Showing 42001 words to 45000 words out of 59965 words

Chapter 15 - JARUMAN DUNIYA Book Complete Littafin yaki Writing by Sarkin Marubutan Yaki .txt

09 Dec 2024

9373

safiya suka yi cincirindo a fadar maza,mata,yara da manya tamkar DANDAZON kiyashi babu masaka tsinke, da yawa daga cikin su ko kalacen safe ba su yi ba.
Sai da aka shafe tsawon daƙiƙa latalin ana cikin wannan hali ne sannan aka fara jiyo bugun tambura da bushin algaita alamar gimbiya na daf da bayyana,
Daga can sai aka hango gimbiya tafe shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini daban tsoro, a ɓarin hannunta na hagu boka Hushaib ne cikin shigar yaƙi irin ta su ta hamshaƙan matsafa, a hannun dama kuwa wani kyakkyawan saurayi ne shirye cikin gagarumar shigar yaƙi, kallo ɗaya za ka yi mashi ka fahimci cewa ya cika Gwarzon mayaƙi saboda yadda ya tara gwanji damatsanshi suka tumbatsa,
Wa bani ba ne face sarkin yaƙin barnin Rum da ake kira da suna Nuhairu ibnu uzaib.
Sa'adda jama'a suka ga gimbiya Hulaifa da tawagar ta sun iso fadar sai suka sunkuyar da kawunansu domin girmama a gare su,
Kai tsaye gimbiya ta huce izuwa kan karagar mulki ta hakimce, boka Hushaib da sarkin yaƙi Nuhairu suka je suka zauna akan waɗansu ƙayatattun kujeru da ke daf da na 'yan majalissa,
Ɗaya-bayan-Ɗaya 'yan majalissar suka dunga zuwa zubewa a gaban gimbiya suna kwasar gaisuwa, bayan an kammala ne fadar tayi tsit tamkar mutuwa ta kawo ziyara.
Sannan gimbiya ya miƙe tsaye ta fuskanci jama'a ta yi gyaran murya ta ce "Yaku jama'ar wannan fada mai albarka da farko ina maku Barka da zuwa da amsa wannan kira nawa,
Dalilin da ya sanya na tara ku ana shi ne domin in sanar da ku cewa a yanzu ne zan tafi nemo maganin da zai warkar da sarki da jama'ar birnin mu daga cututtukan da suka same su sakamakon suɓucewar sarƙar tsafi a gare mu,
Da wannan na ke maku fatan alheri sai mun sa ke saduwa da alheri.
Lokacin da gimbiya tazo nan a jawabinta sai fadar ya ruɗe da shewa kowa na faɗin albarkacin bakin shi ina da su ke nuna goyonsu akan tafiyar.
Daga wannan gimbiya ta miƙe ta shiga izuwa cikin gidan sarauta suka yi bankwana da sarki suna masu zubar da hawayen rabuwa da juna, Sannan ta dawo fada ta tarar da abokan tafiyar ta su boka Hushaib da sarkin yaƙi Nuhairu sun kimtsa ita suke jira suna zaune akan waɗansu jajayen dawakai ɗauke da abin guzuri.
Kawai sai ta je inda dokin ta ya ke ta kama ta haye ta sakar mashi linzami ta shige ga ba, boka Hushaib da Nuhairu suka mara mata baya sauran jama'a kuwa su ka bi su a baya ɗuhhh!.
Duk inda aka huce a cikin birnin sai ka ga jama'a na ɗaga ma su hannu suna masu fatan samun nasara akan abin da za su tafi nema.
Sai aka iso mararrabar hanya sannan mutane suka koma izuwa cikin gari lokacin da su gimbiya suka nausa izuwa cikin daji suna fara tsala gudu.




****

Āl'amarin su sarki Baddadul-arus kuwa, tun da duku-dukun safiya bayan hudowar rana kowa ya farka daga barci shi aka yi kalaci bayan an kimtsa sai aka sake hayewa bisa kan alajni zamzaru domin isa birnin kisra domin tashin boka sharubu daga kushewar shi,
Sai aka shafe tsawon Sa'a shida ana tsala gudu a sararin samaniya ana keta gajimare, yayin da sa'a bakwai ta cika a dai dai wannan lokaci ne aka iso birnin kisra aljani zamzaru ya sauka a turba,
Shi dai birnin kisra yakasance ƙasaitacce da aka ƙawata shi da dogayen gine-ginen zamani, babu wata halitta a doron duniya walau mutum da aljan da zata tsinci kanta a cikin wannan birni face ta zamo cikakkiyar 'yar ƙauye.
Ya yin da aka tsaya sai sarki Baddadul-arus ya ɗauko madubin tsafin shi ya shafe shi da hannun shi na hagu ya shiga gudanar da bincike, sai daga bisani ya juya ya dubi abokan tafiyar shi ya ce "Yanzu sai kowannen ku yakasance cikin shiri domin shirin ko ta kwana domin binciken da na yi yanzu ya tabbatar da cewa akwai manyan musibu a tare da kushewar boka sharubu.
Ko da jin wannan batu daga bakin sarki Baddadul-arus sai hadimi shaibat ya dube shi cikin alamun matuƙar damuwa ya ce "ya shugabana shin yanzu ta ya zamu iya yaƙar dakarun da ke tsaron kofar birnin bayan cewa sun ɗora na birnin Rum yawa da kwarjini ?.
Da jin wannan tambaya sai Baddadul-arus ya bushe da 'yar ƙaramar dariya sannan ya murtuke fuska ya ce " Yakai Shaibat ka yi sani cewa matsawar muna tare da wannan sarƙar tsafi babu wani abu da zamu saka a gaba face mun samu nasara.
Ko da gama faɗin hakan sai ya nuna gimbiya uzaima, sarki Huraisu, hadimi shaibat da aljani zamzaru da hannunshi na hagu ta ke suka ɓace ɓat tamkar ba su taɓa wanzu ba,
Su ka bayyana a cikin wani ƙasaitaccen kogon dutse, shi dai kogon dutsen yakasance mai matuƙar tsawo,girma, da ban tsoro.
Komai dakewar zuciyar jarumi idan ya tsinci kan shi a cikin wannan kogon dutse dole ne tsoro ya kama zuciyarshi, saboda yadda kogon yakasance mai tattare da sarƙaƙiya kuma ya yi tsit tamkar babu wata halitta mai numfashi a ciki,
Sai dai abin da ya bawa su sarki Baddadul-arus mamaki kuma ya ɗaure masu kai shi ne yadda wani farin haske ya gauraye kogon tamkar an ajiye fitila.
Kawai sai sarki Baddadul-arus ya zare wata sharbebiyar takobi a damtsen shi ya kunna kai izuwa cikin kogon batare da wata fargaba ba,
Ko da ganin hakan sai sarki Huraisu, gimbiya Uzaima, hadimi da shaibat suka yi mara mashi baya suna masu zare makaman su aljani zamzaru ne a ƙarshe.
Sai da aka shafe tsawon daƙiƙa ɗari biyu ana tafiya batare da an iso ƙarshen kogon ba kuma ba a haɗu a wata halitta mai cutarwa ba.
Ana cikin wannan hali ne aka ji wani mahaukacin gurnani ya cika kogon baki ɗaya ya fara girgiza kamar zai rushe wata irin wata walƙiya ta dunga bayyana a saman kogon tamkar hadari ya gangamo za a ɓarke da ruwan sama.
Ba shiri su sarki Baddadul-arus su ka sanya hannayensu suka toshe kunnuwan su gami da sunkuyar da kawunansu ƙasa, domin tsoron ka da walƙiyar ta makantar da su.
Sai da aka shafe tsawon daƙiƙu a cikin wannan hali sannan komai ya ɗauke kogon dutsen ya daina raurawa.
Daga can kuma sai aka ɓarke da wata irin mahaukaciyar dariya mai ban tsoro,
Cikin hanzari su sarki Baddadul-arus suka ɗauko da kawunansu domin su ga wanda ya ke ƙyalƙyala dariyar,
Ya yin da suka yi arna da shi sai hankalin su ya dugunzuma ainun har hadimi shaibat ya ja da baya,
Ba wani abu suka gani ba face wani narkeken aljani mai matuƙar kwarjini.
Aljanin yakasance narkeken ƙato mai ƙirar sadaukai yana da tsawo har ya tokare da saman kogon, fuskarshi mummuna ce mai ɗauke da manyan idanuwa ƙwala-ƙwala tamkar garwashin wuta, bakin shi tafkeke ne tamkar bakin rijiya yana da zabgegen gemu mai kamu goma,
A gwaiɓin hammatar shi hagu da dama yana ɗauke da manyan fuka-fukai guda biyu.
Haƙiƙa wannan aljani ya cika abin tsoro ga duk wata halitta mai numfashi, duk da dakewar zuciya irin ta aljani zamzaru sai da ya firgita ainun tamkar a ce ƙyat ya zura da gudu, domin gaba da gabanta aljani ya taka wuta.
A lokaci guda aljanin ya tsuke bakin shi daga dariyar sannan ya ƙurawa su sarki Baddadul-arus idanu cikin wata Irin kakkausar murya mai tattare daban tsoro ya ce "Lale marhaban da zuwan bil'adama ma'abota gajeran kwana izuwa Kogon Garul-Shimshan matattarar dukkan musibun duniya,
Ya ku waɗannan bil'adama kuyi sani cewa haƙiƙa ilimin tsafi ya yaudare ku da ya bayyana ma ku cewa za ku iya tashin mai gidana sharubu daga kushewar shi har ya yi maku rakiya izuwa ɗauko shirtaccen kundi domin mallakar takobin sihiri.
Kafin aljanin ya gama rufe bakinshi sarki Baddadul-arus ya tari numfashin shi ya ce " ƙaryarka ta sha ƙarya ya kai wanan rafkanannan jarumi a jerin JARUMAN DUNIYA.
Ba ka san ko mu ɗin su waye ba kuma baka san wane ne bil'adama shin ka manta cewa mai gidan na ka da kake ƙoƙarin karewa shi ma bil'adama ne kamar mu.
Ko da jin wannan batu daga bakin Baddadul-arus sai aljanin ya fusata ainaun jikin shi ya kama tsuma har wani irin tiririn ɓakin hayaƙi na fita daga ƙofofin hancinshi.
"Wai yau har ni bil'adama zai kalla ya ce mani rafkanannan jarumi na rantse da gemun mahaifina ɗayan ku ba zai tsira da rayuwar shi ba.
Yana gama faɗin hakan sai kawai ya kurma ihu mai firgita DANDAZON MAYAƘA a filin daga ya shiga kaiwa su sarki Baddadul-arus naushi da bugu hannu da ƙafa.
Sarki Baddadul-arus, Uzaima, hadimi shaibat, sarki Huraisu da aljani zamzaru suka shiga kare hare-haren shi aka kacame da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro.




*****
Kashe gari tunda duku-dukun safiya kafin hudowar rana jama'ar birnin arnar daji suka dunga tururuwa a kofar fadar birnin, manya,yara mata da maza, zukatansu cike da matuƙar farin ciki domin a yau ne za su shayar da abin bautar su jinin su sarki Himras tare da murnar ɗaura auren sarki da sharilat.
Lokacin da suka kammala taruwa sai suka ga wani abu da ya dugunzuma hankulan su kuma ya ɗimauta su,
Abin da su ka gani shine kejin da aka saka su sarki Himras wayam babu kowa a ciki,
Shin wane ne ya kuɓutar da waɗannan fursunoni?
Sannan ma taya ya aka hallaka waɗannan dakarun masu tsaron ƙofa?.
Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kansu kenan kawai suka zuba idanu suna jiran fitowar sarki daga cikin sarauta,
A dai-dai wannan lokaci ne aljani Narguz ya farka daga dogon barcin da ya ke yi sakamakon hodar sihirin da arnar dajin suka shaƙa ma shi.
Shin wane ne ya kawo ni nan, su wane ne waɗannan mutane ina kuma su sarki Himras su ke?,
Amsar tambayoyin da Narguz ya kasa bawa kan shi kenan kawai ya zuba idanu yana ganin abin mamaki.
Sai da daƙiƙa hamsin ta shuɗe ana jiran fitowar sarki daga cikin gidan sarauta amma shiru ka ke ji malam ya ci shirya,
Al'amarin da ya haddasa ce-ce ku-ce tsakanin jama'a kenan kowa na faɗin albarkacin bakin shi.




****
Al'amarin su sarki Himras kuwa lokacin da safiya ta yi kowa ya yi kalaci ya kimtsa cikin shi,
Sai wannan kyakkyawar budurwa 'yar sarkin arnan daji da ake kira da suna Mashlira ta dubi sarki,yarima da tasoho kuhairu ta ce "Ya ku waɗannan fursunoni masu daraja ku yi sani cewa a halin yanzu ba mu ga ta zama ba domin nasan mahaifina yana cikin ƙunci da baƙin ciki bisa tseratar da ku da na yi, don haka dole mu kasance cikin shiri domin a kowa ne lokaci za'a iya kawo mana farmaki, a yanzu ne mu ke da ikon kai farmaki zuwa birnin mu.
Ko da jin wannan jawabi daga bakin Mashlira sai su sarki Himras suka shiga yin shirin yaƙi, ita kuwa sai ta shiga izuwa cikin duhuwar bishiyu domin ta yi bawali,
Tabbas rashin sani ya fi dare duhu inda Mashlira ta san abin da zai faru da bata shiga wannan dubuwa ba, domin tana ƙoƙarin cire tufafin ta ne kwatsam bazato babu tsammani sai ta ji an bangaze ta ta baya saboda ƙarfin bangazar sai da ta yi ƙundumbala sau biyu ta kife a ƙasa kanta ya daku da wani ɗan ƙaramin dutse jini ya yi tsartuwa.
Cikin baƙin zafin nama ta miƙe tsaye zumbur ta gyara tsayuwar ta tana mai zare takobin ta daga cikin kube,
Ai kuwa sai ta yi arba da wata murgujejiyar zakanya tana gurnani,
A iya tsawon rayuwar Mashlira bata taɓa ganin halitta mai kwarjinin ta ba,
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin su na wani lokaci daga can sai zakanyar ta dako watan tsalle tana mai buɗe farantanta ta yi ɗauki kan Mashlira domin ta yi mata farat ɗaya.
Cikin matuƙar zafin nama Mashlira ta daka tsalle guda zakanyar ta bangazi wata bishiya da ƙirjinta take bishiyar ta jijjigo da saiwoyinta ta faɗi ƙasa rikica!,
Nan take suka kacame da azababban yaƙi, zakanyar ta wanzu tana kaiwa Mashlira yakushi da farata da cizo da bakinta,
Mashlira ta wanzu tana zillewa hare-haren cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta gami da mayar da martani.
Ana fara wannan gumurzu ne fa gimbiya Mashlira ta fara gane kuren ta yazamana cewa duk sa'adda ta kaiwa zakanyar hari da takobin ta sai ta ji tamkar dutse ta sara, a wasu lokutan bata iya mayar da martani sai dai ƙoƙarin kare kanta.
Sa'adda aka shafe daƙiƙa hamsin ana wannan artabu babu sassauci sai yazamana Mashlira bata iya mayar da martani sai dai ƙoƙarin kare kanta,
Ana cikin wannan hali ne zakanyar ta dako wawan tsalle ta bangazi ƙirjin ta,
Saboda ƙarfin bangazar sai da ta yi katantanwa sau uku a sama sannan ya faɗo ƙasa a matuƙar galabaice numfashin ta na fita sama-sama.
Ko da samun wannan nasara sai zakanyar ta ja da baya tana wani gurnani da ke nuna samun nasara,
Kawai sai ta dako tsalle a karo na babu adadi domin ta turmushe Mashlira ta yaga sassan jikinta,
Nan fa Mashlira ta shiga ƙoƙarin kare kanta da ƙarfin shirin tsafi amma shiru babu labari al'amarin da ya sanya ta miƙa wuya cewa babu wata hanya da zata tsira daga sharrinta.
Ko da ya rage saura kuma biyu zakanyar ta cimma ma ta bazato babu tsammani sai wani kyakkyawan saurayi ma'abocin kwarjini da haiba sanye da fararen tufafi a kwiɓin cinyarshi yana ɗauke da salkar ruwa, a gadon bayanshi yana rataye da wata sharbebiyar takobi ya yi fitar burgu da ga Cikin duhuwa, kafin zakanyar takai ga sauka akan Mashlira ya saurayin ya gabzawa mata wawan naushi a wuya, take wuyan ya karye ji ka ke ruƙus ƙas!, Ta fado ƙasa matacciya ko shurawa ba ta yi ba.
Sa'adda Mashlira ta ga gagarumar bajintar da saurayin ya yi sai ta cika da matuƙar mamaki domin a bata taɓa ganin jarumi mai bajintar shi ba,
Kawai sai ta miƙe tsaye ta ƙura saurayin idanu ya dube shi ta ce "Ya kai wannan ma'abocin kwarjini da jarumtaka shin wane ne mai kuma mene ne ya kawo ka wannan nahiya ta mu?, Mene ne ya sanya ka ceto rayuwa ta ?
Ko da jin waɗannan tambayoyi sai saurayin ya yi tattausan murmushi a gare ta sannan ya buɗe baki cikin Murya mai daɗi ya ce "Da farko dai a tsarin addinin mu an horar da mu da mu taimaki dukkan halittar Allah,
Bayan haka ni dai suna na Humairu ibn kamis ni ma'abocin addinin Musulunci ne na fito ne daga nahiyar gabashin duniya domin na yaɗa addini na a sassan duniya.
Ko da jin amsar waɗannan tambayoyin daga bakin saurayi Humairu sai mamaki ya kama Mashlira ta dube shi ta ce "Shin dama akwai wani Addini da huce tsafi a doron ƙasa ?.
Da jin wannan tambaya sai dariya ya suɓucewa Humairu har fararen haƙoranshi suka bayyana masu ɗauke da wushirya ya ce "Tabbas akwai wani Addini bayan sihiri wato addinin Allah Ubangiji maɗaukakin sarki mahaliccin kowa da komai wanda bai haifa ba ba a haife shi ba.
Cikin matuƙar mamaki Mashlira ta ce "Haƙiƙa ikon Ubangijin ka cike ya ke da daban al'ajabi ya kai wanan jarumi ma'abaocin kyawu da jarumtaka ka yi sani cewa nafara gamsuwa a zuciyata cewa Ubangijin ka shine ya can-canta a bauta mashi tun da ga shi ya tseratar da ni daga sharrin wannan zakanya.
Amma abu ɗaya ne zai sanya na bada gaskiya da Ubangijin na ka shine ka tseratar da rayuwar wata budurwa daga sharrin mahaifina da ke shirin aure ta, domin ya samu gagarumin sihirin tsafin da zai zamo gagarabadau a cikin sarakunan nahiyar mu.
Ko da jin wannan batu sai jarumi Humairu ya sunkuyar da kanshi ƙasa ya na mai zurfafa cikin Kogin tunani,
Daga bisani ya dubi Mashlira ya ce "Wannan buƙata ta ki mai sauƙi ce tamkar cire silin gashi daga cikin tandun mai, matuƙar baza ki saɓawa alkawari ba.
Sa'adda jarumi Humairu ibn kamis yazo nan azancen shi sai suka ji alamun motsi a gefen su ko da suka waiga sai suka yi arba da su sarki Himras shirye cikin gagarumar shigar yaƙi ashe tun ɗazu suna laɓe cikin duhuwa sun ga abin da ya faru tsakanin Humairu da zakanyar.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login