Showing 51001 words to 54000 words out of 59965 words

Chapter 18 - JARUMAN DUNIYA Book Complete Littafin yaki Writing by Sarkin Marubutan Yaki .txt

09 Dec 2024

9367

Cikin matuƙar zafin nama Humairu ya miƙe tsaye zumbur ya raba ƙafafuwanshi akan wuyan sarki Shabbar ya dube shi ya ce a lokacin da ya ke kakarin mutuwa ya "Ya kai wannan sarki yanzu gashi kana kan gaɓar mutuwa shin bazaka bada gaskiya da Ubangijin da ya haliccin duniya da abin da ya ke cikin ta ?.
Ko da jin wannan batu daga bakin Humairu sai sarki Shabbar ya bushe da dariyar ƙarfin hali ya furzar da gudan jini daga bakin shi, sannan ya dubi Humairu Muryar shi na sarƙewa ya ce "Ya kai wannan hatsabibin jarumi ka yi sani cewa lokacin ina yaro ƙarami mahaifiya ta ta taɓa faɗa min cewa akwai wani addini na gaskiya ba namu na bautar gumaka ba,
Sai dai baza mu bi addinin ba saboda ba shi ne mu ka Gada a wajen zuri'ar mu ba,
Ni ma tun da iyaye na basu bi addinin ba ni ma bazan bi shi ba.
Ko da sarki Shabbar ya zo nan a zancen shi sai ya sanya hannayenshi ya murɗewa kan shi wuya ya sheƙa barzahu ko shurawa bai yi ba.
Nan take Jarumi Humairu ya cika da matuƙar baƙin ciki bisa ganin yadda sarki Shabbar bai ƙarɓi addinin musulunci ba.
A dai-dai wannan lokaci ne sauran dakarun marigayi Shabbar suka zubar da makaman su suka yi mubaya'a bisa ganin an kashe shugaban su,
Kawai sai Humairu ya taka da ƙafafuwanshi har izuwa inda gimbiya Mashlira ke kwance ya karanta ayatullah kursiyyu ya tofa ma ta take igiyoyin da suka ɗaure ta suka ɓace ɓat kuma ta miƙe tsaye cikin ƙoshin Lafiya tamkar babu wani abu da ya shafe ta.
Ta dubi Humairu cikin annurin fuska ta ce "Ya kai SARKIN SADAUKAI ka yi sani cewa tabbas a yanzu zan cika maka alƙawarin da na yi na ƙarbar addinin musulunci,
Sai dai kafin hakan ina roƙon wata alfarma a wajen ka?, alfarmar kuwa ita ce ina so ka amince mani na bika duk inda zaka a cikin wannan duniya.
Ko da jin wannan batu sai Humairu ya sunkuya kanshi ƙasa yana nazari, daga bisani ya ɗago da kai ya ce "Na amince da wannan alfarma ta ki amma kuma yanzu muka tafi tare wane ne zai cigaba da riƙe sarautar birnin ku?.
Da jin wannan tambaya sai Mashlira ta yi murmushi ta ce "Ba buƙatar na ɗauki nauyin al'umma akai na zan ɗora dukkanin wanda ya dace a bisa KARAGAR MULKI.
Ko da gama faɗin hakan sai ta ƙwallawa wani badakare kira daga cikin dakarun su, badakaren ya bayyana gabanta ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa,
Mashlir ta ce "Ya kai Luhzul ka yi sani cewa ina so ka sanya a busa ƙahon shela ina so kowa ya taru anan.
Ko da jin wannan umarni sai barde Luhzul ya risina ya ce "An gama ya shugabata,
Yana gama faɗin hakan ya koma gefe guda ya hau bisa wani dogon gini ya ɗauko wani zungureran ƙaho a aljihun shi ya kafa a baki ya busa da ƙarfi, ƙarar sautin busar ya mamaye wajen ya amsa kuwwa izuwa cikin birnin,
Faruwar hakan ke da wuya sai ga jama'a na tuttuɗowa daga kowa ce kusurwa, saƙo da lungu, maza, mata, yara da manya suna taruwa a waje guda,
A dai-dai wannan lokaci ne yarima Muzaifar ya hangi jaruma Sharilat a cikin dandazon jama'a ta rugo zuwa gare shi fuskarta cike da annuri.
Abin da yarima bai sani ba shi ne bakomai ne ya hana Sharilat ta fito daga cikin gidan sarautar sarki Shabbar ba ba,
Sai domin sihirin da ya yi mata bai karye ba sai da ya mutu sannan sihirin ya karye.
Ya yin da Sharilat ta iso daf da su sarki Himras sai ta rungume mahaifin ta tsoho kuhairu su duka biyun sun fashe da kukan baƙin cikin rabuwa da juna, sun ɗauki tsawon lokaci a cikin wannan hali sannan daga bisani Sharilat ta janye jikinta daga na mahaifin ta ta jefi yarima Muzaifar da wani irin ƙayataccen murmushi mai tattare da tsantsar SO da ƙauna.
Sannan ta mayar da duban ta ga Humairu ko da ta haɗa idanu da shi sai ta ji tsikar jikinta ta tashi kuma wani abu ya ɗarsu a zuciyarta wanda ya kasa tantance ko mene ne?.
Ashe duk wannan abu da ke faruwa tsakanin Humairu da Sharilat, sa'adda ya ga irin kallon da Sharilat ke yiwa Humairun sai ya ji kishi ya turnuƙe shi ya ce a cikin ran shi shin me Sharilat ke nufi da wannan kallon da take yiwa Humairu?.
A inda wani ɓangare a zuciyarshi kuma ke cewa da shi baka tunanin cewa matuƙar mamakin ganin Humairu ne ya sa ta ke yi ma shi wannan kallo? ba wai don ta kamu da soyayyar shi ba, amma kuma masu iya magana na cewa labarin zuciya a tambayi fuska, tabbas kallon da Sharilat ke yi ma shi akwai alamun soyayya.
Amsar tambayoyin da yarima ya kasa bawa kan shi kenan, nan take ya ji zuciyarshi ta yi ma shi ƙunci.
Lokacin da kawo ya kammala hallara a filin sai gimbiya Mashlira ta ɗaga hannunta kowa ya tsuke bakin shi tamkar mutuwa ta gifta, ta kawo gworon numfashi ta ajiye sannan ta yi gyaran murya cikin tattausan lafazi "Ya ku jama'ar wannan birni namu mai albarka ku yi sani cewa fiye da shekaru ashirin mahaifina sarki Shabbar na shimfiɗa mulkin KAMA KARYA amma ba a samu wani mahaluki da lashi takobin kawo KARSHEN ZALUNCI na abbana sai wannan baƙon jarumin da ya ke tseratar da rayuwar mu daga sharrin sarki,
Na sani cewa da yawa daga cikin ku suna bin abbana ne saboda tsoron makircin shi ne saboda babu yadda za su yi.
Da wannan nake yi maku fatan alheri da cewa kowa ya samu 'yanci zan ƙarɓi addinin wannan Jarumi domin haƙiƙa shi ne addinin gaskiya.
Sa'adda gimbiya Mashlira ta zo dai-dai nan azancen ta sai ta juya ya dubi Humairu ta ce "Ya kai SARKIN SADAUKAI yanzu a shirye nake ka shigar da ni addinin ka mai daraja.
Ko da jin wannan batu daga Mashlira sai Humairu ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa ya karantawa Mashlira kalmar shahada ta maimaita, nan take ya yi kabbara da salati domin nuna godiyar shi ga Allah,
Kana ya buɗi baki ya dube ta fuskarshi cike da annuri ya ce "Ya ke Mashlira ki yi sani cewa daga yau kin zama 'yar uwata a musulunci duk wani hukunci na addini ya hau kan ki.
Koda jin wannan batu sai Mashlira ta juya ta fuskanci jama'ar ta ta karanta masu kalmar shahada dukkanin su suka maimaita, nan fa farin ciki ya sake mamaye zuciyar Humairu ya yi godiya ga Allah bisa shiryar da ma'abota bautar gumaka izuwa TAFARKIN GASKIYA.
Har Mashlira ta juya da nufin ta shige izuwa cikin gidan sarauta sai kawai aka jiyo ƙarar takun sawaye da haniniyar dawakai daga can bakin ƙofar gari, cikin hanzari kowa ya waiga domin aka kowa su wane ne?.
Ya yin da aka yi arba da su sai aka shiga yin kallon-kallo tsakanin su da jama'ar birnin,
Ba wasu ba ne face boka Hushaib, gimbiya Hulaifa da Sarkin yaƙi Nuhairu, duk daga nesa su boka Hushaib suka ƙurawa su sarki Himras idanu fuskokinsu a murtuke babu annuri.
Abu na farko da ya faɗowa su boka Hushaib a rai shi ne, tabbas su sarki Himras da su ke nema ruwa a jallo domin ɗaukar fansa akan raba su da sarƙar tsafin su mai daraja?.
Shin yanzu za su tattauna da Humaira ne domin tunkarar matsalar da ke gaban su?.
Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kan su kenan, lokacin da yazamana tazarar da ke tsakanin su da jama'a ba sai suka ja linzamin dawakan su suka tsaya cak.
Ciki maɗaukakiyar murya boka Hushaib ya buɗi baki ya ce "Ya ku jama'ar wannan birni ku yi sani cewa bakomai ne ya kawo mu gare ku sai domin mu sadu da Jarumi Humairu ma'abocin addinin Musulunci.
Ko da jin wannan batu daga bakin Hushaib sai Humairu ya taka da ƙafafuwanshi ya durfafi inda suke jama'a suna masu darewa suka buɗe ma shi hanya, ya yin da ya isa gare su sai ya dube su ɗaya-bayan-ɗaya ya yi gyaran murya ya ce cikin annurin fuska "Ya ku waɗannan baƙi masu daraja kuyi sani cewa tun kafin zuwan ku Ubangiji na ya bayyana mani buƙatar ku da zuwan ku nan a cikin mafarki na,
Abin da ke tafe da ku ɗin shi ne kuna so na yi maku rakiya izuwa ɗauko TAKOBIN SIHIRI daga nan a nemo Shajarul-kair wacce za'a yi amfani da ita ne wajen saro sauwar bishiyar, domin warkar da al'ummar birnin ku da cututtukan da suka addabe su sakamakon suɓucewar sarƙar tsafin ku.
Ko da jin wannan jawabi daga bakin Humairu sai su boka Hushaib suka cika da matuƙar mamaki da al'ajabi.
Boka Hushaib ya yi gyaran murya a karo na biyu sannan ya kawo gwaron numfashi ya ajiye ya ce "Ya kai jarumi ma'abaocin al'ajabi ka yi sani cewa haƙiƙa mun yi matuƙar mamakin yadda aka yi ka san da buƙatar da ke tafe da mu izuwa gare ka, muna fatan za ka biya buƙatar cikin abinda bai gaza kwanaki ƙalilan ba ?, Sannan ka faɗi ladan da za mu biya ka da ya danganci zinare, jauhari da yaƙut.
Ko da jin wannan batu daga bakin boka Hushaib sai jarumi Humairu ya yi murmushi mai taushi da ya daɗawa fuskarshi kwarjini ya dubi Hushaib ya ce "Ya kai wannan dattijo ka yi sani cewa na amince zan biya maku buƙatar ku amma abin da kawai na ke buƙata ku bayar da gaskiya da Ubangiji na.
Ko da jin wannan batu daga bakin Humairu sai boka Hushaib ya ce "Ka ɗan bani lokaci zan tattaunawa da abokan tafiya ta,
Humairu ya gyaɗa kai alamar gamsuwa.
Boka Hushaib matsa kusa da su Hulaifa inda ya dube su ya ce "Yanzu dai kun ji abin da Humaira ya ce shin yanzu kuna ganin za mu amince da buƙatar shi ta imani da Ubangijin shi bayan cewa namu abin bautar na tare da mu ba ku tunin cewa zai yi fushi da mu?.
Ko da jin wannan batu sai gimbiya Hulaifa ta buɗe baki a karo na farko ta yi gyaran murya ta ce "Ya abin dogaro ina ganin fa babu wata hanya da za mu bi face mu amince da buƙatar Humairu domin bijirewa hakan tamkar rushe birnin mu ne baki ɗaya".
Cikin ladabi sarkin yaƙi Nuhairu ya dubi gimbiya ya ce "Ina ganin abin bautar mu ya fi kowa sanin halin da mu ke a ciki me ya sanya bai kawo mana ɗauki ba shin mene ne amfanin Ubangijin da bazai share hawayen bayin shi ba,
Amincewa da buƙatar Humairu shi ne mafita kawai, sannan ina so na ja hankalin mu kada wani a cikin mu ya yi yunƙurin ɗaukar fansa akan su sarki Himras domin hakan zai rushe cikar burin mu baki ɗaya.
Sa'adda boka Hushaib ya ji wannan batu daga bakin sarkin yaƙi Nuhairu sai ya gyaɗa kai alamar gamsuwa, sai kawai ya durfafi inda Humairu ke tsaye ya dube shi ya ce "Ni da abokan tafiya ta sun amince da buƙatar ka kuma ba zamu taɓa yaudarar ka ba.
Sa'adda Humairu ya ji wannan batu sai ya a cika da matuƙar farin ciki ya yi wa gimbiya Hulaifa wani kallo mai ɗauke da alamar tambaya da ya sanya su dukan biyun zukatan su suka buga da ƙarfi.
"Ya ku zauna da ni a wannan birni zuwa wani lokaci kaɗan kuna cikin kulawa ta, sannan mu shirya tafiya.
Humaira ya yi wannan furici yana satar kallon Hulaifa.
Ko da gama faɗin hakan sai jarumi Humairu ya juya ya shiga gab, boka Hushaib, gimbiya Hulaifa da sarkin yaƙi Nuhairu na biye da shi suna masu sakarwa dawakan su linzami, nan take aka ɗunguma izuwa cikin gidan sarauta shi ma aljani Narguz ya yi koyi da su.

*****
Lokacin da wannan macijiya mai kawuna casa'in da tara ta shiga kaftawa su sarki Baddadul-arus sara a dukkan sassan jikkunan s. sai nan take dukkan su suka taƙarƙare suka kurma wawan ihu sakamakon raɗaɗi da azabar da suka ji.
Amma saboda JURIYA DA BAJINTA irin ta hamshaƙan sarakai kuma JARUMAN DUNIYA a cikin wannan hali ne suka zare makaman su suka shiga kaiwa macijiyar sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da nacin tsiya.
A duk sa'adda makamansu suka sari jakinta sai su ji tamkar dutse suka sara ko gezau ba ta yi sai dai tartsatsin wuta ya tashi gami da ƙara mara daɗin saurare.
Al'amarin da ya yi matuƙar dugunzuma hankalin su sarki Baddadul-arus kenan suka shiga damuwa ainun bisa ganin babu alamun nasara, sai da aka shafe tsawon rabin sa'a da daƙiƙa hamsin ana wannan artabu babu sassauci, yazamana cewa babu alamun nasara ga ɓangaren su Baddadul-arus amma ita macijiyar ta yi masu sara fiye da goma.
Wohoho haƙiƙa tashin hankali ba'a sa masa rana, wutar bala'i kafin ta zo ake tunanin ya za a yi da ita, idan kuwa ta zo sai dai a nemi mafita kawai, lokacin da sarki Baddadul-arus ya ga cewa shi da abokan tafiyar shi sun jigata ainun sai nan take ya faɗa izuwa kogin tunani domin samun mafita.
Ko da samun mafitar sai kawai ya dunƙule hannayensa ya damƙi kawunan macijiyar guda shida a lokacin da suka kawo ma shi hari ya kanannaɗe su tamkar zai tufka igiya, ya cizge kawunan da dukkan ƙarfin shi nan take jini ya yi tsartuwa ya zuba a ƙasa, macijiyar ta kurma wawan ihu kuma ta saki su sarki Huraisu da ta kanannaɗe su da jelarta suka faɗo ƙasa tim a matuƙar galabaice.
Kafin macijiyar ta sake wani yunƙuri sarki Baddadul-arus ya daka tsalle sama tamkar an harbo shi daga cikin baka ya sanya hannayenshi biyu ya gabza mata wawan naushi a idanuwanta biyu dake jikin wannan ƙaton kai na bil'adama.
Take idanun suka fashe jini ya shiga kwaranya tamkar an buɗe kan fanfo, take ta faɗi ƙasa ko shurawa ba ta yi ba, sannan ta rikiɗa izuwa wani farin haske ya ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa ba, a sannanne duhun dake kogon ya ragu ainun, kuma su Baddadul-arus suka hango wani ƙasaitaccen makulli na zinare ajiye a ƙasa ne da kaɗan da inda suke.
Cikin matuƙar farin cikin sarki Baddadul-arus ya miƙe tsaye zumbur ya taka zuwa inda makullin ya ke, sarki Huraisu, gimbiya Uzaima, shaibat da aljani zamzaru suka miƙe tsaye tsaye.
Baddadul-arus ya dube su ya a nutse ya ce "Ya abokan tafiya ta ku yi sani cewa wannan makulli da kuka gani a hannu na shine mabudin kushewar boka sharubu, duk da mawuyacin halin da mu ke ciki amma yazama wajibi gare mu mu isa ida kushewar take domin kammala aikinmu.
Ko da jin wannan batu daga bakin Baddadul-arus sai kowa ya gyaɗa kai alamar gamsuwa, kawai sai ya shiga gaba ya fara tafiya yana tunkarar kushewar su gimbiya Uzaima na biye da shi.
Ya yin da aka iso sai kowa ya ja ya tsaya, sarki Baddadul-arus ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login