu takobin na ajiye ne a fadar Sarkin bokayen kuma sarakunan da suka zo wannan birni namu suka raba mu da sarƙar daraja sun yi haka ne domin mallakar takobin domin ɗayan su ya samu nasarar hallaka abokin gabar shi don ya zamo sarkin sarakunan nahiyar su.
Ko da jin wannan ƙarin bayani sai gimbiya Hulaifa ta ɗora hannayenta akan kafaɗun mahaifinta ta ce "Ya Abbana ina mai yi maka alƙawarin cewa za shiga duniya ba zan dawo ba face na samo maganin da zai warkar da kai daga wannan lalura.
Sa'adda Hulaifa tazo nan a zancenta sai duk su biyun suka sa ke fashewa da matsanancin kuka mai tsuma zuciya gami da ban tausayi.


*****
Kamar yadda tsoho kuhairu ya faɗa haka al'amarin yakasance, wato tunda duku-dukun safiya bayan kowa ya ɗauko abin kalaci ya ci ya ƙoshi an kammala shiri tsaf, Sai Aljani Narguz ya ɗauke su su duka huɗun ya tashi izuwa sararin samaniya ya shiga tsala azababban gudu domin isa fadar boka zammar.
Sai da aka shafe tsawon kwanaki ashirin ana tafiya babu sassauci, Yazamana cewa babu abinda ke sanyawa a yada zango face idan wani zai yi bawali ko lokacin barci ya yi, kuma ba a haɗu da wani abu mai cutarwa ba.
A ranar kwana na talatin ne aljani Nargzu ya sauke su a cikin wani ƙasaitaccen daji, shi dai dajin yakasance yana ɗauke da waɗansu irin bishiyu baƙaƙe,duwatsu, kwazazzabai da sarƙaƙiya haɗi da ƙoramu, hakan ne yasanya duhu ya mamaye dajin.
Nan fa kowa ya sha jinin jikin shi domin ko ba a ce komai ba dole ne a samu halittu masu cutarwa a cikin dajin.
Sai da aka shafe tsawon daƙiƙa ashirin ana tafiya a turba,
Wohoho! haƙiƙa rashin sani yafi dare duhu" inda ace su sarki Himras sun san abinda zai faru da ba su yi gangacin shiga dajin ba.
Ana cikin wannan tafiya ne kwatsam bazato babu tsammani sai aka ga waɗansu miyagun mayaƙa na fitowa daga kowa ce kusurwa a dajin.
Su dai dakarun sun kasance masu ƙirar samudawan farko sun tara ƙwanji tamkar duwatsu aka cusa masu, suna ɗauke da miyagun makamai ma su barazana ga rayuwar bil'adama, adadin su haura dubu hamsin da ɗoriya.
Tabbas wadannan dakaru sun cika abin tsoro domin komai dakewar zuciyar jarumi idan ya yi arba da su dole ya ɗimauce ya yi nadamar wanzuwar shi a doron ƙasa.
Dakarun sun kasance arnar daji sun wanzu a dajin fiye da shekaru dubu, a duk sa'adda da suka tare ayarin fatake zasu kai su ga shugaban su ya aure mayen ciki mazajen kuwa a kai su kurku ba ci ba sha azaba ce zata hallaka su.
Sa'adda sarki Himras,yarima Muzaifar, tsoho kuhairu,jaruma sharilat da aljani Narguz su ka yi arna da dakarun sai suka ɗimauce ainun, domin a iya tsawon rayuwar su basu taɓa gani ko jin halitta mai kwarjini tamkar su ba.
Shi kanshi aljani Narguz duk da kasancewar shi gwarzon mayaƙi sai da ya firgita ainun.
Nan fa aka fara kallon kallo tsakanin su da arnar dajin na wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login