Showing 18001 words to 21000 words out of 59965 words

Chapter 7 - JARUMAN DUNIYA Book Complete Littafin yaki Writing by Sarkin Marubutan Yaki .txt

09 Dec 2024

9377

koda a tarihi bai taɓa gani ko jin labarin tsuntsaye ma su kwarjini irin su ba, Abin tambaya anan shine ya aka yi tsuntsayen su ka ketare tsoron dake gidan sarautar, bayan cewa fiye da shekaru goma hakan bai taɓa faruwa ba.
Sa'adda kuhairu yazo Nan a tunaninshi sai ya sake zurfafa cikin Kogin tunani, Nan take ya fahimci cewa tabbas ɗan uwanshi Yarima Himras ne ya aiko waɗannan tsuntsaye, Domin shi ne ƙaɗai sihirin tsafin shi zai yi tasiri akan nawa.
Ko da yazo nan a tunaninshi sai hawayen su ka kwaranya daga idanunshi yana mai cewa yanzu a ce ɗan uwana Himras ne ke farautar rayuwata saboda kwaɗayin mulki, haƙiƙa mulki musiba ne.
Kawai sai kuhairu yayi jifa da Takobinshi da ta rine da JININ SADAUKAI, Ya ciri sabuwa a jikinshi ya afkawa tsuntsayen aka ruguntsume da azababban yaƙi.
Ana fara wannan gumurzu ne duka ɓangarorin biyu su ka fara gane cewa tabbas shayi ruwa ne ba'a abinci mai nauyi ba.
Sai da aka shafe tsawon Sa'a guda ana wannan ɗauki badaɗi babu alamun nasara, Abinda sarki Kuhairu bai sani ba shine, Takobin dake riƙe a hannun shi yana sana'anta ta ne da shirin tsafin da Mahaifin su ya ba shi, haka ma tsuntsayen da ya ke gumurzun da su yarima Himras ya samar da su ne da sihirin. Bisa hakan ya sanya ya kasa samun nasara akan tsuntsayen.
Lokacin da sarki Kuhairu ya fahimci cewa tabbas wankin hula zai kai shi dare, sai kawai yayi wurgi ta takobinshi ya shiga yaƙar tsuntsayen da ƙarfin damtsenshi, Nan fa labari ya sha Bambam yana zamana cewa duk sa'adda kuhairu ya naushi wata gaɓa a jikin su sai kaji tayi ƙara ruƙus! Ƙas ta karye, Nan fa tsuntsayen suka dunga yin kururuwa suna faɗuwa ƙasa magashiyan, waɗansu kuma matattu.
Amma su ma tsuntsayen sun yi ma shi miyagun raunuka da faratansu, kafin cikar daƙiƙa hamsin ya hallaka tsuntsayen, A wannan lokaci jiri na ɗibarshi tamkar ya sha barasa ya bugu, Amma saboda juriya irin ta JARUMAN DUNIYA a haka ya cigaba da tafiya yana mai Kusantar ɓangaren turakar Amaryarshi Hashmila.
Aɓangaren Sadauki Rauzub da wannan Badakaren kuwa, tuni labari ya sha bamban, Domin yanzu yaƙi ya canza salo Badakaren ba ya iya mayar da martani, Sai dai ƙoƙarin kare kanshi.
Ana cikin wannan gumurzu ne Rauzub ya kaiwa wani badakaren hari, cikin matuƙar zafin nama Badakaren ya sunkuya ya kaucewa harin, amma duk da hakan sai da takobin Rauzub ta zaftare wani yanki da ya rufe fuskarshi.
Nan take fuskar Badakaren ta bayyana a fili ƙarara, Yayin da Rauzub yayi arba da fuskar mahayin sai ya cika da matuƙar mamaki.
Abin da ya ba shi mamaki shine ba wani bane Badakaren ba face Hashmila, Rauzub ya bushe da dariyar mugunta tamkar bazai daina ba, daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko mashi da sakon mutuwa. Ya dubi Hashmila a wulaƙance yace" Amma fa kin burgeni ainun da har kika fafata yaƙi da ni, sai dai kuma kinyi babban kuskure da ki ka kawo kanki Izuwa gareni, yanzu batare da ɓata lokaci ba zan hallaka ke mai gidan ki, domin kuwa nan da lokaci kaɗan zan zamo Sarkin mayaƙan wannan ƙasa.
Kafin Rauzub ya gama rufe bakinshi, Hashmila ta tari Numfashinshi yana mai daka ma shi tsawa tace"kaiconka yakai azzalumi kuma maci amana, haƙiƙa ka tafka babban kuskure da ka ke tsammanin cewa za ka iya hallaka mu, ka yi sani cewa yarima Himras ba zai cika ma ka burinka ba, shin ko ka manta ne cewa kuhairu ɗan uwanshi na jini ya ci amanar shi, to ina ga kai karan kaɗa miya, kuma ban taɓa tsammanin kai butulu ba ne sai yau, ka da fa ka manta cewa da kai bawa ne, kuhairu ya 'yan taka ka zamo ɗa. Kuma yayi ma ka aure, ka sani cewa ramin ƙarya ƙurarre ne.
Caraf! Rauzub ya tari Numfashin ta ya na mai cewa "ke ƙaramar alhaki kiyi sani, A halin yanzu tamkar yarima Himras ya zamo Sarkin wannan birni Darul-kushur, Domin ya hallaki alƙyabba,gurin tsafi haɗe da kambun sarauta na Sarki, tabbas tamkar burina ya cika ne.
Caraf! Hashmila tace"Ga maza nan bisa kan ka, tana gama faɗin hakan ta yi wurgi da takobinta, ta afka ma shi da dukkanin ƙarfin damtsenta.
Koda ganin hakan sai Rauzub ya bushe da dariyar mugunta ya dunƙule hannayenshi biyu ya ruga Izuwa kanta, su ka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar muni daban tsoro, suna kaiwa junansu naushi da bugu hannu da ƙafa.
Ana fara wannan artabu ne Hashmila ta fara gane kurenta domin ƙarfin naushi Rauzub ya nunka nata sau huɗu, Duk sa'adda Rauzub ya gabzamata naushi sai kaga Hashmila tayi sama tamakar an janye ta da ƙungiya, Sannan daga bisani ta faɗo ƙasa tim, Amma sai ya miƙa tsaye zumbur.
Cikin abinda bai gaza daƙiƙa ashirin ba Rauzub ya haɗa ma ta jini da Majina,tana layi jiri na ɗibarta.
Wohoho! Tabbas masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce ƙyan faɗa akwana ana yi, kuma idan gwani da gwani suka haɗu, juriya da naci suka game waje guda dole ne tsagwaron ƙarfin damtse yayi aiki.
Ana cikin wannan artabu ne Rauzub ya shammaci Hashmila ya ƙirɓa ma ta naushi a ciki, saboda ƙarfin naushin sai da ta maku da wata katanga, sannan ta faɗi ƙasa magashiyan cikin mawuyacin hali dake tsakanin rayuwa da mutuwa.
Koda samun wannan gagarumar nasara sai Rauzub ya ya zare wani mashi a gadon bayanshi ya durfafi inda take kwance yana mai yi mata murmushin mugunta, yana isa zuwa inda take ya ɗaga mashin domin ya caka mata a ƙirji.
Kwatsam bazato tsammani sai Rauzub yaji waɗansu kibbau sun sokeshi a gadon bayanshi, duk da irin raɗaɗin da yake ji amma sai ya waiga domin yaya wanda ya harbeshin, Aikuwa sai yayi arba da shi ba wani bane face sarki Kuhairu ya falfalo Izuwa inda yake yana kurma ihu.
Ko da ganin hakan sai Rauzub ya shafi wani gurin tsafi a damtsenshi take ya ɓace ɓat!
Kuhairu ya durƙusa ƙasa bisa gwiwoyinshi yana mai tallafo wuyan Hashmila yana mai zubar da hawaye cikin matuƙar tashin hankali. Yana cikin wannan hali ne Rauzub ya bayyana a gare shi ya jefa ma shi wannan mashi, mashin ya tafi cikin matsanancin gudu yana keta iska, kafin kuhairu yayi yunƙuri mashin ya sokeshi a idanunshi na hagu, kuhairu ya kurma ihu, Cikin zafin nama ya sa Rauzub ya sake cire mashin ya caka mashi a idanunsa na dama sannan ya ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzu ba.
Nan take Kuhairu ya sake kurma ihu a lokacin da idanuwanshi ke zubar da jini yana gani dishi-dishi, kawai sai ya miƙe tsaye ya ɗauki Hashmila ya goya ta a gadon bayanshi, ya falfala da azababban gudu Izuwa hanyar da za ta sadashi da gidan sarauta, yana cikin gudun ne ya hango dakaru fiye da dubu bisa dawakai na harbo ma shi kibbau, Amma sai yazamana Kuhairu yana Yana zillewa kibbau ɗin cikin baƙin zafin nama, Da ya ke a wannan lokaci dare yafara Kunno Kai, sai kuhairu ya dunga amfani da hannunshi yana kashe fitilun dake jikin katangun.
Lokacin da kuhairu ya shafe tsawon Sa'a yana wannan gudu a dai-dai wannan lokaci ne ƙarfin gudun Kuhairu ya fara raguwa, kuma da ƙyar ya ke iya zillewa haren dakarun. Har yazamana Dakarun sun harbeshi sau bakwai a gadon bayanshi jini na zuba.
Kawai sai kuhairu ya hango wata ƙorama a gabanshi, Don haka sai ya karanto waɗansu ɗalasiman tsafi yana mai nuna ƙaramar da hannun shi na hagu, take ƙormar ta ɓace ɓat!.
Lokacin da kuhairu ya haure Nan take ƙoramar ta sake bayyana tayi ma shi katanga tsakanin sa da dakarun. Nan fa dakaru fiye da hamshin tare da dawakansu su ka afka ciki su na masu ihu da kururuwa mai firgitarwa.
A dai-dai wannan lokaci ne Yarima Himras,waziri tare da sauran hadimanshi su ka bayyana a bisa dawakai,yarima Himras ya dubi Rauzub ya ce ka tabbatar ka cakawa ɗan uwana wannan masu da na baka?
Rauzub yace "kwarai kuwa na aiwatar da komai yadda ya kamata ya shugabana.
Yarima ya bushe dariyar mugunta a karo na biyu, Sannan daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko mashi da sakon mutuwa yace" Na tabbatar da cewa ɗan uwana Kuhairu ya jima da hallaka yanzu zan shimfiɗa mulkina yadda nake buƙata.
Ko da gama faɗin hakan sai Yarima yayi wuf! Ya zare wata takobi a damtsenshi ya shammaci Rauzub ya caka ma shi ita a ciki, Rauzub ya kwalla ƙara yana mai dafe raunin a lokacin da jini ke zuba tamkar an ɓalle kan fanfo, kuma ya durƙushe ƙasa bisa gwiwoyinshi.
"Kana tunanin cewa zan bar ka a raye ne bayan cewa kai kaɗai ne kasan sirrin dake tsakanina da ɗan uwana, tabbas mutuwar ka ita ce dai-dai, yana zuwa nan azancenshi sai kawai ya sanya takobin ya sare wuyan Rauzub, kan na shi yayi fitar burgu, gangar jikin ta faɗi ƙasa rikica!
Kafin ɗaya daga cikin dakarun Rauzub yayi wani yunƙuri yarima ya afka masu da yaƙi, cikin abin da bai gaza daƙiƙa ashirin ba ya hallaka su baki ɗaya ya zubar da gawarwakin su a ƙasa.
Nan take Yarima Himras da waziri Zuraisu suka ci gaba da bushe da dariyar mugunta tamkar bazai daina ba.
Haka dai kuhairu ya cigaba da gudu bisa kan ingarman dokin har ya su ka samu Nasarar ficewa daga cikin gidan sarauta suka nausa Izuwa cikin daji.
Su na cikin gudun ne bisa kuskure sai dokin yayi karo da wani dutse nan take ta hantsila Izuwa ƙasan wani makeken rami, Kuhairu yana mai kurma ihu, kafin su kai Izuwa karshen ramin dukkanin su sun sun sume.yayin da suka faɗa Izuwa cikin ruwan sai igiyar ruwan ta shiga gudu a da su har ta kawo su Izuwa gaɓar wani kogi.




****


Al'amarin yarima Himras da waziri Zuraisu kuwa, bayan sun kammala kyalkyala dariyar, sannan yarima ya karanto waɗansu Ɗalasiman tsafi suka duka biyun suka ɓace daga wajen tamkar ba su taɓa wanzuwa ba, basu bayyana a ko ina ba sai a kofar shiga faɗa,koda tsayuwar su sai yarima Himras ya ƙwallawa wani badakare kira, Badakaren ya bayyana gareshi ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa kanshi a sunkuye, Yarima ya dube shi yace "yakai abu-salimat kayi sani cewa ban kirawo ka nan ba sai domin ina so ka sanya ayi shela Izuwa ƙasashe birane da ƙauye na naɗin sarautata tare da shagalin ɗaura auren na da gimbiya Sharzila, sannan a hana shige da fice a cikin wannan birni, face kawai iya baƙin da zasu halarci naɗin sarauta.
Koda jin wannan umarni sai Abu-salimat ya risina yace"An gama ya shugabana, yana gama faɗin hakan ya miƙe tsaye ya juya ya nufi inda dokin shi ya ke ya kama ya hau ya sakar ma shi linzami, waɗansu zaratan dakaru ma'abota jajayen tufafi su ka mara ma shi baya suna masu zaburar dawakansu.
Kamar yadda yarima Himras ya faɗa haka al'amarin yakasance, wato tun a daren jiya baƙi suka yi cincirindo a ƙasar Darul-kushur, kafin wayewar gari ya cika ya batse, gaba ɗaya jama'ar birnin babu wanda yayi farin ciki da zamowar Yarima sabon Sarkinsu, kuma zukatansu cike suke da tambaya akan a wane hali sarki Kuhairu da Amaryarshi Hashmila ke ciki sun mutu ne ko su na raye, amsar tambayoyin da su ka kasa bawa kansu kenan, saboda tsaron yarima sai kowa ya tsuke bakin shi.
Su kansu sarakunan da suka halarci shagalin bikin naɗin sarautar sun halarta ne kawai saboda girmamawa ga marigayi sarki saruful-uzwar, Da yawa daga cikin su sun so su tambayi sarki Himras cewa shin ina sarki Kuhairu ya shiga, amma sai su ka bar abin a zukatan su.
Tun daga wannan rana yarima Himras ya zamo sabon sarkin ƙasar Darul-kushur, ya fara shimfiɗa mulkin zalunci, Nan fa sata, kwace, fashi da makami gami danne haƙƙin masu rauni ya yawaita a birnin,
Kafin Kuhairu ya cika shekaru biyu da hawa karagarshi ya mamaye dukkanin birane da ƙasashen dake maƙwabtaka dashi ya cinye su da yaƙi ta ƙarfin tsiya, sun dawo zuwa ƙarƙashin daularshi. Sai wata ƙasa guda ɗaya da wani sarki mai suna Baddadul-Arus ke mulki ita ce ta gagreshi ya mamaye ta.
Daga wannan rana zaman lafiya yayi ƙaura daga nahiyar baki ɗaya, Kowa ne sarki ba shi da burin da ya huce ya mamaye biranen dake makwabtaka dashi ya cinye su da yaƙi.




****
Kuhairu da Hashmila basu farfaɗo daga dogon suman da suka yi ba sai da safiya tayi, ai kuwa koda suka buɗe idanuwansu su ka gansu kwance a bisa waɗansu kadaje na itace masu kwari, a cikin wani ɗaki da akayi da zallar itacen bishiya masu kwari aka rufe saman da fatun dabbobi.
Zaune a gefen gadon da kuhairu ke kwance wani Dattijo ne ma'abocin cikar kamala, shekarun shi ba zasu Haura hamsin da ɗoriya ba, bisa gefen gadon da hashmila ke kwance, wata tsaleliyar kyakkyawar budurwace sanye da fararen tufafi.
Koda ganin su kuhairu sun farfaɗo, sai kyakkyawar budurwar ta miƙa tsaye ta fice daga cikin turakar, jim kaɗan bayan shuɗewar daƙiƙa ashirin sai gata ta dawo ɗauke da wani ƙaton akushi da salkar ruwa ta ajiye a gaban su kuhairu.
Dattijon ya dubi kyakkyawar budurwar yace " Ai bai kamata su fara cin abinci mai nauyi ba, zai fi su sha abin da zai warware musu cikin su sannan su ci abincin, ko da jin wannan batu sai budurwa ta risina ta juya ta fice a karo na biyu Batare da tace uffan ba.
Zuwa can sai kaga ta dawo ɗauke da tacecciyar Madarar shanu a cikin akushi guda biyu, duk wannan abu dake wakana tsakanin Dattijon da kyakkyawar budurwar, sarki Kuhairu da Amaryarshi Hashmila na kallo, Yayin da su ka yadda suke ɗawainiya dasu sai su ka cika da matuƙar mamaki, su na masu tambayar kansu kansu akan cewa taya ya waɗannan Mutane suka taimaka masu bayan cewa basu taɓa ganin juna ba.
Amsar tambayar da su ka kasa bawa kansu kenan, kawai suka zuba idanu suna kallo.
Ko da kyakkyawar budurwar ta kawo Madarar shanun sai Dattijon da budurwar su riƙe kafaɗun kuhairu da hashmila su ka tashe su zaune su ka kafa mu su akushin baki ya shiga kwankwaɗar Madarar har sai da su ka sha suka ƙoshi, Sannan su ka shiga ɗibar abincin a baki suna basu suna ci, har sai da su ka kimtsa cikin su.
Da yake Kuhairu da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login