Showing 57001 words to 59965 words out of 59965 words
Chapter 20 - JARUMAN DUNIYA Book Complete Littafin yaki Writing by Sarkin Marubutan Yaki .txt
Nan fa ihun mazaje ƙarar karafniyar ƙarafa ta cika dodon kunne jini ya dinga kwaranya tamkar an buɗe ƙorama, sassan jikkuna suka dinga shawagi a sama suna zubowa ƙasa, duk inda mutum ya kai duban shi babu abin da zai gani face gawarwakin dakarun duku-dukun kwance cikin jini babu kyawun gani.
Su Humairu suka wanzu suna aika rayukan dakarun barzahu ta hanyar sara da sukar su da takubbansu cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta irin ta Dakarun musulunci ko a ce irin ta Bajakade,
Al'amarin da ya yi matuƙar bawa su sarki Himras dake kwance magashiyan mamaki kenan bisa ganin wannan gagarumar bajinta da su kuhairu ke yi,
Kuma ya sanya Sharilat, Mashlira da kuhairu suka ji sun ƙara imani da Ubangiji a zukatansu.
Sai da aka shafe tsawon rabin sa'a ana wannan ƙazamin artabu bisa taimakon Ubangiji su Humairu suka hallaka baki ɗaya dakarun ba su bar ɗayan su a raye ba,
Bayan komai ya dai-dai su sarki Himras sun sanya raunukan su magani sai aka sake ɗunguma aka tusa kai izuwa cikin fadar ana tafiya cikin hanzari.
***
Al'amarin su sarki Baddadul-arus kuwa tun sa'adda suka ɓace daga cikin wannan ƙasaitaccen gida bayan sun ga abin da ya faru da abokan gabar su su sarki Himras a cikin halarar tsafin boka Sharubu ba su bayyana a ko ina ba sai a ƙofar fadar sarkin bokayen duniya.
Ko da bayyanar ta su sai boka Sharubu ya kama kalle-kalle da dube-dube yana nazarin takun sawayen su sarki Himras,
Kawai sai aka ga ya taƙarƙare ya kurma wawan ihu daga bisani Kuma ya murtuke fuska tamkar an aiko ma shi da saƙon mutuwa, fuskarshi har gatsine ta ke yi saboda matuƙar fushi ya dubi Baddadul-arus, Gimbiya Uzaima, Sarki Huraisu, Hadimi Shaibat da aljani zamzaru ya ce "Ya ku abokanan tafiyata ku yi sani cewa wannan takun sawayen da kuke gani ba na wani ba ne face na abokan gabar mu, Kuma bisa nazari da na yi na gano cewa suna kusa da mallakar TAKOBIN SIHIRI,
Kun ga kenan a halin yanzu shiga fadar Sarkin bokaye bai taso ba zai fi kyau mu yada zango a nan mu jira fitowar su domin a yi GUMURZUN SHEKARA DUBU da ba shi da mara ba da ɓallewar taskar ANNOBA DARI,
Ana mai tabbatar maku da cewa zan shiga maku burinku na mallakar TAKOBIN SIHIRI, Ni kuma zan shanye jinin jarumi Humairu domin cika burina na zamowa duniya GOBARAR ANNOBA kuma Gagarabadau makashin maza.
Ko da jin wannan batu sai kowa ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa.
***
A cikin fadar Sarkin bokaye boka oAyyamul-layal kuwa al'amarin su jarumi kuwa sun cigaba suna haɗu da miyagun aljanu da musibu mara adadi,
Duk lokacin da aka faɗa wata musiba Humairu, Sharilat, kuhairu da Mashlira ne ke fitar da su sarki Himras, yazamana duk ƙarfin damtse da girman jiki irin na aljani zamzaru ya tashi a banza,
Bisa nasarar Ubangiji Humairu ya samu nasarar ɗauko Takobin Sihiri a cikin wata tsafaffiyar kwalba ya damka a hannun sarki Himras, amma kowannen su takobinshi da tufafinshi ya rine da jini.
Lokacin da aka aka ɗunguma aka fito daga fadar sai kawai aka yi turus ba wani abu suka gani ba face su sarki Baddadul-arus a tsaye,
Nan fa aka fara kallon-kallon tsakanin su cikin matuƙar ƙiyayya da baƙar gaba,
Sarki Himras ya katse shirun da wanzu ta hanyar bushewa da dariyar mugunta ya dubi sarki Baddadul-arus ya ce "Ya kai babban abokin gaba na har abada yanzu ga shi ina ɗauke da takobin sihiri wacce kowannen mu ya yi imanin cewa da ita ne kawai za mu iya hallaka junan mu,
Shawarar da zan baka ita ce ka rubuta wasiyyar ka zuwa al'ummar ƙasar ka kafin na zare ruhinka daga gangar jikinka ka yi mutuwar wulakanci".
Ko da jin wannan batu daga bakin Himras sai Sarki Baddadul-arus ya bushe da dariyar ƙarfin hali daga bisani ya murtuke fuska ya daka mashi tsawa ya ce "Kai tsohon maci amana ka yi sani cewa koda cewar kana ɗauke da takobin sihiri ba zai sa ka yi nasara a kaina ba domin ai masu iya magana na cewa kaɗe mage ba yankawa ba ne, kuma mugu shi ne makwantar mugu,
Ka sani cewa kamar yadda ka ci amanar ɗan uwanka kuhairu ka nemi ka raba shi da rayuwar shi to yanzu kai ne za ka rabu da ta ka rayuwar domin har kullum ƙaikayi shi ne ke koma kan masheƙiya, kuma idan za ka gina ramin mugunta ka gina shi gajere yadda idan ka faɗa za ka iya fitowa".
Ko da jin wannan batu sai zuciyar yarima Muzaifar ta buga da ƙarfi ya ce a ranshi dama Kuhairu uwa ɗaya uba ɗaya suke da mahaifina kenan Sharilat 'yar uwata ta jini ashe ba a banza kuhairu ya ke kama da ni ba kuma salon yaƙin mu yazo ɗaya ni da Sharilat a lokacin da muka fafata yaƙi da ita a kasuwar birnin Darul-kushur?
Amsar tambayoyin da yarima ya kasa bawa kanshi kenan ya ji gaba ɗaya Kunyar Sharilat da kuhairu ta kama shi,
Ya ƙura wa gimbiya Uzaima idanu yana yi mata kallo mai tattare da tsantsar gaba da mugun tanadi.
Kafin sarki Baddadul-arus ya sake furta wani abu sarki Himras ya ɗaga takobin sihiri izuwa sama ya kwarara wawan ihu ya ruga izuwa gare shi,
Ko da ganin hakan sai Baddadul-arus ya zare takobinshi ya ruga gare shi domin tarar juna,
Ko da ganin sai yarima Muzaifar da gimbiya Uzaima suka zare makaman su suka ruga izuwa kan junan su suna ihu da kururuwa mai firgita ZARATAN MAYAKA a FILIN DAGA,
Aljani Narguz da Aljani Zamzaru suka ruga kan juna domin KARON BATTA batare da sun zare makami ba
Boka Sharubu kuwa sai ya zare mashinsa ya ruga kan jarumi Humairu
Lokacin da ɓangarorin huɗu suka haɗu da juna sai aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar muni da tashin hankali,
Ko da ganin an fara fafatawar sai jarumi Sharilat, Mashlira, Gimbiya Hulaifa, boka Hushaib da sarkin yaƙi suka koma gefe guda gami da zuba idanu suna kallon fafatawar da ake yi.
Ƙarar karafniyar ƙarafa gami da ihun mazaje ta cika dodon kunne, ƙura ta turnuƙe sararin samaniya, duk sa'adda makaman jaruman takwas suka haɗu da juna sai ka ga sun haddasa wata tsawa da walƙiya da ka iya kurumtar da kunnuwa,
Kaico! Haƙiƙa gumurzu Mazaje daban ya ke da na ƙananun jarumai, kuma Idan BABBAR GIWA ta fito Filin fama babu wanda ya ke iya tunkarar ta ayi KARON BATTA face JARUMAN DUNIYA da suka saba yin ɗauki ba daɗi a birnin MAZAN JIYA.
A ɓangaren sarki Baddadul-arus da sarki Himras kuwa sun wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta duk sa'adda Himras ya kaiwa Baddadul-arus hari da takobin sihiri idan ya zillewa harin duk abin da takobin ta sauka a kai sai ka ga ya narke ya zama ruwa, idan a kan bishiya ta sauka kuwa sai kaga ta kama da wuta ta ƙone ƙurmus.
A ɓangaren yarima Muzaifar da gimbiya Uzaima kuwa sun wanzu suna ɗauki ba daɗi suna kaiwa juna hare-hare cikin gwaninta da salon yaƙi irin na JARUMAN DUNIYA,
Kafin shuɗewar daƙiƙa ashirin sun yi junan su raunuka guda biyu kowanne na ZUBAR DA JINI,
Rauni na farko a damtsen cinyarsu ta hagu suka yi wa juna,
Na biyun kuma a kafaɗa.
Sa'adda Jaruman suka ga yadda jini ke zuba a jikkunansu sai suka fusata ainun suka ZAGE DAMTSE tare da kaiwa juna sabbin hare-hare.
A ɓangaren MAZAN JIYA kuwa Jarumi Humairu da boka Sharubu sun wanzu suna shayar da junansu azabar KAIFIN TAKOBIN su babu sassauci,
Komai hassadar mutum idan ya ga yadda suke yaƙin dole ne ya jinjina masu ya tabbatar da cewa sun cika ZARATAN JARUMAI masu ƙarfin damtse.
Sai da aka shafe tsawon Sa'a biyu ana wannan ƙazamin artabu babu sassauci Kuma babu alamun nasara ga kowa ne ɓangare,
Sai da ta kai jaruman shida na yanke jiki suna faɗuwa ƙasa magashiyan amma saboda juriya da bajinta irin ta MAZAN JIYA da suka saba gumurzu a BIRNIN SADAUKAI sai su miƙe tsaye zumbur su ci gaba da mayar da martani.
Wohoho! haƙiƙa a wannan rana an fafata ƙazamin artabu da ba a taɓa yin kamar shi ba,
Inda yarima Muzaifar da gimbiya Uzaima suka yi RAGAS ma'ana sun galabaita ainun numfashi su yana fita sama-sama.
Sarki Baddadul-arus da Himras kuwa MUTUWAR KASKO suka yi inda suka karya takobin sihiri gida biyu kowanne su ya sokawa abokin gabar shi a kan ƙahon zuciya suka yi mutuwar wulakanci,
Kaico! ka ji aikin kafirai duk abin da aka aikata an tafi an bar shi a duniyar,
Yanzu duk cin amanar da sarki Himras ya yi wa ɗan uwanshi tsoho kuhairu saboda ƙwaɗayin mulki yanzu ga shi ya tafi ya bar duniyar a banza,
Allah ka raba mu da mutuwar asara,
A ɓangaren Aljani Zamzaru da Narguz kuwa su ma mutuwar kasko su ka yi ta hanyar murɗewa junan su kawuna a lokaci guda.
Jarumi Humairu kuwa daƙyar da siɗin goshi ya samu nasarar hallaka boka Sharubu ta hanyar sare mashi wuya da takobinshi amma shi ma kan shi yasha ɓakar wahala,
Bayan ya hallaka shi wani baƙin aljani ya bayyana mai munin halitta ashe shi ne wanda ke sarrafa ke sarrafa gangar jikin boka Sharubu,
Domin Allah ya yi alƙawarin cewa babu wata halitta walau MUTUM DA ALJAN da zata wanzu a doron ƙasa face ta zamo gawa, don haka boka Sharubu ya mutu ba shi ne ya dawo duniya ba kawai lamari ne na ma'abota shirka da sihiri.
A wannan karon sai da Humairu ya sha baƙar azaba tamkar zai rasa rayuwar shi sannan ya hallaka aljanin ta hanyar tofa mashi Ayatul-kursiyyu ya ƙone ƙurmus!,
Haƙiƙa a wannan rana su tsoho kuhairu sun ga iko da buwayar Ubangijin halitta kuma zukatansu sun ƙara samun nutsuwa da Ubangiji.
Ko da samun wannan gagarumar nasara sai Humairu ya yanke jiki ya faɗi ƙasa sumamme,
Cikin kaɗuwa Sarkin yaƙi Nuhairu ya ruga zuwa inda yake ya shiga ba shi taimakon gaggawa,
Gimbiya Hulaifa ta nufi inda gimbiya Uzaima ta ke domin bata taimako,
Boka Hushaib kuwa ya ruga zuwa ga yarima Muzaifar ya shiga ba shi kulawa gimbiya Mashlira bintu Shabbar na taimaka ma shi.
Sai da aka kwana uku a wannan waje kowa ya yi jinyar raunukan jikin shi ya warke sumul, A ranar kwana na huɗu ne da hantsi kowa na zaune sai Humairu ya dubi su boka ya yi gyaran murya ya ce "Ya ku abokanan tafiyata yanzu ga shi mun rasa takobin sihiri wacce da ita ne za a yi amfani a saro sauwar bishiyar Shajarul-kair domin warkar da al'ummar birninku daga Annobar cutukan da ke addabar su shin yanzu mene ne abin yi?.
Ko da jin wannan tambaya daga bakin Humairu hankalin gimbiya Hulaifa,boka Hushaib da sarkin yaƙi Nuhairu ya dugunzuma ainun aka rasa wanda zai ce ƙala a cikin su,
Sai daga bisani ne gimbiya Hulaifa ta dubi Humairu fuskantarta cike alamun damuwa ta ce "Ya kai Jarumin jarumai ka yi sani cewa a halin yanzu ba abin da zamu iya cewa dukkanin rayuwar al'ummar ƙasarmu ta dogara ne akan ka sai abin da ka ce,
Amma bisa nazari da na yi a tafiyar mu na ga iko da buwayar Ubangijin ka ina ji a raina cewar zai iya warkar al'ummata batare da an yi amfani da saiwar Shajarul-kair ba.
Ko da jin wannan batu daga bakin Hulaifa sai Humairu ya ce "Haƙiƙa zancen ki dutse babu wani abu da ya gagari Ubangijina,
Abin da nake so da ku shi ne ku yi mani alƙawarin za ku bayar da gaskiya da Ubangijina idan har ya warkar da jama'ar ki.
Ko da boka Hushaib, gimbiya Hulaifa da sarkin yaƙi Nuhairu suka ji wannan batu daga bakin Humairu sai suka ce mun amince da hakan ya JARUMIN JARUMAI kuma SARKIN SADAUKAI.
A can inda tsoho da 'yarshi Sharilat ke zaune kuwa suna fira cikin nishaɗi, sai suka hango yarima Muzaifar ya tawo gare su yana zuwa ya zauna a daf da kuhairu ya dube shi cikin ladabi yana satar kallon Sharilat ya ce "Ya abbana ka yi sani cewa a halin yanzu na gano cewa mahaifina ne ya ci amanar ka saboda ƙwaɗayin mulki da son abin duniya, a halin yanzu bani da wasu 'yan uwa na jini da suka rage mani face ku, ina roƙon ku da ku yafewa mahaifina kada laifin shi ya shafe ni ku riƙe ni da wani abu, kuma kada Sharilat ta yi watsi da soyayyata".
Sa'adda yarima Muzaifar ya zo nan azancen shi sai kawai ya fashe da kuka hawaye na zuba daga idanuwanshi,
Al'amarin da ya sanya Sharilat da kuhairu suka ji sun kamu da matuƙar tausayin shi har ƙwalla ta cika masu idanu,
Kawai sai kuhairu ya miƙe tsaye ya tashi kafaɗunshi ya dube shi fuskarshi cike da annuri ya ce "Ya kai Muzaifar ka sani cewa ba ka yi mana komai ina mai tabbatar maka da cewa ba za mu rike ka da komai ba, zan riƙe ka tamkar 'yata Sharilat,
Kuma zan aura maka ita domin bani da wani buri a duniya da ya huce naga zuri'armu a tare da juna cikin matuƙar farin ciki,
Sai dai inda gizo ke saƙar shi ne a halin yanzu mu musulmi ne saɓanin kai.
Ko da jin wannan batu murmushin yaƙe ya suɓucewa Muzaifar ya ce "Ya abbana ai tuni na bayar da gaskiya da Ubangijin halitta kawai dai tsoron fushin mahaifina ne ya sa ban bayyana ba".
Ko da jin wannan batu sai kuhairu ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa ya rungume yarima a ƙirjinshi,
Sai daga bisani ne ya janye jikinshi ya tafi ya ba su waje suka shiga firar soyayya tsakanin sa da Sharilat.
Kamar yadda Humairu ya faɗa haka al'amarin yakasance wato sun gabatar da sallar azahar sai ya kira wani hadimin aljanin shi mai kyawun sura mai suna Hadimul-khair ya ɗauke su baki ɗaya ya nufi birnin Rum yayin da aka isa ne jarumi Humairu ya karanta ayatul-kursiyyu a ruwan ƙoramar garin duk wanda suka kamu da cututtuka suka sha ruwan har da sarki Usulu-haibar suka warke sumul!.
Nan take suka cika alkawari suka karɓi kalmar shahada sannan aka ɗaura auren gimbiya Hulaifa da sarkin yaƙi Nuhairu, Sannan aka sake ɗunguma aka nufi birnin Madinatul-husuf aka ɗaura auren gimbiya Uzaima da sarki Huraisu ma'abocin baiwa ashe tun sa'adda da ya fafata yaƙi tare da ita da mahaifinta ya kamu da soyayyar ta amma bai bayyana ba, bayan sun ƙarbi addinin Musulunci sai sarki Huraisu ya zamo sabon sarkin ƙasar Madinatul-husuf aka ƙarya dukkan gumaka,
Shi kuwa hadimi Shaibat sai ya koma izuwa birnin Jarul-iman a matsayin halifan sarki Huraisu domin tabbatar da addinin Musulunci.
Sannan aka sake ɗunguma aka nufi Kasar Darul-kushur aka ɗaura auren Jaruma Sharilat da yarima Muzaifar, Jarumi Humairu da Gimbiya Mashlira yar shugaban arnar daji marigayi Shabbar,
Labari kuma ya watsu a nahiyar cewa kuhairu ya na raye kuma dawo tare da 'yar shi Sharilat kuma sarki Himras ya mutu,
Nan fa sarakunan suka dinga zuwa suna yin mubaya'a a gare shi tare da nuna farin cikinsu,
A wannan rana an yi gagarumin shagalin bikin da ba a taɓa yin kamar shi a gaba ɗaya nahiyar.
Bayan an kammala ne sai rigima ta ɓarke akan wane ne zai gaji karagar mulki, inda wasu ke ganin cewa yarima Muzaifar ne ya cancanta yazama sarki domin shine zai gaji mahaifin shi, wasu kuwa suka ce ai Humairu ne ya kamata domin kuwa shine ya zamo silar samuwar duk wani farin ciki tsakanin su,
Wasu kuwa suka ce kuhairu ne ya fi kowa dacewa domin ai dama can baya sarautar ta shi ce bata marigayi sarki Himras ba,
Yarima Muzaifar da jarumi Humairu kuwa sai suka dage akan cewa ba za su karɓi sarautar ba sun kyale wa kuhairu.
Haka kuwa aka yi aka naɗa tsoho kuhairu a matsayin sabon sarkin birnin Darul-kushur,
Farin ciki a wajen al'ummar birnin kuwa ba a cewa komai tamakar su zuba ruwa a ƙasa su sha, wasu har da zubar da hawaye domin sun tuna irin ƙuncin da suka shiga a lokacin mulkin sarki Himras bayan jin labarin cewa an hallaka kuhairu,
Yarima Muzaifar kuwa aka naɗa shi Magajin gari, jarumi Humairu kuwa ya zamo sarkin yaƙin birnin domin tabbatar da addinin Musulunci.
Tun daga wannan rana a kawo KARSHEN ZALUNCI zaman Lafiya da farin ciki ya ci gaba da wanzu a ƙasar Darul-kushur da nahiyar baki ɗaya musulunci ya ci gaba da bunkasa, aka rushe dukkan gumaka da shaiɗanu, arzikin birnin ya dunga bunƙasa wanda ba'a taɓa samun kamar shi tun kafuwar birnin saboda HASKEN MUSULMI.
Alhamdulillah
Ƙarshe
Daga mai ɗebe muku kewa a kullum da ko yaushe.
MANSUR USMAN SUFI
08137237071